My Destiny (Ƙaddarata)

Page 3

by @matarsayyadee3

Ɗaga labule Ladi katifa ta yi tare da faɗin, "To! Cin danƙo harda su kaza. Kai kuma kana garjejan ƙato mai ya kawo ka nan wajen?"

"Ke! Wallahi ahir ɗinki. Ko da wasa kar ki kuma kai ni wannan jinsi. Can gasu gada billahi. Ni ba abun kunya bane a wajena inyi tumɓur mu dambace a goge raini. Wanene ƙaton? Tsohon da aka baro can gida ko?" Faɗin Salmanu yana tauna chewing gum tare da bada sautin ƙas-ƙas.

"Kai! Ashe baka da kunya? Fice min da gani a ƙofar ɗakin nan." Ladi Katifa ta faɗi a fusace.

"Wallahi ina wanke fuskanki da mari kika kuma kai ni jinsin ƴan maza. Haba! Wannan wani irin bala'i ne haka? Kalli nan ki gani; Rigar mama ce jikina. Ga abu nan tantsama-tantsama sun cika ƙirji kina kallo amma shine don tsabar iskanci kike kira na da kai abun ko daɗin ji. Ke ni ban iya dogon zance. Kin san shi wannan abun na mu na mata bai fiye son surutu ba. Yanzu kyaji shaa yana zubowa. Miƙo min ɗiyar kawai na wanke ta, ko kuma ki bani hanya in shiga ciki nai mata saɓi bakwai." Ya ƙarisa maganar da buga cinya tare da bada sautin ƙas-ƙas da chewing gum.

"Ungo nan!" Ta yi masa daƙuwa tare da cigaba da faɗin, "Wani lalacewar ne zai saka na ba gansamemen ƙato irin ka jaririya kai mata wanka." Ladi katifa ta faɗi har da dungure masa kai ɗankwalin da ya kima a kai ya faɗi ƙasa.

Buɗe baki yayi yana kallonta kamun ya ce, "Lalacewar da ta kawo ki bariki. Ke bari dai ki gani." Ya ƙarisa maganar tare da wurgi da zanin dake jikinsa sannan ya soma ƙoƙarin tattaro jallabiyar dake jikinsa zai cire.

Da gudu ɗan uwansa ɗan ɗaudu mai suna Sadisu, amma sai ya mayar da sunan zuwa Sadiya ya riƙe jallabiyar gam tare da faɗin, "Hajj Lanti! Hajja Lanti!! Fito kiga tereran bankaɗa a cikin gidan nan. Salma Nice ke neman yin tsirara tana neman tona mana asiri mu ƴan matan gidan nan. Haba Salma! Ina hankalin naki ya tafi ne? Tsirara! Oh ni na shiga Aljanna ban fito ba ni Sadiya!!" Ya ƙarisa maganar yana tafa hannu bayan sakin jallabiyar Salma nice ɗin.

"Bar ni! Bar ni Sadiya in nuna mata nima kwallon Shegiya ce. Idan ban da iskanci ta kalli damɓasheshiyar budurwa kamar Ni a gabanta, amma sai ta riƙa turani jinsin ƴan maza. Ai da niyyata in tuɓe in yi zigidir domin ta tabbatarwa idanunta mi ɗin jinsi ɗaya muke da ita. To me zata nuna min, ƙirjin ko mazaunan?? Aikin banza. Ai da kin bar ni Salma na gwada mata iskanci."

"Wai hayaniyar me nake ji haka? Ban san iskanci da sassafen nan fa. Ke kuma Sadiya mai ya kawo ki nan ɓangaren?" Faɗin Hajja Lanti rai ɓace.

"To kin ganni nan makanta na gujewa ƴan gidan nan domin kuwa Salma nice ce ta yi ƙoƙarin bayyana tsiraici domin ta tona mana asiri mu ƴan matan gidan nan duk da dai kowacce mace da irin ƙirar jikinta; Wata celinedion, wata Shakira, wata kuma Nikiminaj. Amma kuma ai abunda ke jikin wancen ita ke jikin ƴar uwarta." Faɗin Sadisu (Sadiya). "Eh lallai! Babu shakka." Ladi katifa ta faɗi tana watsa masa harara.

"Hajja Lanti, wannan ƴar iskar karuwar ce ta kai ni bango. Daga zuwa karɓan jaririya domin na yi mata wanka sai kawai ta hau zagina tana tura ni jinsin ƴan maza! Ni wallahi da wanke fuskata ta yi da mari hakan sai ya fi min da tura ni jinsin ƴan mazan da ta yi." Faɗin Salmanu (Salma) tare da ɗaukar zanin da ya yar ya ɗaura a kan ƙirjnsa.

"Ke, Ladi ki tsaya iya matsayinki a cikin gidan nan. Waɗannan da kike gani sune gidan nan. Ban wasa da su kuma ban bari aci zarafin su ko kaɗan. Mun ga irin ku da yawa. Nan gaba kaɗan kuma sai ku riƙa bin su kuna ƴar murya. To duk wasu manya-manyan da masu kuɗin garin nan kaɗan ne basu sani ba. Sune ke haɗa duk wacce ta amsa sunanta da alhazawa a cikin gidan nan. Kuma Salma ni ce nan na turo ta domin ta wanke jaririyar. Sannan ba cewa na yi ki same ni a ɗakina ba?" Hajja Lanti ta faɗi tana kallon Ladi Katifa.

"Ehe! Faɗa mata dai." Faɗin Salmanu yana rausaya tare da kaiwa Sadisu (Sadiya) hannu suka kashe tare da haɗa ɗuwawu su kai shewa.

"Kiyi haƙuri Hajja Lanti. Na ga yana namiji kuma zai yi wa jaririya wanka." Ladi katifa ta faɗi kanta a ƙasa.

"Wallhi ina mai sharara maki tafi kika kuma ce min ƙato. Ke wallahi Allah ya isa tsakanina da ke! Hajja Lanti a gabanki!!" Ya ƙarisa maganar kamar zai fashe da kuka.

"Ki iya bakinki Katifa!" Hajja Lanti ta faɗi da ƙarfi. "Ki min afuwa hajja!" Ladi katifa ta faɗi ta tausashe.

A can cikin ɗakin ƴar sita inda maijego ke ciki kuwa; tun lokacin da ta ji daga bakin Hajja Lanti su Salma da Sadiya (Salmanu da Sadisu) ke kai karuwar da ta amsa sunanta a cikin gidan ta yi wuff ta miƙe daga azabar ciwon cikin da ke nuƙurƙusarta tare da dadumar jinjirar da ke kwance bisa katifa nannaɗe a cikin zani ta yi wuff ta fito tare da faɗin, "Ungo nan Salma nice. Ni ce nan uwar jinjirar nan. Babu uban da ya isa ya hana ki wanke ta. Ba ma wannan kaɗai ba, na baki wuƙa da nama ki zaɓi sunan da ya dace ki saka mata. Ai duk jinsi ɗaya muke."

Wani uwar guɗa Salma nice ta saki tare da buga buje.....

Mu haɗu gobe Please. Yau ɗin ma don kar nai disappointing ɗin ku ne.

_MATAR SAYYADEE_ *** *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee