Page 4
"Kai Jama'a! Wato idan har kai ne fa to kai ɗin ne. Za ki iya matsawa yanzu ki ban waje na amshi jinjirar ko kuwa? Tun da dai wacce ta yi wahalar buɗa ƙafafun ta ɗau cikin ta kuma sha wuya ta haife ta ta ban izinin wankan. Ko tare kuka ji daɗin da kuma wuyar fitar kan jinjirar?" Salmanu ya ƙarisa maganar yana zazzarowa Ladi Katifa idanu.
"Waiiii! In mutu mata ƴan uwana su kai ni ba garada ba. Wannan baƙar jinjirar fa? Tun da uwata ta haifan ban taɓa ganin jinjira baƙa ba sai yauuu. Asheee!!" Sadiya (Sadisu) ya ƙarisa maganar tare da riƙe haɓa yana ƙara leƙen fuskan jinjirar da Salma nice ya karɓa a hannun uwarta.
"Ke, Sadiya! Ban son iskanci wallahi. A kan wannan jinjirar sai in mance mu ɗin ƙawayen yarinta ne. Oh ni Salma ya ma ake kiran sallah? Au na tuna...." Ya ƙarisa maganar yana mai karkata kan yarinyar ya soma kiran sallah a kunnenta.
"To! Allah na tuba. Ni ban tambayi shin ko mace mai haila za ta iya huɗuba ba. To astagfirullah idan ma ba'a yi. Jama'a ni Salma na raɗawa yarinyar nan suna 'Fareeda' amma kuma za'a riƙa yi mata inkiya da ( _Meema_). Sannan ina gayyatar kowa da kowa, rana ita yau za'a raƙashe a shashe sannan aci a sha kowa yayi koduma. Sannan kuma matsayina na maraɗin sunan _Meema_ na bada danƙareran rago kyauta domin ayi sunan kowa bakinsa ya sashe. Maijego kuma na dau nauyin ɗinkuna har kala bakwai domin ta shiga ta fita ranar suna. Ƴan baƙin ciki kuma sai a kunna risho a zauna a kai."
Kasancewar kusan rabin da kwatan gidan suna wajen, sai suka hau ihu da shewa tare da saki batsa. Laushi kuwa; ji ta yi ta kammala saboda gindin zaman da ta samu a wajen Salma nice.
"Sadiya, muje ki aran bahon nan da kike gashin basir. Sannan ki taimaka min ki jona min ruwan zafi a heater tunda akwai wutan lantarki. So nake na gasa Meema sosai don kar ta yi warin ƙashi. Ban san ko ni kaɗai na ke hangen wani abu ba tattare da jinjirar nan. Ku na lura bakin fatarta kawai kuke iya hange. Amma ba ku hango tsantsan kyawun da Allah ya yiwa wannan baiwar Allah. Ni nan Salma ni ce zan raine ta."
"A'a fa! Kar ki kai Sadiya inda Allah bai kai ta ba. Ni na isa na ce Yarinyar nan mummuna ce! Kawai dai mamaki na ke yi don yau ne na fara ganin fatar jaririya baƙi. Amma kuwa in dai magana ake ta tsantsan kyau, idan aka zo kan jaririyar nan anzo ƙarshe. Kuma da gani za tai diri. Allah dai ya raya." Faɗin Sadiya (Sadisu).
Da "Ameen." Salma Nice ta amsa tare da nufa ɗakin da ya kasance na shi. Cire zanin da aka lulluɓe jinjirar yayi sannan ya gyara zanin ya mayar da ita ya lulluɓe sannan ya kwantar a katifa. Miƙewa yayi yana ƴan waƙe-waƙe tare da nufa wajen kayansa ya ciro wata farar robar sabulun salo ya ajiye a kan gadon daidai shigowar Sadiya (Sadisu) da baho a hannunsa tare da faɗin,
"Ga bahon nan. Sai kuma me zan kawo miki ƴar zaman wanka?" Ya ƙarisa maganar da dariya.
"Ban son iskanci Sadi baby! Ki ɗau kuɗi gashi nan kan katifa ki tafi kantin broda ki sayo min wannan set ɗin kayan sanyin na jarirai. Bai wuce dubu uku ko biyu da biyar ba."
"Ahayyye camassss! Gaskiya yarinyar nan ta zo da goshi cikin gidan nan tun da har Salma ta iya cire kuɗi maƙudai ta yi uban hidima haka; ga rago, kayan fitar sunan uwar, abincin suna da kuma kayan jaririai. Ko da yake, na san Salma ba ta abun banza. Kin san inda za ki fanshe ne shiyasa."
Wani dariya Salma Nice ta kwashe da shi tare da faɗin, "Ke ma dai kin sani! Idan kika ga ina rawar jiki to na samu bayanai daga bakin Hajja Lanti. Mahaifiyar yarinyar nan da kike gani, ba ƙaramin ƙaruwa za muyi da ita ba. Daga ni har Hajja Lanti. Kin san kuwa wa ake wa tanajin ta? Kawo kunnan ki ki ji."
Waro idanu Sadiya (Sadisu) yayi tare da faɗin, "Ke, Salma! Alhaji Bab....."
Saurin toshe masa baki yayi tare da faɗin, "Daɗina da ke iskanci da hauka. Ya muna maganar sirri za ki nemi tona min asiri duniya ta ji. To wannan magana dai idan ta fita ke ce. Kin san dai burin Kyandir ne hakan sai ga shi Hajja Lanti ba itan ta zaɓa ba."
"Caɓ! Akwai ƙura kenan a cikin gidan nan! Wai-wai-wai!! Hajja Lanti ta san kan tsiya. Amma ita ta san halin uwar jaririyar sosai da har za ta yi wannan kasadar?"
"Ke! Kibar kaza cikin gashinta. Yanzu dai mu bar maganar nan ki tashi ki sayo min kayan da kuma ƙunzugun yara (Pampers). Ga ruwan nan ma alamun tafasa yi ke yi. Yi maza Sadiya." Salmanu ya faɗi yana tafa hannu.
Miƙewa Sadiya (Sadisu) ya yi har da botsaro mazaunai sannan ya tashi ya fice. Ko da ya dawo har Salma nice ya juye ruwan ya sirka ya ɗora ƙafafunsa biyu a kan bahon sannan ya kawo jinjirar ya ɗaura a kan ƙafafun. Yanda ya ke wanke jinjirar zaka rantse da Allah wata tsohuwa ƴar shekaru sittin da doriya ne ke wanke jariri. Kamar yanda ya faɗi, sai da yayi wa Meema saɓi bakwai. Tun tana tsanyara kuka har ta soma jin daɗin jikinta tai lumui. Yana gamawa ya nannanɗeta cikin wankakken zani. Shi kuma Sadiya ya fitar da ruwan.
Shafa ya yiwa Meema sosai da man kaɗe. Ya saka mata a hanci sannan ya lakuto ya saka mata a baki sannan ya saka mata Pampers tare da kayan sanyin. Tun kan ya gama tuni tai bacci.
A can ɗakin Ƴar sita kuwa; Ladi Katifa ce ta saka Laushi a gaba sai zazzaga mata masifa take, "Idan ba iskanci da rashin sanin ciwon kai ba, ina ke ina bawa ɗan daudu jinjira domin yayi mata wanka! Menene amfani na kenan? Gaskiya kin ban mamaki Laushi. Wai ke da kan ki kika ɗauki ƴar da ta hudo daga jikinki kika bawa ɗan daudu, har yana mata huɗu ba. Wallahi ba ki da hankali."
"Nuna min inda ake sayar da shi sai inje in sayo! Ke, Ladi Katifa. Ni fa barikin da gaske na taho inyi sa. Ba zai yu in baro Mahaifata ba domin sana'a sannan kuma in bari wani abu ya kawo min shamaki ba. Wallahi cikin nan da na haife ma kin san Allah yayi zuwansa ne kawai. Amma ni ban shirya hakan ba. Don kin fi kowa sanin shaye-shayen da na yi domin ya fita. Har birge tsinannen akai amma gashi nan sai da ta fito duniya. A cikin kwaratan nawa ma ban san wani mai tsinannan nacin bane da har ya yi min cikin nan. Allah dai ya tsinewa koma wanene. Shege ɗan iska!"
"Shegu ƴan iska dai! Domin kuɗinsa ne ya kai ki, shi kuma jikinki ne ya birgesa. Bai maki tilas ba. Kuɗi kika gani." Ladi Katifa ta faɗi.
"Kuma a nan ɗin ma shi na zo nema da gasken-gaske ba. Don haka ki bar yin kamar kina min nasiha. Don duk sana'ar mu ɗaya. Batun Salma kuma ai duk jini ɗaya muke." Laushi ta faɗi tana kaɗa ƙafa.
"Laushi kenan! Neman kuɗi ba hauka bane fa. Tom! Idan za ki natsu ki bi komai a sannu, ki natsu." Ladi ta faɗi.
"Uhm! Baki san wacece Zinatu Laushi ba har yau. Wallahi wannan jinin biƙin da ke zuba a jikina, da ina da yanda zan yi ya tsaya wallahi da na yi. Don na ƙagu na fara buga wasa na a cikin gidan nan. Ni baki faɗa min yanda kuka yi da Hajja Lantin ba."
Ladi Katifa ta ce "Ta ce ki kai mata sarƙar idan kin huta?"
Da sauri Laushi ta miƙe tare da faɗin, "Ban gane in kai mata sarƙar ba? Kin kuwa san ta yanda na samu sarƙar nan da har kika faɗa min ta ce in kai mata? Uwata ce ita? Ita ɗin magajiyar karuwai ce kawai ba wai magajiyata ba! Wannan ai rainin wayau ne ma."
"Na ce ba, ke ɗin ya ma sunan ki?" Ladi katifa ta jefa mata tamabaya.
"Zinatu Laushi! Ko sai na faɗi da babbar murya." Ta faɗi tana mai maka mata harara.
"A'a ba wannan ba. Sunanki na sana'a." Ta kuma jefa mata tambaya.
"Laushi!" Ta bata amsa a tsiwace tana kallonta. Girgiza kai Ladi Katifa ta yi tana murmushi tare da faɗin, "Sunanki shine *Karuwa*. Ka a ra u wa a.! Idan kin haɗe haruffan zai baki kalmar Karuwa! Don haka Hajja Lanti magajiyarki ce."
[1/28, 8:38 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
*ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._