Page 1
*_Huɗu ga watan Satumba, Alif ɗaya da ɗari tara da casa'in da tara. Wanda ya kasance ranar asabar, karfe biyu da mintuna goma sha uku na dare. Amma a turance, idan har dogo da gajerer hannu suka sauka a kan sha biyu na dare, to hakan na nufin an shiga (Am) wato an shiga rana ta gaba. Hakan na nufin a wannan lokaci an shiga rana ta Lahadi. (Saturday/Sunday 04-09-1999)_*
Dare ne sosai, amma duhun daren bai hana ta fitowa daga cikin gidan ubanta ba a wannan lokacin. Tafiya take tare da waiwayar hanyar gidansu gudun wani ya hango ta.
Tirnitsetsen cikinta da yayi tsine bai hana jikinta motsawa da sauri ba domin a wannan halin da take ciki har ta mance da wani cikin watanni tara cif da ke jikinta. Domin tafiya ce take yi da sauri-sauri.
Zanin jikinta ɗaya yayi sama, ɗaya kuma yayi ƙasa. Lokacin sanyi-sanyi ne, amma hakan bai hana zufa yankowa daga goshinta har zuwa wuyanta ba. Sam bata damu da ta kai hannu domin warce zufan ba, burinta kawai shine taga ta yi nisa da unguwar gaba ɗaya gudun tonuwar asirinta na kisar gillar da tayi wa mahaifinta mintuna ƙalilan da suka wuce.
"Ke! Ina zuwa haka cikin daren nan?" Faɗin wani jami'in ɗan sanda da ya haske fuskanta da tocila mai hasken gaske har sai da ta saka hannu ta kare fuskanta saboda yanda hasken fitilar ya dallare mata kwayan idanunta.
Da sauri ta waiga baya sannan ta dawo da kallonta ga ɗan sandan tare da daidaita natsuwarta sannan ta furta, "Na fito motsa jiki ne sakamakon naƙuda da ta taso min. Kuma ɗazu mun je asibiti amma sai suka ce ba haihuwar bace da saura amma na riƙa motsa jiki hakan zai taimaka min wajen kusanto da lokacin haihuwar."
Ɗayan ɗan sandan dake bayansa ne ya ƙariso wajen tare da faɗin, "Wai me take faɗa ne a wajen? Halan karuwa ce? Samin ita a mota yanzu!" Ya ƙarisa maganar da ɗan tsawa. Ja da baya ta ɗan yi kaɗan jin abunda ɗayan police officer ɗin ya ce tare da faɗin, "Mai na yi da za'a saka ni a mota? Halan ba ku da mata ne a gida? Kuna ganin wannan hali da nake ciki baza ku tausaya min ba sai ka ce a saka maka ni a mota kamar wata criminal." Ta ƙarisa maganar tare da riƙe mararta ta kwantsama wani ihu tana mai ɗage zanin jikinta wanda jini ke gangarowa daga jikinta har zuwa idon sahun ƙafarta kuma hakan yayi daidai da hasketan da police ɗin ya sake yi a karo na biyu. "Subhanallah! Baiwar Allah yi haƙuri don Allah. Amma bai kamata a cikin wannan hali ki fito ke ɗaya da. Gashi yanzu mota ta yi nesa da mu balle mu taimaka maki zuwa asibiti. Kofur Ɗanjuma akwai wani asibiti mafi kusa a nan!" Ya ƙarisa maganar fuskansa ƙunshe da tausayinta kasancewar a cikin irin wannan hali da take ciki mahaifiyarsa ta haifesa sannan ta koma ga Allah.
"Gaskiya yallaɓai babu asibiti kusa anan wajen. Sai ka yi tafiya sosai zuwa bakin titi kamun ka samu abun hawan da zai kai ka can asibitin, kuma ga shi yanzu dare ne sosai."
Waigawa ta kuma yi a karo na uku duk da a duƙe take. Da hannu ta yi masu nuni tare da faɗin, "Na kusa isa inda zani. Tafiya kaɗan ce za ta sada ni da gidan ƙanwar mamata. Akwai babur a gidan za su kai ni asibiti idan na ƙarisa."
Da sauri police officer ɗin ya ce, "Idan za ki iya tafiya muje sai muyi maki rakiya." Ya ƙarisa maganar tare da waiwayawa ya yiwa kofur Ɗanjuma magana akan ya taho su tafi tare.
Ba haka ta so ba, amma haka nan ta yi ta yin ɗingishin ƙarya da riƙe ciki har su ka yi tafiya mai nisa sannan suka iso wani gidan ƙasa mai ɗauke da ɗaki ɗaya tal a ciki sai ƙofar da ake jinginawa a rufe idan dare ya yi gudun barin gidan wagaga.
"Yauwa nan ne gidan." Ta fadi tana mai kai hannu ta dafi bangon gidan tana mayar da numfashi. "Nagode." Ta faɗi bayan ta waiwaya ta kallesu sannan ta maido da idanunta akan kofar tare da matsar da langa-langar ƙyauran sannan ta shige ta mayar ta rufe.
Haske gidan kofur Ɗanjuma yayi sosai ya na raya wani abu cikin ransa sai dai bai yi kuskuren furta ko kalma guda ba kasancewar ya san wacce take zaune cikin gidan. Don duk akai albashi rabin kuɗinsa a wannan gidan yake ƙarewa.
"Muje kofur Ɗanjuma. Wannan mata ta yi namijin ƙoƙari da har ta iya wannan tafiya mai tsayi kuma tana cikin halin naƙuda."
"Gaskiya kam ta yi ƙoƙari. Allah ya raba lafiya." Shine abunda kofur Ɗanjuma ya ce yana mamakin ta yaya Ladi katifa za ta kasance ƙanwar mahaifiya ga wancan matar mai ciki bayan ko Ladin za ta girme ta bai fi da shekara ɗaya ba ko su zo sa'annin juna ma."
A hankali ta leƙo domin tabbatarwa shin sun wuce. Ganin sun wuce sai ta yi saurin shiga ainahin cikin gidan tare da soma jijjiga ƙofar ɗakin Ladi katifa da ƙarfi ta na kuma kiran sunanta kasancewarta mai mugun nauyin barci.
Can cikin baccinta mai daɗi ta ji ana jijjiga ƙofa kuma ana kiran sunanta. Mutun biyu ne ta san za su iya mata hakan; Yahuza ko Laushi. Saukowa ta yi daga katifar bacci a idanunta tare da isa wajen ƙofar ba tare da ta buɗe ba ta d'aure fuskarta tamau kana a kausashe ta ce, "Waye a wajen nan da daddaren nan?" Kasancewar ta ƙuduri aniyar idan Yahuza ne sai ta shuka masa rashin mutunci.
"Dalla matsa! Ki zo ki buɗe ƙofar maza yanzu kar jinina ya ƙare, Laushi ce." Matar da ke ƙofar ɗakin wacce ta kira kanta da Laushi ta faɗi rai ɓace don gaba ɗaya ta ƙagu ta buɗe mata ƙofar don hankalinta a tashe ya ke kasancewar yau ne ta fara kashe rai a iya tsayin rayuwarta kuma ta mahaifinta.
Da sauri Ladi katifa ta buɗe Ƙofar tare da faɗin, "Laushi, ya na gan ki yanzu a wannan daren? Ko har kin kammala? Ina sarƙar?" Ta watso mata tambayoyi.
Babu ko ɗaya daga cikin tambayoyin da Laushi ta amsa mata, sai ma ture ta da ta yi sannan ta shigo ɗakin ta kunna hasken lantarki tare da kama ƙasan zaninta ta yaga da ƙarfi.
"Inna lillahi! Laushi naƙuda kike yi? Yau mun bani. Kuma naƙudar jini." Faɗin Ladi katifa a ruɗe.
Harararta Laushi ta yi tare da faɗin, "Sai kace yau kika fara ganin haihuwa. To ba haihuwar bace basaja na yi."
"Basaja kuma?" Faɗin Ladi katifa don sam bata fahimci mai ƙawar tata take nufi ba.
"Na haɗu da masu baƙin kayan nan ne a hanyata ta zuwa nan gidan har ɗaya daga cikin su ya ke faɗin wai a saka masa ni a mota. Shine cikin dabara na karci tsokar cinyata da ƙarfi jini ya ɓalle domin su yi tunanin naƙuda na ke yi." Ta ƙarisa maganar tana mai ƙulle cinyarta da kyallan da ta yanka a jikin zaninta.
Ajiyar zuciya Ladi katifa ta yi tare da faɗin, "To yanzu Laushi ya ake ciki? Ki faɗi min dalilinki na dawowa nan ɗin bayan ga abunda muka tsara."
Laushi ba tare da ta yi magana ba ta sama hannu cikin rigarta ta zaro wata sarƙa da ɗankunne tana murmushi. "Ba wannan shine burinmu ba? To na ɗauko. Zaman mai kuma zan yi cikin gidan?" Waro idanu Ladi katifa ta yi tare da faɗin, "Tabbas babu sauran zama a gidan. Amma tambayata shine; ta yaya kika ɗauko wannan sarƙar da ɗankunnen a yau har kuma kika fito babanku bai gan ki ba? Sannan na san mamarku da tsinannan wayau, don ita kika ɗauko a ɗankaran wayau wallahi."
"Katifa!" Laushi ta yi kiran sunata. "Na'am Laushi." Ladi ita ma ta yi kiran na ta sunan.
"Ki adana tambayoyinki a yanzu don ba su da wani mahimmanci. Da asubar fari za mu bar gidan nan mu tafi Legas (Lagos). Idan ba haka ba kuma, to ina mai tabbatar miki zamu ƙare rayuwarmu a magarƙama." Sai ta kalli tirnitsetsen cikin da ke jikinta tare da shafawa sannan ta ce, "Kuma ni ban shirya hakan ba don ina da burika da dama."
Hankali tashe Ladi katifa ta ce, "Laushi mai kika aikata haka?"
A zafafe Laushi ta ce, "Na ce maki ki adana tambayoyinki ba su da mahimmanci a yanzu! Kawai abunda za ki yi shine; Haɗa duk wani abunda kika san masu mahimmanci ne ki ƙulle su domin asubar fari za mu bar gidan nan tun da dama ai kin riga kin sayar tun jiya."
Shuru Ladi katifa ta yi tana kallon ƙawarta na tsawan sakonni tare da soma haɗa duk wani kayanta masu mahimmanci cikin jaka. Don idan ta kalli kwayar idanun ƙawar tata sai taji hankalinta ya tashi. Don Laushi babu abunda ba za ta iya ba akan kuɗi.
Laushi na kallonta ta gefen idanu. Kuma tana lure da irin halin da Ladi katifa ta ke ciki kasancewar ta hango tsoro ɓaro-ɓaro a cikin idanunta. Murmushi ta yi tare da faɗin, "Ki kwantar da hankalinki Katifa. Ni babu wani abunda na yi na kuskure. Na amshi wannan sarƙan zinarin ne ta yanda ya kamata. Mahaifiyata da kanta ta damƙamin wannan sarkan bayan karanto mata ƙanzon kurege. Na yi amfani da ƙawazuci da kuma makauniyar soyayyar mahaifiya na amshi wannan sarƙan. Shi kuma babanmu, yanzu haka ina mai tabbatar miki yana kwance yana bacci cikin salama da kwanciyar hankali. Sai dai fa ina mai tabbatar miki idan har gari ya waye mana a wannan garin kashin mu ya gama bushewa. Shiyasa na ke so asubar fari mu bar garin nan."
Sai a wannan lokacin Ladi katifa ta ɗan jin sanyi cikin zuciyarta tare da faɗin, "To ai ke ɗin ce akwai tsoratar da mutum. Kuma sanin da na yi maki babu abunda ba za ki iya aikatawa ba akan kuɗi."
Murmushi Laushi ta yi tare da faɗin, "To ki kwantar da hankalinki babu wani abun da na aikata mara kyau. Ki na da ragowar sigari?"
Hankaɗa filo Ladi katifa ta yi tare da ɗauko kwalin sigari mai suna *_Aspen_* ta miƙa mata tare da lighter. Amsa Laushi ta yi tare da buɗe kwalin ta ɗauki sigari ɗaya ta saka a baki sannan ta kunna lighter ta shiga zuƙar sigarin cike da kwarewa ta na fesar da hayaƙin. Hakan ne ya yunƙurowa Ladi katifa da sha'awar shan sigarin ita ma. Hannu ta kai ta zari ɗaya tare da kunna masa wuta ita ma ta shiga zuƙa ta na fesar da hayaƙi. A cikin su babu wacce ta rutsa har alfijir ta fito. Ana shiga masallaci suka yi saɗaf-saɗaf suka fice daga gidan suka nufi tasha. Ko kamun takwas motarasu ta ɗaga zuwa garin Legas.
Tafiya ce su kai mai matukar tsayi a cikin wannan mota. Laushi ta gyara zama yafi sau shurin masaƙi kasancewar wannan shine karonta na farko zuwa garin Legas (Lagos). Sun zaunu iya zaunuwa. Amma a wajen Ladi katifa hakan ba komai bane don wannan ba shine zuwanta na farko ba.
Cikin dare suka sauka. Abunda yayi matuƙar baiwa Laushi mamaki shine; ganin jama'ar garin nata zirga-zirga kamar rana, masu cin kasuwar dare na yi, haka ƴan shaye-shaye da masu sana'a irin ta su.
"Katifa, wannan wani irin gari ne haka kika kawo ni? Wallahi duk iskancina a tsorace nake. Kalli yanda wancen tsohon ke mana wani irin kallo." Faɗin Laushi tana mai damƙar hannun Ladi Katifa.
Murmushi Ladi katifa ta yi tare da faɗin, "Tsarguwa ce kawai. Amma nan garin da kike gani ka zo na zo ce. Babu ruwan wani da wani. Amma idan kika yi sake aka fahimci ke baƙuwa ce. Za ki matuƙar shan mamaki wallahi. Kawai ki yi duk abunda na umarce ki da kiyi. Abu mafi muhimmanci kuma shine; riƙe jakar sarƙarki da kyau da kuma kuɗinki. Domin nan ɗin cike yake da manya-manyan ƴan sibarar na'ayye."
Da jin haka sai Laushi ta damƙi jarakarta da kyau ta maƙaleshi a hammata ƙirjinta na dukan tara-tara. Wani lunguna suka dunga bi har suka iso wani ɗan tsukukun layi. Babu abunda ke tashi a wannan layi sai kiɗe-ƙide. Mata kuwa iri-iri sai shige da fice suke a wani gida dake gabas da inda suke.
"To Alhamdulillah, mun iso." Faɗin Ladi Katifa tana mai nuna mata gidan da hannu.
Ajiyar zuciya Laushi ta yi tare da faɗin, "Har na ji sanyi wallahi. Ni gaba ɗaya ma barci ne a idanuna."
Gaba suka yi kaɗan suka iso ƙofar wannan gida wanda ya kasance gidan karuwai. Ladi Katifa ita ce a gaba, Laushi biye da ita a gaba. Daga waje sam gidan bai nuna alamun girma ba sai da suka shigo gidan sannan suka ga ashe gidan na da girma. Ɗakuna ne a jera guda ashirin a hannun hagu da dama a ta farkon gidan. Ta can ciki ma akwai ɗakuna goma sha bakwai shima hagu da dama. Maza ne danƙam a wannan gida da kuma ƴan daudu. Wasu zaune a bakin ƙofar ɗakinsu daga su sai ɗaurin ƙirji suna hira. Wasu kuma sun ci uban ado sai karairaya suke. Yayin da wasu matan ke gaban wani makiɗin garaya da babu abunda ke fita daga bakinsa sa batsa yana wasa wata wacce ludayinta ke kan dawo a gidan don sai liƙi ƴan sabbin hamsin-hamsin take masa. Tun da suka shigo gidan idanun Laushi ke kan wannan yarinya da ke liƙi.
"Ah! Wa nake gani kamar Ladi Katifa?" Wata budurwa ta faɗi cike da mamaki tana mai kama haɓarta.
"Ni ce ba gizo nake maki ba. Ina hajja Lanti?" Faɗin Ladi Katifa.
Kamun Budurwar ta bata amsa sai da ta ƙarewa Laushi kallo sannan ta mere baki tare da faɗin, "Tana can ciki. Baƙi take dashi. Ban tsammanin za ta saurare ki a yanzu kam. Don baƙin masu matuƙar muhimmanci ne. Sam ba ta wasa da su."
_Comment_ _Vote_ _Share_
_MATAR SAYYADEE_ *** [1/28, 8:52 PM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee