My Destiny (Ƙaddarata)

Page 2

by @matarsayyadee3

Gyaɗa kai Ladi katifa ta yi sannan ta ce, "Don Allah ƴar sita ki ɗan ara mana masauki mana kamun hajja Lantin ta gama da baƙinta."

Hannu ta saka cikin jaka ta fiddo key Kasancewar a shirye take tsaf, kwanan gida za ta. "Ungo ɗan makullin nan don sauri na ke zan fita. Ɗaki na 34 daga can cikin shine nawa."

"Ahhh! Na shiga aljanna ban fito ba ni Salma! Mi zan gani haka namiji da suna Hajara. Yau kuma kamun da Hajja Lanti ta yi kenan. Ciki kuma tirtsetse a wannan gida?" Faɗin wani ɗan daudu ɗaure da zani a kan dogon wandon da ke jikinsa, sai uban ɗaurin da ya kima kamar gwaggwaro da irin zanin da ya ɗaura.

"Ka ga Salmanu......." Saurin katseta ya yi tare da faɗin, "Wallahi tallahi ina maki mummunar rashin mutunci a gidan nan! Menene kuma Salmanu kamar wani gansamemen ƙato. Kar ki ƙara kai ni wannan jinsi. Salma nake! Ko kuma kice Salma nice." Ya ƙarisa maganar yana firirito.

"To naji Salma. Wuce mu tafi ki kai ni inda za ki kai ni. Idan ya so bayan kin dawo sai ki ɗaura daga inda kika tsaya da gulmar tun da ke ba ki iya gani kiyi shuru. Ai da daren ya yi garin ke wayewa. Mai kike ci na baka na zuwa?" Cinya ya buga tare da yin farrr da idanu sannan ya ce, "Kuma fa hakane. Ni ɗin ce Allah ya yi min tsinannan san zance. Muje kin ji. Alhaji Mansur yana can yana jira. Ni ba ma wannan ba. Ina jin alamar baƙonmu na mata zai zo min. Gashi ban tanaji audugarmu ta mata ba. Ohhhh ni Salma. Muje kin ji ƴar sita." Kallon Ladi katifa ƴar sita ta yi tare da faɗin, "To ni sai na dawo. Akwai abinci na nan cikin tukunya ku cinye kar ayi asararsa. Don ban tunanin zan dawo gobe. Daga can ma wani wajen na nufa."

"To Allah ya kiyaye. Sai kin dawo." Faɗin Ladi ta na mai kallon Laushi wacce gaba ɗaya hankalinta ya na kan budurwar da ta kewa mawaƙin nan liƙin kuɗi.

"Don Allah mu wuce kar ki ma fara abunda kike rayawa a zuciyarki daga zuwan mu. Wallahi wannan garin ba kamar Tafa take ba. Da yawan matan da kike gani a wannan gidan suna da wanda ke tsaya masu. Abun mai sauƙi ne mace ta yi kisa kuma wallahi ta kwana lafiya." Faɗin Ladi Katifa.

Wani murmushi Laushi ta yi tare da faɗin, "Uhm! Har yanzu ina ganin ba ki san da wa kike tare ba. Idan Laushi ta ƙuduri abu babu uban da ya isa ya dakatar da ita har sai ta cimma burinta. Waccen yarinyar ba tai min ba. Domin na hango matsayin da ya kamata na hau take hawa. Ko baki lura da wani abu ba tun da muka shigo gidan nan?"

"Ya Rasulullahi Manzon Allah! Wai me ke damun ki ne, Laushi? Yau fa kika soma shigowa cikin gidan nan amma har matsayin da wata take kai ya birge ki." Faɗin Ladi katifa.

"Barikin kenan. Kowa ya iya allonsa sai ya wanke. Na yi rantsuwa da jinin mahaifina sai na zama tauraruwa abun kallon kowa a cikin gidan nan. Bari dai na rabu da wannan _ƙaddarar_ da ke manne a jikina tukun. Kin fi kowa sanin wacece Laushi. Laushi wane fulawa!" Ta ƙarisa maganar cike da wani irin alfahari.

Girgiza kai kawai Ladi katifa ta yi tare da yin gaba har zuwa nombar ɗakin da Ƴar sita ta faɗa mata sannan ta saka key ta buɗe. Ɗaki ne guda ɗaya mai ɗauke da ledan ƙasa, madaidaiciyar katifa, fankan ƙasa, risho, tukwane guda uku, robobin cin abinci da kofi da sauran tarikacen da ba'a rasa ba. Gefe can kusa da gado wata ƙatuwar Ghana must go ne na kayanta. Sai radio wanda ake saka masa kaset ƴar madaidaiciya.

Zama Laushi ta yi a gefen katifar tana mai faɗin, "Wash! Wallahi ƙafafuna gaba ɗaya tsami suke min. Da zan samu ruwan zafi da na watsa wallahi."

"Idan za ki kwanta ki kwanta. Don babu inda za ki samu ruwan zafi yanzu. Za ki ci abincin ne?" Ladi katifa ta jefa mata tambaya.

Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Ciye-ciyen da muka yi a mota ya cushen ciki. A cikin daren nan babu abunda zan iya sakawa cikina. Allah ya tashe mu lafiya." Tana gama faɗin haka ta haye kan katifar ta kwanta.

Can wajajen ƙarshen ukun dare Laushi taji kamar an tsunguleta. A gigice ta miƙe tare da riƙe mararta da yayi wani irin murɗawa. Cikin ƴan daƙiƙu wasu zufan azaba suka shiga kwaranyo daga goshinta.

Wani irin rawa jikinta ya hau yi gab-gab-gab na azabar da tun da uwarta ta haife ta bata taɓa jin makamancin irinsa ba. Wani wawan duka ta kai wa cinyar Ladi Katifa tare da faɗin, "Ki tashi mutuwa zan yi yau."

Saukar sautin muryarta da taji a masarrafar jinta ya saka ta watstsake lokaci guda daga nannauyar baccin da ya kwashe ta, ta diro da daga katifar tare da faɗin, "Laushi haihuwar ce? Inna lillahi! Gashi babu abunda muka tanada." Ta ƙarisa tare da nufa wajen makunni ta kunna filitar ɗakin haske ya gauraye ɗakin.

Jujjuya kai kawai Laushi ke yi tana cizan baki don idan kaga mutun na kukan ciwo to ba ciwon bane. Don wani azabar mantar da kai yanda ake kuka ko ihun yake. Tun cikin daren nan ta ke abu ɗaya har gari ya waye. Ƙarfe bakwai dai-dai hannu yarinya ya fito yana lilo. Dogon salati Ladi Katifa ta saki tare da fita da sauri ta nufi ɗakin hajja Lanti. Babu kwankwasawa ta murɗa ɗakin ta faɗa ciki.

"Wata ƴar iskar karuwar ce ta faɗo min ɗaki haka?" Faɗin Hajja Lanti a fusace tare da miƙewa tana kallon Ladi Katifa ɗai-ɗai.

"Ki min afuwa hajja Lanti. Wacce muka taho tare ne jiya take naƙuda a ɗaki tun dare. Kuma hannun jaririyar ne ya soma fitowa maimakon kai."

Wani dogon tsaki hajja Lanti ta ja tare da faɗin, "Amma kin dai fi kowa sanin ba'a haihuwa a gidan nan ko? To yanzu ni mai zan yi mata?"

"Ki taimaka Hajja don Allah mu kai ta asibiti." Faɗin Ladi katifa jiki na rawa.

Saukowa tayi daga kan ƙaramin gadonta tare da zira takalmi ɗan Madinar da ke ƙasa kusa da gadon sannan ta ce, "Muje na ga ko zan iya taimaka mata. Kin san kamun na fara harkar nan, unguwar zoma ce ni."

Ba tare da Ladi Katifa ta bata amsa ba ta fice da sauri, Hajj Lanti a bayanta. Ko da suka shiga ɗakin ba ƙaramin tausayawa Laushi su ka yi ba. Domin ta fita daga hayyacinta gaba ɗaya. Cikin sauri Hajja Lanti ta fita daga ɗakin ta koma ɗakinta. Can sai gata ta dawo hannunta sanye da handgloves. Duƙawa ta yi sannan cikin dabara irin ta unguwar zoma ta mayar da hannun jinjirar sannan ta juyo da kan jaririyar. Wani irin ihu Laushi ta kwatsatsa sai da gidan ya ɗauka.

"Ya Rasulullahi ni Salma! Wannan irin ihu kuma daga ina haka kamar ana farke budurwa." Faɗin Salmanu ɗan daudu har da saka hannu biyu ya dafe ƙirji.

"Yauwa-yauwa, ni nishi ga gashin ɗa nan ina hangowa. Daure-daure. Ke Ladi danno min can farkon cikin a hankali ki riƙa turowa." Faɗin Hajja Lanti.

Wani irin yunƙuri Laushi ta yi mai tafe da ƙaƙƙarfen nishi sai ga kan ƴar jinjirar fit ya fito. Wani irin ajiyar zuciyar salama Laushi ta yi. Don ji ta yi kamar an zare mata ƙaya.

"Caɓ! Tun da nake karɓan haihuwa lokacin ina amsa sunan unguwar zoma, ban taɓa cin karo da baƙar jaririya kamar wannan ƴa ba. Wai! Duna. Sunan wani baƙin kare." Faɗin Hajja Lanti bayan ta yanke cibiya da sabuwar rezar da ta shigo da shi lokacin da ta je ɗauko handgloves. "Kin ga uwar ma ta biyo baya. Gaskiya ƙawar nan ta ki ta taki Sa'a. An tsallake rijiya da baya." Ta sake faɗi tana mai kwaso jini a jikin Laushi wanda ke fitowa guda-guda.

Ladi katifa kuwa ƙurawa jinjirar idanu tayi tana so ta hango kamanni Laushi ko ɗaya a jikin jinjirar. Sai dai babu ko ɗaya. Don ko dogon hancin jinjirar ba irin na Laushi bane. Jinjirar ta fita hanci sosai..

Hajja Lanti ta gama taimaka mata ta miƙe tare da cire handgloves ta jefar a nan tsakar gidan tare da kallon Ladi katifa ta ce, "Ki same ni a ɗaki idan kin gama kimtsata uwar. Ita kuma ƴar zan turo Salma yanzu ta zo ta karɓe ta ta yi mata wanka."

"Mun gode sosai Hajja Lanti. Allah ya ƙara miki tsawon rai kici karenki babu babbaka." Faɗin Ladi Katifa.

Ba tare da Hajja Lanti ta kuma furta wani abu ba ta fice daga ɗakin tana mai tsirtar da yawu a bakin ƙofa, a cewar ta jinin Laushi matukar ƙarni ne da shi.

Babu kayan jarirai da Laushi ta tanada ko ɗaya. Hakan ya sa Ladi Katifa ɗauko sabuwar zaninta ta lulluɓe jinjirar tare da kwantar da ita.

"Ah! Kice haihuwa akai mana cikin gidan nan. Gaskiya kam akwai buduri. Gaskiya wannan karuwa ta shigo da ƙafar dama. Eh mana! Ai dole na faɗi haka tunda har kece da kanki kika karɓi haihuwar. Bari kiga in gyara jikina in canza auduga don abun namu na mata nake yi." Faɗin Salmanu ɗan daudu da yayi saurin tarar Hajja Lanti yana rausaya tare da kwance zani yana ƙara ɗaurawa a ƙirji bisa dogowar farar jallabiyar dake jikinsa.

Dafa shi Hajja Lanti ta yi tare da faɗin "Ki saurareni da kyau Salma Nice. Wannan baƙin ne da suka so jiya ce ɗaya daga ci ta haifu. To so nake ki amshi jaririyar ki wanke ta tas. Za ki samu kaso mai tsoka."

Wani irin uwar guda Salmanu ɗan daudu ya saki tare da kwance zani ya kuma ɗaurawa sannan ya ce, "Ke duniya! Ni wallahi ma duk sai naji kunya ta rufe ni. Ni da ko haihuwar fari ban yi ba, amma nice yau da wanke jinjira. Ko da yake, ai aikina ne. Don billahil lazi ba zan iya irga maki cibiyoyin jariran da na yanke ba. Kuma masu jegon ma ni ke wanke su sumul da ganyen dalbejiya sannan kuma nayi masu gashi. Ke wani lokacin ma haka zaki ga an buga uban layi ana jiran Salma nice ta amshi haihuwar mata. Unguwar zoma ce da kike gani na nan. To menene a ciki? Duk jinsi ɗaya muke ai."

"Kiyi maza kizo ki amshi sabulun salo ki wanke ɗiyar tass. Za dai kiga jaririya." Hajja Lanti ta ƙarisa maganar tana mai fashewa da dariya sannan ta nufi ɗakinta.

Salmanu ɗan daudu kuwa; kai tsaye ya nufi ɗakin da su Laushi ke ciki tare da kama ƙugu da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ya dafe jikin ƙofar ɗakin tare da faɗin, "Gafarar ku dai. Zan iya shigowa? To menene ma abun tambayar izinin shigowa tun da dai duk jinsi ɗaya muke. Salma nice ce!" Ya ƙarisa maganar yana fari da idanu.

_MATAR SAYYADEE_ ***

*SHARE FISABILILLAH!* [1/28, 8:52 PM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee