My Destiny (Ƙaddarata)

Page 13

by @matarsayyadee3

Da gudu ta juya ta koma cikin ɗakin bayan ta faɗa cewar Meema ba ta numfashi. Salma ɗan daudu ya bi bayanta da saurin shi da Ladi Katifa.

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Meema," faɗin Salma nice yana mai jijjigata da ƙarfi kamar zai fashe da gudu.

Laushi kuwa, komawa gefe ta yi tare da ɗaura hannunta biyu a kan ƙirjinta tana leƙen fuskan Meeman, amma gaba ɗaya jikinta rawa yake yi.

Shi kuwa Bros, tun sa'arda Salma nice ya sake sa ya samu hanya ya gudu bayan ya ɗauki wandonsa da ke yashe a ƙasa.

"Ɗauko min ruwa, Sadiya maza!" Salma nice ya faɗi yana mai ɗago kan Meema ya ɗaura a kan cinyarsa. Da sauri Sadiya ɗan daudu ya miƙa masa ruwan cikin wata ƙaramar buta tare da komawa gefe yana kiran sunan Allah cikin zuciya.

Sai da Salma nice ya shafa mata ruwan nan sau uku a fuska sannan ta ja wani dogon ajiyar zuciya tana wawware idanu don gaba ɗaya a firgice ta farfaɗo.

"Alhamdulillah!" Kusan gaba ɗaya ƴan ɗakin suka faɗi cike da farin cikin ganin ta farfaɗo.

Ita kuwa Meema, wawwara idanuwa kawai take ta yi. Can ta hango mahaifiyarta da ke jikin kyauren ɗakin dafe da ƙirji. Hannu ta miƙa mata tare da faɗin, "Aunty!"

Ƙarisowa Laushi ta yi har bakin gadon tare da miƙawa hannu ta riƙe hannun Meeman sannan ta zauna a inda Salma nice ya matsa mata. Mayar da kan Meema ta yi a kan cinyarta tare da faɗin, "Babu abunda zai same ki, kin ji ƴata?"

Gyaɗa kai Meema ta yi tare da shigewa jikin mahaifiyarta domin wannan wani abu ne da ta daɗe tana jiran sa.

Wani wawan harara Salma nice ya jefi Laushi da shi sannan ya ce, "Aikin banza! Ashe kina son ta? Ohh! Idan ba ka mutu ba za ka ga abu a cikin duniyar nan," ya ƙarisa maganar yana mai riƙe haɓa.

Hararar sa Laushi ta yi tare da faɗin, "Duk da a kwararo na haifi abata ai ina son ta. Ko ka taɓa jin uwar da taƙi abunda ya fito daga jikinta?"

"Ke! Wallahi ki kiyayi kanki da turani jinsin da ba nawa ba. Menene wani kai sai kace kin ga ƙato a gabanki? A'a kul! Kar ki sake," faɗin Salma nice yana maka mata harara.

"To ubana!" Laushi ta faɗi tare da mayar da dubanta ga Meema da ta damƙi yatsunta biyu.

"Wallahi, tallahi ina jin kunyarki Laushi. Ki fita idanuna da tura ni jinsin ƴan maza. Ina laifin ki ce to uwata ba to ubana ba," Salmanu ya faɗi yana mai tattaro jallabiyarsa.

"Bar tcinannar! Yanzu ka gama fita hayyacinka akan ɗiyarta amma saboda ita ba ƴar halas bace dole ta raina maka wayau. Ba hwata ba, dama mutuwa ƴar ta yi ko kuma hyaɗen akai mata muga tciya," faɗin wata bakatsiniyar karuwa wacce dama ta tsani Laushi.

"Kuji min ƴar bakatsiniyar bura uba! Har ni za ki faɗawa katika da mugunta? Na ci uwarki a iskanci wallahi! Ina ruwanki da sha'anina? To bari kiji, na gaba ya riga da ya yi gaba, na baya kuma sai labari. Ni na yi maki nisa wallahi. Wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa!" Faɗin Laushi wacce ta miƙe tsaye tana nuna Marka da hannu.

Da sauri Salmanu ɗan daudu ya miƙe tare da faɗin, "Ah! Magana ta gaskiya fa Marka kece ba ki da gaskiya. Ina ruwanki da tsunduma baki a cikin lamarin da babu ke a ciki? A'a haza haramun, tabbas."

Wani ƙanƙance idanu Marka ta yi tare da faɗin, "To munahiki wanda bai san abun arziki ba! Daga tare maka saboda ganin za a ci maka mutunci. Wawa kawai ɗan daudun banza da hofi," Marka na gama faɗin haka ta juya za ta bar ɗakin. Da sauri Salmanu ya riƙo rigarta ta can wajajen ƙeyarta tare da faɗin,

"Dawo mutuniyar banza da hofi. Kuji min tsinanniyar karuwan nan! Ai ni Laushi ba ta cimin mutunci ba, kece wacce ki ka yi fata-fata da rigar mutuncina a tsakiyar kasuwa. Uban wane ne ƙaton? Ubanki da ki ka baro a gida ko? Wallahi sai in maki tsirara a gaban jama'a babu ruwana. Shegiya ƙaramar karuwa!"

"Ubanka ai shi ya hwara lalata ni! Don shi na hwara bawa budurcina. Kuma gwara ni karuwanci na ke yi, kai kuwa luwaɗi ka ke yi. Ko an hiɗi maka ban san cewa kai da Sadiya da aunty Madara bin ɗuwawun juna ku ke yi ba? To na san komai ai."

Tass! Sadiya ɗan daudu ya wanke fuskanta da mari. Yana sauke hannu, Salmanu ɗan daudu ya tsinka mata wani. Hannu bibbiyu ta dafe kuncinta tare da liliyo wani mugun ashar ta banka masu,

"Yau cikin gidan nan akwai bala'i da masihwa. Billahil lazhi la'ilaha illahuwa, sai na gwada maku ni cikakkiyar bakatcina ce! Bura uba, ni! Ni Marka za ku saukewa sawayenku a huskata? (Ta girgiza kai) wallahi sai na ci kaza-kazan ku," Marka ta faɗi tare da ficewa fuuuu daga ɗakin.

Ƙawarta Rahila ta ce, "Idan Marka ta haƙura da wannan cin mutuncin da ku ka yi mata, Allah gwada mu ku ya yi. Wannan abu da ɗwaci ya ke. Dukkan ku sai kun ji a hwatarku!" Ta na gama faɗin haka ta fice.

"To! Cin kaza har da su danƙo? Ita kuma wannan wacece? Banza da ita!" Faɗin Sadiya ɗan daudu.

Taɓe baki Laushi ta yi tare da kallon Ladi Katifa ta ce, "Katifa taimaka ki ɗauki Meema ku je can ɗakinki da ita ta samu ta kwanta. Ni da Salma za mu yi wani ɗan aiki ne. Kowa zai iya kama gabansa yanzu," tana maganar tana yatsine.

Hannu Ladi Katifa ta miƙa ta kama hannun Meema ta ɗagota tare da sauko da ita a kan gadon suka fita. Sauran da su kayi curko-curko suma suka kama gabansu. Ya rage daga Salma nice, sai Laushi. Tashi Laushi ta yi ta rufe ƙofar ɗakin tare da kunna wutar ɗakin ta jona socket ɗin radio ta saka kaset ɗin waka sannan ta duka dai-dai inda Salma Nice ya ke ta ce, "Taimaka ki zage min zip ki ɓalle min bireziya."

Hannu Salmanu ɗan daudu ya kai ya zuge zip ɗin sannan ya ɓalla maɓallin bireziyar. Ita kuma ta saka hannu ta cikin riga ta janyo bireziyar ta ɗaura a kan gado tare da ɗaukar zani falle guda ta ɗaura sannan ta cire rigar dake jikinta da skirt.

"Gaskiya kin ci sunanki, Laushi. Caɓ! Wannan iri Laushi haka. Ai kamun mutum ya kai ga headquartern daɗin ya hau iyo ya kawo sau babu adadi. Hannun nan nawa da na kai ina cire maki bireziya kar kiji wani uban shocking da naji na madarar daɗi. Ni wallahi da badan wani abu ba, da na cire wannan rigar daudun na tumbuji daɗi," faɗin Salmanu ɗan daudu.

Wani wawan kallo laushi ta jefa masa, shi kuma ya yi saurin faɗin, "A'a, wai da misali!"

Zama ta yi a bakin gadon tare da faɗin, "Ƴar iska! Da wani ko wata ce ta kira ki ɗan daudu da yanzu kina nan kina surfa bala'i an kai ki jinsin ƴan maza."

Wani dariyar bariki Salmanu ɗan daudu ya yi tare da faɗin, "Uhm! Ke dai a bar zancen kawai. Ɗazu a hanyarmu ta dawowa na ji kina zancen barin nan gidan a waya ke da Saurayinki, menene gaskiyar zancen?"

Laushi bata bashi amsar zancensa ba sai da ta murɗa wiwi ta kai baki tare da kunna mata wuta ta yi mata zuƙa ɗaya tukun ta ce, "Salma akwai ki a kwai son gulma da jin kwakwaf. Wato shiyasa kika yi lamoo kina saurarar abunda na ke cewa. To wannan maganar kar na ji ta a ko ina. Ki barta a tsakanin mu. Amma dagaske zan bar nan. Likafa ce ta cigaba. Ya siya min gida a nan cikin Lagos. Kuma abunda zai baka mamaki wallahi ba domin yin dadiro ya saya min gidan ba, kuma komai na Meema ya ɗauke min."

" _Dama ance mana daɗi zai zo bayan wuya!_" faɗin Salmanu ɗan daudu bayan ya miƙe yana rawa. Can kuma ya zauna a bakin gado tare da faɗin, "Amma kuma anya babu lauje cikin naɗi? Hakanan mutum sai mutum ya kama ya saya maka gida kuma babu amfanin da za kai masa?"

Murmushi Laushi ta yi tare da faɗin, "Waya faɗa maka haka nan ne kawai?"

Ɓata rai Salma nice ya yi tare da faɗin, "Menene kuma wa ya faɗa maka fisabilillahi? Ban son haka gaskiya."

Dariya Laushi ta yi tare da faɗin, "Yi haƙuri to. Wa ya faɗa miki haka nan ne. Ni ma akwai aikin da zan masa. Sannan idan yana gari zai riƙa zuwa yana kashe ƙishirwarsa a wajena. Amma hakan ba yana nufin ban isa in kawo wani cikin gidan bane. Sai idan yana gari in tabbata dai babu namijin da zai zo. Kwayoyi da ƙananan makamai kawai zai riƙa ajiyewa a cikin gidan a wani ɗaki ina kula masa da su."

Na san wannan ya yi kaɗan. In Sha anjima za ku jini da wani ko kuma gobe in yi maku 5 or 6 readmores.

_Matar Sayyadee_ *** [2/8, 12:32 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._