My Destiny (Ƙaddarata)

Page 12

by @matarsayyadee3

Wani irin tausayinta ne ya dabaibaye Ladi Katifa har bata san lokacin da ta ƙara matso da Meema jikinta ba tare da soma jijjigata alamar rarrashi.

"Bar kuka, kinji Meemata. Kema kina da uba kamar kowa. Babu wani ɗa ko ƴa da ya faɗo daga sama. Duk wanda kika gani haihuwarsa aka yi kamar ke ɗin nan. Mamanki kuma, duk lokacin da kika ji tana wannan kukan ki toshe kunnenki kar ki ƙara bari yayi tasiri a kanki. Magagin bacci take yi ba kukan gaske bane. Kuma zan yi mata magana da dena," faɗin Ladi Katifa.

Jinjina kai Meema tayi tare da faɗin, "Nagode, Aunty Ladi. Ke kina sona sosai ke da su uncle..... Au aunty Salma da aunty Sadiya," ta ƙarisa maganar da dariya har sai da Ladi Katifa ta dara itama.

"To yanzu abunda nike so da ke, ki cinye wannan abincin dake gabanki duka har ma ki ƙara," faɗin Ladi Katifa.

Waro idanu Meema tayi tare da faɗin, "Kai! Aunty Ladi bazan iya ƙarawa ba idan na cinye wannan saboda cikina zai cika."

"To shikena, amma ki cinye wannan. Idan kin gama kizo ɗakina in kwaɓa miki madara da suga kisha," ta faɗi hakan tana mai miƙewa tsaye.

"Aikuwa zan zo. Zan baki labarin abunda ya faru ɗazu a ƙofar gidan su Kayinde," ta faɗi tana mai kai spoon baki.

Murmushi Ladi Katifa tayi tare da faɗin, "To ina jiran ki sai kin zo," tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin.

Fitarta da mintuna bakwai saurayin Laushi mai suna Bros ya faɗo ɗakin. Kallo ɗaya za kai masa ka fahimci a bige yake. Da kallo ya dunga bin ɗakin ɗai-ɗai har idanunsa ya sauka a kan Meema da ke tsince ƙwayoyin abincin da ya zuba a ƙasa.

"Ke! Ina uwarki, Laushi?" Ya faɗi hakane kamar zai faɗo kanta. Fuskan nan nashi ya sha kwalli ranbaɗau.

"Ban....ban san inda taje ba. Amma tare da unc... Au, aunty Salma suka fita," faɗin Meema.

Wani wawan harara ya zabga mata tare da faɗin, "Munafuka! Menene wani aunty Salma? Ki ce min dai ta fita da gansamemen ƙaton nan. Aikuwa wallahi baza ta saɓu ba, sai da na mata pay before service tukun zata kama hanya ta tafi gantalin da ta saba. Aikuwa a kanki zan fanshe kuɗina ba ruwana da ƙanƙantarki," ya faɗi yana mai ɗaga mata hannu alamar ta miƙe tsaye.

Jikin Meema na rawa ta miƙe tare da tsare shi da idanun tsoro, amma ko kwakkwaran motsi ta kasa.

"Don uwarki kau da idanun nan naki a kai na! Ko an faɗa miki su zasu saka naji tausayinki?" Yana gama faɗin haka ya kama gaban rigar vest ɗin jikinta ya jawota kusa dashi sannan ya ɗagata cak ya ɗaura a kan gado.

"Tashi ki cire kayan jikinki duka!" Ya faɗi da ƙarfi jikin nan nasa a sake don har wani lilo yake yi.

"Kkkkayi haƙuri, uncle!" Meema ta faɗi tare da rushewa da kuka tana mai damƙe skirt ɗin jikinta.

Wanka mata mari yayi wanda ya saka bata san tayi ƙundunbala ba har kanta na buguwa da gaban gadon don ba ƙaramin gigicewa tayi ba.

Hannu ya saka ya jawo ƙafarta da ƙarfi har kusan ƙarshen gadon sannan ya saka hannu a ƙugu ya zaro sharɓeɓiyar wuƙar da suke sokewa ya nuna mata tare da zaro mata idanu sannan ya ce, "Wallahi kika sake kika min ihu sai na soka miki ta ɓullo ta bayanki sannan inja wuƙar a cikinki ta yanda za ta tsitstsinka hanjin cikinki."

A take wani irin fitsarin tsoro ya shiga zirarowa daga jikin Meema. Ƙirjinta sai wani irin ɗagawa yake yi numfashinta na sama-sama alamar tana son somewa.

Bai damu da yanayinta ba ya finciko skirt ɗin jikinta daidai lokacin da ta saki wani irin numfashi sannan jikinta ya saki ta some nan take. Shi kuwa wawan bai fahimci haka ba don tuni yayi fatali da skirt ɗin jikinta ya yasar a ƙasa. Yana cire pant ɗin jikinta, Salma nice na kutso kai ɗakin kasancewar ɗan sakaya ƙofar kawai Bros yayi.

"Ƙalu Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'una! Mai nake shirin gani haka ni Salma?" Salma ya faɗi tare da sakin ƙatuwar leda Viva dake hannunsa yana mai dafe ƙirji.

Shi kuwa Bros da sauri ya sauko daga kan gadon yana kallon Salma nice fuska haɗe, kuma a wannan lokacin ne Laushi ta samu shigowa ɗaki.

"Bros, mai ya faru? Yaushe kazo? Ina Meem......" Ƙasa ƙarisa maganar tayi ganin Meema yashe a kan gado, sannan ga pant ɗinta a hannun Bros ɗin.

Da idanuwa kawai Laushi tayi ta binsa speechless. Amma bakinta sai rawa yake yi. Can da kyar ta iya fizgo magana ta ce, "Bros, fyaɗe kayi wa ƴata?"

Da gudu Salma nice ya fita daga ɗakin, sai da ya kai tsakiyar gidan sannan ya kwatsatsa wani irin ihu tare da faɗin, "Yeeeeekuwa jama'a! Jama'a kuna ina??? Wai kuna ina ne? Kwarto a ɗakin Laushi yayi wa Meema fyaɗe."

Kan kace kwabo rabi da kwatan gidan sun fito. Yawancin su daga wanda ya ɗauko muciya, sai mai taɓarya, katako, wata wuƙa, wata kwalba, wata kuma muburgin kaɗa miya.

"Na shiga uku ni, Sadiya! Wani magana nike ji haka, Salma nice? Allah yasa mafarki nike," faɗin Sadiya ɗan daudu.

"Muje ku gani da idanunku. Ɗan iskan yana can ɗakin Laushi tsaya. Ke, aunty Madara (Wani daga cikin ɗan daudu) yi maza je rufo mana kwar gidan nan don yau mai raba mu da ɗan iskan nan sai Allah," Raliya (Ɗan daudu) ya faɗi.

Da sauri wanda aka kira da Aunty Madara ya nufi ƙofar gida ya kulle sannan gaba ɗaya suka nufi ɗakin Laushi wacce ta ƙame kamar statue.

Jin hayaniyar dandazon mutane suna tunkaro kwar ɗakin Laushi, da sauri Bros ya ce, "Kinga, Laushi wallahi babu abunda nayi wa yarinyar nan. Ban kai ga yi mata komai ba kuka shigo."

Wani wawan harara Laushi ta jefa masa tare da faɗin, "Munafuki annamimi! Da mun jinkirta kenan fyaɗen za kayi mata?"

Salma Nice ne kan gaba ya faɗa ɗakin tare da turo Bros waje yana mai faɗin, "Mu halaka ɗan iskan."

"A'a sabon kaciya za muyi masa," faɗin Sadiya ɗan daudu.

"Cillar kawai za'a yanke duka. Kunga sai muga da abun da zai bibiyi mata a gidan karuwai balle har yayiwa yarinyar ƙarama fyaɗe," faɗin Raziƙa (Ɗan daudu).

"Wannan Shawara taki tai daidai. Ai dama haka ya kamata a yiwa duk mai yin fyaɗe. Idan ban da iskanci, ba saboda irin haka bane aka wadata gidan karuwa! Idan karuwan nan basu yi maka ba sai ka tafi _Allen avenue_ kuɗinka ya koka, yau ubanka zaka ci a cikin gidan nan. Miƙo min wuƙar hannunki ƴar sita," Salma nice ya ƙarisa maganar tare da amsar wuƙar hannunta.

"Tsaya-tsaya kuji, wallahi tallahi babu abunda nayi wa yarinyar nan. Na san nayi kuskuren yunƙuri, amma ban aikata komai ba. Kuna iya tambayan yarinyar kuji gaskiya daga bakinta," Bros ya faɗi jikinsa na rawa don yau ɓarawo ne tsamo-tsamo a hannun mata.

"Au, har wani sauraransa kuke? Rabi'a, Aunty Madarar, Raziƙa, Tinene, aunty Asabe, aunty Munari, aunty Khairat duk kuzo kuyi min kama-kama dashi in cire cillar shege in yasar. Yo to mai za ai da ita tun da ƙanana ƴaƴa take wa fyaɗe," faɗin Salma Nice.

Salma Nice na rufe baki ƴan daudun nan su kai ram dashi tare da cire masa wando kuma kowa na gidan na kallo.

"Yauwa juyo min shi da kyau in yanke shegiyar abar," Salma ya faɗi bayan ya saka hannu biyu ya riƙe mazantakar Bros dake faman yanka ihu kamar zai tsaga gidan yana faɗin bai yiwa Meema komai ba wallahi.

"Kai! Kai!! Kai!!! Mai zan gani haka a cikin gidan? Salma wani irin iskanci ne haka? Idan kin cire masa mazantakarsa, naki zaki liƙa masa?" Faɗin Hajja Lanti da duk ihun nan da ake sai yanzu ta samu nasarar fitowa daga ɗakinta.

Shi kuwa Salma nice sauri kai hannu yayi ya dafe al'aurarsa tare da faɗin, "Haba Hajja Lanti, ya zaki min haka? Ai abun ba iri ɗaya bane. Ina zaki haɗa al'aurar gansameman ƙato da na budurwa iri na! Ai halittar ba ɗaya bace."

"To naji. Yanzu dai kuyi min bayani wannan taron da kuka haɗa har kuke ƙoƙarin cirewa wani mazantakarsa," Hajj Lanti ta faɗi tana mai kallon Bros da ya buɗe murya irinta ƴan shaye-shaye yana faɗin ya gode da tayi saurin fitowa da yanzu an kashe sa tare da saka hannunsa biyu yana kare al'aurarsa.

Kamun Salma Nice yace wani abu, Laushi ta fito da gudu tana faɗin, "Na shiga uku, Meema bata numfashi......"

*MATAR SAYYADEE* *** [2/7, 8:43 PM] Matar Sayyadee: *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._