Page 9
*_Bogotá (Colombia)_*
Su shidda ne cif. Huɗu maza sai mata biyu da suke cikinsu. Matan sanye suke cikin wando jeans baƙi sai riga mai gajeren hannu. Farar ciki mai wani spot a gefen hanci ita ce mai sanye da pink ɗin riga. Kyakkyawa ce sosai, gashin kanta irin curly hair ɗin nan ne kalar baƙi siɗik tayi masa style ɗin side braid ponytail.
Ita kuma ɗayar baƙa ce sosai, kyakkyawar gaske kuma doguwa. Tana da dogon hanci wanda yayi kyau da fuskanta. Idanunta sunfi komai ɗaukar hankali a fuskanta. Farare suke ƙal-ƙal. Baƙinta ɗan ƙaramin mai ɗauke da laɓɓa masu ban sha'awa kasancewar su pink. Tana da ƙirar jiki kamar ita ta halicci kanta. Gashin kanta wavy ne, shi ba ja ba, shi kuma ba maroon ba ta yi masa waterfall braid style. Farar riga ce a jikinta amma iri ɗaya ne da na jikin ɗayar sak. Bambancin su launi ne kawai.
Suma mazan riga da wando ne a jikinsu sai jacket da wani hula mai gashi da suka ɗaura a kai. Tafiya suke a jere sannan gaba ɗayan su a ankare suke. Sun zo wajen wani T junction sai suka rabu bibbiyu. Wannan baƙar suka bi hagu ita da dogon cikin samarin. Ita ma ɗayar tabi ɗaya daga cikin su. Sauran mazan biyu suma su kai hanyarsu daban. Baza ka taɓa tunanin tafiyarsu ɗaya ba.
A daidai wani shago suka tsaya su biyu, baƙar da dogon saurayin amma kowa yana ɗaya side ɗin a kofar shagon. Kallonta yayi tare da yi mata alama da idanu, ita kuma tayi saurin ɗaga ƙafa ta harbi kofar ta buɗe. Shi kuma yayi saurin pointing ƙofar da bindigar dake hannunsa.
"Leonardo! Please, remember you're my very close friend," faɗin saurayin da yayi saurin miƙewa tare da ɗaga hannunsa biyu sama yana kallon su a tsorace.
"Mai yasa za kai haka, Carlos? Kasan wacece Esmeralda. Idan har kaci amanarta duk inda ka shiga sai ta nemo ka ta kashe ka. Mai yasa zaka kawo ƙarshen rayuwarka da kanka?" Gaba ɗaya maganar da yaren Spanish yayi kuma still be daina pointing masa gun ɗin ba.
Duƙawa yayi tare da fashewa da kuka ya shiga faɗin, "I want to be free, Leonardo. Na gaji da bautan nan. Ina son inyi nesa da Colombia tare da iyalina. Suna buƙatata a kusa dasu. I have to take this risk," da harcen turanci yayi maganar, daga baya ya juya Spanish sai kuma ya ƙarƙare da turanci.
Yatsa ta saka a baki, sai kuma ta ciro ta ɗan yi taku biyu zuwa gaba da baya sannan a fusace ta ƙarisa gaban Carlos ta shaƙi wuyansa tare da faɗin, "We're all tired, Carlos! But none of us try to do something foolish like you did. Baka tunanin halin da Isabella zata shiga. What about your little son Nicolas? Esmeralda will never rest until she kill you. Ko ina mutananta ne ke dubaka. Kuma ka san duk wanda yayi arba da kai apart from us, harbinka zai yi," da turanci ta fara maganar ta ƙare da Spanish.
"Keep the gun down, Leonardo!" Faɗin Carlos ganin har wannan lokacin bai sauke bindigar ba.
Miƙewa Lulu tayi tare isa wajen Leonardo ta ce, "Keep the gun down," ta faɗi hakane tare da sauke hannunsa ƙasa. Sai dai from nowhere suka ji ƙarar harbi, kuma bai sauka a ko ina ba sai a cikin Carlos. Cikin daƙiƙa guda ya faɗi jini na malama.
Da sauri suka juya baya a gigice, arba su kai da; Diego, Alejandro, Mateo da kuma Isabella. Kuma dama tafiyarsu ɗaya rarrabuwa su kai a hanya.
Da mugun gudu Isabella ta nufo wajensa tana faɗin, "Caaarloos!" Guiwowinta biyu ta zube a ƙasa tare da tattarosa zuwa jikinta tana wani irin kuka tare da jijjigasa.
Lulu kuwa a fusace ta nufi Alejandro da shi ne yayi harbin ta wanke fuskansa da mari tare da faɗin, "How dare you. Who ordered you to shoot him you son of a bitch!!" Ta ƙarisa maganar a matuƙar hargitse.
Da mugun sauri Leonardo ya shiga tsakaninsu ganin yanda Alejandro ya fusato alamar zasu raba hali kamar yanda suke yi duk suka haɗu waje ɗaya.
Hannun Isabella dake kuka Carlos yayi tare da faɗin, "cuidar a nuestro hijo (Take care of our son)".
Wani irin ihu kuka Isbella tayi tare da faɗin, "no me dejes. no puedo vivir sin ti. no me hagas esto! (Kar ka bari, bazan iya rayuwa babu kai ba. Kar ka min haka!).
"Siempre estarás en mi corazón y siempre te amaré (you will always be in my heart and I will always love you)" Carlos ya faɗi yana mata murmushi.
"y siempre te amaré también (And I'll always Love you too)" cike da gurnanin kuka ta faɗi hakan.
"Mira muy bien cuidando a nuestro niño. Te amo. (Ki kula da yaron mu sosai. Ina sonki!" Yana gama faɗin haka rai yayi halinsa.
"No, no me hagas esto! Carlos, Carlos, Carlossss!!" Wani irin kuka take yi tana dukan cikinsa jini na tsartuwa a fuskanta.
Da gudu Lulu da itama kukan take yi ta ƙarisa wajenta ta riƙo hannunta tare da rungumeta a jikinta tana faɗi, "Lo siento, Issabella. Lo siento (Sorry Issabella, sorry)."
Wani mahaukacin ƙarar harbi suka soma ji ta ko ina. Da sauri Leonardo ya ce, "Lulu, Isabella, La policía viene. Corre por tu vida. (Police are coming, run for your life)."
Da wani irin mugun sauri, Lulu ta fizgi hannun Isabella dake ciccijewa alamar baza ta bisu ba. Ta window suka dura suka soma wani irin gudu hukumar NDLEA na ƙasar na bin su suna harbi. Ko sau ɗaya Lulu bata yarda ta saki hannun Isabella dake kuka tana faɗin Carlos ba. A wajen wani dogon katanga suka tsaya gaba ɗayan su. Leonardo ne ya tsuguna, Diego ya taho da gudu ya taka tafin hannunsa da kafaɗansa yayi tsalle ya kama katangar ya dira sannan yayi saurin janyo ladder ya ajiye. Lulu ta tura Issabella, ita ma ta yi kamar yanda Diego yayi. Haka sauran ma suka yi ya rage daga Lulu sai Leonardo. Hango hukumar suna ƙarisowa Lulu ta yi wani irin tsalle ta taka hannun Leonardo ta hau katangar sannan ta duƙa tare da miƙawa Leonardo hannu. Tsalle yayi ya tattaka bango ya kama hannunta, sai da suka yi kamar za su faɗo ƙasa duka Allah dai ya kiyaye. Ya hau katangar da kyau daidai lokacin police suka ƙariso tare da soma sakin uban harsashi.
Wani ihu Leonardo ya saki sakamako harbin kafaɗansa da aka yi. Amma duk da haka sai da ya dira. Rungumosa Lulu tayi suka hau gudu. A gabansu mota Bus tayi parking su kai saurin shiga bayan Isabella dake ciki ta buɗe.
Wani irin mahaukacin gudu suka shiga kwararawa ganin har wannan lokacin police basu haƙura ba. Dakyar suka ɓacewa ganinsu sannan suka ɗauki hanyar mazauninsu.
Daga cikin ana ganinsu aka yi saurin buɗewa. Wani wuri ne kamar garage. A ciki a kwai wani ƙaramin ƙofar da zai sadaka da ainahin cikin wajen. Ba ƙaramin girma wajen yake dashi ba. Irin tsarin wajen kamar Prison haka yake. Mutane ne babu adadi a ciki maza da mata yara da manya. A kwai wani ƙatoton cage da aka zagaye shi da iron wire, nan ma mutane ne a ciki da yawa. Babu abunda ake yi a wajen sai harkar Cocaine.
Lulu ita ke riƙe da Leonardo wanda hannunsa ke zubar jini sosai. Da sauri ta saka hannu ta watsar da kayan dake kan table ɗin ta kwartar da Leonardo a kai sannan ta saka hannu ta tattare gashin kanta ta ƙulle. Farka rigar jikinsa tayi sannan ta karɓi wani abu mai kama da wuƙa a hannu Isabella dake miƙa mata tare da kwalbar giya. Giyan ta fara tuttulawa sannan ta saka wannan ƙarfe ta fara ɗago namansa ta luma ƙarfen sai da Leo ya saki wani mahaukacin ƙara daidai lokacin da ta fiddo bullet ɗin waje. Ihu kawai yake yi yana jijjiga kansa.
"es doloroso verdad? Lo siento, lo siento. (Akwai zafi ko? Yi hakuri, yi haƙuri)." Ta faɗi tana mai cigaba da dressing hannun....
_Za ku ga kamar mun sauka akan labarin zuwa wani labari wanda sam ba haka bane, idan kuka bini sannu a hankali zaku fahimta_
*MATAR SAYYADEE* *** [1/28, 8:38 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._