Page 18
_You guys are really motivating me! I really love you comments. Keep it up 🤩🥰🤩👌_
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
"Kar ka damu babu wani abun da zai faru. Ai tana jin tsorona, da na kankara mata warning shikenan," Laushi ta faɗi.
"To ai shikenan! Da yake ma ƴarki ce," ya ƙarisa maganar tare da cire rigar shaddarsa.
Laushi ta nufi wajen da Meema ke kwance har bacci ya fara ɗibanta ta saka hannu ta bibbigi ƙafarta. A hankali ta buɗe idanunta gaba ɗaya kasancewarta mara nauyin bacci ko kaɗan.
"Tashi ki fita ki jira mu a waje. Kar kije ko ina ki zauna."
Kallonta Meema ta riƙa yi babu kyaftawa har sai da Laushi ta zaro mata idanu ƙasa-ƙasa ta ce,
"Ba na hana ki yi min irin wannan kallon rainin ba? Wata rana sai na kwakwule miki idanun don ubanki! Sauko ki fita, kuma ki gaishe shi kamun ki fita," ƙasa-ƙasa ta ƙarisa maganar.
"Cire kayanki za kiyi ko? Aunty wallahi babu kyau!" Meema ta faɗi.
Hannu Laushi ta saka ta ɗalle mata leɓe tare da zaro mata idanu ciki-ciki ta ce, "Ubanki ne zai riƙa kawo mana abinci da wajen zama idan ban yi ba? Fita ko inci ubanki da duka a ɗakin nan! Shegiya makira!!" Laushi ta faɗi tana nuna mata ƙofa.
Gaba ɗaya duk abunda ke faruwa akan idanun Sabo da kaza. Wani murmushi ya yi tare da girgiza kai.
Miƙewa Meema ta yi tare da nufa ƙofa ba tare da ta kalli inda Sabo da kaza ya ke ba balle ta gaishe sa. Har ta murɗa ƙofar ta fice yana kallon ta.
"Zeenah, dagaske wannan ƴarki ce?" Ya jefa mata tamabaya bayan ya mayar da dubansa gare ta.
Wani dariya ta yi tare da faɗin, "Baka ga kamanni ko ɗaya ba ko? Ai ni ban san inda ta ɗauko munin nan ba. Ni dai ka ganni fara tas nake kyakkyawa."
Ganin Laushi kwata-kwata ba ta fahimci inda ya dosa ba sai ya kau da maganar tare da faɗin, "Kuma wallahi ta fiki kyau nesa ba kusa ba. Hasken fata kawai za ki gwada mata. Kina ganin yarinyar kamar ƴar ƙasar Ethiopia. Gashin kanta ma kawai abun sha'awa ne."
Ɓata rai Laushi ta yi tare da faɗin, "Allah na fita kyau. Wancen baƙar!"
"Uhm! You're deceiving you're self don wallahi ko makaho ya shafa sai ya san ta fiki kyau. Anyway mu bar maganan don lokaci na ja, and nan hotel ne ya kamata yarinyar can ta dawo ciki da wuri," ya faɗi yana warware zariyar wandon shaddar da ke jikinsa.
"As you wish, your majesty!" Laushi ta faɗi tare da soma zame kayan jikinta.
_After 3hours_
"Ke! Kin san kuwa ƙarfe nawa? Wallahi sha ɗaya da mintuna takwas. Yarinyar nan fa na waje! Subhanallah, dubo ta maza. Bari na watsa ruwa ni ma na wuce suna can suna jira na wallahi," ya ƙarisa maganar tare da sauka daga kan gadon.
Da sauri Laushi ita ma ta duro tare da ɗaukar doguwar rigar da ta saka ɗazu ta saka sannan ta kunna wuta ta buɗe ta saka silifas ta murɗa ƙofar gabanta na faɗuwa.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Meema, Meema, kina ina? Na shiga uku wayyo Allah na," faɗin Laushi ta na yarfe hannu tare da bin dogon koridon da zai sadata da matattakala zuwa ƙasa. Sai dube-dube take amma bata ganta ba.
Kuka ta saka wiwi bayan ta fito harabar hotel ɗin tana waige-waige. Akwai mutane sosai a harabar kuma sai kallonta suke ganin tana kuka.
"Baiwar Allah lafiya kike kuka? Mai ya faru? Ina ƙawarki?" Mutumin da ya bawa Ladi Katifa waya ɗazu ya ke mata wannan tambayar.
"Ƴata! Ban ga ƴata ba. Na shiga uku!! Meeemaaaah!" Ta kuma kwala kiran sunanta tana kuka har da saka hannu biyu tana riƙe guiwarta.
"Ƴarki kuma? A nan cikin hotel ɗin? Ta yaya ta ɓata to? Ke garin yaya kika sake ta?" Ya jeho mata tambayoyin.
Ba ta tsaya ba shi amsa ba ta yi gaba tana dube-dube. Ta fi ƙarfin mintuna goma tana zagaye hotel ɗin tana kuka da kwala kira amma babu Meema. Wajen parking space ta nufa ita da saurayin Ladi Katifa suka riƙa leƙa motocin jama'a ko za su ga Meeman ko jin muryanta amma shuru har Sabo da kaza ya sauko ƙasa.
"Kin ganta?" Ya tambaya shi ma fuskansa da ɗan damuwa.
"Ban ganta ba! Na shiga kuwa ƴata!! Ina Meema ta ke? Ina ta shiga?"
"Wallahi ni ban so kika turata waje ba a cikin daren nan. Kun duba wajajan bishiyoyin can?" Ya ƙarisa maganar yana nuna wajen da hannu.
Da sauri ta nufi wajen, suka rufa mata baya da sauri suna haska wajen da fitilar waya kasancewar wuta bata wadata a wajen ba. Kwance suka ganta a kan wani dandamali ta ɗaura kanta a hannunta biyu tare da dunƙulewa tana bacci. Ajiyar zuciya suka sauke a lokaci guda, yayin da Laushi ta nufe ta da sauri ta ɗagota tana kiran sunanta. Buɗe idanu Meema ta yi tare da faɗin,
"Aunty har kun gama? Ina ta kwankwasa ƙofa kun ƙi buɗewa shiyasa na sauko na kwanta a nan. Kuma wani ma yana ta kira na wai in shigo ɗakinsa shine naƙi zuwa. Har chocolate ya kawo min naƙi amsa," Meema ta faɗi.
Sabo da kaza wani kallo ya yiwa Laushi sannan ya juya tare da faɗin, "Na wuce sai mun yi waya. Allah ya kiyaye gaba."
Laushi kuwa rungume Meeman ta yi tana jin wani abu na mata yawo cikin kai saboda labarin wanin da ya so Meeman ta bi shi amma Allah ya tsare ba ta bisan ba. Miƙar da Meeman ta yi tare da matso mata da takalmanta ta saka sannan ta kama hannunta tare da kallon sabon saurayin Ladi Katifa ta ce, Nagode sosai da taimakon ka."
Gyaɗa kai ya yi yana wani tunani cikin zuciyarsa. Can ya kalli Laushi kasancewar jerawa su kai suna tafiya tare da faɗin,
"Don Allah idan babu damuwa zan iya tambayarki?"
Sai da ta kallesa sannan ta kawar da kai tare da faɗin, "Eh, ina jin ka." "Na san dai wannan mutumin da ya wuce ba mijinki bane. Amma don Allah wannan yarinyar ƴarki ce dagaske ta cikinki?"
Murmushi ta yi don wannan ba tambaya bace da za ta ba ta mamaki don mutane da yawa sun sha yi mata kasancewar babu ta inda suke kama da Meeman.
"Ƴata ce ta cikina. Ni na haifeta, amma mai yasa kai min wannan tambayar?"
"Ki yi haƙuri don Allah. Don akwai tambayoyi sosai a bakina sai dai ban san ta yanda za ki fahimta ba," ya faɗi.
Murmushin dai da ya kasance ɗabinta ta kuma yi tare da faɗin, "Kar ka damu, ka yi min duk tambayar da kake so, ni kuma zan baka amsa."
Gyaɗa kai ya yi tare da faɗin, "Wanene mahaifinta? Rabuwa kuka yi ko mutuwa ya yi? Mai yasa kike zaune a hotel yanzu? Kuma ya aka yi kika bar Meema ta fito cikin dare nan? Allah ne fa ya tsare domin nan garin Lagos ne kuma cikin hotel. Akwai mutane iri-iri ciki kuwa har da masu safarar ƙananun yara da kuma ƴan shan jini har da masu fyaɗe."
Ɗan shuru ta yi kamun nan ta ɗago ta kallesa tare da faɗin, "Ni ban taɓa aure ba. Mahaifin yarinyar nan, ni kai na da na ɗau cikin ban san shi ba!"
Cak ya tsaya tare da faɗin, "Ban gane baki san shi ba? Fyaɗe a kai miki?" Ya faɗi with confusion.
"Eh, domin sana'a ta ita ce karuwanci! Ban san iya adadin mazan da na ke kwanciya da su ba a rana. Wallahi ba zan iya nuna uban Meema ba," Laushi ta faɗi.
Girgiza kai ya yi tare da faɗin, "This isn't true, maman Meema. Ta yaya za ki kasa gane wanene ubanta? Ai ko da kamanni kya gane tunda ga dukkan alamu ubanta ta biyo."
"Halan baka ji statement ɗina ba da kyau? Wallahi tallahi ba zan iya nuna ubanta ba. Don a rana ba zan iya ƙidaya mazan da suke kwanciya da ni ba. Domin wasu ma sau ɗaya na taɓa ganinsu kuma tun daga wannan lokacin ba mu kuma haɗuwa ba. Wasu ma ba ƴan garin bane matafiya ne kawai. Kuma a wannan lokacin ba ruwana da ƙarewa mutum kallo burina kawai ya yi abunda zai yi ya gama ya biya ni ya ƙara gaba," Laushi ta faɗi da iya kacin gaskiyarta.
Jinjina kai ya riƙa yi kamun ya ce, "Ok na fahimta. To amma mai yasa kike yawo da yarinya idan za ki tafi sana'arki wanda kin san it isn't safe. Yanzu ki duba ki gani, da yanzu wannan yarinyar da baza ta wuce 9 ba mugun hannu ta faɗa fa? Duk wannan rayuwar da kike yi, ko kuma in ce da muke yi tunda dole in saka kai na tunda ni ma matan na ke bi, baza mu taɓa so mu ga ƴaƴanmu suna yi ba. Don Allah ki kiyaye hakan."
Gyaɗa kai Laushi ta yi tare da faɗin, "In Sha Allah! Yanzun ma tsautsayi ne. Nagode da shawara."
"Idan babu damuwa ki faɗa min inda kike da zama mana. Ko nan kike zama?"
Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "A'a, ba nan nake da zama ba. Nan da 2days zan koma gidana a nan cikin Lagos. Sai dai fa bari na ɗan yi saurin taka maka burki, ba zan bari wani alaƙa ya shiga tsakanin mu ba saboda ƙawata. Don ita ce budurwarka."
Murmushi ya yi tare da shafa gemunsa ya ce, "Ban taɓa ganin haka a bariki ba. Na san dai duk iya amintar ƙawa da ƙawa in dai a bariki ne bai hana su cin amanar juna. Kuma har ga Allah wajenki na nufo amma ganin baki ban fuska ba sai na juya aƙalata zuwa ga ƙawarkin. Amma duk da hakan babu matsala. Ƙawar takin ma ai ta yi duk da kuwa ba haɗuwa muka yi ba. Ki ban contact ɗin ki ko gaisawa sai mu riƙa yi."
"Hakan ya yi, 0803333........ Za ka iya saving da Zeenah ko kuma Laushi," ta faɗi tare da yin gaba don sun iso reception ɗin.
"Maman Meema will be better! Zan kira yanzu, sai ki saving da Habibu." Ya faɗi yana murmushi.
Juyowa ta yi ta sakar masa murmushin shima sannan ta shige ta nufi matattakalar da zai sadata da ɗakin da Sabo da kaza ya kama mata.
"Ashe ke jahila ce ban sani ba? Daƙiƙiya wawuya mahaukaciya. Wannan ba komai ba ne face ɗabi'un dabbobi! Yanzu mai kika aikata kenan? Wallahi duk hukuncin da mahaifinku ya yanke a kanki ko tari bazan yi ba balle in bashi haƙuri. Ba ki da iyaye ne ko kuma shi Nuran bai da su ne? Sha-sha-sha dabba! Ki tashi ki kwashi zugan ƙawaye ku tafi har gidan karuwar domin faɗa da budurwar miji! Wallahi kin ji kunya. Yanzu wa gari ya waya?" Faɗin mahaifiyar Marwanat matar Alhaji Nura.
"Wallahi tallahi Ummu ba budurwarsa bace, karuwars......" Da sauri ta rufe bakinta da hannu biyu sakamakon wawan dukan da babban wansu ya kai mata a baki.
"Shegiya sakarya banza! Kuma wallahi ko mai ƴan uwan Alhaji Nura za suyi maki babu uban da zai saka baki ko da kuwa gidan yari za su tura ki." Yayan nata ya faɗi.
"Ummu dan girman Allah ku yi haƙuri ku saurare ni. Ai Nuran bai mutu ba. Yana asibiti likitoci sun ce Allah ya taimaka wuƙar bai taɓa kayan cikinsa ba. Wallahi ina son mijina. Kishi ne ya kai ni ga aikata aikin dana sani," Marwanat ta faɗi.
"Mu za ki faɗawa bai mutu ba? Mun fiki sanin haka ai tunda a gabanmu a kai komai. Kuma kin san Allah, Ni da kai na zan yagi biro da takarda in ba Nura ya sauwaƙe miki. Kuma wallahi ba za ki zauna min a nan muna haɗa kafaɗa ba, can Lafiya zan tura ki wajen goggo Sa'a ai maganinki a can," Ummu ta faɗi bayan ta zabga kwafa.
"Na shiga uku, na shiga uku ni Marwa! Rana zafi inuwa ƙuna. Wai ni kaina!! Allah ya tsine miki Laushi! Allah ya isa tsakanina da ke! Ubangiji ya saka min akan wannan abun da kika min. Kece kika ja min duk wannan. Allah ya hana ki farin ciki a rayuwarki gwargwadon yanda kika ƙuntata min," Marwanat ta faɗi tana kuka sosai.
A fusace ya faɗo ɗakin hannunsa da wata narkekiyar bulala yana wurga idanu a parlourn. Marwanat da ganinsa ta yi wani tsalle ta koma bayan gujera. Yana hango ta ya nufi wajen har da haɗawa da gudu. Sai da ya cire malum-malum tukun ya ja ƙafar wandonsa sannan ya tsallaka kujeran ya ɗaga bulalan ya dunga shimfiɗa mata bulalan tare da haurin cikinta a lokaci guda. Ihu kawai ta ke yi tana kiran nai man taimako. Hatta Yaya Aliyu da ke zaune a parlourn ya tausaya mata ganin irin dukan da Baffan na su ke mata.
Ummu da Inna ƙarama (Mahaifiyar baffa) ne suka fito daga wani ɗakin da ke cikin parloun. Ganin mahaukacin dukan da ɗan nata ke wa jikarta bata san lokacin da ta isa wajen ba tana faɗin,
"Kai, Modibbo ya isa haka! Dukan nan ya isa haka. Na san Marwa bata kyauta ba kwata-kwata. Amma duka ba shine magani ba. Allah huci zuciyarka."
"Inna amma......" A mugun zuciye ya soma magana amma sai Inna ƙarama ta ɗaga masa hannu alamar ya isa.
"Zauna nan, Modibbo. Ke Nafisa ɗauko masa ruwan gora a firji ya sha zuciyarsa ya yi sanyi," Inna ƙarama ta faɗi.
Juyawa Ummu ta yi tare da yin abunda Inna ƙaramar ta umurce ta da ta yi. Sai da ya sha ruwan kusan rabin gora sannan ya kalli Inna ƙarama tare da faɗin,
"Inna, Yarinyar nan jahila ce. Yanzu fisabilillah sai ta kwashi ƙawaye su tafi gidan karuwai da mutuncinta na aure domin faɗa da budurwar miji! Tur! Wannan ba tarbiyar gidan nan bane wallahi. Ni kin san mai ya fi ƙona min rai kuwa? Irin yanda Marwa ta taka ƙafatan ta tafi gidan karuwa da kuma yunƙurin ƙisan kan da ta yi. Na yi miki imani da Allah, Inna da yarinyar nan ba ta ɗau wani mataki da hannunta ba, da zan tsaya mata har sai inda ƙarfina ya ƙare domin ni ma ban goyi bayan zama da fasiƙi ba. Amma tunda haka ta zaɓa, sai ta yiwa kanta maganin matsalarta. Yanzu haka wannan maganar da nake maki, ƴan uwan wannan yaro Nura da ta yi ƙoƙarin kashewa suna can suna bala'i akan ba zasu yarda ba. Kuma ke don ubanki kin fi kowa sanin wacece uwarsa a kan ƴaƴanta. Ai tun farko sai da na faɗa mata ban yarda da tarbiyar Nura ba don haka ba zan bashi aure ba. Amma Yarinyar nan har da ke mahaifiyata sai da ta haɗa mu, bayan takakkiya da ta yi daga nan Lagos har Adamawa wajensu Baffa Mamman da su Hamma Tukur. Haka nan ba don raina ya so ba a kai auren. Kuma ai kece kika hana shi yin aure don ba sau ɗaya ko biyu ba, Nura ya zo gidan nan yana faɗa min zai sake aure, amma daga kwana biyu sai inji shuru. Duk kin bi kin ɗaga masa hankali. Kece fashe-fashen kayan ɗaki. Zaginsa har titi da yaga masa kaya. Shekaru biyu da suka wace har asarar motar miliyan huɗu kika masa. Ba ma wannan ba Inna, akwai lokacin da saura sati biyu ɗaurin aurensa da wata ƴar bayarabiyar yarinya, amma wannan yarinya ta dunga tsorata yarinya da iyayenta, daga ƙarshe gidan ta je da fake result akan tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki. Wallahi a haka aka fasa auren nan. Kun ga kenan duk abunda Nura ya aikata da saka hannun Marwa don ke ce kika nuna masa sa kishiyar gida gwara ta waje. Kuma yanzu abunda nake so da wannan yarinyar, tunda ba sakinta ya yi ba ta tashi ta bar gidan nan ta tafi ko can gidanta ko kuma asibiti. Babu ruwana ko dafata dangin Nura za suyi!" Yana gama faɗin ya miƙe ya soma tafiya.
Har ya yi taku uku, sai kuma ya juyo tare da faɗin, "Ina babbar daƙiƙiyar jakar da ta biye maki kuka yi faɗa a titi? Ta fito ta bar min gidana yanzu!"
_Ƴan laɓe marasa comments, masu jira a yi update su karanta su koma gefe, duk ina sane da ku kuma tabbas kun kusa jin ku a waje🤷_
#Meemah #Habibu #Laushi #Baffa #Marwanat #Alhaji Nura #My Destiny #Matar Sayyadee
*** [2/15, 9:21 AM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._