My Destiny (Ƙaddarata)

Page 14

by @matarsayyadee3

Da sauri Salmanu ɗan daudu ya ce, "Gaskiya Laushi wannan abu da za kiyi da akwai mummunar hatsari a cikin ta. Ban baki wannan shawarar gaskiya. Makamai fa, Caɓ! To shi ɗin kin san wani irin ta'addanci ya ke yi? Kiyi tunani da nan ɗinki," ya ƙarisa maganar yana nuna kansa.

Murmushi Laushi ta yi tare da faɗin, "Nagode da kulawar. Amma ina so ka sani, duk wanda zai nuna min soyayya ba kamar kaina bane. Na san duk abunda nake yi kuma na iya takuna. Yanzu abunda nake so da kai, mu harɗaɗa wannan wiwi ɗin mu bar wancan maganar."

"Yanda kika ce!" Faɗin Salmanu tare da tsuke fuska yana wani tunani daban.

Tun daga ƙarfe biyar na yamma matasa suke suntiri a ɗakin Laushi. Wannan na fita, wannan zai shigo kasancewarta mai sayar da kwaya. Meema kuwa na can ɗakin Ladi Katifa.

"Aunty Ladi, don Allah yaushe zamu bar nan gidan? Bana son zama a cikin gidan nan," faɗin Laushi.

Da gefen idanu Laushi da ke zuƙar sigari ta kalli Meema tare da faɗin, "Uhm! Ki cire wannan tunanin a ranki, kin ji Meema? Don baki da gidan da ya wuce nan."

Shuru Meema ta yi na wasu daƙiƙu kamun ta ce, "Kenan mamana ma haka mamanta ta haife ta kamar yanda ta haife ni? Ina son ganin iyayen mamana in tambaye su mai yasa suka bari mamana ta haife ni a nan bata zauna a wajensu ba."

Da sauri Ladi katifa ta juyo gaba ɗaya tana kallon Meema ba tare da ta iya cewa ko ƙala ba. Hannunta Meema ta kama tare da cigaba da magana, "Aunty Ladi, ke ƙawar mamana ce. Don Allah ki faɗa min a ina iyayen mamana suke inje wajensu inyi masu wannan tambayar? Na san kin san inda suke."

Girgiza kai Ladi Katifa ta yi tare da faɗin, "Ban sani ba Meema. Ban san iyayen Laushi ba. Nima a nan muka haɗu da ita. Ban san kowa nata ba."

Kai hannu Meema ta yi tare da zare karen sigarin da Ladi Katifa ta kai bakinta tare da faɗin, "Aunty, a jikin kwalin wannan abun suna rubuta cewar _The federal ministry of health warns that smokers are liable to die young!_ kuma cigarrate causes lungs cancer kuma ke da aunty Laushi duk kun san haka amma kuke sha, why? Do you people want to die young or have lung cancer?"

Murmushi Ladi Katifa ta yi tare da faɗin, "Ni ba nice na haife ki ba, amma ina alfahari da ke, Meema. Ina sonki sosai ƴata," ta ƙarisa maganar tare da rungume Meeman.

"Watarana, in Sha Allah za kiyi nasarar raba mahaifiyarki da wannan mummunar sana'ar da muke ki wanda mu kanmu mun san ƙarshen mu ba zai yi kyau ba idan bamu tuba ba," Ladi Katifa ta raɗa mata a kunne.

"Aunty Ladi, don Allah ki riƙa yin Sallah. Alfa ɗinmu a school wanda ke mana IRS ya ce duk wanda bai sallah wuta zai shiga. Kuma ya ce sallah tana hana manyan alfasha wato zunubi. Tun ɗazu ana ta sallah ni kaɗai ke tashi ina yi, amma ke bakya yi. Haka aunty Laushi ma ba ta sallah"

Murmushi kawai Ladi Katifa ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ganin haka sai Meema ma ta tsuke bakinta.

Wajajen ƙarfe tare na dare Meema ta tashi daga kwancen da take a kan gadon Ladi Katifa ta sauko tana murza idanu domin har bacci ya fara ɗibanta. Babu kowa a ɗakin, hakan ne ya saka Meema ta fice daga ɗakin tare da janyo ƙofar ta nufi ɗaƙin mahaifiyarta da ke can farkon gidan. Mutane ne cike a gida, ƙida kota ina ke tashi na garaya. Salma Nice ta hanga sai magana yake yi yana tafa hannunsa. Murmushi Meema ta yi tare da ɗaga labule ta shige ɗakin mahaifiyarta.

Turus ta tsaya ko kyafta idanu bata yi ba ganin mahaifiyarta da wani ƙato a kan gado haihuwar uwarsu suna zina kuma a lokaci guda suna shan taba.

Su basu ji shigowarta ba, ita kuma tunda ta ƙame waje ɗaya ko kwakkwaran motsi bata yi ba gudun abunda hankalinsu ya dawo kanta, Laushi ta jibgeta. Ta fi tsawan mintuna biyar tana tsaye tana ƙare masu kallo. Duk yanda saurayin Laushi ya canza mata position a kan idanun Meema yake. Can dai da ta gaji da kallo sai ta durƙusa ta yi rarrafe har zuwa kan katifarta ta kwanta ta yi lamo. Amma kuma ta ƙasa bacci domin sound ɗin da Laushi suke making ita da saurayinta ya hana Meema sukuni har ya kai ta tashi zaune dirshan fuskanta cike da hawaye tana kallon su duk da kuwa ɗakin ba farin haske bane, irin mai canza launin nan ne zuwa ja, blue, da kuma green ne. Ga kuma gadon da suke kai sai wani irin bada sauti yake kamar zai karye. Komawa ta yi ta kwanta flat tare da rintse idanunta. Sai kusan bayan awa guda Meema ta daina jin wannan ƙaran gaba ɗaya, sai kuma fira ta ɓarke tsakinsu. Tun tana jinsu sama-sama har bacci mai nauyi ya fizgeta.

Can cikin dare Meema ta ji ana mugun cinyanta kuma a lokaci guda ana kiran sunanta. A hankali ta buɗe idanunta tana kallon mahaifiyarta.

"Kin ci abinci? Da yaushe ki ka shigo ɗakin nan?"

Meema bata ba ta amsa ba sai kallonta kawai ta ke yi. Zaro mata idanu Laushi ta yi tare da faɗin,

"Ke zan ci ubanki! Ba tambayan ki nake yi ba?"

Maimakon Meema ta bata amsa sai kawai ta koma ta kwanta tare da lumshe idanu kuma sarai ta farka babu gigin bacci a tare da ita. Ɗagota Laushi ta yi don ta san Meema ba ta da gigin bacci ko kaɗan.

"Zan ci ubanki a ɗakin nan idan ba kiyi min magana ba. Ba tambayan ki nake ba?" Laushi ta kuma faɗi a harzuƙe tana jijjiga ta.

Sai a lokacin Meema ta buɗe baki ta ce, "Na ci abinci a ɗakin aunty Ladi, kuma tun sanda kuke wannan abun a kan gado ke da wani na shigo ɗakin na kwanta."

Hannu Laushi ta kai bakinta ta buge tare da faɗin, "Ohh! Don kin ga na sakar maki fuska ɗazu shine kika samu damar raina ni? To ki rubuta ki ajiye ba zan ɗauka b wallahi. Shegiya da kika shigo kuma sai kika tsaya ƙare mana kallo ko?"

"Ni ban kalle ku ba. Ina shigowa na kalli gadon sai na ganku. Shine na tsaya kaɗan kamun nayi rarrafe don kar nayi motsi mai ƙarfi kuji ƙara ki dake ni ki ce ina muku laɓe. Mom ki kai ni wajen mamanki in zauna ni bana son ina ganinki babu kaya wani na taɓa ki," ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka mai ƙarfi.

"Ke! Ke!! Ke!!! Rufe min baki a nan wajen. Mutane za ki tara min cikin daren nan? Zan miki mugun sakwara wallahi," faɗin Laushi tana mai ɗaura yatsanta a saman bakinta."

Tsit Meema ta yi tana jan numfashi a hankali tare da jan zanin gadon da take kai.

"Maza ki yaga min zanin gadon tunda ubanki ya saya min. Kinibabbiyar banza da wofi! Tunda kin riga kin ƙoshi, maza ki koma ki kwanta ban son jin ko tari," Laushi ta kuma faɗi tana nuna mata kan katifar.

Kwanciya Meema ta yi tare da rintse idanu ba don baccin ne a idanunta ba. Laushi kuwa ɗan tsaki ta yi tare da soma magana ciki-ciki, "Ai wallahi dole ma ina tattara in bar gidan nan. Yarinya duk ta gama gane min ilahirin jikina," ta ƙarisa maganar da siririn tsaki.

Washa gari sukuku Meema ta tashi. Ko breakfast bata wani ci sosai ba. Kayan makaranta ta saka tare da goya jakan bayanta ta ɗauki lunch box ɗinta tare da fita daga ɗakin ba tare da ta kalli gefen da Laushi ta ke ba. Da sauri Laushi ta miƙe tare da bin bayanta ta kamo hannunta ta juyo da ita da ƙarfi tare da faɗin,

"Dan uwarki ni sa'ar ubanki ce da za ki fita ba tare da kin min magana ba? Wato gaba kike da ni shiyasa kika ƙi gaishe ni ko?"

A hankali Meema da idanunta suka cicciko da hawaye ta ce, "Kiyi haƙuri mummy, ni ba....."

"Don ubanki ba na hana ki ce min mummy ba?" Ta faɗi a harzuƙe tana murɗa kunnan Meeman.

"Kiyi haƙuri Aunty Laushi!" Meema ta faɗi tare da fashewa da kuka.

"Shegiya baƙar banza! Ni wallahi da a asibiti na haihu sai in ce canje a kai min don wannan halin munafuncin da kike yi ba halina bane. Sai dai idan can na ubanki wallahi. Wuce ki ban waje!"

"He-he-he! Aikin banza da wofi. Sai kace ba nan jiya kika yi ta mana ihun Meeman ba ta numfashi ba. Kanki dai a ke ji. Meema dai daga jikinki ta hudo," faɗin kwalba uwar sharri wacce ke bakin ƙofar ɗakinta tana saka lagwani a risho.

"Uban wa ya kasa da ke a nan? Annamimiya me barci da ido ɗaya. Meema dai ƴata ce kamar yanda kika faɗa. Don haka ki cire idanunki a kan duk abunda za ki gani na yi mata," faɗin Laushi tana maka mata harara.

Taɓe baki kwalba uwar sharri ta yi tare da faɗin " _Fiffita fita fiffita mana shayi saissaita muji sanyi ka sanya mana Luna madara!_"

Laushi bata ƙara kallon ta ba, sai kai hannu da tayi ta kafawa Meema rankwashi tare da nuna mata hanyar fita daga gidan. Ficewa Meema ta yi tana sharar hawaye.

Suku-suku ta nufi bakin titi inda anan ta ke jiran school Bus ɗin su. Tana isa bakin titi bata yi jiran mintuna uku ba school Bus ɗin ta iso. Tafiyar mintuna goma ta kawo su makarantar. Da ɗan gudunsu suka ƙarisa kasancewar duk ɗaliban da suke makarantar sun hallara a assembly ground amma banda Meema da ke cat walking wanda haka Allah ya halicci tafiyarta tun tana mitsitsiyarta.

"Meema, why are you walking majestically? They're about to start singing the national anthem, and you know the quenciquences if you miss it," wata wacce baza ta wuce mate ɗinta ba ta faɗi tare da rugawa zuwa assembly ground ɗin.

Meema ta ɗan ƙara saurin tafiyarta, sai dai saura taku huɗu ta isa inda line ɗin ajinsu ya ke aka buga gangan, nan take student suka haɗa baki suka hau rera wakar taken Nigeria. Ƙem suka ƙame har da Meema da sauran ɗaliban da basu samu damar isa ba.

" _And uphold her honour and glory. So help me God!_" gaba ɗaya students ɗin suka faɗa. Su Meema kuma suka yi saurin ƙarisawa su suka tsaya according to their heights and classes.

Bayan malamai sun gama passing information zuwa ga ɗaliban sai suka sallame su, yayin da waɗanda ba su samu National anthem ba suka zube bisa guiwowinsu don sun riga sun san dokar. Headboy ya taho da bulaliyarsa ya zane su. Lokacin da ya zo kan Meema, sai da ya zo kusa sosai da ita sannan ya raɗa mata a kunne, "Illegitimate Daughter (ƴar da aka haifa ba da aure ba)"

Da sauri Meema ta kallesa hawaye na zubowa daga idanunta. Kunnanta ya kama ya murɗa da ƙarfi sannan ya ce, "Answer me now!''

Cike da shassheƙar kuka ta ce, "Yes, senior!" Ta ƙarisa maganar idanunta na kallon flowers ɗin da ke can kusa da principal office.

Wani murmushin mugunta ya yi yana gyara bulalan da ke hannunsa tare da faɗin, "Hey, Illegitimate girl, join your hands together. I'm giving you five stroke of cane, if you miss one, I'm going to stand from the beginning."

"Yes, senior!" Meema ta faɗi tana mai haɗa hannunta guda biyu. Ƙawarta Rashida da ke gefe sai kallonta take cike da tausayi.

"One, two, three, fourrrr, fivvve!" Meema ta ƙarisa da ƙarfi tare da fashewa da kuka saboda zafin bulalan da ya shige ta. Sai da ya sake zuba mata a tsakiyar bayanta ta yi wani irin banƙarewa. Shi kuma ya ce,

"Please, tomorrow you should carry that big mouth of yours and report me to uncle Meeram again. Stupid illegitimate girl!" Ya ƙarisa maganar tare da shurinta ya wuce.

Da sauri Rashida ta iso inda take tare da kama hannunta ta ɗagata suka soma tafiya hanyar class ɗinsu. Suna shiga class gaba ɗaya pupils ɗin class ɗin suka juyo suna kallon su. A kunne Rashida ta raɗa mata,

"Faridat, Please go to your seat and sit-down. Do not look at their faces, they are soo mean. I don't like them."

Ɗan turo baki Meema ta yi tare da faɗin, "I don't want to befriend them too," ta ƙarisa maganar tare da nufa wajen da take zama kasancewar ba waje ɗaya suke zama da ƙawarta Rashida.

Tana saka mazaunanta, Amina Yaƙub wacce ita ce seatmate ɗinta ta yi saurin matsawa alamar nuna ƙyama. Ɗan kallon ta Meema ta yi tare da taɓe baki ta cire jakar dake rataye a bayanta ta ajiye a kan desk ɗin.

"Good morning sir, we are happy to see you sir!" Gaba ɗaya ajin suka haɗa baki suka faɗi bayan sun miƙe.

"Good morning children, how are you this morning? You may all sitdown.Faridat, come over here," faɗin Teacher Meeram.

A hankali Farida ta miƙe ta nufi wajen Teacher Meeram tana wasa da fingers ɗinta.

"What's happening, Meema? Did anyone hurt you?" Ya faɗi yana kallonta.

Da sauri ta girgiza kai tana hawaye. Kallonta yake fuska a ɗaure kamun ya kuma cewa, "It's is Rashidi, right?"

Gyaɗa kai ta yi sai kuma ta yi sauri girgiza kai tana faɗin, "No Teacher Meeram. I didn't even see him this morning. We didn't meet."

Hannunta kawai ya kama suka fita daga class ɗin suka nufi nasu Rashida. Gaban Meema babu abunda yake yi sai faɗuwa domin tun ba yau ba Rashidi ya kafa mata ƙahon zuƙa a makarantar saboda rashin mutuncin da suka je suka yi a ƙofar shagon mamansa su ka faɗawa mamansa cewar babansa yana zuwa karuwanci wajen mamanta. Kuma hakan ba ƙaramin tashin hankali a ka yi ba tsakanin iya Rashidi da babansa.........

#Meema #Laushi #Drug trafficking #Fornication #Banditry #React #Share #Comment #Matar sayyadee

*** [2/10, 6:26 PM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._