Page 11
"Laushi, yanzu dai na lura ban isa dake a cikin gidan nan ba tunda wuyanki yayi kwari. Lallai! Kamar ni a cikin gidan, in aiko Salma nice ta miki jagora zuwa gidan Alhaji Shafi'i, amma sai ki aiko min da maganar banza ni, Laushi?" Faɗin Hajja Lanti.
"Hajja, magana ta gaskiya fa komai yanzu don samu ake yinsa. To to minene a jikin Shafi'i? Haba! Mai na ƙasa yaci bare ya kaiwa na sama? Sam Shafi'i ba sa'an yina bane. Banƙi ba dai ko ƴar sita ko kuma Katifa ba... Kai ko Katifa tafi ƙarfin Shafi'i wallahi. Mutumin da ko Nijar bai taɓa ƙetarewa ba, caɓ! Ba dani za ai wannan iskancin ba." Ta ƙarisa maganar tana mai zana kwalli a ƙasan leɓanta tare da haɗe leɓen ta murza.
"Eh, lallai! Na ƙauye an shigo birnin. To wallahi dani kike zancen, kuma sai na ɓata miki rai cikin gidan nan." Ta ƙarisa maganar da kwafa tare da barin wajen daidai shigowar Meema sanye da doguwar rigar boko, kanta kuma Barrett ne an karkata shi gefe. Lemon green ce rigar mai zane-zanen farin kala. Hular ma lemon green ce. Jakar baya baƙa mai hoton Tom and Jerry goye a bayanta sai farar safar ƙafa wanda ke cikin brown ɗin sandal ɗin dake ƙasarta. Sosai kayan ya haskata kasancewarta baƙa kuma sun yi matuƙar yi mata kyau. Amma fuskan nan a murtuke take tamau.
"Ke kuma uban minene kika tsaya min a kwar ɗaki fuska a ɗaure? Kuma ubanki ne ya saya min labulen da kike takawa da takalmi?" Faɗin Laushi.
Da sauri Meema ta ɗaga labulen da bata san ta taka ba tare da kai hannu ta cire sandal ɗin ta ajiye a ma'ajinsa sannan ta cire safar ta saka ɗaya cikin ɗaya ta ajiye a kan wani ƙaramin basket tare da cire jakar bayan dake goye a bayanta ta rataye jikin wani ƙusa sannan ta ƙarisa wajen mahaifiyar tata tare da faɗin,
"Ina wuni aunty Laushi? Na dawo daga school," Meema ta faɗi respectfully cikin zazzaƙar muryanta.
Harara Laushi ta zabgata mata tare da faɗin, "To uban minene kike wani ɗaure fuska? Kuma ga hawaye nan yana taruwa a idanunki."
Meeman kamar jira take sai ta fashe da kuka sosai tare da soma magana cikin in'ina, "Ba Kayinde ajinmu bane ya tara yara suna ta tsokanata wai ba ni da uba kuma wai ke karuwa ce. Nace karya ne ina da uba shine Tola ya ce idan ina da Baba mai yasa a school nake amfani da Faridat Zinatu Laushi," ta ƙarisa maganar tana shashsheƙar kuka.
"To! Zo nan muje gidansu. Wallahi ko ɗan _Oduduwa_ ne shi sai na ci uban ubansa. Kaji min ɗan kafurar yaro," faɗin Salma Nice (Salmu ɗan daudu) wanda zuwansa ƙofar ɗakin kenan yaji abunda Meema ke faɗi.
Ita kuwa Laushi, taɓe baki tayi tare da hararar Meema sannan ta mayar da dubanta ga Salma ta ce, "Kinga, Salma kyale wannan shiriritar ki raka ni ƙarbo ƙayana a Ajegunde. Ke kuma, mayya idan kin gama gulmar ga abincinki can cikin tukunya sai ki ɗauka kici kuma kar in sake in dawo inga kin yi min ɓarna ko kuma ki ɗibar min madarar da ba ubanki ya kawo ba ko kwaɓa da suga kina lasa kamar tsohuwar mayya. Muje, Salma," faɗin Laushi tana mai miƙewa tare da kakkaɓe gyalenta.
"Ehh lallai! To bari kiji Laushi, wallahi idan har kika ga na ɗaga ƙafafuna na rakaki gantalin karɓo kwayoyinki da kayan maye, to na karɓowa Meema ƴancinta wajen ƴan iskan yaran yarabawan can," faɗin Salma Nice.
"Ke! Kar ki saki ki zagi yarabawa domin sun gama miki komai tunda suka baki muhallinsu kika zauna. Yanzu suna korarki ƙauye kika nufa. To menene abun haushi don anyi tusa a masai? Karya aka faɗa mata? Ta nuna uban nata idan ta san shi. Ko ni da na ɗau cikin ban isa na nuna shi ba don ba saninsa nayi ba. Haba! Yarinya ta fitine ni da maganar uba-uba. Kuma da take cewa ana mata gorin uwarta karuwa ce, karya aka faɗa mata? Mecece ni idan ba karuwar ba? Kowacce ƴa tana alfahari da sana'ar uwarta don ubanki. Kuma karuwanci yanzu na ɓalle zani sai dai ki mutu. Duk ɗan iskan yaron da ya kuma ce maki ni karuwa ce, ki faɗa masa idan ubansa na ciki yazo zan buɗe masa," faɗin Laushi.
"Wa'innahu Sulaimanu!" Faɗin Salma nice yana mai dafe ƙirji yana kallon Laushi.
"Suna ina aljanun mu tofe su da ayoyin ubangiji do uwa tasu," Laushi ta faɗi.
"Ke, Laushi wallahi ki kula da titi. Yanzu Meema ce kika tsaya fayyacewa wannan maganganun ɗibar albarkar?"
"Idan zaki ki bar jira na, Salma. Je ɗauko mayafinki mu tahi don Allah, ki raba ni da wannan shiriritar," Laushi ta faɗi.
Hannun Meema, Salma nice ya fizgo tare da faɗin, "Wallahi, tallahi babu uban da ya isa ya hana ni cin uban dangin Oduduwan can akan Meema. Idan zaki iya jira na, ga bakin gado nan ki zauna," Salma ya faɗi tare ficewa fuuu hannunsa riƙe da hannun Meema yana mita.
Kiciɓus suka yi da Sadiya (Sadisu ɗan daudu) a kwar gida zai shigo ciki, "Su Salma sai ina da da zafin ranar nan?"
Rangwaɗa Salma yayi tare da faɗin, "Kin ganni nan, Sadiya zuwa zan yi naci uban jikokin Oduduwa akan Meema," daga nan ta kwashe duk abunda ya faru ta faɗa mata.
Wani irin tafi Sadiya ɗan daudu yayi tare da faɗin, "Akwai bala'i a garin Legas yau! Muje, muje, muje in miki rakiya muci uban shegu la'ada waje. Kai! Har mu za'a gwadawa iskanci. Aikuwa zan ci buredi in yaga leda yau," ya ƙarisa maganar yana gyara karin ɗankwalin kansa sannan ya juya, Salma nice da Meema suka bi bayansa.
"Kin ce ɗan gidan uban wanene, Meema?" Salma Nice ya jefawa Meema dake matsar kwalla tambaya.
"Kayinde Rashidi da Tola Soyinka!" Ta ƙarisa maganar hawaye na zubo mata.
Hannu Sadiya ɗan daudu ya saka ya share mata hawayen tare da faɗin, "Bar kuka, Meema. Bar mu da ƴan iska yau sai sun san sun tono tsukiyar dodo. Da Salma Nice da Sadiya suke zancen," ya ƙarisa maganar yana mai zabga kwafa.
"Ba dai zaki gane gidan ba?" Faɗin Salma yana mai shafa kanta alamar rarrashi.
Gyaɗa kai tayi tare da nuna wani rakwaɓaɓɓan gida da hannu ta ce, "Ga gidan can, can ne gidansu. Ai dukkansu gidansu ɗaya. Ga ma baban Kayinde can."
Wani juyi Salma nice yayi tare da buga cinya sannan ya kalli Sadiya ɗan daudu tare da faɗin, "Ki jimin ƴan iskan yara! To kwantar da hankalinki, Meema domin waccan ɗan iskan da kika gani, Kusan kullum sai yayi wa mamanki ciniki. Bai iya cikakken cefane amma kullum sai ya zo wajen uwarki Laushi ta ɗage masa ƙafa shi kuma ya zube mata kaf kuɗin aljihunsa," ya ƙarisa maganar yana kallon Meema.
"Ashe yau akwai bankaɗa kenan. Wani ƴaƴansa sun taro masa match!" Sadiya ɗan daudu ya faɗi yana mai yin ƙas-ƙas da chewing gum ɗin bakinsa.
Kai tsaye inda Rashidi mahaifin Kayinde suka yi. Shi kuwa Rashidi yana hango su gabansa ya faɗi yana leƙen kantin dake gefenta da matarsa Iya Kasim take ciki tana saide-saide. Ga kuma cincirindon mutane a gefe guda kowa na hada-hadarsa na saye da sayarwa.
"Shege, daga ganin mun dumfarosa har yasha jinin jikinsa. Waya faɗa maka Borno gabas take? Ɗan kuka mai jawa uwatai jifa!" Salma nice ya ƙarisa maganar da kwafa.
"È kàasàn ma, Mo fe ra garri twenty naira (Good afternoon, ma. I want to buy twenty naira garri)" faɗin wani yaro yana miƙawa Iya Kasim Naira hamsin amma sam hankalinta bai wajen, yana wajen su Salma Nice da taga sun yi tsaye a gaban Baban Kasim.
"ọkọ mi, awọn eniyan wọnyi n ṣe nibi? (Mijina, me waɗannan mutanan suke yi a nan waje?)" Faɗin Iya Kasim.
Da sauri ya kalleta tare da faɗin, "Iyawo mi, wñn wá síbí láti kó ohun kan. kan pada si iṣẹ rẹ, ẹnikan fẹ lati ra nkankan. (Matata, sun zo amsar wani abu ne. Ki koma kan aikin, ga wani nan zai saya wani abu)," faɗin Rashidi yana ƙirƙirar murmushi yaƙe.
"Rashidi, Rashidi, Raashidi! igba melo ni mo pe e, Rashidi? Mo nireti pe o ko ṣe ohunkohun aimọgbọnwa (Rashidi, Rashidi, Raashidi! Sau nawa na kira ka? Ina fatan dai ba wani banzan abun kaje kayi ba)," ta ƙarisa maganar tana harararsa.
"Haba, Iya Kasim ẽṣe ti iwọ fi n sọ eyi (Mai yasa kike faɗin haka?) eniyan n wo wa (mutane fa suna kallonmu)."
"Kai dalla matsa can, ɗan mijin tacen bura uba! To yau zuwa muka yi muci maka mutuci mutumin banza da wofi. To ka jawa ƴaƴanka kunne akan wannan Yarinyar," Faɗin Salma nice yana mai turo Meema gaba sannan ya cigaba, "Har suna da bakin kiranta Karuwa bayan ubansu ƙasurgumin ɗan iskan ne shima. Ina ce jiya a gidanmu ka raba dare a ɗakin uwar yarinyar nan?"
Da mugun sauri Iya Kasim ta fito daga shago bayan ta sallami mai siyan garri sannan ta ce, "Ahh kini o ti ṣẹlẹ? le ẹnikan jọwọ se alaye? (Mai ke faruwa? Shin wani zai iya min bayani?) Baba Kasim, Kilode?"
"pada si ile itaja rẹ, Ahhh Iya Kasim ( ki koma shagonki, Iya Kasim, ahh)," ya faɗi yana nuna mata shago.
Harararsa iya Kasim tayi sai kuma ta juya ta kalli su Salma nice tare da faɗin, "Yaro, minini yasa kinzo nan kina fada?"
"Yaro yana bayan uwarsa idan yayi kuka a kwantosa a basa nono?" Faɗin Sadiya ɗan daudu yana harare-harare.
"Ahh! Yaro, ni ban gane minini kana sewa ba. Minini yasa kana fada da Baba Kasim?"
Rashidi sai girgiza kai yake yi yana ɗaura yatsa akan bakinsa alamar kar Salma ɗan daudu ya ce komai.
"Ke, uwar kwarmato. Tunda kin matsa to saurare ni; ƴarki, mai take da suna.....?"
Da sauri Sadiya ɗan daudu ya ce, "Kayinde."
"Minini Kayinde yayi?" Iya Kasim ta faɗi tana mai gyara ɗaurin zanin jikinta.
"Zagin yarinyar nan tayi. Ce mata tayi wai uwarta karuwa ce."
"Aaaaahhh! Kayindeeee." Faɗin Iya Kasim da ƙarfi tana mai ɗaura hannu a kai.
"Abun haushi shine, idan eh uwar yarinyar nan karuwa ce, to mijinki wannan (Ya nuna Rashidi) kullum sai yazo gidanmu wajen uwar tata, ma'ana karuwar dai, ta ɗage masa ƙafa shi kuma ya zube mata duk kuɗin dake jikinsa yayi gaba. Ku kuma ya barku da babu kuɗi."
"Ehhhhh, Rashidiiiiiii!" Iya Kasim ta faɗi da mugun ƙarfi tana mai tattare zaninta tare da yin gaba sannan ta dawo baya kamun ta kai masa wani irin cafka a wuya.
Mutanan dake wajen suka taho da gudu, wani ɗan dattijo a cikinsu mai kwaya-kwaya irin zanen yorubawa ya nufo tare da yiwa Salma nice daƙuwa har yana taɓa fuskansa sannan ya ce, "munafiki, segen yaro. Ke ne kin hada wannan fada, olofofo. Segen yaro."
Matsawa baya Salma nice yayi tare da faɗin, "Ko ba yaro ba. Yaro na can yana amsan kiɗi a sama. Tsaleliyar budurwa ce a gabanka, ehe. Gaga min ɗan iskan tsoho yana kai ni jinsin ƴan maza." Faɗin Salma ɗan daudu.
"Bar ɗan guguwar, taho mu wuce ko da wannan ƙurar muka bar su mun ci riba. Taho mu tafi Meema." Ya kama hannun Meema suka wuce.
A can gidan karuwai kuwa, Laushi ta cika tai fam saboda fitarsu customers masu sayan kwaya da wiwi sun shigo domin saya amma babu, sai ta ɗaura laifin akan Meema. Cewar ta da bata yi magana Salma ya ji ba da yanzu suna hanyar dawowarsa da kayan sana'arta a hannu. Hakan ya saka ta kudurta irin dukan da za ta yiwa Meema yau da daddare.
Suna shigowa, wani irin kallo Laushi ta bi Meema da shi na zaki ci ubanki anjima kamun ta zuba kwafa ta miƙe gyale a hannu suka fice daga gidan ita da Salma Nice.
Meema kuwa sai da ta fara cire uniform ta ajiye sannan ta canza kaya zuwa vest da skirt na kanti sannan ta janyo tukunyar abinci ta buɗe. Taliya ce wacce taji busasshen kifi na manja da kuma alayyahu. Zubawa tayi cikin plate daidai cinta sannan ta rufe tukunyar ta soma ci. Loma biyu ta kai baki sai ta fashe da kuka mai sauti. Duk da ƙarancin shekarunta, Kasancewar shekarunta tara kawai a duniya, amma ta san cewar ba ta hanyar kwarai aka haifeta ba, kuma ta san dagaske mahaifiyarta karuwa ce tunda ita ganau ce ba jiyau ba, amma duk da haka tana matuƙar ƙaunar mahaifiyarta kuma tana son sanin wanene mahaifinta domin ta tambayesa mai yasa ya bari mamanta ta haifeta ba tare da sun yi aure ba kamar kowa.
"Meema, kukan me kike yi ga kwanan abinci a gabanki kin ƙi ci?" Faɗin Ladi Katifa wacce shashsheƙar kukan Meeman taji ta ɗaga labulen ɗakin ƙawar tata.
"Aunty Ladi!" Faɗin Meema tare da ƙara fashewa da kuka.
Da sauri Ladi Katifa ta faɗo ɗakin tare da duƙawa ta rungumo Meema sannan ta ce, "Meemata, kukan me kike yi? Kina son wani abu ne?"
Girgiza kai Meema tayi cikin shashsheƙa tare da faɗin, "Daddyna nake son gani. Ina son in faɗa masa yazo ya ɗauke aunty Laushi suyi aure sai mu koma gidanmu mu zauna kamar yanda baban Munira da mamanta suke. Bata son ina ganin mamana tana cire kayanta a gaban maza suna taɓa ta. Shekaran jiya haka tayi ta ihu a nan da daddare ita da wani. Ina ji amma na rufe kaina ina kuka don idan na tashi dukana Aunty Laushi za tayi kuma gashi ina son temaka mata saboda ihu take yi. Haka take ta cewa, wayyoooo, shssshsh, asshhhh! Kullum idan wani yazo ɗakin sai aunty tayi irin wannan kukan, kuma nima kuka nake yi idan tana yi," ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka......
*MATAR SAYYADEE* ***
_SORRY 4 D LATE UPDATE_ 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._