Page 8
Lokacin da mahaifinta ya dawo, har ɗaki taje ta faɗa masa gobe iyayen saurayinta za su zo. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce mata ta fita ya ji. Da murna ta fice daga ɗakin.
Washa gari kuwa tun bakwai na safiya saurayin nata ya hau mota ya bar garin. Baba kuwa ya tara mutane bayan magrib ya na jiran zuwan manema auran Zinatu amma shuru har a kai isha'i. Ransa ya gama ɓaci ganin har tara na dare ya wuce amma ko gittawar tsuntsu basu gani ba. A fusace ya shiga cikin gidan ya hau Zinatu da masifa kamar ya ari baki. Ita kuwa tuni hankalinta ya tashi. Baba na komawa domin ya bawa ƴan uwa da abokansa haƙuri, Zinatu ta silale ta fita domin neman Safiyanu. Sai dai duk inda take tunanin ganinsa babu shi a wajen. Hankali tashe ta nufi ɗakin abokinsa inda yake kai ta idan zai kashe ƙishirwarsa. Allah ya taimaka tana zuwa ta samu Saminu yana ƙoƙarin kulle ƙofa da kwaɗo. Saurin juyowa yayi saboda motsin da yaji.
"Ah! Zinah, Kar dai ace Safiyanu bai faɗa maki ya koma Kaduna ba yau da safe?"
Wani irin ƙamewa Zinatu tayi jin saukar maganar Saminu kamar saukar aradu a cikin masarrafar jinta. Wani irin juwa ya soma ɗibarta. A gigice ta kalli Saminu tare da faɗin, "Saminu bama irin wannan wasan da kai! Don Allah ina abokinka? Ya min alƙawarin zai turo iyayensa domin su zo neman aurena yau. Gashi yanzu goma saura babu wanda yazo."
"Caɓ! Lallai Safiyanu anyi ɗan iska na bugawa a jarida. To wallahi ƙarya yake maki. Iyayansa ma ba ƴan nan bane. Daga can ƙauyen Katsina yake. Ni na ji yana cewa ko Dabai ko Inaaa..... Gaskiya na mance sunan ƙauyen. Ko maƙotanku da kike gani yana zama a gidan wallahi taimaka masa suke yi. Shi ɗan ƙarya ne kawai! Almajiranci yake yi a nan ɗin shekaru can da suka wuce. To ya taɓa aiki a gidan suna ɗan bashi abinci da ihisani shiyasa kika ga kamar ya zama ɗan gida. Ganin sa kuma da kike yawan yi har kuka ƙulla soyayya; zuwa yayi domin su gaisa amma ko su mutan gidan basu san mahaifarsa ba." Hannu Zinatu ta ɗaura a kai tare da rushewa da kuka ta shiga faɗin, "Allah ya isa tsakanina da ku. Kuma sai Allah ya saka min. Da haɗin bakinka aka yaudareni." Tana gama faɗin haka ta wuce da gudu.
Wani dogon tsaki ya ja tare da faɗin, "Aikin banza aikin wofi! Kwaɗayinki dai ya ja maki. Dama ai ance duk wanda ya hau motar Kwaɗayi babu inda zata sauke sa sai a tashar wulaƙanci. Kuma ai dama kwaɗayi mabuɗin wahala ce! Sha-sha-sha sakarya."
Da sanɗa ta shigo gidan tana tafiya tana waige-waige. Fizgo hijjab ɗinta taji anyi da ƙarfi sannan akai ball da ita.
"Daga gidan uban wa kike a cikin daren nan? Duk cikin ƴaƴana kece fitinanniya wacce bata gudun zuciyata." Ya faɗi hakane yana mai kai mata duka da zabgegiyar bulalan hannunsa.
Ihu ta buga da ƙarfi tana mai sosa bayanta tare da turo baki.
"Ni zaki mayar mutumin banza? To bari kiji; Wallahi aure tsakanin ki da Mansur babu fashi, kuma sannan daga yau ko kwar gida ban yarda ki sake fita ba idan har nine mahaifinki. Dama ni na san babu wasu da zasu zo gidan nan neman aurenki. Kin ji na rantse da girman Allah idan kika sake kika bijiremin a karo na biyu, ko kuma kika watsa min ƙasa a idanu ta hanyar ɗauko min abun kunya, wallahi sai dai ki nemi wani gidan zaman ba nan ba. Mutuniyar banza mutuniyar hofi..." Ya mayar da kallonsa wajen mahaifiyarsu tare da faɗin, "Ke kuma Atine, idan kin ga dama kar ki saka mata idanu. Ki barta ta cigaba da fita tana gantali ana zagina a titi." Yana gama faɗin haka ya yar da bulalan ya wuce ɗaki.
Wawan harara uwar ta bita da shi tare da faɗin, "Ke dai Zinah ba kiji daɗin rayuwarki ba wallahi! Ke yanzu baza kiyi koyi da ƴan uwanki ba? Wallahi ki natsu ki kama kanki."
Tun daga wannan rana Zina bata ƙara samun sararin fita ba. Kullum tana ƙumshe a ɗaki tana kuka. Gashi bikinsu sai daɗa matsowa yake yi. Kullum da wani irin mugun zazzaɓi ta ke kwana. Ga wani irin miyau da ke taruwa a bakinta. Kasancewar mahaifiyarta fushi da ita take shiyasa ko bi ta kanta ba ta yi. Ƴarta Sa'adatu ce ta soma lura, sai dai ita ma bata fahimci ciki bane da ƙanwar tata har sai da ta samu mahaifiyarsu ta faɗa mata Zinatu fa bata da lafiya sosai sannan mahaifiyar ta nufi ɗakinsu domin duba ta.
Tana shiga ɗakin lokacin Zinatu ta tashi zaune, Maryama kuma ta miƙa mata ruwan da ta buƙata zata sha. Tana kai ruwan baki ta soma kelaye amai kamar zata amayar da hanjinta. Aman kuma kore shataf. Wani irin bugawa ƙirjin mamar tasu ya dunga yi tana ta ƙoƙarin ƙaryata abunta take zargi a zuciyarta. A hankali ta taka gaban Zinatu tare da buɗe kwayar idanunta ɗaya bayan ɗaya sannan ta jeho mata tambayoyi kamar haka;
"Zinah, abunda zaki mana kenan? Zina yaushe rabon da kiyi al'ada? Wani ɗan iskan kika bawa mutuncinki? Kin cuce mu! Wannan ba ita ce tarbiyyar da mukai maki ba. Kin cuce mu kin cuci kanki. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Ta faɗi tana mai rushewa da kuka.
Zinah kuwa hankalinta ne yayi mugun tashi jin kalaman da mahaifiyarta ke yi. Cikinta ya bada sautin ƙulululuuuu. Don sai yanzu lissafin ya faɗo mata; lokacin da ta fara bawa Safiyanu kanta, bata jima sosai da kammala al'adarta ba. Kuma tun daga wannan lokacin bata kuma yin wani ba. Kuma a ƙalla yanzu ya kamata tayi jini uku ko biyu.
"Na shiga uku ni, Zinatu. Safiyanu ya cuce ni ya gudu ya bar ni!"
Wani wawan mari mahaifiyarsu ta ɗauke ta dashi a baki sai da bakin ya fashe.
"Don ubanki da baki kai masa kanki ba, har gida zai zo ya miki cikin? Kin cuce mu Zinatu."
Wani irin juyawa suka yi duka su huɗun suna kallon bakin ƙofa jikinsu na rawa jin furucin mahaifinsu.
"Allah ya tsine maki albarka Zinatu. Allah ya hana ki jin daɗin duniya. Allah ya ɗaura maki bala'i da tashin hankali a cikin duniyar nan. Allah ya haɗa ki da masifa da bala'i. In Sha Allah baza ki taɓa ganin haske a rayuwarki ba. Ki tashi ki fitar min a gidana. Na cire ki daga cikin sahun ƴaƴana. Na yi maki rantsuwa da Allah duk na ƙara arba dake cikin gidana sai na kashe ki da hannuna. Kije duniya za ta koya maki hankali. Allah ya isa tsakanina da ke gwargwadon ciyar dake da nayi a cikin gidana tun kina tsumma. Abu mafi muhimmanci kuma; kar ki kuskura ki ƙara amfani da sunana matsayin mahaifinki. Ni ba ubanki bane. Abun kunya ne a gare ni idan har duniya ta san ni ne ubanki. Kije na yafewa duniya ke!"
Wani irin kuka Maryama, Sa'adatu da mahaifiyarsu suka fashe dashi. Da gudu Maryam ta kama ƙafar mahaifinsu tare da faɗin, "Abbanmu don girman Allah ka yafe mata. Bakinka a gareta dafi ne."
A fusace malam Ayuba ya ce, "Duk wacce ta ƙara bani haƙuri a cikin ku ƴaƴana in dai akan Zinatu ce, wallahi tallahi ban yafe mata ba. Ke kuma Atine, na ga bakinki rawa yake kina son nemawa ƴarki yafiyata, to ko da wasa kika kuskura kika roƙeni, wallahi a bakin aurenki. Kuma yanzu yarinyar nan ta fice min daga gidana."
Luuuuuu mahaifiyarsu ta tafi ƙasa ta sume. Maryama da Sa'adatu su kai kanta suna jijjiga. Zinah kuwa tunda ta ƙame waje ɗaya bata ko motsawa ba sai maganganun mahaifinta da ke mata amsa kuwa a masarrafar jinta.
Shuru-shuru mal Ayuba bai ga fitowar Zinah ba. A fusace ya fito daga ɗaki zuciyarsa na masa tuƙuƙin baƙin ciki ya nufi wajen tsohuwar injin ruwa da da yake niƙa kamun ya lalace ya finciko bulalan injin ya nufi ɗakinsu Zinah. Zagaye ya gansu sun saka mahaifiyarsu a tsakiya wacce ta zama kamar mutum-mutumi suna kuka. Zinah kuma na daga gefe ta haɗa kai da guiwa. Wani irin faɗawa ciki yayi ya shiga zubaba mata bulalan ta ko'ina a jininta yana haɗawa da shurin cikinta da ko'ina ya samu a jikinta.
Tun Zinah na ƙoƙarin karewa har ta miƙe ta fita da gudu zani a hannu daga ita sai pant ko underwear babu. Su Maryama da Sa'adatu biye da ita a baya suna kuka babu damar bawa mahaifin nasu haƙuri.
Har titi mal Ayuba ya bi Zinah yana duka yana zagi tare da tsine mata albarka. Jama'a sun taru sai kallonta ake gata ko zani babu a jikinta. Daga ita sai panta. Kanta babu ɗankwali. Mutane na jan mal Ayuba suna bashi haƙuri tare da nuna masa illar abunda yake aikatawa amma sai idanunsa sun rufe yaƙi sauraran kowa.
Wani irin tsanarsa tare da takaicin kasancewarta ƴarta ya dira cikin zuciyarta. A hankali ta duƙa ta ɗauki zaninta da Maryama dake kuka a kwar gida ta ba wani yaro ya cillo mata. Sai da ta ɗaura zanin jikinta sannan ta taka ta isa har gaban malam Ayuba da wani abokinsa Malam Ussaini ya samu nasarar riƙe sa ta ce,
"Billahil lazhi la'ilaha'illahuwa sai na zame maka bala'i. Kuma wannan sunan naka da kake matuƙar ƙauna sai na yi yaga-yaga da su. Sai na zama wata tantiriyar ƴa a duniyar nan kuma duk inda na je sai nuna kai ne wanda ya kwanta da mahaifiyata har ta samu cikina. Karuwanci kuma yanzu na fara, malam Ayuba. Mu zuba ni da kai!" Tana gama faɗin haka ta juya ta soma tafiya ba tare da ta waiwayi baya ba.
Zina daga nan bata zarce ko ina ba sai gidan karuwai da yayi ƙaurin suna dake nan jihar Bauchi. Kai tsaye ta samu jagora har wajen magajiyar gidan. Tana isa gabanta ta zube tare da ɗaura kanta a cinyar magajiyar ta dunga rera kuka. Magajiya bata ce mata komai ba kuma bata hana ta kukan ba. Sai da tayi mai isarta sannan magajiyar ta kama hannunta ta kai ta ɗakinta ta zaunar da ita tare da gabatar mata da abinci da ruwa. Bayan ta gama ci ta bata ruwan wanka ta je tayi sannan ta dawo ta kwanta saboda zazzaɓin da ya rufe ta. Cikin daren ranar Zinah ta soma wani azababben ciwon ciki mai tsanani wanda ya haifar mata da zubewar cikin dake jikinta. Sam ba haka Zinah taso ba. So tayi ta haife cikin sannan ta koma gida ta nunawa mahaifinta jikansa ko jikarta da ta haifa silar karuwanci.
Magajiya haka ta cigaba da kula da Zinah ba tare da ta tambayeta abunda ya baro ta daga gida har ta zo nan ba, duk da tana ji a jikinta silar cikin da Zinah tayi ɓarinsa ne dalili domin kaso casa'in na nuna cikin shege ne.
Sai bayan sati uku, lokacin Zinah ta gama warwarewa gaba ɗaya. Magajiya ta same ta har ɗaki ta tambayeta labarinta. Zinah bata ɓoye mata komai ba daga cikin labarinta. Sai ma ƙarin bayani da tayi mata na cewar so take ta zama shahararriyar karuwa. Sunanta ya buga tambari a lungu da saƙo na garin Bauchi.
Murmushi magajiya tayi bayan ƙarewa Zinah kallo ganin irin kyau da kuma diri da Allah yayi mata sannan ta ƙara mata kwarin guiwa tare da bata assurance akan sai ta cika mata burinta.
Haka kuwa aka yi. Domin cikin shekara ɗaya kacal Zinah ta zama wata shahararriyar karuwa. Domin duk wani saurayi da zaka gansa a gidan karuwai, to burinsa ya kwanta da Zinah wacce sunanta ya rikiɗe ya koma Laushi saboda yanda mata da maza suke kuranta laushin jikinta. Matan har tambayanta suke da wani mai take amfani. Murmushi kawai take yi don haka ita halittar jikinta yake da Laushi. Kuma a wannan gida suka haɗu da Ladi Katifa. Don tare suke tashe. Don ita ma tana kan cin nata duniyar. Ladi katifa irin masu maka-makan mazaunai ne da ƙirji. Wannan dalilin ne ya saka ake ce mata Katifa. Don haka samarinta suke faɗi jikinta tamkar gadone da Katifa ne a wajensu.
Yanda sunanta yake zaga garin Bauchi da kuma sunan mahaifinta da an sanshi sosai saboda sana'arsa kuma shi ɗin malamin allo ne ya saka duk inda Malam Ayuba ya gitta sai an nuna shi ana faɗin dube shi kamar na Allah, yana iƙirarin shi malamin tarbiyane amma ya kasa baiwa ƴarsa tarbiya tana can tana buga karuwanci. Tun ana yi a ɓoye, har ya zam ana faɗa a gabansa. Daga baya ma sai mutane da dama suka daina binsa sallah a masallacin da yake yi har hakan a ya jazo aka hana shi yin limanci. Zama waje yazo ya gagare sa. Hatta wajen sana'arsa wuyan zuwa yake masa. Hakan ya saka babu ranar da zata hudo ta koma bai tsinewa Zinatu yafi sau dubu ba. Maryama dake gidan miji kuma kishiyoyi sun hana ta sukuni da gori. Daga ƙarshe ma sakinta mijin yayi ta dawo gida ta zauna da ɗanyen goyo.
Mahaifiyarsu kuwa tsabar damuwa ya saukar mata da ciwon zuciya. Bata isa ta je gidan biki ba ko suna. Haka za ayi ta zunɗenta ana nuna ta da hannu.
Burin Zinah ya gama cika ganin yanda ta wulakanta mahaifinta don yazo ko fita bai iya yi. Hatta sallah a cikin gida yake yinta. Kuma tana samun labarin komai daga bakin jama'a. Hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba.
Laushi ba zata taɓa iya ƙidaya adadin mazan da ta kwanta da su ba. Wasu ma ba ƴan jihar bane zuwa kawai suke yi. Ba ƙaramin kuɗi take kamawa ba. Sai dai kuɗin kamar ana cinna masu wuta. Nan da nan sun ƙare. Ciki kuwa ta cire babu adadi. Domin tana fahimtar tana ɗauke da juna biyu take cirewa saboda huɗubar da magajiya tayi mata akan idan ta yarda ta haihu kasuwarta zai yi ƙasa domin jikinta zai lalace.
Bayan shekaru huɗu, kwatsam sai ga ciki a jikinta wanda ko wuƙa aka ɗaura mata a wuya baza ta iya nuna uban cikin ba saboda adadin mazan da ta kwanta da su ba masu ƙidayuwa bane. Kuma ikon Allah babu yanda ba'a yi ba cikin ya fita amma yaƙi.
Wata rana Ladi Katifa da Laushi suna zaune suna hira, lokacin cikin jikinta watansa bakwai. Ladi Katifa ta ɗauko mata labarin Hajja Lanti da kuma zaman da tayi a Lagos na shekara ɗaya zuwa biyu. Nan da nan Laushi ta gigice taji tana son zuwa garin saboda yanda Ladi Katifa ke nuna mata irin kuɗin da ake samu idan mutum yayi dace.
"Katifa don Allah mu tafi Lagos ɗin nan. Don Allah ki kai ni," Faɗin Laushi.
Zaro idanu Ladi Katifa tayi tare da faɗin, "Zaman Legas fa ba wasa bane. Don wallahi ba kamar nan bane. Dole sai mutum ya rike kuɗi a hannunsa."
Shuru Laushi tayi na wasu ɗan lokaci kamun ta ce, "Kamar nawa kike ganin zamu riƙe?"
"Kin ga kuɗin mota kawai dubu uku ne (Kar a manta a shekarar 1999 ake a wancen lokacin) sannan za mu riƙe kuɗi domin cin abinci a hanya. Sannan ga kuɗin haya da zamu kama a gidan Hajja Lanti. Ga hidimar kayan abinci kamun ki haihu ki fara sana'a." Faɗin Ladi Katifa.
Dafa ta Laushi tayi tare da faɗin, "Ki bar mi komai a hannuna. Nan da wata biyu muna garin Legas. Kuma maganar nan ta tsaya tsakanin mu. Ko magajiya ban so ta sani."
Gyaɗa mata kai Katifa tayi tare da ɗauko wani zancen suka cigaba da hira.
Kamar yanda Laushi ta faɗi, bayan wata ɗaya da sati biyu ta samu Katifa tare da faɗa mata shirinta na zuwa gida domin ɗauko sarƙar zinarin da mahaifinta ya saya bayan sayar da gonarsa da yayi a can Zamfara. Da farko Ladi Katifa bata bata goyan baya ba. Amma kuma daga baya sai ta amince bayan ita ma ta saka nata ƙaramin gidan da ta tara kuɗi ta saya a kasuwa.
Ranar Sati Laushi ta tattara ta tafi gidansu bayan samun labarin mahaifinta yayi tafiya. Lokacin da mahaifiyarta ta ganta harda suma tayi. Bayan ta farfaɗo ta rungumeta tana kuka tana roƙonta akan kar ta ƙara tafiya ta barta. Kamar da gaske itama Laushi tayi ta kuka tana nadamar ƙarya. Ƴan unguwa kuwa sai leƙe suke kasancewar sun gan shigar Laushi gidan da ƙatoton ciki.
Ita kuwa Laushi cikin dabara da tsabar makirci ta samu nasarar ɗauke sarƙar da babanta ya bawa mahaifiyarta ajiya. A cikin tsohon kwallar mahaifiyar tasu ta ɗauko kasancewar ta san anan mahaifiyar tasu take ajiya mai mahimmanci.
Malam Ayuba kuwa Jos yaje. Kuma dama kwanansa ƙila wa ƙala ce. Yana gama abunda yaje yi ya juyo. Cikin dare ya shigo don ɗaya saura na dare. Tun a hanya mutane suka soma shaida masa dawowar Zinatu da tsohon ciki. Namar jikinsa har rawa yake yi ya nufi gida. Yana shiga kai tsayi madafi ya nufa ya ɗauko sharɓeɓiyar wuƙarsa ya nufo ɗakin matarsa inda yake da yaƙinin Laushi na can.
Suna zaune gaba ɗaya duk da dare yayi sosai amma sun kasa bacci musamman mahaifiyarsu da babu abunda gabanta ke yi sai faɗuwa. Ita kuwa Laushi Allah-Allah take suyi barci ta samu ta sulale tunda ta samu abinda tazo nema.
Burum suka ji an turo ɗakin. Gaba ɗaya suka miƙe a gigice ganinsa da kaifaffiyar wuƙa a hannu. Gadan-gadan yayi kan Zinah yana faɗin, "Dama na faɗa maki duk ƙafarki ta kuma shigowa cikin gidan nan sai na kashe ki!"
Da sauri mahaifiyarsu ta shiga tsakani tare da ware hannayenta tana kuka, "Don girman Allah Abban Maryama kai haƙuri kabi komai a sannu."
Wani irin hankaɗata yayi tare nufa kan Zinah yana faɗin, "Sai na kashe ki yau." Tare da kai mata wani irin suka tayi saurin kaucewa. Kuma kai mata yayi sai Allah ya bata nasarar cafkar hannunsa suka hau kokawa har Allah ya saka ta burma masa wuƙar a ciki. A tare suka saki wani irin ihu.
Zinatu jikinta babu inda bai rawa ganin wuƙar a cikin mahaifinsu jini na malaman. Maryama take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa sumamma. Dama kuma ita mahaifiyarsu tun jifar farko da malam Ayuba yayi mata ta sume. Ganin haka Laushi ta ɗauki hijjab ta saka jikinta na rawa ta fito cikin daren domin guduwa. Washa gari kuma suka gudu Lagos ita da Ladi Katifa.
_Wannan shine taƙaitaccen labarin Laushi._
*Sorry for the late update*🤫
*_Matar Sayyadee_* *** [1/28, 8:38 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._