Page 17
Jikin Laushi ba ƙaramin sanyi ya yi ba. Miƙewa ta yi ta soma zagaye ɗakin tare da dunƙule hannunta tana naushin ɗayan hannun. Dogon tunani ta shiga yi ta yanda _Sabo da kaza_ ya yi mata farin sani haka. Sam ta mance da ciwon da ke goshi da kuma damtsenta duk da jinin ya bushe a jikinta har zuwa rigar da ke jikinta.
"Duk da ni ban taɓa yarda da mutum, amma ina ji a jikina sam ba Ladi Katifa bace za ta yi leading Sabo da kaza zuwa garinmu. To amma idan ba ita ba a nan garin Lagos wanene ya san ni haka? To kuma ai Ladi bata san na kashe Abbanmu ba," Laushi ke wannan maganar a bayyana tana zaga ɗakin.
"Zai iya yiwuwa da ya samu brief labarinki a wajenta sai ya tafi can domin bincike. Maybe a nan ya samu cikakken labarin tunda doge washa garin ranar da na cakawa Abbanmu wuƙa a ciki magana ta bayyana tunda a gaban yayata Maryamu komai ya faru," wannan karan a cikin zuciya ta yi maganar.
Ta jima tana saƙa da warwara. Sai dai duk inda ta kawo zargin Ladi Katifa sai ta ji wata zuciyarta tana ƙoƙarin ƙaryata ta saboda It's been 14years kenan da haɗuwar su kuma bata taɓa kama Ladi Katifa da ƙoƙarin cin amanarta ko munafuntarta ba.
"Anya ban ɗebo ruwan dafa kaina ba kuwa ni Zeenah? Wannan shi ake kira reshe ya juye da mujiya. Amma duk da hakan ba zan yi giveup ba. Zan bisa a yanda ya so. Sai dai idan ya san wata to bai san wata ba. Makircin mace ya fi na shaiɗan don ko shi tsoranmu ya ke," ta faɗi cike da bawa kanta kwarin guiwa tare da shiga bayi..
Tana fitowa wayar da Sabo da kaza ya bata ya hau ringing. Towel ta kai ta share ruwan da ya gangaro daga goshinta sannan ta nufi kan gadon ta ɗauki wayar tare da picking ta kara a kunne,
"Hello, ina ji!" Ta faɗi a dake duk da ta san mai kiran.
"I like your confidence! Sai dai ki sani, duk motsinki a tafin hannuna yake. Zan dawo anjima saboda wani aiki da ya tsayar dani. Ki gyara min kanki da kyau sai na dawo Hajiya Laushi," ƙit ya kashe wayar ya barta da sakakken baki tana kallon wayar.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku ni Zeenah. Bi diddigi ya saka min kenan?" Ta faɗi maganar tana bin ɗakin hotel ɗin da kallo daidai lokacin da aka yi knocking ƙofar ɗakin.
Ƙarisawa wajen ƙofar ta yi tare da murɗawa kaɗan. Ganin saurayin ɗazu ne hannunsa riƙe da hannun Meema, sai Ladi Katifa da kuma Salma nice da ke bayansa riƙe da ƙaruwar akwatin kayanta da na Meema.
Buɗe ƙofar ta yi da sauri ta basu hanya domin shigowa. Kallo ɗaya saurayin nan ya mata ya kawar da kai domin ƙaramin towel ta ɗauro a jikinta, santala-santalan cinyoyinta duk a waje, don tana duƙawa mazaunanta za su bayyana. Shi kuma saurayin zunubi ne a gare sa ya kalli abun hutawar mai gidansa.
Da gudu Meema ta isa wajan uwarta ta rungume tare da soma hawaye ganin yanka a can saman goshinta.
"Mai ke faruwa Laushi? Mai yasa kika turo a ɗauki Meema?" Faɗin Ladi Katifa kuma kusan a tare suka yi maganar da Salma nice.
"Uhm! Allah ya taƙaita min wahala ne da yanzu ina kan gadon asibiti ko kuma ana shirye-shiryen kai ni kabarina. Don wallahi ba ƙaramin duka na sha ba a hannun matar Alhaji Nura da yayarta ba. Na ci wuya Katifa," faɗin Laushi tana mai kai hannu kan goshinta.
"To duk garin yaya a kai haka? Kuma ke kika tsaya? Gaskiya kin ban kunya. Sai ka ce ba ƴar bariki ba!" Ladi katifa ta faɗi cike da takaici.
"Bari! Bari Ladi!! Sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Su biyu fa! Ai wallahi na ma yi namijin ƙoƙari," ta faɗi tare da buɗe akwatin da Salma Nice ya ajiye a tsakar ɗakin ta fiddo pant da bra da kuma wata doguwar riga mai hula sannan ta rufe akwatin.
"Ni ba kiga na kasa magana saboda takaici ba? Ai wallahi zuciyata tafarfasa take akan wannan cin mutuncin da a kai wa uwar ɗakina.. Mtsw (Tsaki) wallahi takaici nake saboda ɗazu ba muyi mata dukan sakwara tare da karya ƙafar shegiyar sannan munyi mata tsirara ba. Kuma yanzu shikenan ta ci banza?" Fadin Salmanu ɗan daudu.
"Salma, to ai bala'in da take ciki yanzu ya wuce na karya ƙafa da tsirara don kuwa dai yanzu na san tana can ƴan sanda sun tasa ƙeyar ƴar banza. Wuƙa fa ta taho caka min, sai Allah ya tsare ni ta caka a cikin mijinta," Laushi ta faɗi tana mai ƙarisa saka bireziya ɗinta sannan ta saka doguwar rigar.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" A tare Salmanu ɗan daudu da Ladi Katifa suka faɗi.
"Wallahi kuwa. Yana can cikin jini a kwance sai tsartuwa yake. Wai kuwa kunga uban gudun da na sha? Hmm! To ai wannan dalilin ne ya saka a ka turo ku da Meema da kayanmu don zaman gidan Hajja Lanti ya fi ƙarfinmu kuma. Don na san ƴan sanda sai sun bi diddigina."
Wani kallo Ladi Katifa tabi Laushi da shi tare da faɗin, "Ban gane zaman gidan Hajja Lanti ya fi ƙarfin ki ba? Kina da wani wajen ne da yafi can ɗin? Kuma ai naga ba kece kika yi kisan ba."
"To shine nima na gani, Katifa!" Faɗin Salmanu ɗan daudu.
Kallon su Laushi ta yi tare da faɗin, "Wallahi ba ni ce na kashe Alhaji Nura ba. To don mai yasa zan kashe shi? Kun manta a gaban kowa da kuma matarsa ta sunna ya zaɓe ni sama da uwar ƴaƴansa? Kishi ne ya kai ta ga hakalaka mijinta, babu hannuna a cikin mutuwar Nura."
"To dama can kin yi niyyar barin gida Hajja Lantin kenan? Don idan ba haka ba ban ga ta yanda kisan Alhaji Nura ya ke da alaƙa da ke ba. Muma fa mun san manyan nan da hukumomin. Wallahi ko da ace ke kika yi kisan nan babu abunda zai faru da ke a cikin Lagos ɗin nan. Nawa suka yi kuma suka sha!" Salma Nice ya faɗi.
"Lallai ba ku da hankali da kuke cewa ban da alaƙa da kisan da a kai wa Nura! To wacece sanadi idan ba ni ba? Zan cen gaskiya ba zan koma gidan Hajja Lanti ba, daga nan gidana na yi," Laushi ta faɗi tana mai zubawa Meema harara kasancewar tsuru ta yi tana sauraran hirarsu.
"Don ubanki wannan zubo mana idanun na minene? Wato kin baza kunnuwa kina rekodin ko? To maza juya ki kalli can, kar ki kuskura in juyo mu haɗa idanu da ke!"
Da sauri Meema ta kau da idanunta ta kwanta flat a kan wani resting chair da ke ɗakin hawaye na zubo mata a idanunta.
"Don Allah ki daina tsangwaman yarinyar nan haka," fadin Ladi Katifa.
"Ta ma kashe ta kawai, Mtsw (tsaki) aikin banza da wofi!" Faɗin Salma Nice.
Murmushi Laushi ta yi sai da kumatunta ya loɓa tare da faɗin, "To kuyi haƙuri. Gani na yi ta zubo mana idanu kamar ta samu talabijin."
Babu wanda ya ce mata uffan, sai ma hararan da suka bita da shi.
"Dama ai kai na fara ƙyanƙyasa maka zancen barin gidan Hajja da zan yi, to yanzu lokacin ne ya yi. Salma don Allah zauna a nan kai da Meema bari na ɗan yi magana da Katifa a waje," Laushi ta faɗi.
Mera baki ya yi tare da faɗin, "Ba matsala ku je."
Ba tare da sanya mayafi ba Laushi ta fita daga ɗakin mazaunanta na motsawa duk yanda ta yi taku. Da idanu Salma ya bi Laushi da shi ciki zuciyarsa yana faɗin, "Mace har mace amma ta banza!"
Sai da suka nufi farfajiyar hotel ɗin ta baya sannan Laushi ta zauna a wani ɗan dandamali tare da nunawa Ladi wajen zama itama ta zauna.
"Ladi, wata magana na ke so muyi amma na roƙe ki da girman Allah ki faɗa min gaskiya. Kin fi kowa sanin ban da yarda sam, amma ke kina daga cikin waɗanda na amince da su ko da kuwa ban furta miki ba," Laushi ta faɗi tana kallon Ladi cikin idanu.
"Laushi, ki je kan maganarki kai tsaye. Ke ma kin san ba ƙawa ko abokiyar sana'a kawai na ɗauke ki ba, ke ɗin tamkar ƴar uwa kike a wajena," Ladi ta bata amsa itama tana kallon Laushin.
"Ladi, a ina kika san Sabo da kaza?" Ta jefa mata tambayar tana kallonta sosai domin ta ga reaction ɗinta.
"Sabo da kaza? Wanene haka ɗin? Wallahi ban taɓa jin wannan sunan ba idan ba yanzu a bakinki ba. Wanene shi?"
Wani ajiyar zuciya Laushi ta saki domin yanzu ta gama gamsuwa babu hannun Ladin a farin sanin da Sabo da kaza ya yi mata. Don ko iyayen Ladi ba zasu nuna mata sanin halinta ba.
"Wanda ya saya min gidan da zamu koma can," Laushi ta faɗa.
"To menene haɗina da shi kuma? Ta yaya zan yi alaƙa da shi bayan ban taɓa ganinsa ba, kuma ke ma baki taɓa nuna min shi ba? Laushi babu wanda zai faɗa min wacece ke a nan garin. Na san sam baki da yarda da aminci shiyasa ban taɓa damuwa da shiga shiga al'amuranki ba akan sai na san komai na ki. Kina zargina ne da wani abu?"
"Ladi, na ɗauko ruwan dafa kaina da alama. Kin san cewar kuwa Sabo da kaza ya san wani sirrina wanda ko ke ɗin nan baki san shi ba! Babu tarihina da bai sani ba. Ina tsoron kar ya yi amfani da hakan wajen azabtar dani nan gaba. Jikina ya yi mugun sanyi!"
Da idanu Ladi ke bin Laushi ka mun ta ce, "Wani sirri ne wannan wanda Sabo da kaza ya sani na ki?" Ta jefa mata tamabaya.
Shuru ta yi na wasu daƙiƙu kamun ta kama hannun Ladi Katifa duka biyun ta ce, "A lokacin da naje ɗauko sarƙar zinarin nan a gidanmu, babana ya dawo gida a wannan daren. Sai dai ya yi wani alƙawari a kan duk na kuma tako masa cikin gida sai ya kashe ni. Ina tunanin tun a hanyarsa ta dawowa daga Jos ya samu labarin zuwana gidan don kusan duk ƴan unguwan sun ga dawowana. Abbanmu na shigowa kai tsaye kitchen ya nufa ya ɗauko wuƙa ya taho ɗakin mamana domin kashe ni gadan-gadan. Na tsorata sosai ganin da gaske kashe ni yake son yi don sai kawo min sukar wuƙar yake yi da ƙarfinsa," tana kawowa nan ta yi shuru.
Ladi katifa kuwa ƙirjinta ba ƙaramin bugawa ya ke yi ba tana fatan Allah yasa ba abunda take tunani bane ƙawarta ta aikata.
Hawaye sosai Laushi ke yi. Ta jima kamun ta buɗe baki ta cigaba, "Kokuwa ce ta sarƙe a tsakaninmu har na yi nasarar caka masa wuƙa a cikinsaa!" Ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka.
Ƙamewa ƙam Ladi Katifa ta yi jikinta na rawa sosai don zahiri kake gani hakan.
"Wallahi tallahi ba da niyya na yi hakan ba. Ban da option ne. Kuma da shine ya samu damar kashe ni zai yi."
Sai a sannan bakin Ladi Katifa ya soma motsi ta shiga faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir!" Har sau uku.
"Ladi, Sabo da kaza ya san wannan sirrin nawa. Na rasa a ina ya sani. Hatta cikin da na yi na farko da zaman gidan magajiya da nayi duk ya sani."
Ladi katifa sai kallonta take yi da idanunta da su kai jajir ta kasa magana har sai da Laushi ta jijjigata da ƙarfi.
"Laushi wani irin rayuwa ce wanna?" Ladi katifa ta faɗi tana hawaye.
"Tsoro nake ji Laushi, tsoro nake ji sosai! Ta yaya kika iya cakawa Abbanki wuƙa a ciki? Ba zan iya ba! Ba zan taɓa iya hakan ba wallahi."
"Na rantse miki da darajar ubangiji ban kashe sa da gangan ba. Self defense ne wallahi. Shine mai niyyar kashe ni. Na fahimci kamar baki yarda da abinda na faɗa miki ba. Wallahi ban da wannan mummunar zuciyar da har zan iya kashe mahaifina da gangan. Ki yarda dani." Laushi ta faɗi.
Ajiyar zuciya Ladi ta saki tare da faɗin, "Na ji tsoro ne Laushi, jikina duk ya mutu. Abun ya tsaya min a rai. To amma mai yasa wancen ranar kika ƙi faɗa min gaskiya? Ke nan shiyasa kika kasa barci asubar fari kika saka muka taho nan?"
Gyaɗa kai Laushi ta yi tare da faɗin, "Gudun kar a kama mu shiyasa!"
"Laushi wallahi idan ni ce hakan ya faru dani, na rantse da girman Allah zuciyata ba zata taɓa nutsuwa ba kuma kullum a firgice za a riƙa gani na. Kai haƙƙin jini ma ba zai taɓa bari inyi tsawon rai har wannan lokacin ba. Amma tunda kin ce bisa tsautsayi ne, Allah ya tsare na gaba don wanna ya riga ya wuce. Sannan abu na gaba kuma, mai shi Sabo da kazan ya umurci da ki masa? Don na san ba zai taɓa siya maki gida banza. Sannan gashi ya tafi ya biɗo tarihinki gaba ɗaya. Dole akwai abunda ke zuciyarsa." Ladi Katifa ta faɗi.
"To ni dai na kasa ganewa Ladi. Har fa faɗa min yake wai ni ɗin maciya amana ce tunda har na iya ɗanawa Yasaar tarko aka kama shi shi wanda har yanzu yana Prison," Laushi ta faɗi.
"To ke yanzu, menene kika sani dangane da sana'ar da shi Sabo da kazan yake yi?"
Ɗan shuru Laushi ta yi tana tunanin anya ta faɗa mata duk sana'arsa kuwa.
"Kin yi shiru Laushi," Ladi ta faɗi tana kallonta da ɗan murmushi a fuska don ta fahimci ita kanta Laushin ba wani yarda ta yi da kanta sosai ba.
"Irin sana'ar Yasaar ɗin dai yake yi shi ma," faɗin Laushi.
Dariya Ladi Katifa ta yi tare da faɗin, "Yanzu na gano dalilinsa na yin bincike a kanki. Yana gudun ki yi masa abunda kika yiwa Yasaar ɗin ne shiyasa ya yi bincike a kanki domin samun abunda zai iya miki baraza gudun cin amanarsa. Amma a ginina idan har za ki kiyaye hakan baza ku samu matsala da shi ba."
Kallonta Laushi ta yi tare da faɗin, "Aikuwa idan hakane ban buƙatar fargaba don ko shi Yasaar ɗin shiga hancina ya yi shiyasa na ci amanarsa. Shi kuwa bai shimfiɗa min wasu dokoki ba, cewa kawai yayi bai buƙatar ganin wani saurayina a gidan idan har yana gari. Amma idan bai nan zan iya kawo duk wanda nake buƙata a cikin samarin nawa. Sannan zai ɗauke duk wata nauyi nawa da kuma na Meema."
"To! Amma dai shawarar da zan baki shine; ki bi komai a hankali don girman Allah ko don saboda Meema."
"To ai da ke za mu koma gidan. Wallahi ƙafata ƙafarki. Tare muka zo bariki, infact ke ce wacce kika kawo ni garin Lagos. Duk wani cigaba da na samu ke ce sila. Saboda haka tare za mu koma gidan," faɗin Laushi.
"To ya za muyi da Hajja Lanti?" Ladi ta faɗi.
"Ina ruwanmu da wata Hajja Lanti? Dama haya ce kuma mun samu na kanmu yanzu. Tsananin mu da ita yanzu sai sallama. Nii sai dai ma muyi ta waya don ni da gidan mata haihata-haihata!"
Dariya Ladi ta yi tare da faɗin, "Laushi ashe dai akwai abunda ke razana ki?"
"Bari! Bari Ladi! Na ga tashin hankali ganin idanuna. Allah dai ya tsare gaba," faɗin Laushi.
Hannu Ladi ta bata suka tafa tare da faɗin, "Ameen ƙawata!"
Gaba ɗaya suka miƙe daidai lokacin da wani mutum ya iso wajen da murmushinasa,
"Tsala-tsalan ƴan mata ya kuke? A taimaka min a ɗan ba ni aron mintuna biyar kacal! Tun ɗazu nake hango ku daga sama, naji kai bazan iya ba har sai na zo mun ɗan gaisa." Ya faɗi yana shafa cikinsa.
"To sannunka!" Faɗin Ladi Katifa don Laushi kallo ɗaya kawai ta masa ta kau da kai.
"A taimaka min da number waya don Allah," ya faɗi yana mai miƙawa Ladi wayarsa ƙirar _Motorola Rezar_.
"Ai ni ban da waya!" Ladi katifa ta faɗi yayin da Laushi ta yi gaba kaɗan domin ta basu damar tattaunawa.
Da gefen idanu ya bi mazaunanta da ido. Don har ga Allah wajenta ya zo amma ganin babu fuska sai ya mayar da aƙalan zuwa wajen Ladi Katifa.
"Haba! Tsaleliyar budurwa kamar ki a ce ba ta da waya a hannu. To ɗan jira ni mintuna biyar kacal idan ba damuwa," ya faɗi tare da saka hannu ɗaya cikin aljihun wandon jeans ɗin da ke jikinsa.
"Ok, babu matsala!" Ta faɗi shi kuma ya juya ya nufi hanyar baya domin shiga cikin hotel ɗin.
"Kin yi new catch kenan?" Laushi ta faɗi tana murmushi.
Kashe mata idanu Ladi ta yi tare da faɗin, "kuma na ga alamar kamar za a je da shi."
Gaba ɗaya suka kwashe da dariya. Bayan ƴan mintuna kaɗan sai ga mutumin ya dawo hannunsa riƙe da kwalin waya.
"To ga wannan ƴar ƙaramar ki maneji da ita kamun zuwa nan gaba. Wannan shine number ta. Idan kin kunna wayar sai ki min ko flashing ne. Ga wannan tsohuwar layin nawa ki amfani da shi."
Amsa Ladi Katifa ta yi tare da faɗin, "Nagode, sai ka ji ni," tana faɗin haka ta ƙarisa wajen da Laushi ke tsaye suka nufi cikin ɗakunan hotel ɗin.
Da kallo ya bi su, musamman Laushi da ya ke ganin kamar da gangan take kaɗa masa mazaune. Ko da suka shiga ɗakin, kwance suka samu Salma nice ya yi ɗai-ɗai yana sharar bacci. Meema kuma tana nan inda suka barta sai kalle-kalle ta ke a ɗakin. Ba su tashi Salma nice ba sai gab magrib.
"Ta shi a wannan baccin asarar mu tafi gida. Wanda ya kama ɗakin yana hanyarsa ta dawowa," Ladi ta faɗi.
Mittsike idanu ya yi tare da yin miƙa sannan ya ce, "Sanyin AC naji wallahi. To ke Laushi sai yaushe kenan za ki tare a sabon gidan naki?"
"Nan da kwana biyu. Kai ma ai tare za mu tafi da kai. Hajja Lanti sai dai ka riƙa zuwa mata ziyara," faɗin Laushi.
"Duk inda kika saka ƙafa ina wajen ai," Salma nice ya faɗi.
Har bakin gate ta yi masu rakiya sannan ta dawo ɗakin don har duhu ya soma yi. Tana shiga ɗaki ko zama bata yi ba aka yi knocking. Buɗe ƙofar ta yi sai ta yi arba da saurayin yaron ɗazu hannunsa riƙe da ƙatuwar farar leda. Amsa ta yi shi kuma ya juya.
Bayan ta rufe ƙofar sai ta dawo tsakiyar ɗakin ta buɗe ledan. Take away ne guda biyu wanda ke ɗauke da lafiyayyar jellof rice da kaza. Sai ƙatuwar gorar five alive da su kankana da apples.
"Sauko ga abinci nan ki zo kici," Laushi ta faɗi tana kallon Meema.
A hankali ta sauko ta zauna a ƙasa tare da jawo takeaway ɗin dama kuma yunwa take ji. Bayan sun gama ci Laushi ta tattare wajen sannan ta ƙara tsantsara kwalliya ta canza kaya mai suna fan ɗarinka tsirara sannan ta feshe turare a jikinta.
Ƙarfe takwas daidai Sabo da kaza ya shigo ɗakin. Kallon Meema da ke zaune ya yi tare da faɗin, "Ya za muyi da wannan yarinyar? Don gaskiya hutawa na ke so na yi da ke kamun in wuce don ba a nan zan kwana ba."
"Ba matsala sai ta jira mu a ƙofar ɗaki ai."
Da sauri ya kalleta tare da faɗin, "Kina ganin babu matsala? Nan fa hotel ne!"
#Sabo da Kaza #Laushi #Ladi Katifa #Meema #Sorrow #Regret #My Destiny #Matar Sayyadee
*** [2/15, 9:21 AM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._