Page 9&10 (last free page
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _***_
Tun k'arfe takwas na safe Ahmad ke kwance a sume cikin kangon nan, bashi ya farfad'o ba, sai bayan la'asar. A gigice ya farka, duburarsa kuwa kamar zata zazzago don tsabar azaba, kuka ya fashe dashi yana kallon bushasshen jinin da ya zuba a k'asa a wajen. Kuka yake yi sosai, da kyar ya iya mik'ewa tsaye yayi k'ok'ari ya saka wandonsa, ko kallon d'ari-d'arin dake yashe a k'asa bai yi ba ya fito daga kangon gaba d'aya zufa ta jik'e jikinsa, a gwaggwale yake tafiya yana turo 'duwawu sabida idan ya had'e k'afa ya tsaye a tsaye da kyau, ji yake kamar a lokacin mutumin ke amfani dashi. Hanyar gida ya nufa yana kuka, duk wanda ya gansa sai yayi magana ya tambaye shi mai ya same shi, amma Ahmad bai kula su. Da kuka ya shiga gidan yana tale k'afafun, da Inna Murja ya soma arba tana daka a tsakar gidan. Tana arba dashi ta zaro idanuwa ta saki tab'aryan tana kallonsa har ya gitta ta, hannunsa tayi saurin kamawa tare da fad'in, "Dan uwarka zo nan, mai ya same ka? Allah ya saka ba kwad'ayi ya jaka an lud'e ka ba!" Ta fad'a tana mai jan wandon sa k'asa da k'arfi, sai da ya saki wani irin k'ara sabida ji yayi kamar ta tura hannunta a wajen har tsakar kansa yaji. "Inna lillahi! Allah ka tsare min y'ay'ana da wannan muguwar k'addarar! Gidan uban wa kaje akai maka wannan aikin?" Kuka sosai Ahmad ya ke yi, cikin kukan ya shiga mata bayanin abunda ya faru. Wawan mari ta d'auke shi da shi tare da fad'in, "K'arya kake yi d'an iska, kwad'ayin ka ya ja maka. Kai ka kai kan ka. Allah ya k'ara dama kashe ka yayi ai uwar taka ta huta da ganin ka da bata so". Ta fad'i haka tare da tura shi gaba da k'arfi sai da ya fad'i. Da rarrafe ya k'arisa d'akin Innar ta su, sai dai babu kowa a cikin d'akin, an dai sakayo kyaure alamar bata nan. Kwanciya flat yayi a tsakar d'akin da ko arzikin leda babu sai siminti. Kuka yake yi kamar ransa zai bar jikinsa. Tuni wani irin zazzafan zazzab'i ya rufe sa, har wani irin makerketa yake yi hak'oransa na had'uwa da na juna. Duburarsa kuwa kamar zata zazzago don tsabar azaba, jikinsa kamar *GARWASHI*. Inna Laadi kuwa ba ita ta dawo ba, sai k'arfe hud'u da kwata, kasancewar Jaji taje wajen uwar rik'on ta. Ganin d'akin ta a bud'e, da kamar baza ta shiga ba, sai kuma tayi shahada ta shiga d'akin. Bata lura da Ahmad ba, kasancewar ya jawo kayan da ke kan gadon har da zanin gado ya maka a jikinsa sabida tsabar zazzab'in da yake ji. Shikuwa Ahmad yana jin shigowar ta, ko kwakkwarar motsi ba ya iya yi, hatta idanuwansa bai iya bud'e su sosai. Ita kuwa Inna kai tsaye wajen manja ta nufa tare da jawo galon d'in ta fitar dashi waje kasancewar ya daskare, sai ta dawo d'akin ta jawo k'aton kwalla da ta juye galan d'in mangyad'a a ciki ta d'auko leda ta shiga d'aurawa. Ahmad kuwa, a hankali yayi ta jan jiki har ya iso inda Innar take ya d'aura kansa a kan cinyarta, a take hawaye ya zubo a kan zaninta. Ita kuwa wani irin zabura tayi cike da tsoro don bata d'auka a kwai mutum a cikin d'akin ba, ganin fuskan Ahmad ya saka ta ja wani dogon tsaki tare da ture kanshi a k'asa sai da ya bugu da siminti k'asan ta mik'e tsaye zata bar dakin. Ahmad kuwa bai damu da zafin k'umuwar da yayi ba, sai yayi saurin cafkar k'afafunta ya fashe da kuka tare da fad'in, "Innar mu, wayyoo Innar mu, zafi! 'Duwawu na azaba yake min, dan Allah Innar mu ki duba min d'uwawu na zan mutu. Wayyo kai na Innar mu. Zan mutu. Innar mu mutuwa zan yi". Tun lokacin da Ahmad ya kai hannu kan k'afafuwanta gabanta ya buga da k'arfi saboda irin zafin da taji alamar yana fama da matsanaicin zazzab'i, wani irin abu ne ya daki zuciyarta, amma kuma ko da alama baza ka ga hakan a kan fuskanta ba. K'ok'arin fizge k'afarta kawai take yi amma Ahmad d'in yak'i bata dama don ba k'aramin rik'o yayi wa k'afar ba. "Innar mu baza ki duba ni ba? Innar mu mutuwa fa zan yi. Wallahi 'duwawu na kamar ana soka min k'arfe har a cikina. Yanzu Innar mu baza kiji tausayi na ba? Innar mu kar ki bar ni a haka dab girman Allah ki tausaya min zan mutu, wani ne ya jani kang......." Ko kamin Ahmad ya k'arisa Inna Laadi ta ja k'afarta da mugun k'arfi tayi waje da sauri. Ahmad kuwa wani irin kuka ya fashe dashi yana jujjuya kansa tare da buga kansa a kan simintin har sai da kan ya fashe yana fad'in, "Na shiga uku! Na shiga uku!! Wayyo Inna Abu, Wayyo Allah, wayyooo na shiga uku, Allah ka kashe ni in huta tun da Innar mu bata sona. Wayyo 'duwawu na zan mutu". Haka ya dunga yi yana kuka. Inna Laadi da tana d'an gaban d'akin ta ne kad'an, amma da taji magiyar Ahmad d'in yayi yawa, sai ta koma bayan d'akin Daada ta zauna a wajen. Ahmad kuwa a cikin d'akin nan, ya suma har uku yana farfad'owa. Wani irin zabura yaje yi can kuma sai ya fashe da kuka yana fad'in, "Kar ka min, kar ka saka min! Innar mu zai saka min abun fitsarinsa a 'duwawu na ki cece ni. Wayyo Allah ya saka min Innar mu, ki zo ki cece ni zan mutu, 'duwawu na zai fashe na shiga uku Innar mu!". K'arfe biyar da rabi su Abubakar suka dawo daga islamiya, ko da ya shiga d'aki yaga halin da d'an uwansa yake ciki, sai ya fashe da kuka ya fita da gudu ya shiga nai man Inna Laadi, a can bayan d'akin Daada ya ganta, da kuka ya shiga fad'in, "Innar mu ki taho Ahmad zai mutu wallahi yana can kwance a d'aki sai firgita da kuka yake yi. Ki zo muje Innar mu dan Allah ki duba shi". Hannunsa ta damk'o tare da fad'in, "Idan ka k'ara min wannan maganar sai na yanka maka bakin ka! Kuma yanzu kaje ka ce masa ya fita daga d'akin nan ya koma madafi inda yake kwana, idan na zo na ganshi a nan d'akin sai na masa tsinannan duka. Wuce maza yanzu!" Ta k'arisa maganar tare da daka masa tsawa. Da kuka Abbakar ya bar wajen ya koma d'akin Innar, nan ya tarar da Ahmad yana kelaye amai kamar zai mutu, don babu komai a cikinsa ban da kokon safen da yasha wanda Abbakar d'in ne ya rage masa, kuma shima d'an kad'an, sai ya kasance kakari yafi aman da yake yi yawa..... Kukan Abbakar d'in ne ya k'aru, ya shiga fad'in, "Sannu Ahmad! Kayi hak'uri kaji, Allah zai saka maka. Innar mu muguwa ce, ta ce ince maka ka bar d'akin nan ka koma madafi idan ba haka ba idan tazo ta same ka anan zata maka duka. Muje in raka ka madafin, bana so ta dake ka kaga baka da lafiya!". Abbakar ya k'arisa maganar yana gogewa Ahmad bakinsa wanda ya b'ata da amai bai ji kyamarsa ba kuma. Shi ya taimaka masa ya mik'e dakyar kafafunsa na rawa sabida yanda zazzab'in ke nuk'urk'usan k'asusuwan jikinsa. Dakyar ya iya jansa zuwa madafin bayan ya shimfid'a masa tabarmar Inna Laadin. Kwanciya Ahmad yayi ruf da ciki yana fad'in, "Lullub'e ni, lullub'e ni Abbakar. Mutuwa zan yi. Lullub'e ni Abbakar". Da gudu Abbakar ya fita ya samo zannunwa har da na mutane dake shanye a igiya yazo ya lullub'e san. Ganin abun cigaba yake yi, sai ya fice da gudu yana kuka har wajen aikin Baban su. Sun kusa su goma a wajen suna hira suna cin asara kowa da ledarsa a gabansa. Kai tsaye wajen mal Bawa ya nufa yana kuka tare da fad'in, "Baba kazo muje gida Ahmadu zai mutu bai da lafiya sosai, jikinsa kamar wuta". Mal Bawa yaso tutturawa Abbakar d'in zagi, amma ganin mutane sai ya nuna concern na k'arya har da saurin mik'ewa yana fad'in, "Shi Ahmadun? To mai ya same shi? Da safe fa lafiya muka rabu zai tafi makaranta har na d'auki kud'in tara na bashi". Mutanan wajen suka shiga fad'in, "To ai shi ciwo da mutuwa haka suke, yanzu zaka bar mutum lafiya anjima kaji zance ya canza". Hannun Abbakar Mal Bawa ya kama tare da fad'in, "Bari naje na duba jikin nasa, sai da safen ku!" Mutanan su kai masa Allah ya kawo sauk'i shi kuma ya ja Abbakar suka soma Tafiya. Sai da suka yi nisa da jama'a sannan Mal Bawa ya kama kunnan Abbakar d'in yana fad'in, "Dan uban ka duk ranar da ka kuma zuwa wajen aiki na ka kowa min zancen banza da na wofi, sai na ci ubanka, ina ruwa na da ciwon Ahmadun? Ni zan bashi lafiya ko Allah! Tafi can ka wuce gida ai uwar ku na kallonsa kuma ai tana sana'a, ta baka kud'i ka sayo masa kwaya ya sha, ni ban da ko sisi a waje na". Ya fad'i haka tare da tallabe k'eyar Abbakar d'in. Shikuwa Abbakar ya nufo gida yana kuka. D'akin Ahmad d'in ya fad'a, amma sai yaga jikin nasa worse yayi, don firgitan da yake yi yafi na d'azu, don yanzu yi yake kamar zai tashi ya zura da gudu yana ihu, kuma duk abunda yake yi, Inna Laadi naji, don d'akinta yafi kusa da madafi, idan akwai wanda ba zai jiwo Ahmad sosai ba, to Daada ce, don ita d'akin ta yana can lungu ne daga k'arshen gidan. Abbakar yana shiga d'akin Innar ya tarar bata nan, sai dai ya d'ari biyu nan a tsakar d'akin da alama man gyad'a aka saya ko manja. Aikuwa wuuf ya d'auka ya fito da gudu yayi waje. Kai tsaye bakin titi ya nufa domin sayo magani. Sai da ya isa bakin chemist d'in kuma ya fara tunanin wani irin magani zai saya. Fad'awa chemist d'in yayi lokacin da ya tuna mai zai ce. "A bani maganin zafin jiki da na amai, a had'a min har da na wanda zai saka mutum ya iya mik'ewa tsaye da kansa".
*_IDAN KINA SON CIGABAN D'AN FAARI, KI BIYA D'ARI SHIDDA ZUWA WANNAN ASUSUN BANKIN 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK BANK, SAI KI TURO SHAIDAR BIYAN KI ZUWA GA WANNAN LAYI, ***. DAN ALLAH IDAN KIN SAN ZAKI SAYI LITTAFI NA NE DOMIN KI FITAR MIN DA SHI, DAN ALLAH KI RIK'E KUD'IN KI NA YAFE._*
SHIN YAYA RAYUWAR AHMAD ZAI CIGABA NE ANAN GABA? KAR KU MANTA AKWAI K'URA A TA BANGAREN AKEELA, DON SHI MA LABARI NE MAI ZAMAN KANSHI. (Mahaifin ta ya nuna mata matuk'ar soyayya tare da nuna mata babu abun da zata nai ma a duniya ta rasa idan har yana raye. Sai dai kash, ya manta ba ko wani soyayya bane ake sayanta da kud'i.) Kar ki bari ayi babu ke. Biya kud'in ki sha labari mai tab'a zuciya. Baza ki yi asarar kud'in ki ba I assure you!
*MATAR SAYYADEE* [6/11, 1:44 PM] Matar Sayyadee: *_DF_*