Page 15
Teacher Meeram yana shiga Ss3 ya shiga ƙarewa ɗaliban kallo har idanunsa ya sauka a kan Rashidi. Suna haɗa idanu fuska a tamke Teacher Meeram ya ce, "Follow me!" Sannan ya kama hannun Meema suka nufi primary 3.
Sam Meema bata so haka ba don ta san hakan na nufin mugun dukan da ya fi na ɗazu da kuma tsangwama da kyara.
"Go back to your seat, Meema. I will definitely deal with that boy," yana gama faɗin haka ya fita daga class ɗin ya kalli Rashida da goes on his knees.
Meema tsuru ta yi gabanta na faɗuwa don ta san ba ƙaramin duka zai ci ba a wajen Teacher Meeram. Bayan mintuna biyar Teacher Meeram ya dawo class ɗin ya soma koyar da su darasin English wanda shine subject ɗin da yake koyar da su. Bayan 45minutes ya bar ajin, mathematics teacher ta shigo. Itama ƙarfe goma ta fice sakamakon kararrawar break da timekeeper ya buga. Nan da nan ajin ya hargitse da surutu.
Wata ƴarinya ce ta shigo class ɗin wacce itama anan class ɗin take, Mrs Oni mai masu darasin mathematics na fita itama ta fita shine ta dawo yanzu ta tsaya a gaban board tare da amfani da hannunta kamar ansakuwa (microphone) ta soma magana,
"Hi, class! My name is Laurat Abdulfatah. I'm here to tell you something very nice about my parents. I'm living with my dad and mom at Olusegun Road. My daddy is a banker while my mom is a lecturer. My dad really love my mom soo much. They live together, eat together, go out together and even watch movies. I like seeing my mom and dad together. They really love me alot!"
Tana kawo wa nan gaba ɗaya ajin suka hau tafa mata. Ɗaya bayan ɗaya sauran suma suka fito suna faɗin abubuwa masu daɗi a kan iyayensu. Can wacce ta fara fitowa ta yi magana ta nufi inda Meema da Rashida suke zaune ta kamo hannu Meema da ƙarfi ta kai ta gaban board tare da faɗin,
"Now it's your turn. Tell us something nice about your parents."
Meema ɗago manyan idanunta da suka yi ja ta yi tare da kallon ƴan ajin gaba ɗaya, sai kuma ta mayar da kanta ƙasa hawaye na zubo mata har suna ɗiga a ƙasan ajin.
"Who is your dad? where is he working at? Is he a teacher, pilot, banker, engineer, police, soldier or what? Do you even know him?" Ohh I Almost forgot! Where do you live please?"
Wasu biyu daga cikin ajin suka fito tare da tsayawa a gaban Meema da ke tsiyayar da hawaye. A tare suka furta wajen faɗin, "Can you please talk, Faridat Zinatu Laushi! Ooh please, answer this question before telling us something nice about your parents. Why are you bearing your mother's name instead of your father?"
Kuka mai sauti Meema ta fashe da shi tare da yin gaba domin ta koma wajen zamanta. Da sauri Laurat ta kamo rigarta ta baya tare da faɗin, "hey! Where do you think you are going without answering our questions? Come back here."
"Leave me alone I'm begging you!" Meema ta faɗi tana mai haɗe hannayenta biyu.
"I swear to God you must answer our questions before leaving here, or else........hmm" ta ƙarisa maganar tana wani jijjiga kai.
"My daddy....... I wish I know him," Meema ta faɗi tana hawaye sosai sannan ta cigaba cikin shassheƙar kuka, "I wish I was like you. I wish I'm spending my night together with him on his shoulder. I wish.... I wish.. he's.... He's dropping me to school everyday and kiss my forehead. Daddy where are you? I miss you Soo much!" Ta ƙarisa maganar tare da zube guiwowinta a ƙasa tana wani irin kuka wanda ya kashewa kusan duka ƴan ajin jiki.
A hankali Laurat ta ɗago ta tare da faɗin, "I'm really sorry, Faridat. I'm very sorry for what I did to you. It's not my fault. I was forced to do so. I was forced by the headboy, Rashidi. I hope you will find a place in your heart to forgive me!"
"It's alright!" Meema ta faɗi tare da miƙewa daidai shigowar Teacher Meeram, ƙawar Meema Rashida a bayansa.
"Yes Teacher, they are the ones teasing Meema," faɗin Rashida.
"No! We.... we are just playing." Meema ta faɗi da sauri tare da kamo hannun Rashida ta furta a daidai kunnanta, "What have you done, Rash! Sun bada haƙuri fa, and everything is alright now."
Harararta Rashida ta yi tare da bige hannun Meema da ke kafaɗanta ta zauna a kujeran da ta tashi.
"Are You sure you were just playing?" Faɗin Teacher Meeram yana kallon Meema.
Gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi. Shi kuma ya gyaɗa kai tare da ficewa daga ajin.
"Why do you do this, Rashida?" Meema ta faɗi har da ɗan rausayar da kai.
"Why won't I?" Rashida ta hayayyaƙo mata saboda ta ji haushin abunda Meeman ta faɗawa Teacher Meeram.
"I'm sorry, let eat," Meema ta faɗi tare da kama hannun Rashida. Sam ita bata ƙaunar tashin hankali..
"Kiyi haƙuri Rashida. Senior Rashidi ne ya saka ta. And if I report them to Teacher Meeram, it will be worse to me. I appreciate what you did, Rashida," Meema ta faɗi.
"Ai shikenan. Komai ya wuce. Amma saboda kina sanyi-sanyi ne shiyasa suke raina ki. Wata rana idan kika zage kika ci ubansu za su kiyaye ki. Amma tunda kin ce ya wuce, shikenan. Let's eat," ta faɗi haka tare da buɗe cooler suka soma cin Irish ɗin dake ciki.
Ƙarfe ɗaya da sha biyar aka tashe su. Irin su Meema masu tafiya a school Bus kuma suka hau mota. A titin bakin layin da zai kai ta lungun da gidan karuwai ya ke aka sauke ta. Sai da ta kalli titi da kyau ka mun ta tsallaka ta bi lungun ta ƙariso har ƙofar gidan Hajja Lanti. Tura ƙofar ta yi ta shiga gabanta na faɗuwa. Haka take duk ta bar gidan idan za ta dawo ko kuma ta saka ƙafarta cikin gidan sai ƙirjinta ya buga.
"Wallahi yau sai na ga uban da ya tsayawa uban ubanki a gidan karuwan nan. Sai na ƙona gidan nan! Idan ban kashe ki ba yau kice uwata shegiya ta haife ni. Ni! Mijina!! Da mijina za kiyi iskanci? Lallai kin tono wa kanki tsukiyar dodo. Sai na babbake gaban da kike rabawa mazajenmu suna manne maki. Ba Laushi kike ba, wallahi ko flour ce ke sai na ci uban da ya sanadin kawo mana annoba duniya!" Wata mata wacce baza ta wuce sa'ar Laushi ba ke wannan kururuwan ƙawayenta guda uku sun rirriƙeta tana zabura akan a barta ta daki Laushi wacce ta jingina da jikin ɗakinta tare da kalmashe hannu tana kallon matar ƙasa-ƙasa tana dariya mai ƙona zuciyar wanda ake wa dariyar.
Salma ɗan daudu ya wani daki ƙirji tare da kwance zani ya kuma ɗaurawa a kan ƙirjin tare da faɗin, "Na rantse miki da girman mahaliccin wata da taurari, ko yatsanki ne ya taɓa jikin Laushi sai mun miki shegen duka a cikin gidan nan mun miki tsirara sannan mu jefa ki waje. Ke har kin isa ki shigo gidan ki daki ɗaya daga cikin mu kuma ki tafi scot free!" Salmanu ɗan daudu ya ƙarisa maganar tare da buga cinya.
"Dalla matsa ɗan daudun banza da wofi! Ɗan iska, mai makon yanzu haka kana ƙauye kana noman rani, amma ka tsaya cikin mata kana kamanceceniya da su tare da kawalci sannan ana binka ta baya. Kasan wacece ni kuwa a cikin garin Lagos?"
"Uwarki! Kin ji ko baki ji ba in maimaita maki? Ka ga shegiya mai ƙirar kenkyaso! Kuma wallahi bakinki ya kuma kuskuren kai ni jinsin da ba nawa ba, sai na sharara miki mari. Kawalci kuma na yi, ke ma idan kina da buƙata ki taho a haɗa ki da wani Alhajin. Baya kuma da kike maganar ana bi, mai dattin hula ma yana yi," Salmanu ɗan daudu ya ƙarisa yana mai nuna mazaunansa.
Wani dariya Laushi ta saki tare da faɗin, "Gaba ai mu muka iya rabawa mazajen naku shiyasa kullum suke manne da mu. Ba ku iya kula da su bane shiyasa mu muke kula muku da su. Kuma mijinki ko yanzu ya shigo gidan nan ya nuna yana son in bashi, a gaban idanunki zan kama hannunsa in shiga dashi ɗaki in turo ƙofa. Kina nan tsaye za ki riƙa jiyo ihu da sambatun da mai taɓa kwatanta irinsa idan yana kanki ba. Ni nan da kike gani na, Master's degree gare ni a iya sarrafa ɗa namiji. Wawuya sakarya! Ke nan baki ji kunya zuwa nan ke da shashashun ƙawayanki ba? Ai idan nuna isa da taƙama za kiyi, mijinki ya kamata ki natsar a gida ki hana sa kallon irin mu. Amma muddin kuka sake su sakaka, wallahi muna nan ƴan titi muna jira kuma tabbas za muyi wuff da su," ta ƙarisa maganar tana taunar chewing gum.
Wani irin kukan kura matar ta yi ta fizge daga riƙon da ƙawayenta suka mata ta shaƙi wuyan Laushi ta hau dukanta. Cikin daƙiƙa wani mahaukacin dambe ya sarƙe a tsakaninsu. Ba ƙaramin dakuwa matar nan da ƙawayenta suka yi ba, domin taran dangi su Salmanu ɗan daudu suka yi masu.
Meema kuwa gefe ta koma tana ta ihun kuka musamman idan aka kai wa mamanta duka. Bayan an janye Laushi daga jikin matar, sai ta yi wuff ta shiga ɗakinta tare da dannawa Alhaji Nura kira a waya ta shaida masa ga matarsa nan da ƙawayenta sun zo gidan karuwai suna dukan ta. Haƙuri da ban baki alhaji Nura ya soma bata sannan ya ce mata gashi nan zuwa nan da wasu ƴan mintuna yana kusa da unguwar. Tana katse kiran ta canza kaya zuwa wani wando 3quater da shirt Polo ta fito tana jijjiga.
"Wallahi, wallahi sai na yi sanadiyar rushe gidan nan! Ba dai ni kuka daka ba? Ke kuma wallahi sai na miki illa, sai na illata ki," ta faɗi tare da ƙara zaburowa ƙawayenta suka rike ta.
"Ku barta, dukan ne bai ishe ta ba. Ku rabu da ita muyi mata tsirara," faɗin Sadiya ɗan daudu da Salmanu.
Matar Alhaji Nura Kallon gefenta ta yi sai ta yi arba da kwalbar Coca-Cola, sai ta nufi wajen da sauri ta ɗauka tare da aunawa da gudu ta rotsa kwalbar a goshin Laushi. A tare Laushi da Meema suka saki wani irin ihu. Meema ta yi kanta da gudu ganin jini a na zubowa daga kan mahaifiyarta. Kuma a daidai wannan lokacin Alhaji Nura ya shigo gidan kuma a idanunsa komai ya faru.
Da gudu ya nufi inda matarsa Marwanat take ya ɗauke ta da mari hagu da dama sannan ya nuna ta da yatsa tare da faɗin, "Ki tafi gidanku sai na neme ki!" Yana gama faɗin haka ya nufi inda Laushi take riƙe da goshi su Salma nice zagaye da ita ya riƙo hannunta tare da faɗin, "Baby, I'm sorry. I caused all this. Muje in kai ki asibiti a duba min kai."
"Kutumar kaza-kazan can! Idan ka fita da karuwar nan Allah ya tsine min albarka wallahi. Kan bala'i! Karuwar ce kake gwadawa kulawa haka a gaban idanuna, Ni matarka ta sunna? Idan ban kashe matar nan ba shegiya uwata ta haife ni," tana gama faɗin haka ta rarumi wata wuƙa da idanunta ya kai a ƙofar ɗakin kwalba uwar sharri ta yi kan Laushi.
Da gudu Laushi da ke riƙe da goshi ta zuba a guje ta nufi cikin gidan tana ihu.
"Ke! Ke!! Ke Marwa!!! Wallahi ki dawo nan kar ki kuskura ki jiwa baby ciwo da wuƙar nan!" Faɗin Alhaji Nura da ya bi bayansu da gudu.
Ita kuwa Laushi babu abunda ya faɗo mata a rai kamar lokacin da suke kokuwa ita da mahaifinta da wuƙa har ta yi nasarar caka masa a cikinsa.
"Kutumar ubanka kai da babyn taka. Kuma a gaban idanunka zan kashe ta sai dai ni ma a kashe ni wallahi!" Tana gama faɗin haka ta zuba da gudu ta bi Laushi da ta faɗa ɗakin Teema ta rufo ƙofa da ƙarfi tare da saka sakata.
Marwanat na zuwa wajen ta shiga jijjiga ƙofar kamar zata ɓalla. Wani irin duum ta ji a cikin kanta sakamakon wani mahaukacin ɓarin makauniyar da Alhaji Nura ya sauke mata a tsakiyar fuska har sai da ta tafi luuu kamar za ta kifa ta yi saurin dafe kyauren ɗakin da Laushi ke ciki.
"Ni ka mara Nura? Ni?" Faɗin Marwa tana nuna kanta.
Wani marin ya kuma ɗauke ta da shi tare da faɗin, "An mare ki ɗin wawuya sakarya. Da izinin uban wa kika fito har kika zo nan gidan ɗin? Ba na hana ki mu'amala da ƴan iskan ƙawayenkin can ba? Wato ni ban isa ba ko? Ban wuƙar nan," ya ƙarisa maganar tare da fizge wuƙar hannunta.
"Azzalumi, macuci ɗan iska! Shiyasa kullum kana cikin bibiyata. Da wa nayi waya, wa ya kira ni last, ina zani, ina na fito. Ƴaƴana kuma ka hana su sakat ko bikin dangi baka bari su wataya ashe ka san ɓarnar da kake shukawa. Allah ya isa tsakanina da kai kuma daga nan asibiti na yi domin ayi min gwajin cutar ƙanjamau," faɗin Marwa cikin kuka.
"Yauwa gata can officer," faɗin Salmanu ɗan daudu yana nuna Marwanat matar Alhaji Nura.
Da sauri Marwanat ta kalli ƴar saddar da ke ƙoƙarin ƙarisowa wajenta. Sai kuma ta mayar da dubanta ga mijinta tare da faɗin, "A haukanka sai ka bari matar nan ta taɓa ni ko?"
"Madam, you're under arrest!" Matar ta faɗi tana mai nuna mata ankwa.
"Under uban me? Uban mai na yi?" Ta ƙarisa maganar tana kallon Alhaji Nura da ya sha mur.
"Idan mun je office kya ji. Kiyi shuru kawai ki kama hanya mu wuce domin duk abunda kika faɗa zai zama shaida a kanki," faɗin police officer ɗin.
"Nura kana kallo za a wulaƙanta ni a gabanka ba za ka yi magana ba?" Faɗin Marwanat.
"Uban wa kika tambaya da za ki zo nan ɗin. Madam, ki haɗa har da waɗancan matan guda uku. Kuma kar ku bada bailing su har sai mazajensu sun zo," faɗin Alhaji Nura.
"Ƙalu inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Alhaji don girman Allah ka rufa mana asiri. Wallahi mazajenmu idan suka ji wannan maganar aurenmu mutuwa zai yi," suka haɗa baki suka faɗa.
"Amma ni kuma kun yi gangami domin kashe min nawa auren ba. To duk sai kun je station wallahi. Matata ma na ce a tafi da ita bare ku ɗin banza," yana gama faɗin haka ya hau knocking ƙofar ɗakin yana faɗin, "Baby buɗe ƙofar na kwace wuƙar. Fitowa in kai ki asibiti."
"Wallahi baza ta saɓu ba a shigo har cikin gidanmu ai mana cin fuska. Sa'a ma kuka ci saura ƴan bala'in gida basu nan," faɗin Salmanu ɗan daudu.
Buɗe ƙofa Laushi ta yi tana leƙe. Ganin Alhaji Nura a ƙofar ɗakin sai ta fito gaba ɗaya tana gyara hannun bireziya.
"Muje baby, kiyi haƙuri zan biya ɓarnar da ta yi miki," faɗin Alhaji Nura ko kunya bai ji ba matarsa na wajen.
Meema cikin kuka ta riƙe hannun mamanta jikinta na rawa ganin har wannan lokacin jini ne sosai ke zuba daga kanta.
"Wuce ɗaki don ubanki! Tsayuwar me kike yi a nan? Ki wuce ki je ki cire kaya abincinki na can cikin tukunya," tsawan da ta buga mata ne ya saka ta sake ta da sauri ta koma gefe tana kuka.
"Wato har ma shegiya kuka ajiye tare ke nan? Wannan baƙar ƴar taka ce Nura?" Faɗin Marwa tana ƙanƙance idanu.
Ko ƙala bai ce mata ba sai kama hannun Laushi da ya yi suka nufi ƙofa. A haukace ta bi bayansu tana zunduma manyan ashar...........
#Team Laushi #Team Meema #Team Salma Nice #Team Marwanat #Team Alhaji Nura #Ladi Katifa #Rashidi #Drug Trafficking #Fornication #Adultry #Matan Sayyadee
*** [2/10, 6:26 PM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._