My Destiny (Ƙaddarata)

Page 6

by @matarsayyadee3

Da sauri Laushi ta dakata tare da kallon Hajja Lanti ta ce, "Hajja don Allah ba ki san wani maganin da zan iya sha ba da zai tsayar min da wannan jinin? Wallahi ban so na kai tsayin kwanakin nan ina fitar da jini."

Murmushi Hajja Lanti ta yi tare da faɗin, "Ba zan ba ki wannan shawarar ba. Kiyi haƙuri ki bari ya tafi don raɗin kansa. Kwanaki nawa ne suka rage idan da rai da lafiya. Customers har sai kin rasa yanda za kiyi da su. Ki daina wutar ciki!" Tana gama faɗin haka ta wuce ciki.

"Ahh Ma sha Allah tubarakallah! Mazaunai sun yi tuɓu-tuɓu. Ke kuma haka ake yi ƴar sita? Tun daren da maman Meema ta tare a gidan nan kika tafi kwanan gida shine sai yau! Uhm. Aiko an sha shagali babu ke." Faɗin Salma ɗan daudu.

"Ke dai bari Salma. Bai tashi faɗa min rakiya zan masa zuwa Imo ba sai da naje. Washa garin ranar muka bar garin Lagos. Kin ganni nan jiya muka dawo da daddare. Wacece kuma maman Meema a gidan nan?" Faɗin ƴar sita.

"Wacce suka zo gidan nan ita da Ladi Katifa daren ranar da za ki tafi kwanan gida wajen Saurayinki."

"Haba! Mai cikin nan da suka zo tare? Kuma Hajja Lanti bata ce komai ba? Lallai an zo da bidi'a a cikin gidan nan. Kamun wannan bari na shafa maka wannan labarin; jiya dai da hannuna na riƙe wayar hannu. Ashe da gaske shugaban ƙasan nan na mu yake. To ganin idanuna na ga wayar hannu sunanta *_Nokia 3310_*. To abunda zai matuƙar baki mamaki shine; Akwai wani ɗan ƙaramin abu da ake sakawa a cikin wayar (Sim) wanda dole sai da shi zaka iya kira kuma kai ma a kira, to wannan abun yafi wayar ma tsada. Domin dubu saba'in ake sayar dashi."

"Dubu uban me? Caɓ! Ashe mu da waya sai dai hange daga nesa. Banƙi ba dai ko zan iya latsata idan ta shigo hannun ku. Bari kiga inyi nan in ɗauko ɗiyata Meema." Yana gama faɗin haka ya nufi ɗakin Laushi ta farkon gidan inda a nan ɗakin su ya koma.

_Bayan wata guda_

Sabuwar duniya ta buɗewa Laushi. Domin kuwa a tsayin wata ɗaya da ƴan kwanaki babu wanda bai santa ba a cikin da wajen gidan karuwai. Ta kasance fara kuma doguwa mai ƙirar jiki da manya-manyan idanu gami da dogon hanci. Jikinta kamar auduga haka yake wannan dalilin ne ma ya saka ake kiranta da Laushi. Sosai take shaye-shaye shiyasa idan ta yi luuu da idanunta ko bata cikin maye zaka ɗauka a buge take. Gaba ɗaya ƴan daudun gidan nan ta haɗe dasu. Tafawa da haɗa mazaunai da su ya zama kamar guɗa a wajen mace lokacin murna. Meema kuwa wani lokacin tun daga fitowar rana har sai ta faɗi basu haɗu ba saboda yawace-yawacenta don Laushi bata zama waje ɗaya sam. Sannan babu rana da namiji bai kwana a ɗakinta. Tsakiyar dare haka kukan Meema zai karaɗe gidan amma Laushi tai burus saboda tana tarawa da saurayinta. Wani lokacin kuma Salma ɗan daudu yaje har ƙofar ɗakin yayi ta kwankwasawa har sai an buɗe sannan ya amshi Meeman ya koma ɗakinsa kuma Ladi Katifa wacce tuni itama ta samu na ta dadiron da ya kama mata ɗaki anan gidan karuwan duk da shima idan yana nan bai yarda ta fita zuwa amso Meeman.

Ɓangaren Hajja Lanti kuma anyi disappointing ɗin ta. Domin kuwa wanda za suyi alkarla dasu akan za ta ba su ƙaruwai uku masu tashe daga cikin karuwan gidanta. Sai ga shi tsawon wata guda bata gan su ba. Gashi ta riga ta kwallafa rai da nairorin da zata samu dasu. Shiyasa da ta samu labarin Laushi a wajen Ladi Katifa ta matsa mata akan taje ta taho mata da ita.

Gangan Laushi ba ƙaramin zaƙi da tashe yake ba a gidan Hajja Lanti. A rana idan ba ayi faɗa akan ta sau goma ba to tabbas za ayi fiye da so biyar. Don samarin karuwan da ke gidan da dama sun koma jam'iyyar Laushi. Meema kuwa ba ƙaramin wahala take sha ba. Watanna goma sha biyu cif ta yaye ta acewarta tana hana ta rawar gaban hantsi. Domin mafi yawan lokuta sai suna tsaka da sheƙe ayarsu take saka babin kuwa. Sun yi faɗa da samarinta babu adadi akan Meema. Wani lokacin idan ta rasa ciniki saboda Meeman, duk da ƙanƙantar yarinyar haka za ta saka bayan hannu ta mammake ta.

Lokuta sun shuɗe, satittuka sun lula, haka shekaru sun ja. Domin yanzu kwanan watan ishirin da uku ne, watan huɗu, shekarar dubu biyu da takwas (04/9/2008). Wanda yayi daidai da shekarun Meema takwas cif-cif.

" _Happy birthday to you! Happy birthday to you!! Happy birthday, Happy birthday day, Happy birthday to you_"

Kusan rabin ƴan gidan ne zagaye a ita. A gabanta kuma ƙatoton cake ne mai rubuce da sunanta a tsakiya sai candle ɗin dake zagaye da shi. A tare ita da Salma nice suka hure candle ɗin sannan suka yanka cake ɗin tare. Hannu ta kai ta gutsiro cake ɗin tare da kai wa saitin bakin Salma nice, sai ta yi saurin turawa Ladi Katifa a baki tana dariya.

"Yau naga lalata ni Salma. Inci kashi da fitsarinki amma shine za ki fara bata kamun Ni! Ni da ke ne wallahi a cikin gidan nan."

"Sorry Uncle Salman...... Au! Aunty Salma. Buɗe baki in saka maki." Faɗin Meema tana dariya ƙasa-ƙasa saboda ganin dagaske fushi Salma nice ɗin ta yi.

"To ya na iya da samarin kakannina ina gudu suna bina. Haka nan zan buɗe bakin." Ya faɗi tare da buɗe bakin ita kuma ta saka mata. Nan da nan gidan ya harmutse da sauti. Duk wannan shagalin da ake yi, Laushi bata wajen tana can ɗaki sa sabon saurayinta kasancewar tsayayyen dadironta da ya ɗauke ɗawainiyarta kaf har da na Meema ya bar garin domin sana'arsa kuma ya faɗa mata zai kai wata guda. A wannan lokacin da kowa ke raye-raye da shaye-shaye, Meema wajen cake ɗin ta ta nufa tare da yanko kaɗan daga ciki domitm kaiwa mamanta.

Tun kamun ta kai ƙofar ɗakin gabanta ke wani irin bugawa da ƙarfi kasancewar tana matuƙar tsoron mahaifiyarta don bata mata da wasa. Kyara ce sosai a tsakaninsu don mahaifiyar cewa take dalilin Meema ɗin zaƙin da take dashi ya ragu saboda ta fito ta jikinta ta ƙara ta. Akwai wani duka da ta taɓa yi mata sai da ta kwanta a asibiti daga ta tambayeta wanene mahaifinta saboda a school ana mata dariya wai bata da uba. Tun da maman ta yi mata wannan dukan bata kuma tambayanta ba. A wajen mutane uku kawai take samun kula; Salma nice (Salmanu), Ladi Katifa da kuma Sadiya (Sadisu).

Hannunta har rawa yake yi wajen murɗa handle ɗin kofar. Labulen ta ɗaga ta shiga ɗakin. Cak ta tsaya tana kallon mahaifiyar nata kur, duk da ba wannan bane karon farko da ta taɓa ganin ana tarayya da mamanta ba. Ɗagowa da sauri Laushi ta yi tare da mulmulo ashariya sannan ta ce, "Yau ma kin yi min laɓen ne domin ki ga yanda mahaifinki ya samar dake?"

Girgiza kai Meema ta yi jikinta na rawa. Don duk wannan maganar da mahaifiyar ta ke yi, shi saurayin da ya kasance bayarabe ko gizau bai yi ba sai ma cigaba da kusantar mahaifiyar ya ke yi. Juyawa Meema ta yi da sauri za ta fita suka ci karo da asalin dadiron mahaifiyar tata ya shigo ɗakin. Wani irin ture bayaraben Laushi ta yi tare da rarumar zanin gado ta lulluɓe jikinta.

"Don abu kaza-kazanki Ni zaki ciwa amana? Yau sai kin raina kanki." Yana gama faɗin haka yayi kwallo da Meema sannan yayi kukan kura ya cafki zanin gadon da ta lulluɓe jiki da she ya yar ya hau wankawa fuskanta mari yana haɗa kanta da bango. A gigice Meema ta miƙe ta nufe sa domin Allah ya ɗaura mata wani irin ƙaunar mahaifiyarta. Wani plate ɗin da suka gama cin abinci a tsakar ɗakin ta ɗauka ta jefi dadiron da dashi. Kamar an saita sai a ƙeyarsa. Da sauri ya dafe wajen tare da juyowa ya nufo kan Meema. Jikinta ne ya hau wani irin rawa ta hau faɗin, "Sorry! Sorry!! Sorry!!!" Ɗauketa ya yi da mari sannan ya taka ruwan cikinta daidai shigowar Hajja Lanti saboda ihun da taji...

_Matar Sayyadee_ *** [1/28, 8:38 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

*ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._