Page 7
"Kai! Kisan kai a cikin gidana? Zo ka fice!" Hajja Lanti ta ƙarisa faɗin haka tare da turesa ta nuna masa hanya.
Juyawa yayi tare da rufe Laushi da duka ta ko ina yana haurinta. Da kyar Ladi Katifa da Hajja Lanti suka janye sa Laushi ta samu hanyar fita daga ɗakin da gudu. Bai kyaleta ba har wajen ya bita tare da fizge janin da ta kare jikinta da shi ga shi babu komai a jikinta ya cigaba da dukanta. Kuka take yi tana kare jikinta. Gaba ɗaya gidan sun zagaye su. An rasa wa zai ceci Laushi daga hannunsa. Da kyar da suɗin goshi Hajja Lanti, Ladi Katifa, da Salma nice suka janye shi. Baki da kan Laushi babu abunda ke fitarwa sai jini. Kuma bakinta bai mutu ba sai zagi suke aunawa juna suna tone-tonen asirin juna.
"Inna lillahi! Ni wallahi babu abunda ya fi bani takaici sai tsirarar da ya yi mata haihuwar uwarta. Wannan ai an gama tona mana mu mata asiri. Wannan bala'i da mai yayi kama haka? Ni Salmaaaa!" Faɗin Salmanu ɗan daudu bayan ya yafa mata zanin da ya gani shanye a igiya.
"Wallahi sai na nuna miki asalin kalata. Ni ba mutumin da ake cin amanarsa ya kyale bane. Sai na rama fiye da abunda kika min. Kuma daga yau babu ni babu ke." Yana gama faɗin haka ya fice daga gidan fuuuuu.
"A gaskiya baki kyauta ba maman Meema. Wannan irin hidima da yake maki bai ci ace daga tafiyarsa kin masa kishiya ba. Dama ace daɗewa yayi da tafiyar sai mu baki uzurin ko ƙaiƙayi abun ya ke maki. Amma dududu ko sati ya yi da tafiyar! Gaskiya baki kyauta ba." Faɗin Sadiya ɗan daudu.
A fusace Laushi ta ce, "Mijina ne shi da zai ce shi kaɗai zan riƙa buɗewa ƙafa? To wallahi ko mijina ne shi yar da igiyar auren zan yi in kama gabana. Idan har zan iya rayuwa da mutum ɗaya mai yasa na taho bariki? Idan haka nake so in zauna a gidan mu inyi aure mana. Kuma wallahi sai na rama tozarcin da yayi min."
"Uhm. Kan ki ake ji! Ai gashi nan har ƴarki ta samu na ta rabon. Kuma wallahi ba kowani irin Dadiro bane kamar Yasaar. Baki san wanene shi bane. Za kiyi dana sani." Faɗin Hajja Lanti.
Dogon tsaki Laushi ta ja tare da faɗin, "Shi ɗin banza! Wallahi sai na samu ɗarinsa waɗanda suka fisa komai."
Sauran karuwan da ke wajen kuwa dariya suka riƙa yi suna habaici don dama sun tsani Laushin saboda ragewa kasuwarsu darajar da ta yi. Gashi kuma dama ji take ta fi kowa a gidan. Don hatta ita kanta Hajja Lantin kallon uku saura kwata Laushi take mata.
Fizgo Meema dake jikin Salmanu ɗan daudu tana shashsheƙar kuka ta yi tare da wanke fuskanta da mari sannan ta kafa mata rankwashi a kai tare da faɗin, "Duk ke kika ja faruwar komai shegiya mai halin irin kalar fatarta!" Ta ƙarisa maganar tare da dungure mata kai ta faɗi.
A zafafe Salma nice ya ce, "Duk wacce za ta nunawa yarinyar nan ƙauna dai barin ke ce! Don haka idan ma kin yi hakan ne don inji zafi, to ban ji ba. Ke kika tsuguna kika sha azaba wajen kawo ta duniya. Don haka idan kin ga dama ki wasa wuƙa ki dadara a wuyarta har kai ya gangara ba damuwata bace." Ya ƙarisa maganar tare da jan dogon tsaki ya bar wajen.
Abunda ya matuƙar ba mutane mamaki a wajen shine. Duk da abunda uwar ta yiwa ƴar, da mugun sauri ta nufe ta tare da riƙota da dukkanin ƙarfinta lokacin da Uwar ta miƙe juwa ya kwasheta za ta tafi ƙasa. Meema na matuƙar ƙaunar mahaifiyarta fiye da komai a duniya. Ƙaunarta take irin wanda bai misaltuwa.
Bayan sati biyu da faruwar abunda ya faru Yasaar ya dawo gidan Karuwai ya lallaɓa Laushi suka shirya kamar ba waɗanda suka yi kare jini biri jini ba. A wajensa komai ya wuce. Sai dai ita kuma Laushi bai wuce a wajanta ba. Domin kuwa tana nan tana shirya irin nata tuggun.
Shekara guda ya zo ya wuce. Laushi abubuwa sun ci uban na da. Domin kuwa ta faɗa tsundun harkar kwayoyi da tabar wiwi da su codine. Har gida ake zuwa saya. Sosai arziki yaci uban na da don yanzu ba da kuɗin karuwanci take dogaro ba. Hajja Lanti ma tana samun na ta kason sosai shiyasa ta ke goya wa Laushi baya ɗari bisa ɗari. Kasancewar kuma ta san wasu manyan, sai ta ke cin karenta babu babbaka. Shima Yasaar sana'ar da yake kenan. Kuma ta san kaso sittin daga cikin sirrinsa. Don shine ma yayi mata hanyar waɗanda za su riƙa kawo mata kwayoyi da tabar wiwi. Rana ɗaya ta yi masa wani mummunar cin amana. Ita kaɗai a garin Lagos ta san zai shigo da Cocaine bayan waɗanda suka ba shi kwangilar. Yana dirowa daga Mexico a Lagos International airport hukumar NDLEA suka kai ram da shi domin an same sa da hodar iblis dumu-dumu. Kai tsaye a kai Prison da shi. Sai dai bayan an kai shi kotu, duk matsar da a kai masa bai bayyanar da sunan manyansa ba. Alƙali ya yanke masa hukuncin shekaru ashirin a gidan yari tare da horo mai tsanani.
Yasaar kuwa ƙunar da yake ji na cin amanar da Laushi ta yi masa yafi na hukunci da aka yanke masa baƙin ciki da ƙuna. Kuma yayi alƙawarin duk lokaci da ya fito sai ya mata abunda sai ta gwammaci mutuwa da ita. Don ya san ba zai taɓa diɓar shekarun da alƙali ya ɗibar masa ba ba tare da ubannin gidansa sun fitar da shi ba..
_Wacece Zinatu (Laushi)_
Zinatu _Laushi_ haifaffiyar garin Bauchi (Azare) ce. Ita ce ƴa ta uku a wajen mahaifinta da mahaifiyarta. Tana da yayyi mata biyu, ƙannai mata uku da ƙannai maza biyu. A taƙaice dai su takwas ne cif a wajen iyayensu. Su ɗin ba masu arziki bane. Amma kuma suna da rufin asiri da wadatar zuci don mahaifinsu mutum ne tsayayye a gidansa domin ya fi ƙarfin gidan. Ma'ana dai duk talauci suna cin abinci sau uku a rana kuma iya gwargwado yana sauke duk wani nauyin gidansa da ya rataya a wuyansa. Yana da zafi sosai a kan ƴaƴansa musamman matan. Don bai yarda mahaifiyarsu ta aike su ba musamman da yamma. Ya gwammaci ko cefane idan ya dawo daga buga-bugansa shi ya karɓi saƙon ya sayo. Hakan ne ne ya saka yake musu mugun kulle. Mata daga makaranta boko sai ta arabi. Mazan kuma duk inda shida ta yi babu wanda ya isa ya fita.
Asalin tushen Malam Ayuba Sokoto ne (Maradun). Allah ne ya ƙaddari zamansa a Bauchi don a can ya yi almajiranci tun yana ƙanƙani. Tun daga almajiranci kuma sai garin Bauchi ya amshe sa da domin bai koma gida ba dama kuma uwa da uba duka ba su raye sai ƴan uwa. Yana dai zuwa lokaci bayan lokaci domin ziyara. Sana'a ya kama garin har Allah ya haɗa shi da Umaima suka ƙulla soyayya wacce ta kai su ga aure. Ita Umaima haifaffiyar nan garin Bauchi ce kuma bafulatana ce gaba da baya ta nan garin Bauchi kuma kyakkyawa doguwa. Gaba ɗaya ƴaƴanta mata ita suka yo. Maryama ita ce babbar ƴarta wacce ta kasance mai sanyin hali da biyayyar iyaye. Daga ita sai Sa'adatu. Itama yarinyar ce mai haƙuri da biyayya. Daga Sa'adatu sai Zinatu. Ita ta kasance tun tana ƙanƙanuwarta yarinya ce mai kafiya da taurin kai. Idan har ta ce baza ta yi abu ba, to kuwa babu uban da ya isa ya sa ta yi wannan abun duk irin dukan da za ta ci. Ga shegen kwaɗayi da kai kanta inda Allah bai kaita ba. Kasancewar maƙotansu suna da hali daidai gwargwado, sai ta riƙa hangen gidan tana kallon cimarsu da kuma suturarsu. Idan lokacin sallah ya zo, mahaifinsu yana iya ƙoƙari ya yi masu ɗinkuna kala biyu-biyu, hijjab ɗaya da takalmi ɗaya har da sarƙa da ɗan kunne na daidai aljihunsa. Amma da zarar sun saka sun fita ta hango na jikin ƴaƴan maƙota, sai ta dawo gida ta dasa ihu da kuka ita bata son wannan irin na jikin gidan su wance take so. Wannan dalilin ne ya saka basa ga maciji da mahaifinta ko kaɗan. Tsakaninsu hantara ce da kuma duka.
Zinatu tun tana ƙanƙanuwarta ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa mahaifinta kasancewar tsakaninsa da ita zagi da duka ne saboda halayenta sam ba masu kyau bane.
Kasancewar tsakanin Maryama da Sa'adatu babu nisa, sai suka taso kan su ɗaya. Zaka ɗauka ƴan biyu ne. Zinatu kuwa zaka ma ɗauka ita ce babba saboda tana da garin jiki. Sai duk suka taho a tare. Sosai Malam Ayuba ya ke nuna tsan-tsan soyayyarsa a gare su saboda yanda suke masa tsantsan biyayya da gudun maganarsa.
Maryama na da shekaru goma sha takwas, Sa'adatu kuma sha shidda, yayin da Zinatu ke da sha huɗu. Maryama mai shekaru sha takwas bata taɓa zance ba balle kuma Sa'adatu mai sha shidda. Amma Zinatu samarinta basu irguwa duk da kuwa ba'a sani ba a gida. Don duk haukarta sai dai ta ɓoye ta yi taɗin shima sai idan sun taso daga makarantar boko sai ta gudu ta ɓuya har ƴan uwan su gaji da neman ta su tafi ita kuma sai ta biye ta inda take tsayuwa domin zancen. Haka za su dawo gida mamar ta yi ta musu kumfan baki akan baro Zinatun a baya da suke yi. Idan ta dawo gida kuma ta dasa kukan ƙarya idan uwar ta nemi sanin dalilin jimawarta da kuma rashin haɗa hanya da ƴan uwan. Nan da nan za ta hau rantse-rantse akan tana can tana duba su ne. Duk wannan budurin da ake yi baban bai taɓa sani ba.
Bayan shekara ɗaya, lokacin Maryama da Sa'adatu sun kammala secondary, ita kuma Zinatu tana aji ɗaya ta babbar secondary wato _form 4_ sai ga mazaje har uku mahaifin ya fito masu da shi akan yayi masu miji. Hannu bibbiyu Maryama da Sa'adatu suka amshi mazan. Sai dai tun da Zinatu ta kyallara idanu ta ga wanda baban ya zaɓa mata matsayin miji ta ɗaura hannu a kai ta yi ta rusa ihu ita baza ta taɓa aurensa ba. Mummuna da shi kuma bai da ko sisi.
Maryama da Sa'adatu sun fahimci junansu da samarinsu amma ban da Zinatu. Wata rana da daddare mahaifin ya kira su duka domin jin ta bakinsu a kan mazajansu da ya zaɓa masu. Daga Maryama har Sa'adatu sun yi na'am. Amma Zinatu ana zuwa kanta ta buga tsalle ta dire ta ce bata ƙaunarsa. Ran malam Ayuba ya ɓaci sosai, amma sai ya danne ya ce to ya bata sati guda cur ta fito da miji don nan da sati Uku zai ɗaura masu aure.
Daɗi kamar zai kashe ta. Haka ta shirya bayan fitar Mahaifin ta caɓa kwalliya tare da nufa wajen da take zuwa domin taɗi da saurayin da ta cire a kaf samarinta don tafi sonsa kuma ya fi kashe mata kuɗi. Ko da taje ta kusa awa kamun ya iso. Bayan gama kashe ta da daɗin baki tare da miƙa mata ledan kayan kwalam ɗin da ya saba kawo mata sannan suka nufi ɗakin abokinsa ya biya buƙatarsa kamar yanda suka saba kullum suka haɗu. Bayan ya rakota, sun zo daidai inda suke rabuwa ta fuskancesa sannan cike da ɗoki ta faɗa masa yanda suka yi da mahaifinta. Nan da nan annurin fuskansa ya ɗauke. Cikin zuciyarsa ya shiga faɗin Wannan yarinyar amma jaka ce mara hankali. Allah Nagode maka da gobe-goben nan zan bar Bauchi na koma Kaduna inda na fito.
Ganin annurin fuskansa ya canza sai ta tambayesa mai yasa ya ɓata rai. Sai ya ce mata ba ɓata rai yayi ba mamaki yayi don dama abunda ya daɗe yana jira kenan. Bayan sun yi sallama, cike da farin ciki ta koma gida saboda ya faɗa mata gobe da yamma iyayansa za su zo.
_MATAR SAYYADEE_ *** [1/28, 8:38 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
*ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._