My Destiny (Ƙaddarata)

Page 5

by @matarsayyadee3

Da kallo Kawai tabi Ladi Katifa tana wani irin murmushin da ita kaɗai ta barwa cikinta. "Idan ruwa ya yi zafi kawai ki juye min. Zan je wajen Hajja Lantin idan na fito daga wanka."

"Yanzu kika yi magana. Bari na kai maki ruwan. Amma magana ta gaskiya ki karɓo Meema a wajen wancen ɗan iskan. Kin san dai zamani ya canza. Har jaririai ma ana wa fyaɗe."

Komai Laushi bata ce ba ta fice daga ɗakin domin zuwa ban ɗauki don tai wanka.....

"Hajja, naji saƙonki a wajen Ladi. Ga sarƙar nan. Gobe sai muje kasuwa a sayar ɗin." Faɗin Laushi. Washe baki Hajja Lanti ta yi tare da faɗin, "Madallah! Kuma da gani zai yi kuɗi. Gobe in Sha Allah sai muje ni da Katifa tunda ke jego kike. Sannan maganar ɗaki; Na can ciki kike so, ko kuma na can farkon gidan?"

"Na farkon gidan zai fi. Amma maganar tafiya da Katifa wajen sayar da sarƙa ba zai yiwuwa. Dani za ai komai." Faɗin Laushi.

"Baki yarda da mu bane?" Hajja Lanti ta faɗi tana kallonta.

"Uhm! Ban taɓa yarda da kaina ba balle kuma da wani. Hannun haguna bai taba yarda da hannun damana ba, haka shima hannun damana bai taɓa yarda da haguna ba. Tare za muje Hajja Lanti."

Kallon mintuna biyu Hajja Lanti ta yi wa Laushi murmushi ɗauke a fuskanta. "Tabbas irin yarinyar nan na jima ina nema." Ta faɗi cikin zuciya. Amma a zahiri sai cewa ta yi, "Ki je duk yanda kika yanke hakan za ayi. Amma kuma ki sani, kuɗin hayan gidan nan duk wata dubu da ɗari biyar ne. Kuɗin wuta kuma ɗari biyar. Jimillar kuɗin duka ya kama dubu biyu."

"Idan mun dawo daga kasuwan zan baki kuɗin shekara guda." Laushi ta faɗi.

"Tashi kije. Allah ya raya Meema." Faɗin Hajja Lantin tana kallon Laushi har ta fice daga ɗakin.

Washa gari kamar yanda suka tsara haka ta faru. Sun je kasuwar sun sayar da sarƙar wanda yayi kuɗi har Naira dubu ɗari da hamsin da uku. (Kar ku manta shekarar 1999 ne a wancan lokacin.) Laushi ta cire kuɗi har naira dubu ashirin da huɗu ta bawa Hajja Lanti cass. Katifa kuwa da ƙyar ta karɓi dubu biyar a hannun Laushi ta sayawa Meema kaya. Sayayyar kayan abinci suka yi sannan suka dawo niƙi-niƙi da kaya. Kuma a kasuwanan sai da Laushi ta yi samari har uku. Ladi Katifa kuma ɗaya.

Allah ya ɗaurawa jinjira Meema wani irin haƙuri. Domin idan Salma (Salmanu) ya ɗauke ta tun safe, sai ta wuce fiye da awa biyar tana goye a bayansa tana bacci. Ko mama uwar bata damu ta riƙa bata ba wai a cewar ta zasu lalace su koma kamar silifas. Idan har ta nemi Meema, to ji ta yi mamar sun yi mata nauyi kamar dutse sannan take bata don raɗin kanta.

Bayan kwana uku da haihuwar Meema idan kaga Laushi baza ka taɓa yarda ita ce wacce ta haihu kwanaki uku da suka wuce ba. Sai wani irin gyara da shafa mayukan gyaran jiki take. Ana gobe suna Sadiya (Ɗan daudu) ya zana mata lalli a ƙafa da hannu. Sannan kuma ya tsantsara mata kitson attachment har gadon baya. Tun a daren aka soma kiɗe-kiɗe. Masu kiɗan gurmi har uku Salma ya kira tare da basu kyautar karuwai waɗanɗa za su taya su kwana. Washa gari kuwa, gidan da wani irin shagali ya tashi. Su Salma nice anci uban kwalliya cikin wata blue ɗin jallabiya an ɗaura hular gashi har baya. Fuskan nan an yi masa uban fenti da su hoda, ja gira da janbaki. Haka ma Sadiya da sauran ƴan daudun gidan.

Su Hajiya mandiya maijego kuwa, wani mahaukacin kwalliya ta ci cikin wata tsadaddiyar less ta dubu goma da Salma nice ya ɗinka mata matsayin gudummawa. Wuyannan sanye da sarƙar gold da ɗankunne wanda Sadiya (Sadisu) ya arowa maijego domin ta fito tana sheƙi. Jaririya ma taci kwalliya cikin wasu ƴan kanti pink colour har da takalmi da kuma band na kai. Ga mai ɗaukar hoto duk inda maijego ta bi da ɗiyarta sai an haske su. Salma nice kuwa shi da maijego da jaririya sun sha hotuna.

Kota ina kiɗan gurmi ne ke tashi ana waƙe Salma nice da maijego. Kan Laushi wani irin girma da hayaƙi ya soma fitarwa lokacin da mai kiɗan gurmi ya hau wasa ta;

" *Lallai sunan ya dace da mai ita. Ko da ban taɓa ba na san wane fulawa a Laushi. Kina fitowa na hangi haske na haska gidan magajiyaaaaa! Karuwa mai buga duniya, wacce tauraronta ke haskawa, kyakkyawa mace doguwa. Taho ki nunawa sauran ƙananan Karuwai idan kina waje sun shafe, domin haskenki ne kawai zai haska. Wai ina Laushi ne?"*

Wani irin tsuma ta hau yi tare da miƙawa Salma nice Meema sannan ta nufi wajen mawaƙin ta hau yi masa ɓarin Naira. Shi kuwa ya cigaba da wasa ta iya iyawarsa. Wani irin juyi ta shiga yi tana rawa da mazaunanta wanda ya ja hankalin jama'a aka hau ihu. Cikin sauri Sadiya (Sadisu) ya taho ya kama ƙugunta da hannu biyu suka shiga rawa suna jefa ƙafa tare. Salma nice shima jikinsa ya hau rawa ya miƙawa Ladi Katifa Meema ya tafi ya kama ƙugun Sadiya (Sadisu), shima wani ya kama ƙugunsa. Haka su ka yi layi sai rawa suke yi ana masu liƙi.

Wani daga cikin ƴan kallo wanda ya kasance dadiron Kyandir, tunda ya kyallara idanu a kan Laushi yaji yana son ɗanɗanar zumarta. Amma idanun Kyandir dake kansa ya hana shi motsi. Daga ƙarshe ma hannunsa Kyandir ɗin ta zo ta kama suka wuce ɗakinta ta kullo ƙofa ta hau yi masa bala'i akan idanun da yayi ta bin Laushin dashi.

Laushi kuwa duk da rawa take, amma hankalinta ita ma yana kan saurayin Kyandir wanda take lure yana ta binta da idanu. Babban farin cikinta shine; dalilin wannan shagali da Salma nice ya haɗa mata, ya jawo hankulan jama'a da yawa sun santa. Don ta zama wata celebrity a gidan. Maza da dama sai turo jiki suke wajenta wanda dama hakan take so. Ba su suka bar wajen kiɗan nan ba sai uku na dare tun safiya. Jaririya kuwa ta ɗauku kuma bata samun shan mama sosai ba sai ruwan zafin da aka ɗiga zuma ciki da Ladi Katifa ke ta ɗura mata. Don ma Allah yayi yarinyar da haƙuri.

Da ƙyar ta iya cire sarƙar wuyanta da ɗan kunnen saboda wani bacci dake idanunta. Bayan ta canza kaya zuwa zani ɗaurin ƙirji sannan ta shayar da jinjirar na mintuna goma sai ta kwanta ba tare da lura Ladi Katifa bata ɗakin ba.

Ita kuwa Ladi, saurayin da tayi ranar da suka je sayar da sarƙa ne ya ziyarceta suka kama ɗaki suna sheƙe ayarsu. Don kuɗin kwana ya biya.

"Wallahi tallahi sai na ga wanda ya haifi uwarka yau a cikin gidan nan. Kai ka isa ka kwanta dani cikin gidan nan kama hanya ka fita ba tare da ka biya ni haƙƙina ba! Ubanka ne ya sassaƙa ne?" Faɗin wata karuwa a ƙofar ɗakinta riƙe da kwalar saurayin nata.

"Cika min kwalar riga ko inci ubanki wallahi. Ke!" Ya faɗi maganar cike da muzurai.

"Bazan cika ba!" Ta faɗi da ƙarfi har da jijjigasa tare da cigaba, "Ka gama tumurmusan jikin nawa kamar jakar ubanka, ka kwana a kaina sannan ka hana ni haƙƙina. Wallahi ubanka yayi kaɗan. Lallai ba ka san wacece kwalba uwar sharri ba."

"Ahhh! Na shiga Aljanna ban fito ba. Yanzu kai gansan-gansan da kai, ka tashi ka kwaso shalalau-shalalau ɗin ƙafafunka ka taho gidan karuwai domin jin kashe ƙishirwarka, sai ka tashi kazo hannu rabbana. Ahh wallahi ka yi zunubi. Duk inda za ka naimo kuɗinta ka naimo ka ba ta. Ahhh!" Faɗin Sadiya (Sadisu ɗan daudu).

"Ni ban da sisi. Idan kuma zaka ara min zuwa na gaba sai in biya ka." Faɗin Saurayin.

"Amma dai Allah ya kwashe maka albarka da ka tura ni jinsin ƴan maza. Tare muka ci mintar tata da zan ara maka kuɗi? Kai amma dai Allah ya tsine maka, ɗan akuya kawai. Raba shi da numfashinsa idan bai baki hakkinki ba. Ni ka ganni nan ban yarda da cin haƙƙi da zarafin ƴan uwana mata." Ya ƙarisa maganar yana rangwada tare da yin dogon tsaki ya soma tafiya.

"Wawa kawai ɗan daudu! Ba gwara ni sau dubu ba a kan ka. Ka na namiji gansansan da kai amma ka mayar da kanka mace. Tsinanne kawai!"

"Rabi'a, Salma nice, Raziƙa, Tinene, aunty Asabe, aunty Munari da aunty Khairat duk ku fito!" Da ƙarfi Sadiya ɗan daudu ya kwala kiransu. Sai ga ƴan uwansa ƴan daudu suna fitowa daga ɗakunansu.

"Wani ɗan iskan ne ya taɓo mana ke muyi masa wankin babban bargo?" Suka haɗa baki suka faɗa.

"Mai ke faruwa?" Hajja Lanti ita ma da hayaniyar ya dame ta ta fito. Bayanta kuma Laushi ce wacce ji tayi kamar kawai rufe idanu tayi gari ya waye. Gashi gab asuba Meema ta yi ta kuka har wajajen ƙarfe bakwai na safe.

"Kin ganshi nan. Iyo yayi a kogin kwalba uwar sharri kuma ya hana ta haƙƙinta. Daga na tanka na faɗa masa Allah, Annabi shine ya hau zagina yana kwance min zani a kasuwa."

"Magajiya ba haka aka yi ba. Dama tun jiya na faɗa mata bashi zan yi amma na taho mata da ƙunshin nama. Wallahi jiya gaba ɗaya kuɗin jikina wajen liƙi ya ƙare. To shine fa yau na taso zan wuce wajen sana'a ta shine ta shaƙi wuyana akan sai na bata haƙƙinta."

"Nawa ne kuɗin nata?" Hajja Lanti ta faɗi tana kallonta bayan ta yiwa kwalba alama da hannu da ta saki wuyarsa.

"Dari biyar ne." Ya faɗi yana gyara wuyar rigarsa.

"Kutumar uba! Uban ɗari biyar ba ɗari biyar." Ta faɗi a fusace tare da ɗage laluben ɗakinta tare da faɗin, "Kalli can Hajja Lanti, wallahi Kyandir muka kunna. Bai sauka kaina ba har sai da ya narke. Kuma kuɗinsa shine dubu uku ciff. Kuma wallahi ko ragin kwandala bazan yi ba."

"Anjima da yamma ka kawo dubu uku da ɗari biyar har ɗakina. Idan ba haka ba kar in kuma ganinka a gidan nan." Faɗin Hajja Lanti.

"An gama Hajja Lanti! Har da ƙunshi nama ma. Ke kuma, har abada ni da ke. An faɗa maki ma daɗinki ake ji. Maleji kawai ake yi amma wallahi gwara dusa dake." Ya faɗi tare da ficewa.

Sauran karuwan da suke wajen suka fashe da dariya suna nuna ta. Hajja Lanti kuwa, kallan Laushi ta yi tare da faɗin, "Allah ya sa ba kya daɗewa idan kina jinin biƙi domin a jiya kawai kin samu mataya guda goma sha ɗaya......"

_MATAR SAYYADEE_ ***** [1/28, 8:52 PM] Rahamanatu: *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee