My Destiny (Ƙaddarata)

Page 10

by @matarsayyadee3

Nishi sama-sama Leonardo kawai yake yi saboda azabar da yake ji a kafaɗarsa. Lulu kuwa ba tare da tausayi ba tayi masa dressing hannun sannan ta saka bandage ta ɗaure wajen daidai shigowar Esmeralda, bayanta kuma bodyguards ɗinta ne kowanne rik'e da bindiga. Sanye take cikin wani pepper red mini skirt, sai top mai hannu ɗaya. Ƙafarta sanye da wani dogon takalmi mai tsini, hannunta kuma riƙe da wani dogon sigari tana zuƙa. Gaba ɗaya mutanan dake cikin wajen suka nutsu, hatta Leonardo dake kwance yana fama da kafaɗarsa, miƙewa yayi zaune.

Esmeralda jefar da guntun sigarin hannunta da ya rage tayi tare da takewa da ƙafa sannan ta soma nufa inda Isabella take. Gaban Issabella da Lulu babu abunda yake yi sai bugawa da ƙarfi. Tana isa wajen ta damƙi gashin Isabella da ƙarfin tsiya ta hau janta ƙiiii. Ita kuma Isabella riƙe hannun Esmeralda ɗin tayi tana ihu tare da faɗin, "Ki taimake ni, Lulu." Cikin harshen spanish.

Cikin sauri Lulu ta yunƙura amma sai Leonardo dake kusa da ita yayi saurin cafkar hannunta yana girgiza mata kai.

Sai da Esmeralda ta buga kan Isabella da bango sau uku sannan ta ce, "Me kuke shiryawa ke da mijinki? Faɗa min!" Da harcen spanish ta faɗi.

"I swear to my life, Esmeralda.... I knew nothing!" Isabella ta faɗi da harshen turanci.

Ƙara buga kanta tayi da table ɗin da aka daura Cocaines a kai sannan ta kuma faɗi a kausashe, "You're planning to take me down, your betrayers! I will not spear your lifes if u didn't open up." Ta ƙarisa maganar tana mai ɗaura mata bindigar da ta karɓa a hannun ɗaya daga cikin bodyguards ɗinta.

Da mugun sauri Lulu ta ƙarisa wajen Esmeralda tare da faɗin, "Escúchame por favor, Esmeralda.(ki saurareni don Allah, Esmeralda.)"

Wani tsawa ta daga mata tare da faɗin, "Lulú, no interfieras. (Don't interfere)" tana gama faɗin haka ta kyasta hannu, sai ga wani dogo black american hannunsa riƙe da hannun yaron Isabella mai suna, Nicolas.

Da rarrafe Isabella ta nufi Nicolas amma Esmeralda bata bari ta ƙarisa ba ta taka mata ƙafa da dogon takalmin ƙafarta mai tsini sai da ta saki ƙara mai ƙarfi.

"mamá!" Nicolas ya kwaɗa kiran sunanta da ƙarfi sannan ya fizge daga riƙon da Andrew yayi masa ya nufo uwar tare da rungumeta kuma har a wannan lokacin Esmeralda bata cire ƙafarta a cinyar Isabella ba.

"I swear to my life, Isabella knew nothing. I know what you're trying to do, but I'm begging you in the name of God don't do it. Don't kill Isabella and her only child," faɗin Lulú.

A hankali Leonardo ya furta, "Mamacita! Stay out of this." Shi kaɗai ya jiyarwa kansa abunda ya faɗi. (Mamacita na nufin "little mother" or "hot mom).

A hankali Esmeralda ta nufo har gaban Lulu dake jin gabanta na bugawa tamkar zai faso ƙirji. "Favour again? For what price??" Ta ƙarisa maganar tana ɗago haɓarta.

Shuru Lulú tayi for some seconds kamun ta ce, "Qué querías que hiciera Esmeralda? (Mai kike so nayi, Esmeralda?)"

Wani murmushi Esmeralda tayi tare da kallon Diego dake next to her. Da sauri ya jawo ƙaton table ɗin da gefe, samansa kuma Cocaines ne da yawa a cikin ƙananan farin ballons an nannaɗe guda arba'i. Girgiza kai kawai Leonardo yake yi cikin zuciyarsa yana faɗin, "No lo hagas mamacita (ma'ana kar kiyi haka Mamacita).

Wani irin numfashi Lulu taja tare da nufa wajen da Cocaines ɗin suke don ta riga da ta san mai zata yi. Cikin saurin ba tare da ta kalli inda Isabella take ba duk da irin kwala mata kiran da take yi, ta soma haɗiye cocaines ɗin nan. Sai da ta haɗiye guda ashirin sannan Esmeralda ta ɗaga mata hannu tare da faɗin, "Diego will accompany you," tana gama faɗin haka tsam Leonaldo ya ce, "I'll go with her."

Wani kallon banza ta masa bayan ta kalli ciwon dake kafaɗansa, ba tare da furta komai ba ta nunawa Diego sauran Cocaines ɗin nan guda ashirin da idanu. Cikin sauri shima ya haɗiye duka.

"Mexico!" Esmeralda na gama faɗin haka ta ajiyewa Lulú passport ɗinta a kan table ɗin sannan ta miƙawa Diego nasa tare da juyawa ta nufi wani ƙofa bodyguards ɗinta suka rufa mata baya.

"I'll go with you, Lulu," Faɗin Leonardo yana mai riƙe kafaɗansa da hannun da ke da lafiya.

Girgiza kai Lulú tayi tare da dukan ƙafaɗansa mai lafiyar ta ce cikin harshen spanish, "Kar ka damu. Zan je lafiya in dawo. Ka kula da kanka!" Tana gama faɗin haka ta nufi Isabella dake rungume da ɗanta. Shugunawa tayi tare da faɗin, "Be strong, Isabella. I'll be their for you. Take good care of Nicolas." Ta faɗi haka tare da miƙewa ta shafi kan Nicolas ɗin sannan ta ɗau wani baƙin jacket dake rataye ta saka ta nufi waje, Diego a bayanta riƙe da makullin mota.

*_Mexico_*

It's four hours fourty-four minutes journey tsakanin Colombia da Mexico by flight. Suna sauka a airport suka fito kasancewar masu Cocaines ɗin sun san da zuwansu. Baƙar tinted jeep suka gani a waje. Kai tsaye wajen motar suka nufa, Diego ya zauna a mazaunin driver, ita kuma Lulu ta zauna a gaba tare da saka yatsanta a baki tana tunani. Ba suyi wani mugun nisa ba suka fahimci Lulu ta fahimci ana binsu a baya. Da sauri ta kalli bayan sosai ta cikin glass sannan ta kalli Diego tare da faɗin, "Damm it! Someone is following us."

Saurin kallon mirror Diego yayi domin ya tabbatar. Kwanar hagu ya shiga domin kaucewa mai bin nasu, sai dai a cikin ƴan daƙiƙu shima mai motar ya sha kwana. Taka motar Diego yayi sosai ya hau gudu. Shima mai motar nan take ya hau kwarara gudu yana binsu.

Wani irin gudu suka shiga shararawa a kan titi suna yiwa mutane ɓarna. Bindiga mai jar motar ya fiddo ya sai ta tayarsu ya harba bayan ya harbi glass ɗin bayan motar tayi kwatsa-kwatsa don sai da wani glass yayi tsalle ya yanki damtsen hannun Lulu.

Lulu ɗaukar pistol ɗin dake cikin bonet ɗin mota tayi itama ta hau harbi har tayi nasarar harbin tayar motar mutumin. Wani irin juyawa motarsa tayi daidai lokacin da tasu motar ta tsaya cak saboda fitar da tayar gaba tayi.

Da sauri Lulú ta buɗe murfin mota ta fito ta hau gudu, shima Diego abunda yayi kenan ganin shima na cikin motar ya fito hannunsa riƙe da bindiga yana binsu.

Gudu suke yi kamar za su tashi sama. Sunan shiga wani layi mai ɗunbin jama'a suka rabu ita da Diego. Sai dai kamar ance ta juya ta hangi wannan mutumin yana binta da gudu kuma ya kusa cimmata.

Wani irin tsalle tayi tare da kama wani dogon ƙarfe ta soma hawa har ta kai kan wani kwano ta dira cikin wani ɗaki ta window. Wasu family ne ke cin abinci. Ganinta kwatsam duk suka miƙe suna kallonta ganinta riƙe da bindiga.

Kallo ɗaya tayi masu tayi saurin nufa ƙofa ta buɗe. Sai dai tana buɗewa taji saukar wani naushi a kan hancinta sai da jini ya zubo. Nan wani irin dambe ya harmutse tsakaninsu. Ba ƙaramin ɗauki ba daɗi su kai ba a cikin parloun jama'a. Gashi gaba ɗayansu sun samu atisayi mai kyau. Duk da kasancewarta mace amma ba ƙaramin faɗa ta iya ba da kuma kariya. Duk sun ji jiki, barin ma saurayin don ba ƙaramin duka take kai masa ba kuma babu abunda yake yi sai kariya.

Wani irin duka ya sauke mata da ƙafarsa a kan gefen wuyanta wanda ya saka ta tafi luuuu ta faɗi a kan bindigarta da tun dukan farko da yayi mata a kan hanci ya faɗi. Sai dai kamun tayi kicking har ya rigata yin kicking nasa bindigar tare da pointing mata a kai. Nan take ta ɗaga hannayenta sama tana kallonsa. Wani irin luuuu ta tafi sakamakon dukan da yayi mata a kai wanda ya saka ta sume nan take.

Saɓata yayi a kafaɗarsa tare da fita da ita daga parlourn ya saka ta a bayan mota bayan ya ƙulle mata kafa da hannu.

Watsa mata ruwa yayi a fuska wanda yayi sanadiyyar farfaɗowarta daga suman da tayi. Wani irin wahalallan nishi ta saki tare da ware manyan idanunta tana kallonsa dishi-dishi yana haɗa electric shocking wears.

"You again! Kwanceni nace maka yanzun nan!!" Ta ƙarisa maganar da ƙarfi cikin harshen spanish.

Wani kallon banza ya watsa mata kamun ya tako gabanta ya tsinke ta da mari sai da kumatunta su kai rawa sannan ya ce, "Who is your Master/Mistress, joung lady?"

Miyau ta tufa masa a fuska tare da faɗin, "I rather die than telling you the truth. Just go ahead and kill me." Faɗin Lulú.

Wayarta da yayi ƙara a aljihunta ya saka hannu ya fiddo kasancewar a ƙulle take jikin kujeran da take zaune. Video ne aka tura mata.

"Lulu, please help us. She went with Nicolas, I don't want to loose my only child," tana gama faɗin haka aka ɗaurata a kan wani table tare da tsira wata allura wanda irin ihun da tayi sai da inda take ya ɗauka. A hankali idanunta ya soma rufewa, muryanta ciki-ciki ta furta, "Take care of Nicolas, Lulu. Goodbye." Tana gama faɗin haka ta rufe idanu.

Nan da nan mazan da fuskansu ke a rufe cikin video ɗin, ɗaya daga cikin ya saka wuƙa ya farke cikin Isabella ya shiga yamutsa hannunsa a ciki yana fiddo Cocaines ɗin da suke cikinta.

Wani irin jijjiga Lulu ta hau yi tana wani irin ihu tana kuka tare da kiran sunan Isabella da ƙarfi don tana ganin komai dake cikin wayar. Kuka take yi tana matsowa gaba kamar zata haukace still tana kiran sunan Isabella. Fita daga video ɗin yayi daidai lokacin da message ya shigo wayar. Buɗe message ɗin yayi ya soma karantawa kamar haka a bayyane; _The life of the little child is in your hand, Lulu. Tell him about me and my business, and I promise to skin the little poor child alive_

Kuka sosai Lulu take yi kamar ranta zai bar jikinta, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allahuma arji'ini fi musibati, wa aklifni khairan minha!" Shine abunda ta hau nanatawa wanda hakan ya daskarar da shi a tsaye.

Da sauri ya juyo tare da faɗin, "What did you just said? Did I hear you right?" Mamaki sosai a fuskansa.

Ko kulasa bata yi ba sai kukanta da ta cigaba tare da soma ƙoƙarin kakari ga kuma idanunta da suka kaɗa su kai ja kuma suka soma alamun rufewa. Ƙirjinta sai wani irin ɗagawa suke. Da kyar ta iya nuna cikinta ta furta, "I swallowed cocaines!"

Da wani irin sauri ya ɗauki goran wani liquid ya buɗe bakinta ya soma tuttula mata. Cikin second biyu ta soma wani irin amai mai tafe da Cocaines ɗin da ta haɗiye. Ta fitar da guda goma sha tara saura ɗaya. Alama ta riƙa masa da hannu akan saura guda ɗaya. Amma yaƙi fitowa.

Ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba su duka suna tunanin ɗayan ya fashewa wanda babu makawa idan hakan ne mutuwa za tayi. Wani irin yunƙuri ta kuma yi a karo na ƙarshe, sai ga ɗayan ya fito.

"Alhamdulillah!" Ya furta yana mai riƙe kansa da hannun biyu. Ya kusa mintuna biyar a haka kamun ya kwance mata ƙafa da hannun, don ya san babu ta yanda za ta iya guduwa a halin yanzu.

Sai bayan shuɗewar mintuna ashirin sannan Lulu ta ce, "Na roƙeƙa da girman Allah ka barni na kai saƙon nan na koma Colombia. I promise you ina yin nasarar ɗauko Nicolas zan kawo maka kaina har inda kake."

Wani kallo yayi mata sannan yayi murmushi tare da faɗin, "Where are you from? I mean your Nation."

Sai da ta ɗau mintuna kamun ta ce, "From Lagos, Nigeria.

Wani irin kallo yayi mata cike da mamakin wai she's from Nigeria sannan ya ce, "Tell me more about yourself, Lulu." Ya ƙarisa maganar yana folding hannunsa.

"My real name is Faridat also known as _Meema_. (Cikakken sunana Faridat wacce aka fi sani da Meema.) I was born and raised in Lagos. (An haife ni tare da rainona a garin Lagos) My mother.....(Tana kawowa nan ta rushe da kuka kamun ta cigaba) she's real definition of prostitution..........."

Back to labarin Laushi.......

_MATAR SAYYADEE_ *** [1/28, 8:38 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._