My Destiny (Ƙaddarata)

Introduction

by @matarsayyadee3

[1/28, 8:52 PM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

~FROM THE WRITER OF;~ *ƘANWAR MATATA* *ZINA BABBAR BALA'I CE* *ƊAN FAARI* *AUREN CIKIN GIDA* *BA NI DA GATA* *GARWASHI* *SAI A LAHIRA* *NI DA SHI ABU ƊAYA NE* *ANYA UBANA NE* _AND NOW_ *MY DESTINY ( ~ƘADDARATA~)*

_SHIMFIƊA_ _Mahaifiyata shahararriyar karuwa ce wacce ta daɗe da kwashe kayanta a gaban Allah da ma'aikin shi,ta mummunar hanya ta ƙyanƙyashe ƙwaina har ta samar da ni bi ma'ana zina ta yi ta haife ni,shegiya ce ni bani da uban da kowani ɗa ya ke ado da shi. Ba wannan ne abin da ya ƙara gurɓata rayuwata ba da guba mai muni ba sai tasowar da na yi a gidan Magajiya(Karuwai)._ _Sanannen abu ne ga kowa irin badaƙalar da ake aikatawa a wannan gida ya munana ga maganan masu tsoron Allah amma gareni rainon karuwa ba komai ba ne ciki kuwa har da kwanciyar da ake yi a gaban idona da mahaifiyata tare da lakaɗamata uban duka yayin da kwartonta ya same ta da wani. Uhm! Babban tashin hankalin kuwa shine, Mahaifiyata bata tsaya a iya karuwanci ba domin kuwa ta kasance ƴar kwaya ta bugawa a jarida kuma uwargijyar ƴan ta'adda mai ba su makafa tare da safarar makamai ma su hatsari._ _"...Tir! In haɗa iri da ke. Ni salihin bawa ne da bai taɓa kusantar zina ba. Don haka ba zai taɓa yiwuwa ba in auri ɗiyar da ta kwanta a mahaifar tantiriyar karuwa wacce ta kashe mahaifinta kuma ƴar ta'adda mai safarar miyagun makamai da kwayoyi. Fice min da gani a idona!..."_ _Wannan ita ce maganar da ta yi min amsakuwa a masarrafar jina wanda yayi barazanar fasa ɗan halittar da ke cikin kunnena wanda ke taimaka min wajen sauraran maganganun mutane. Na yi kuka sosai lokacin da na farka a asibiti ɗaure da ƙarin ruwa a hannuna sakamakon maganar da wani likita ya yi min wanda na ji sautin rangaɗaɗau a kunnena. Burina bai wuce in dai na jin sauti a kunnena ba ta yarda babu wani munanan kalaman da zan kuma ji a cikin masarrafin jina a kan Mahaifiyata wacce ita ce *Ƙaddarata* domin ita ce ta rushe duk wani jin daɗina a duniya!_