Chapter 1
***
BA SO BANE.
Story📃 writing
by
Hafsat waziri
Dasunan Allah mairahama maijin ƙai
Page1
Slowly driving motar ya yi parking cikin wani babban Company. Ƙarar tsayuwar motar ce ta jawo hankulan mafi yawan jama'ar da ke tsaye a wajen. Ya koma kan motar, saboda kyau da haɗuwarsa. Ma'aikata, masu gadi da masu zirga-zirgar da ke wurin suka tsaya son ganin mamallakin wannan haɗeɗɗiyar motar. Wasu ma'aikata da ke tsaye a can gefe su uku, ɗaya daga cikinsu da shi ma ya ke cikin masu kallon motar ya taɓa abokinsa da ke gefensa ya ce, "Kai, Habu, ka ga wata arniyar mota?"
Wanda aka kira da Habu ya ɗaga kai ya ga motar, sai kuma ya juyo ya jingi na da motar da ke bayan sa, ya ce, "To ni Adamu menen ne haɗi na da wata mota? Ka bar ni na ji da abin da ke damuna dan Allah."
Adamu ya kalle sa shi ma da ɗan damuwa a kan fuskarsa ya ce, "Allah dai yasa yau kam a da ce" amen ya rabbi'' Habu ya fada a sanyaye. duk suka yi shiru. Ɗaya daga cikin su wanda
tun da suke magana shi bai tanka musu ba, sai yanzu ya ɗago yana kallon agogon da ke manne a hannunsa sannan ya kallesu da damuwa kadan akan fuskar ca ya ce, "Ina ga zuwa yanzu ya yi a ce ya fito."
Adamu ya ɗago daga jinginuwar da ya yi a jikin mota ya ce, "Mu shiga ciki mu duba sa."
Suka nufi cikin Companyn, Adamu na faɗin'' Allah ka sa ƙarshen wahalarsa kenan."
A haka suka ƙarasa shiga cikin Companyn.
A wajen companyn kuma, an ɗauki mintuna masu ɗan yawa kafin a hankali na cikin motar ta fara motsi, alamar zata bayyana. A hankali ta sauke ɗayar ƙafarta da ke sanye da wani takalmi mai uban tsini. Sai da ta kusa sa ke ɗaukar minti ɗaya kafin ta sake turo ɗayar ƙafar waje. Ta sauko cikin natsuwa da yanga kamar mai tsoron taka ƙasa.
Kyakkyawa ce sosai, irin kyau nan na Fulanin Yola. Fara ce ita tas kamar ka taɓa ta jini ya fito. sai dai idan ka kalli fuskarta za ka ga ne ba gonar yin fara'a ba ce ita, saboda yadda fuskar ta ke a murtuƙe. Baƙin abaya ne a jikinta, kasancewar ta fara tas, sai baƙin abayan ya yi mata kyau sosai. Handbag ɗinta da takalminta farare sol. Ta haɗu iya haɗuwa, ta yi masifar kyau, kyau irin sosai ɗin nan.
A hankali take taku cikin natsuwa. Izza, isa, mulki da kwarjini gaba ɗaya ta haɗa a tafiyarta. Sai da ta iso daidai mashigar companyn, sannan ta tsaya tare da ɗaga kanta tana ƙare masa kallo.
A hankali, cikin ɗaɗɗaɗar muryarta, ta furta,
"S and S Sardines."
Sai ta sake wani haɗeɗɗen murmushi wanda ya sake fito da ainihin kyawunta a fili. A hankali cikin da yanga ta sauke kanta daga kallon da take wa companyn sakamakon kiran da ya shigo wayarta. Ta ji idanun mutanen da ke wajen ya fara masa yawa akan ta. Saboda haka Sai ta fara shiga cikin companyn tana laluben wayarta da ke cikin jakarta. Wannan dalilin ne ya sa ba ta kallon hanya sosai saboda ta yi imanin babu wanda zai zo wuce wa idan taza wuce.
Gugu-gugu, sauri sauri haka yake sauko wa daga saman benen. da tsananin ɓacin ran da ke kwance a kan fuskarsa ya ke tafiya wannan tsananin ɓacin ran da yake ciki ya sa ko hanyar da yake bi baya iya gani sosai. Duk su biyun babu wanda ya kula da zuwan wani a tsakaninsu. Hakan yasa suka yi wani mummunar karon da ya bada sautin''
Kapppp!
“Bismillah!” ya furta a hankali, jin wani azaba ya ziyarci goshinsa.
Ita ma cikin jin raɗaɗi ta ce,
“Ashh!”
A gigice handbag ɗinta da wayarta da ta samu nasarar fitarwa bata gaita kunne ba. gaba ɗaya suka faɗi ƙasa. Tagal-tagal ta yi, ta yi baya za ta faɗi. Sai ya yi saurin tarota da dukkan hannayensa ya haɗata da ƙirjinsa.
Da ƙarfi ta rufe idanunta saboda a zatonta ta fadi ƙasa za ta yi. Da sauri ta sake buɗe su dan jin ba ta faɗin ba. Kamar wani kurar ƙarfe idanunsa suka ja nata cikin fararen idanunsa. A hankali ta shiga ƙarewa fuskarsa kallo. Goshinsa mai sheƙi ta fara gani. Sai ta sauƙo kallon kan cikakkun girarsa wanda suke nan baƙin siɗik. A hankali ta sake dawo da idanunta kan dogon hancinsa, wanda tsayin sa ya yi daidai da tsarin halittrsa. Ta sake yin ƙasa da idanunta tana kallon lips nasa masu sheƙi kamar wanda ya shafa musu man baki.
Tsayawa ta yi tana ƙare masa kallo sosai, kamar ba ta taɓa ganin halitta irinsa a duniya ba. Sosai ta shagala da kallonsa.
Duk da yadda ta so ta ɗauke idanunta a kansa, amma sam hakan ya gagara. Kawai sai ta ci gaba ya yin da hannayenta duka biyu ke maƙale da wuyansa. A hankali ya sake faɗin'' ke '' a karo na biyu yana girgizata da nufin ta sakar masa wuya, ita kuwa ta riƙe wuyar gam kamar wacce ta samu abu na musamman da dogara da shi.
ganin irin kallon ƙurillar da take masa, hakan ya matuƙar ba shi haushi. Da ma da haushin da ke cin sa a rai. Yau kajen sati biyu kenan yana bizaron neman aiki, sai da aka gama wulakanta shi, sannan yau da suka ce masa ya dawo, ya zo kuma CEO da kansa ya faɗa masa ba sa buƙatar ƙarin ma’aikaci, ya ɗaga kansa yana kallon jama'ar da ke wajen, ganin mutane sosai duk su zubawa ido ana kallonsu kamar waɗanda suka samu TV suna kallon wasan ƙwallon ƙafa ta duniya, hakan ya sake dagula masa rai. Ya tsani kallon jama'a, ransa ya ji yana sake ɓaci sosai.
Bai tsaya yin tunani na biyu ba, bai yi tunanin mene ne zai je ya dawo ba. Ba tausayi, balle imani ko sassauci. Ya tura ta da karfi
ta faɗi ƙasa. Tammmm! Tana kai wa ƙasa mutanen da ke tsaye a wajen suka sanya dariya sosai, kamar masu kallon wani haɗeɗɗen comedy.
Shi kuwa da ya yi abin, ko a jikinsa. Bai ma bi ta kanta ba. Ya ɗaga kai yana basarwa, irin ai ke kika ja.
Adamu, abokinsa, da mamakin abin da Aziz ya aikata, ya hana shi ko da ƙoƙarin motsi, yau kam tabbas ya ƙara tabbatar wa da lamarin abokin na sa abun tsoro ne sai ya tsaya kawai yana kallonsa.
Dariya da shewar da ma’aikatan wajen ke yi ne ya dawo da ita daga suman kwance da ta yi.
Babu alamar kunya ko jin ƙasƙanci a fuskarta. Amma akwai tsananin mamaki, al’ajabi da rashin fahimta sosai a tattare da ita.
Gaba ɗaya ta kasa fahimta. Ta kasa ganewa. Ta kasa yadda da abin da ya faruwa a nan ɗin. Gaba ɗaya ji ta yi kanta ya daure. Shin ita ce ko ba ita ba?
Shin wai ita ce wani ya yar a ƙasa kamar tsumma?
Ita dai?
Sai abin ya fi yi mata kama da mafarki ta ke yi .
A hankali ta motsa hannunta na dama. Jin wani azababben ciwo a hannun ya sa ta gane da gaske ne ba mafarki ta ke yi ba,
A hankali ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke motsi a cikin ƙirjinta tamkar za ta fasa ƙirjin nata ya fito waje.
Ta buɗe idanunta da suka mugun yin ja, kamar jini ne ke kwance a ciki. Ta ɗaga kanta da nufin ganinsa amma sam babu shi, babu kuma alamarsa a wajen.
Dariya da shewar wani tsoho mai sanye da kayan aiki, wanda ke ɗauke da tambarin companyn, hannunsa riƙe da sandar mopping alamar shi mai share-share ne, ya dawo da ita daga hayyacinta. Ta kallonsa fuskar nan tasa ɗauke da nishaɗi sosai kamar wanda aka yi wa albishir da gidan Aljanna.
Ya taɓa na kusa da shi da ke tsaye da takardu a hannunsa ya ce, " wannan fa irin 'yan matan nan ne 'ya'yan masu kuɗin ƙasar nan, da babu abin da suka sani sai bin kyawawan samari irinsa. Kuma fa kar ka yi tunanin saboda Allah ne. A'a, Su dai suka san manufarsu a kan samarin.
Suka sake kwashe wa da dariya, yana dariya yana gyara takardun dake hannun ya ce, "Sai kuma rashin sani ya sa ta faɗo hannun wanda ya san ciwon kansa. Ai ni wallahi ya yi min dai-dai,."
Nan ma suka sake yin dariya.
Wani da ke gefen tsohon ya na kokarin saka wayarsa a aljuhu ya yi caraf da maganar yana faɗin, "Ai ni ma wallahi yaron ya burge ni sosai da ya sa ta faɗi. Ɗazu fa ina gaya muku yarinyar nan ta zo da wata shirgegiyar mota. Wallahi sai ka ga motar nan kamar ta gwamna. Duk muna son mu ga mai motar, amma sai ta ƙi fitowa. Na taƙaice muku zance dai, kafin yarinyar nan ta fito sai da ta kai kusan rabin awa. Sannan ta fito tana wa mutane rigima, ko me take yi a cikin motar ma ohoo. Yanzu dai ga shi wani ya sa ta gaisa da ƙasa."
Nan ma suka sake kwashewa da dariya har tsohon na share ƙwallar dariyar mutunta.
Haka nan suka ci gaba da maganarsu har suka watse a wajen, tana nan zaune. Hawayen jin zafin kalamansu ta goge.
Ita ta rasa wani irin tunani za ta yi.
"Lallai sai na nuna musu cewa ba bin kyawawan samari kaɗai na iya ba. Tabbas sai na nuna musu ni ce ke da cikakken iko a kan komai da kuma kowa. Da ya san wacece ni, da bai yi irin wannan gangancin da ya yi a yau ba. Amma alkawari ne, wannan alkawari na ne sai na nuna masa uban da ya haife shi ma ya yi babban kuskure."
Sai ta tuna rayuwarta. Ita da tun da take ba za ta iya tuna lokacin da wani ya taɓa mata kallon banza ba ma. Balle har ya kai ga haka,
Wata budurwa ce wacce ke sanye da kayan aiki wanda da dukkan alamu ita ma ma'aikaciyar Company ce. Ta katse mata tunani ta hanyar faɗin,
" Baiwar" a hankali ta daga kai tana kallon ta.
Sai ma'aikaciyar ta sakar mata murmushi, amma ganin irin kallon da ta yi mata sai hakan ya ba ta mamaki sosai. Sai dai ta basar tana murmushi ta ce,
"Hey, ni sunana Suhairat. Ke fa? Aikin kema kika zo nema?
Ta tambaya tana kallon fuskarta. Dake a tamke tamau,
Ba ta ce komai ba. Hakan bai dami Suhairat ɗin ba, saboda ai ta san haka halin yaran masu kuɗin gari yake.
A hankali budurwar ta miƙe kamar mai jin tsoron kada ta sake faɗi. Har ta fara tafiya sai ta ji muryar Suhairat na cewa,
"Hey baki dauki jakar ki da wayar ki ba, sannan ina za ki je ne? Jama'ar company nan fa ba mutunci ne da su ba, daga ma'aikata har masu company ɗin. Gara ki kira wanda kika zo wajensa kafin wani ya ƙara yi miki wani wulakancin." Ta karasa maganar tare da karawa wajen jakarta ta dauka, ta sake zuwa wajen da wayar ke tashe ta dauka sai ta tsaya tana nan jujjuya wayar a hannun ta, waya ce babban iPhone 17. Suhairat ta ɗan taɓe baki bata yi magana ba, ta karaso wajen da take tsaye
"Office ɗin CEO." A fada a daƙila Suhairat ta matso, ta ɗan buɗe idanunta alamar mamaki ta ce,
"Office ɗin CEO kuma? Yasan da zuwan ki? Shi ma yana da wulakanci. Ko Budurwarsa ce ke?"
Ta yi shiru, ba ta ce komai ba.
Sai Suhairat ta mika mata jakarta da ta saka wayar a cikin, ta ɗan yi jimm kamar bazata karɓa ba, sai kuma tasa hannu ta karɓa. "Amma dai ya san da zuwanki ko?"
Ta tambaya ta sake
Budurwar ta.
Ganin ta yi shiru, sai Suhairat ta ce,
"To mu je. Amma dai gaskiya idan bai san da zuwanki ba, zai yi wahala ki samu ganinsa. Idan ma ba ki yi sa'a ba, sai ya yi miki wulakanci."
Sun ɗan yi tafiya mai nisa kaɗan, sannan Suhairat ta ja gefe guda ta tsaya kamar munafuka.
Sai ta ɗaga hannunta ta nuna mata wata ƙofa, wadda a saman ƙofar aka rubuta:
CEO.