My Destiny (Ƙaddarata)

Page 16

by @matarsayyadee3

"Lallai yau Nura ka nuna min kai ɗin cikakken ɗan iska ne! A gabana za ka kama hannun karuwa domin kai ta asibiti? Ina matarka ta sunnar Nura! Saboda ka ga jar fata da manyan mazaunai wanda a ke rabawa mazan titi ko? Ka faɗa min menene ban yi maka Nura. A ina na gaza? Ka taɓa kawo min buƙatarka na yi burus da kai?," Faɗin Marwanat wasu hawayen baƙin ciki na ziraro mata daga idanunta.

Juyowa Laushi ta yi tare da yi mata gwalo sannan ta ɗaura kanta a saman kafaɗar Alhaji Nura tare da faɗin, "Sweetheart jiri nake ji. Jinin da na zubar yana hawa min kai," a shagwaɓe kuma cike da kissa Laushi ta faɗi hakan.

"Kar ki damu, a hanya zan saya maki malt da madara sai ki sha. Ai jinin ne ya zuba da yawa," Alhaji Nura ya faɗi yana satan kallon matarsa da gefen idanu kasancewar sakin baki ta yi tana kallonsu.

Buɗe gaban mota ya yi domin Laushi ta shiga, amma sai Marwanat ta yi wuf ta shige gaban motar. Turu baki Laushi ta yi tare da faɗin, "Kana kallo dai ko? Ka ce mata ta fita in zauna," Laushi ta faɗi har da bubbuga ƙafa kamar yarinyar.

"Yi haƙuri shigo nan baya ki zauna. Kyale ta zan yi maganin ta ai. Zan fara kai ta station sai mu wuce clinic a yi miki dressing," faɗin Alhaji Nura kamae wanda aka yiwa sihiri.

Sai da Laushi ta jefi Marwanat da wani kallo sannan ta shiga gidan baya inda alhaji Nura ya buɗe mata. Zagayawa ya yi ya shiga mazaunin driver. Can kuma sai ya sauka ya rufe motar tare da isa wajen ƴar sandar nan ya ciro kuɗi dubu biyar ya bata tare da faɗin, "Ki rabu da ƴan iskan kawai. Ku kuma idan na ƙara ganin ƙafafunku a cikin gidana wallahi sai na ɗaure ku naga uban da zai saka a sako ku, ƴan iskan mata marasa kamun kai!" Yana gama faɗin haka ya dawo mota.

"Ke ƙaramar karuwa! Wallahi sai na ɗanɗana miki baƙin ciki a rayuwarki fiye da yanda kika min. Sai na saka an miki wulaƙanci mafi muni. Sai kin gwammaci mutuwarki da rayuwa. Bayan mijina, na miki alƙawarin baza ki ƙara samun damar kwace mazajen wasu da salon makircikin ba. Ni Marwa ɗiyar Saifullahi sai na ga bayanki. Kuma mijina sai na raba ku. Ki rubuta ki ajiye."

Wani irin dariyar shaƙiyanc Laushi ta yi tare da faɗin, "Ni kuma idan har ni ɗin ɗiyar Ayuba ce ta sunna a yau ɗin sai na gwada miki tsantsan barikina. Kin ce za ki raba ni da Nura ko? Nura ba ya ɗaya daga cikin samarin da nake ji dasu suma kuma suke ji dani. Yana dai iya kacin bakin ƙoƙarinsa don na tabbata kamun ya miki abu ɗaya, ya min biyar ko goma. To amma a yau, kuma a yanzu zan nuna miki karuwa ta fi matar gida!" Laushi ta ƙarisa maganar da wani irin murmushin bariki.

Marwanat za tayi magana kenan alhaji Nura ya dawo ya buɗe motar ya shigo tare da saka seatbelt ya tada mota. Kai tsaye hanyar gidansa ya nufa wanda ya ɗauke su mintuna ashirin da uku.

"Fitar min a mota ki shiga gida. Kuma ka jira hukuncin abunda kika aikata idan na dawo," faɗin Alhaji Nura yana mai zabga mata harara.

"Nura, Allah tsine maka albarka! Na yi dana sanin aurenka a rayuwata. Macuci azzalumi ɗan asara. Nura da haihuwar irin ka gwara ɓari wallahi. Mazinaci fasiƙi!" Marwanat ta faɗi tana kuka sosai.

Fitowa daga motar ya yi tare da zagayawa ya buɗe gidan bayan ya ce, "Zo ki fita ko kuma in fito da ke da ƙarfi. Kuma ki sani, duk zagin da kike min ina ɗaga miki ƙafa ne kawai saboda ƴaƴan da ke tsakaninmu. Fice min a mota!" Ya ƙarisa a fusace.

Kamun ta fito Laushi ta fito tana jiran ta fita ita kuma ta shiga gaba. Ganin fitowarta sai Marwa ta fito da sauri ta cacumi Laushi da dambe tana haɗata da jikin motar. Wani irin mahaukacin dambe suke yi a kan titi ga shi unguwar ba mai yawan mutane ba balle a raba, shi kuma Alhaji Nura ya kasa raba matarsa a jikin Laushi domin ba ƙaramin daduma ta yi mata ba.

Wata mota ce ƙirar Honda ta yi parking. Da sauri yayar Marwanat ta fito daga motar ta nufo su Laushi tana ƙundume-ƙundumen zagi. Sai a wannan lokacin Marwa ta rabu da jikin Laushi tana haki tare da faɗin,

"Yauwa Aunty Zubee gwara da kika iso yanzu. Wannan ita ce ƴar iskar da ke ɗaukewa Nura hankali. Ki duba fa ki gani, a gabanta yake ci min mutunci yana faɗin in fitar masa a mota zai je kai ta a yi mata dressing ciwon da ya ji mata. Wallahi ba zan yarda ba sai na kashe yarinyar nan."

"Mu kashe juna dai wallahi. Don ba fin ƙarfina kika yi ba. Ko ɗazu da kika ga na gudu don makami kike ɗauke da shi a hannu," faɗin Laushi wacce jini ke zuba a goshinta. Don tsumman da ta yaga a dakin kwalba lokacin da ta faɗa domin ceton rai, Marwa ta cire wajen kokuwa da ita.

"Kai! Kai!! Wannan wani irin hauka ne haka? Da girmanka da mutuncika, Alhaji Nura? Karuwa fa!" Aunty Zubee yayar Marwanat ta faɗi.

"Wallahi Aunty Zubaida don baki ga abinda ya min a gidan karuwai ba. Wallahi har tsirara ƴan daudun nan suka so yi min kuma yana tsaye yana kallo," faɗin Marwa.

"Gaskiya ba zai yiwu ba. Sam ba dai cikin dangin mu ba. Mai yasa kamun ki wuce can gidan karuwan baki kira mu ba mun yo musu zuga guda?" Ta faɗi maganar tare da cire gyalenta ta daura a ƙugu.

"Mai muke jira yanzu Aunty? Muci ubanta tunda Allah ya kawo ki," faɗin Marwa wacce tana rufe baki su kai kan Laushi da ta koma bayan Alhaji Nura dafe da goshi.

Ture Alhaji Nura da ke ƙoƙarin dakatar da su suka yi tare da soma kaiwa Laushi duka ta ko'ina.

Alhaji Nura ganin za su mata illa sai ya finciko Marwanat tare da wanke fuskanta da maruka har biyu hagu da dama sai da ta faɗi sannan ya nufi kan Aunty Zubaida da ke ta aunawa Laushi naushi a hancinta. Ita kuma Marwanat na miƙewa ta yi cikin gida da gudu.

Marwanat irin ƙarfafa matan nan ne shiyasa Alhaji Nura ya kasa kwatar laushi a hannunta har sai da ya shaƙi wuyanta da ƙarji taji bata numfashi sannan ta saki Laushin shi kuma ya wankawa fuskanta mari.

Jini ta goshi da ta hanci haka yake zuba a jikin Laushi wacce duk azabar bai saka bakinta ya mutu ba ko kuma ta yi kuka.

Kwalar Alhaji Nuran ta shaƙa tare da faɗin, "Ni ka mara? Ina yar matarka ka mare ni a kan karuwarka Nura. Lallai kai ɗin ba ɗan halak bane. To yau ka sani, Marwa baza ta kwana da igiyoyinka na aure a kanta ba!"

Da gudu Marwanat ta fito hannunta riƙe da kaifaffiyar wuƙa. A gabansu taci burki tare da faɗin,

"Yau sai na tura ki inda ba'a dawowa don ubanki. Sai na kawo ƙarshe karuwancinki kuma duk wanda ya yi ƙoƙarin hana ni in haɗa dashi ba asarata bace. Ki faɗa min abunda ke jikinki wanda babu shi a jikina da yasa mijina ya zaɓe ki a kaina ni da nake uwar ƴaƴansa," ta fadi tana posting ɗinta da wuƙa.

Da sauri Laushi ta koma bayan Alhaji Nura tare da faɗin, "Ga mijinki nan ki tambaye sa. Don shi ya san qualities ɗina wanda ke ba ki da su. Laushin fatata kaɗai ya isa gigita mijinki bare kuma a zo kan salona. Kuma mijinki yanzu na fara jin daɗin mu'amula da shi."

Zaburowa Marwanat ta yi sai aunty Zubee ta yi saurin riƙe ta tare da faɗin, "Kar ki fara! A kan wannan ƴar iskar karuwar kike son ƙare rayuwarki a prison? To ba zan bari haka ta faru ba, sam! Kuma mijinki ita ce zata rabu da shi ba ke ba."

"Ni kuma a yanzu zan gwada muku isata da ikona a kan mijin da kike ikirarin na ƙanwarki ce," faɗin Laushi tare da kallon Alhaji Nura ta ce, "To ka zaɓa ko ni ko matarka."

Da sauri Alhaji Nura ya ce, "Baby don Allah kar ki biye su. So suke kawai su ga sun raba mu. Ni kuma ban shirya hakan ba. Don wallahi babu uban da ya isa ya raba ni da ke, a shirye nake da na aureki."

Kallon juna Marwanat da Aunty Zubaida suka yi da mamakin furucin Alhaji Nura. Shi kuwa har cikin zuciyarsa ya faɗi hakan don ba ƙaramin so yake wa Laushi ba. Dama burinsa ya shawo kanta ta yi istibura'i su yi aure.

"Kana ruwa can ƙasa kusa da kada!" Laushi ta faɗi cikin zuciyarta amma a zahiri sai cewa ta yi, "Kawai ka zaɓa ko ni ko ina!"

Wani irin shammatarsu Marwanat ta yi tare da kai mata sukan wuƙa ta yanki damtsenta. Wani irin ihu Laushi ta buga tare riƙe wajen da ke zuban jini yana mata wani irin bala'in zugin azaba.

"Ke!" Alhaji Nura ya faɗi tare da wanka mata mari a fuska tare da faɗin, "Don ubanki hauka kike yi?" Sai kuma ya juya wajen Laushi da sauri tare da riƙe hannun Laushin yana kallon jinin da ke zuba a hannunta.

Wani irin kukan kura Marwanat ta yi tare da nufa kansu da wuƙar gadan-gadan daidai lokacin da Aunty Zubaida ta saki wani ƙara, shi kuma Alhaji Nura ya juyo da sauri, ji kake luum! Ta caka masa wuƙar a ciki da ƙarfinta. Da saurin ta yi wani irin baya jikinta na rawa don ba shi taso cakawa ba. Laushi da Aunty Zubaida suka saki ihu ganin lokacin guda jini ya ɓalle a cikin Alhaji Nura da wuƙa ke ciki.

Mota ya dafe da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana dafe da cikinta inda wuƙar ke ciki. A hankali Laushi ta soma tafiya da baya-baya kamun ta juya a guje kamar mahaukaciya. Marwanat kuma kan Alhaji Nura ta yi tana ihun kiran sunansa hankali tashe. Aunty Zubaida kuwa gigicewa ta yi ta shiga zagaye motar Alhaji Nura tana faɗin

"Mun shiga uku! Mun shiga uku!! Mun shiga uku yau!!!"

Laushi kuwa gudu kawai take sharawawa a cikin unguwa har ta fita bakin titi sannan ta tsayar da ɗan acaɓa ta hau. Sun ɗan fara tafiya ta hangi wani ɗan shagon da ake yin kira kasancewar wayar hannu bata wadatu sosai ba a shekarar dubu biyu da takwas (2008).

"Ɗan tsaya a nan bari na kira waya," Laushi ta faɗi yayin da ɗan acaɓa ya gangara gefe ya sauke ta. Ita kuma ta ƙarisa ta yiwa mai Shagon magana.

Maganar tsayin mintuna bakwai ta yi a wayar sannan ta katse tare da miƙawa mai shagon wayarsa ta dawo wajen ɗan acaɓa ta karɓi naira ɗari da arba'in ta ba shi saboda duk minti ɗaya naira ashirin ne. Ita kuma mintuna bakwai ta yi.

"M.I hotel za ka kai ni!" Ta faɗi tare da hawa mashin ɗin.

Tafiyar mintuna goma ya kawo su hotel ɗin. Tana sauka wani saurayin da ba zai wuce shekaru ashirin da ɗaya ba ya ƙariso ya biya mai mashin ɗin sannan ya mata jagora zuwa cikin hotel ɗin. Suna zuwa ƙofar ɗakin saurayin ya juya bayan yayi knocking.

Wani mutum ne wanda a ƙalla zai kai shekaru hamsin ko hamsin da ɗaya ya murɗa ƙofar ya fito.

"Bismillah, shigo zeenah," ya faɗi tare da bata hanya.

Shigowa ta yi tana ƙarewa ɗakin kallon sannan ta zauna a bakin gado. Zama yayi kusa da ita tare da jawota jikinsa ya furta a cikin kunnanta,

"Why are you looking afraid, Zee? You're safe here. Beside ni wallahi kin ban mamaki. Ban taɓa tunanin ganin tsoro a fuskanki ba a kan ɗan wannan abu. Ko dai kece kika yi kisan? Ko da yake ai ko da kece ɗin bai kamata ki damu ba cus this isn't the first time," ya ƙarisa maganar yana wani irin murmushi.

Da sauri zeenah ta kwace kafaɗanta tare da faɗin, "I don't understand! What do you mean? Sorry I didn't get you. What do you mean by saying this not the first time? First time of doing what?" A ruɗe ta yi maganar gaba ɗaya.

"Zinatu, Zinatu, Zeenah Laushin! Zeenatu Ayuba Tanko. Ƴar asalin jihar Sokoto wacce aka haifa a garin Bauchin Yakubu. Ƴa ta uku a wajen iyayenta. Wacce ta taso da mugun kwaɗayi da son abun duniya. Wacce saurayinta almajiri ya yaudareta ya ɗura mata ciki ya gudu bayan ya mata alƙawarin zai aure ta, ita kuma mahaifinta ya riga ya zaɓa mata miji amma ta nuna bata so shi kuma ya ce ta turo wanda take so. Mahaifinta da ƴan uwansa da abokan arziki sun ta jiran zuwan iyayan saurayin Zeenah amma basu zo ba. Hakan ya fusata mahaifin ya ce ko zata mutu sai ta auri zaɓinsa. Kwatsam sai ga ciki a jikinta ya bayyana. Mahaifin na sanin haka ya mata duka tsiya tare da tsine mata albarka. Har waje ya bita yana duka babu zani jikinta. Kuma ya ce duk wanda ya bashi haƙuri cikin ƴaƴansa sai ya tsine masa, mahaifiyarta kuma idan har ta yi magana a bakin aurenta. Sannan ya ƙara da faɗin kar Zeenah ta kuskura ta sake amfani da sunansa ya yafewa duniya ita domin abun kunya ne matsayinsa na malamin addini kuma limami a san cewa shine mahaifinta. Hakane ya saka Laushi yin wani alƙawari a kan sai ta yi fata-fata da sunansa wajen zama shahararriyar karuwa. Kai tsaye gidan karuwai na nan garin Bauchi ta nufa wajen magajiyar gidan. Anan ta cika duk wani burukanta a kan mahaifinta. Sunan Laushi ya shahara sosai domin ganganta ke tashe a gidan karuwai. Daga nan kuma sai ƙawarta ta kwaɗaita mata zuwa Lagos domin ta cigaba da cin duniyarta da tsinke a can. Hakanne ya saka ta shirya domin ɗauko sarƙar zinari a gidansu wanda ta samu labarin mahaifinsu ya sayar da gonarsa ya saya....." Yana kawo wa nan ya tsaya yana wani murmushi tare da miƙewa tsaye ya ɗaura ƙafarsa ɗaya a kan gadon tare da faɗin, "Ƙarasa min labarin Daga nan mai ya faru?"

A gigice Laushi ke kallonsa zuciyarta na bata Ladi Katifa ce ta basa labarin nan da yake maimaita mata. Sai dai kuma amma ai Ladi Katifa bata san cewar ta kashe mahaifinta ba. Duk a cikin zuciya ta ke wannan tunanin. Kamar ya san mai take rayawa cikin zuciyarta sai cewa ya yi,

"Ka da ki zurfafa tunani. Babu wanda ya bani labarin nan a cikin waɗanda kike tunani. Na san suspect ɗinki ta farko ita ce Ladi Katifa wacce ita kanta bata san kin kashe mahaifinki ba."

Da sauri Laushi ta ɗago kai tare da faɗin, "Mai yasa kake faɗa min duk wannan? Dama tarko ka ɗana min shiyasa ka shiga jikina? Mai kake so a tare dani?"

Sauke ƙafarsa ya yi a kan gadon tare da juya mata baya ya fara magana, "Duk wanda zan yi harka dashi to ina da buƙatar sanin komai a kansa saboda nawa dalilan. Zeenah ke ba abun yarda bace kai tsaye domin ina da labarin Yasaar da yake zaune gidan yari saboda cin amanarsa da kika yi bayan babu abunda bawan Allahn nan bai maki ba a rayuwa ke da shegiyar ƴarki." Juyowa ya yi gaba ɗaya tare da faɗin, "Kar ko da cikin mafarkinki kiyi tunanin cin amanar _Sabo da kaza_. Ƴarki tana hanya za a ɗauko maki ita. Za ku kwana uku a nan kamun a gama ɗan gyare-gyaren da ake yi a can gidan da za ku koma. Ga waya nan za ki iya kirana a kowani lokaci idan kina buƙatar wani abu. Wannan kuma, ki riƙe a hannunki," ya ƙarisa maganar tare da ajiye mata rafar ɗari biyar ya ɗauki takunkumi fuska ya saka tare da ficewa daga ɗakin ya turo ƙofa.

_Jama'a ina Laushi ta kai kanta?_🤔

#Laushi #Sabo da kaza #alhaji Nura #Marwanat #aunty Zubee #Meema #Mal Ayuba #Ladi Katifa #Matar Sayyadee #Ƙaddarata

Vote Comment Share *** [2/11, 5:56 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._