My Destiny (Ƙaddarata)

Page 19

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Kamar munafuka aunty Zubee ta fito daga maɓoyarta can wajen koridon hanyar kitchen tana raɓe-raɓe gabanta na faɗuwa don a idanunta baffa ya yiwa Marwanat mugun duka. Wani zuciya ce ta kawowa baffa wuya, bai san lokacin da ya nufi aunty Zubee ba tare da haɗa kanta da bango sannan ya dunga ɗauke fuskanta da mari tana ihu.

"Dan girman Allah Baffa kai min rai! Wallahi tsautsayi ne ba zan sake ba. Kuma na rantse da girman Allah sai da na ce mata kar ta kashe ta amma bata ji har sai da ta cakawa mijinta wuƙa garin kashe budurwar, don Allah Baffa ka yi haƙuri," Aunty Zubaida ta faɗi tana ihu.

"Don ubanki har kina da bakin ce min in yi haƙuri? Yanda kika kaso na ki auren haka kike son kashe na ƴar uwarki ko? To maza ki haɗa kayanki ki wuce wajen Hamma Tukur a Yola yanzu nan kada zuciya ta ɗebe ni in yi aikin dana sani!"

"Modibbo ka bar gidan nan kar yaran nan su saka maka hawan jini, ko kuma ka shige ɗakinka ka kulle ƙofa har sai hankalinka ya kwanta." Faɗin Inna ƙarama.

Jefar da bulalan Baffa ya yi tare da wucewa side ɗinsa. Umma kuma ta kalli Marwanat tare da nuna mata hanyar waje. Jiki na tsami ta miƙe tana sharar hawaye ta fice daga ɗakin tana jin wani irin tsanar Laushi a cikin zuciyarta.

Da sassafe wajajen ƙarfe bakwai da rabi, Habib saurayin Ladi Katifa ya nufi ɗakin Laushi hannunsa riƙe da ledar take away guda biyu a cikin leda da kuma wani madaidaicin flask ya yi knocking ƙofar. A wannan lokacin Laushi ta na cikin bargo tana bacci don sosai jikinta ke mata tsami. Meema ce ta farka tuntuni har ta shiga bayi ta yi alwala ta yi sallah, kwanciya kawai ta yi cikin bargon a bayan mahaifiyarta wacce tun jiya ko juyi ba ta yi ba bare ta tashi ta yi sallah.

Jin knocking na biyu, sai ta yaye bargon ta sauko daga kan kadon tare da saka silifas sannan ta nufi ƙofar tare da faɗin, "Who is that?"

Murmushi Habib ya yi jin muryan Meema, don haka nan Allah ya ɗaura masa ƙaunarta.

"It's me, Uncle Habib. I brought breakfast for you and your Mom," ya faɗi still murmushin be bai fuskansa ba.

"A minute please! Let me talk to Mom first, she's sleeping." Ta faɗi tana ƙoƙarin juyawa ya yi saurin dakatar da ita,

"No, don't wake her up! Ki buɗe kawai ki karɓi breakfast ɗinki," Habibu ya faɗi.

Sai da Meema ta juya ta kalli Laushi da ke bacci sannan ya juyo ta kalli ƙofar, a hankali ta murɗa ƙofar ɗakin ta buɗe ta leƙo da kanta kaɗan tare da ɗaura yatsanta a kan bakinta ta furta, "Shssh! She's sleeping. Shigo a hankali and don't mai noise."

Gyaɗa mata kai ya yi tare da kama ƙofar a hankali kada ta yi ƙara sannan ya soma sanɗa har ya shigo ciki.

"Sit-down here and don't maka sound," ta raɗa masa a kunne bayan ta nuna masa resting chair ɗin da ke nesa da gadon.

Sosai ta ke bashi dariya saboda yanda ta ke magana ciki-ciki da kuma yanda ta ke tafiya kamar wata robot duk don kar ta tada uwar. A hankali ta hau gadon ta ja mata bargo har wuyanta sannan ta sauko ta zauna a kan Centre rug ɗin da ke shimfide a ɗakin. Shima saukowa ya yi tare da fiddo takeaway ɗaga daga cikin ledan tare da madara, bounvita da suger.

"In haɗa maki tea!" Ya faɗi cikin raɗa.

Ita ma cikin raɗan ta ce, "Eh, uncle. But please don't make a single sound."

Gyada mata kai ya yi tare da saka hannu ya fiddo ƙaramin cup ya juye bounvita da madarar da suger sannan ya buɗe ƙaramin flask ya soma tsiyaya ruwan zafin bayan ya mata alama da hannu akan idan ya isa ta dakatar dashi.

"It's ok! It's okay!!" Ta faɗi cikin raɗa-raɗa.

Ajiye flask ɗin ya yi sannan ya motsa mata tea ɗin tare da miƙa mata sannan ya buɗe robar takeaway ɗin da ke ɗauke da Irish da kwai da miyan albasa.

"Wow! My favourite," Meema ta faɗi tana jin daɗi.

"It's all yours. Ki cinye duka. Ga na mom ɗinkin nan, idan ta tashi sai ta ci.

Thumb up ta yi masa tare da kai Irish da kwai ɗin da ta cako da fork a baki.

"Wow, delicious! Have this," ta faɗi tare da kai masa fork ɗin da ta cako Irish a baki.

Bayan Salma nice da Sadiya, Meema ba ta taɓa sakewa da wani namiji ba haka sai yau da ta haɗu da uncle Habib.

"Uncle Habib, you're really nice. I like you. And do you know what?" Sai ta kawo bakinta daidai kunnansa tare da faɗin, "I heard what you told my mom yesternigh."

Da sauri ya kalleta don tsaya mintuna goma da suka yi yanzu ya fahimci Meema akwai wayo da ƙwaƙwalwa, she's indeed very Sharp.

"What did I tell your mom yesternigh?" Ya tambayata yana kallonta. Duk a cikin raɗa su kai maganar.

"Haka ka ce; Duk wannan rayuwar da kike yi, ko kuma in ce da muke yi tunda dole in saka kai na tunda ni ma matan na ke bi, baza mu taɓa so mu ga ƴaƴanmu suna yi ba. Don Allah ki kiyaye hakan."

With shocked and mouth agape ya ke kallon Meema, a yanayin girma da shekarunta bai taɓa tunanin za ta iya haddace ko kuma fahimtar maganganun da suka yi da mamanta ba.

"Uncle, ni ma kenan idan mom ba ta daina cire kaya a gaban maza suna taɓa jikinta ba, ni ma wata rana zan yi haka? Allah ya kiyaye ko a yanzu da nake ƙarama ba zan cire kaya a gaban kowa ba balle kuma idan na girma kaman mum," ta yi maganar kuma ta ba kanta amsa cike da tsanar abunda mom ɗin take yi.

Rasa mai zai ce mata ya yi. Can ya soma in'ina tare da faɗin, "Umm.... A.... Umm.... In Sha Allah haka ma ba zai faru ba. Ai ke ɗin tamkar lulluɓaɓɓiyar lu'u-lu'u kike. Babu ke babu irin rayuwar da mahaifiyarki ta ke yi."

Meema kallon Laushi ta yi sannan ta mayar da dubanta ga Habib tare da faɗin, "Can we please go outside and talk?"

"Sure!" Ya faɗi tare da miƙewa tsaye ita ma ta miƙen.

Shi ya soma fita ita kuma ta biyo sa a baya sannan ta rufe ƙofar a hankali saboda kar Laushi ta farka. Sai da suka ɗan ƙara mintuna biyu sannan suka wuce zuwa downstairs. Can bayan gidan saman suka nufa suka zauna a kan wani kujera. Zama sosai Meema ta yi har da tankwashe ƙafa sannan ta ce,

"Uncle menene ma'anar Karuwa? Kuma mai yasa can gidan da muka baro ni da mamana, matan gidan suke bari ana taɓa su kuma suna cire kaya a gaban kowa? Me yasa ni bani da babana kamar kowa? Idan na tambayi mom ɗina ina babana y ke sai ta hau zagina tana ce min wai ko ita ma bata san shi ba? Ko sayo ni aka yi a kasuwa? Ko kuma tsintata aka yi??"

Wani wawan tagumi Habibu ya zabga yana kallonta speechless har sai da Meema ta saka hannu ta girgiza hannunsa sannan ya dawo daga dogon tunanin da ya fada.

Hannunta ya kama tare da faɗin, "Meema, promise me ba za ki ƙara tambayar kowa wannan tambayoyin da kika min ba, Ni kuma na miki alƙawarin duk lokacin da kika yi hankali za ki fahimci komai ba ma sai na baki amsa ba. How old are you now??"

Sai da ta ɗaga kai sannan ta ce, "I was born September, 06, 1999. I'm 8 and 10months years. I will be nine this year (2008) on September 06, In Sha Allah."

"Ma Sha Allah! Allah ya raya ki. Kin yi min alƙawarin?"

Hannu ta miƙa masa tare da faɗin, "Na yi Uncle." Sannan ta mintsili hannun alama alƙawari.

"To yanzu tashi muje in sayo maki wani abu kamun mummy ta tashi." Ya faɗa tare da miƙewa.

"Ki jira ni a nan in ɗauko key ɗin mota in dawo. Kar ki je ko ina kin ji, Meema?" Ya faɗi yana shafa kanta.

Gyaɗa masa kai ta yi tare da jingina da motar, shi kuma ya nufi cikin enterance ɗin ɗakunan. Mintuna biyar ya dawo hannunsa riƙe da key. Shi ya buɗe mata gidan gaba ta shiga, shi kuma ya zaga ya shiga mazaunin driver ya tada motar. Kai tsaye wani shopping complex suka nufa. Babu abunda Meema ke yi sai farin ciki lokacin da ta ganta a gefen wajen da teddies suke. Guda huɗu ta kwasa, ɗaya jakar baya ce ta elephant. Sai ƙaton teddy bear Wanda ya kasance grey colour da kuma teddyn babie wai launin pinki. Daga nan suka koma wajen chocolate, nan ma ta ɗibi kala-kala sannan suka fito daga mall ɗin suka nufi bakin ruwa. Ba ƙaramin farin ciki Meema ta yi ba, don tunda take bata taɓa zuwa bakin beech ba sai yau. Sai ta tafi da gudu kamar za ta je kusa da wajen sai ta dawo da gudu. Daga karshe uncle Habib ya kama hannunta suka nufi wajen. Sai da ruwan ya taɓa su sannan suka dawo suka zauna a kan wasu kujerun da ke nesa da su kaɗan suna kallon masu wasa a cikin ruwa. Sun jima a wajen don sun ɗauki hotuna kala-kala sannan suka bar wajen lokacin karfe sha ɗaya da mintuna sha bakwai.

Daga nan suka nufi yawo zaga gari cikin mota. Uncle Habib ya buɗe mata saman motar ta leƙo tana kallon sauran motocin da suke kan titi suna gudu. Idan wata mota ta wuce su sai ta hau ihu tana ce masa shi ma ya yi gudu ya wuce su. Ƙarshe ɗaya ya tsaya gaban wani masallaci ya ce mata ta zauna a mota bari ya yi sallah ya dawo. Ta so binsa amma ya nuna mata ta zauna a motar saboda masallacin na maza ne babu na mata. Mintuna goma ya fito ya shiga motar, daga nan ya wuce nearest restaurant ya yi masu oder ɗin abinci takeaway uku sannan ya juyo kan motar zuwa restaurant.

Ɓangaren Laushi kuwa, sha biyu da mintuna sha daya ta farka daga bacci tun jiya. Kuma daman kamun ta kwanta sai da tasha wiwi ɗinta da codine shiyasa ta jima a kwance. Jiki a mace ta miƙe daga kan gadon ga wata uwar yunwar da take ji. Kai tsaye bayi ta faɗa ta watsa ruwa tare da yin brush. Towel Kawai ta ɗauro ta fito. Sai a sannan ta lura da takeaway ɗin Irish ɗin da Meema ta yi amfani da shi da kuma flask da cup. Kallon kan gadon ta yi, sam bata lura babu mutum a kan gadon ba saboda yanda bargo da ta yaye a jikinta ya bata shape ɗin kamar mutum ya lulluɓe. Sai ta ɗauka Meema ɗin ce a kwance.

"Gaskiya na jima ina bacci. Wato har Sabo da kaza ya kawo min abincin kari kenan. To kuma ai baya garin! Ohh ina jin wannan ɗan saurayin ya aiko." Duk a cikin zuciyarta ta yi maganan.

Ba ta jira ta saka kaya ba, ta haɗa tea a cup ɗin da Meema ta sha tea sannan ta buɗe takeaway ɗin ta soma cin Irish da tea din. Sai bayan ta gama sannan ta miƙe ta buɗe akwatinta ta ɗauko wani wando fela da yellow ɗin riga mai siririn hannu ta saka. Kwalliya ta yi a fuska wanda ya mata kyau. Wayarta ta jawo wanda Sabo da kaza ya bata ta buɗe bayan wayar ta cire sun ɗin da ke ciki ta saka ainihin sim ɗinta sannan ta hau kwala kiran sunan Meema domin ta tashi ta yi wanka.

"Meema, Meema, Meeemaaaah!" Ta ƙarisa da ƙarfi ranta na ɓaci saboda ta san Meeman ba ta da gigin barci amma still shuru babu amsa.

Hakane ya fusata ta, sai ta janyo bargon da ƙarfi. Daskarewa ta yi a tsaye ganin babu kowa a kan gadon. Wani irin jifa ta yi da gyalen tare da da ɗaukar hula ta daura a kai ta buɗe ƙofa ta fice da sauri tana kiran sunan Meema hankali tashe.

Kiciɓis suka yi da Ladi Katifa da Salma nice za su shiga cikin reception ɗin.

"Lafiya? Mai ya faru kike wannan gudun haka?" Faɗin Ladi Katifa bayan ta kamo hannunta biyu.

"Meema ce, ban ganta ba. Babu ita a ɗakin. Na duba ko ina a sama ban ganta ba." Ta faɗi hankali tashe.

"Ban gane baki ganta ba? Ba a ɗaki kuka kwana tare ba? Zeenah gaskiya ba ki da hankali!" Faɗin Ladi Katifa tare da juyawa gabanta na faɗuwa.

"Allah dai ya yi wadaranki wallahi! Yanzu ta ina za mu fara neman Meemah? Ohh ni Salma! Gaskiya Meema ba ki dacen uwa ta gari ba." Faɗin Salma nice.

Laushi ba ta kula su ba ta nufi inda su ka ga Meeman jiya, amma bata wajen. Hankali tashe ta nufi parking space tana leƙe-leƙe har ƙarshin mota. Tana ɗagowa motar Habib na shigowa cikin hotel. Tun da ya hangi Laushi da su Ladi Katifa hankali tashi ya yi murmushi don ya san sun ɗauka ta ɓata ne.

"La! Ga aunty Ladi da aunty Salma ce. Kai har da mummyna. Wata ƙila sun ɗauka na ɓace kamar jiya," Meema ta faɗi.

Sai da ya daidaita parking sannan ya fito ya zagayowa ya buɗewa Meema murfin mota ta fito.

"La! Ku duba gata can tsaye da wani," Salma nice ya faɗi yana nuno Meeman.

Da sauri Laushi ta ƙariso wajen ranta a ɓace. Amma kamun ta yi magana Habib ya rigata magana, "Afuwan mummy! Laifina ne. Mun ɗauka zamu dawo da wari har baki tashi ba. Ai mun afuwa ban tambayi permission ba na fita da ita. Gashi na baku wahala."

"A'a ni kam Allah ya isa wannan uban bugun zuciya da ka saka na yi. Wannan ai mugunta ne. Lala-lala haza aramun," faɗin Salma nice.

Baki sake Habib ke kallonsa ganin yana rangwaɗa da fari kamar mace. "Kai kuma wanene?"

Da sauri Meema ta ce, "Aunty Salma ce fa!"

"Ina Aunty Salmar? Ban ganta ba, sai wani garjejan ƙato da na gani a gaba na." Habib ya faɗi.

Meema kuwa zaro idanu ta yi tare da toshe bakinta don ta san yau kam uncle Habib ya taro match tunda ya tura aunty Salma nice jinsin ƴan maza.

"Wallahi, ina maka mummunar rashin mutunci yanzu a nan wajen ka kuma turani jinsin ƴan maza! Wannan ai iskanci ne. Kalli da kyau, mace ce shimfiɗeɗiya a gabanka. Mazaunai da ƙirji ga sunan luɓu-luɓu. Idan kuma tantama kake a hotel muke ga ɗakuna nan birjik sai a buɗe maka ka gani," Salma nice ya faɗi yana jujjuyawa.

"Ni jikan Rahila da Usman! Raba ni da mummunar gani. Wannan mummunar ji da na yi ma, Allah ka taimake ni kar na kurmance," faɗin Habibu da shi kansa dariyar ya ke son yi amma yana gitsewa.

Salma nice kuwa hannunsa biyu ya dafa a ƙasa ya shiga rawa da mazaunansa. Da sauri Habib ya saka tafin hannunsa ya rufewa Meema idanunta.

Duk wannan hirar da suke yi, Ladi gaba ɗaya hankalinta na kan Habib ɗin don sai yanzu ta ƙare masa kallo, wani irin sanyayyan kyau da kyawun hali gare sa. Dogone sosai mai hasken fata amma ba irin dau ɗin nan ba. Yana da dogon hanci da yayi kyau da fuskanta. Idanunsa ba manya bane kuma ba ƙanana ba, sannan yana da zane biyu a gefe-gefen fuskansa kamar na mallawa.

Shi kuwa Habibu gaba ɗaya tunaninsa da zuciyarsa yana ga Laushi musamman shigar da ke jikinta da ya kuma drawing attention ɗinsa. Gaba ɗaya hips ɗinta sai rawa suke duk sa'ar da ta motsa jikinta. Wandon ya mata kyau sosai. Cikin nan nata a ɗame wanda hakan ne ya ƙara fidda ainahin shape ɗinta..

"Yi haƙuri Salma ki bar rawar haka. Yanzu kam na gane ke ɗin jinsun su Aunty Laushi kike," fadin Habib wanda ya kasa riƙe dariyarsa.

"Yanzu na ji batu!" Faɗin Salmanu ɗan daudu yana mai miƙewa tsaye tare da riƙe ƙugu.

"Sabon catch ɗinki ne wannan ɗin," Salma nice ya kuma faɗi yana mai nuna Habib da hannu bayan ya kalli Laushi.

Murmushi Laushi ta yi tare da nuna Ladi Katifa ta ce, "Saurayinta ne. Jiya suka haɗu lokacin da muka fita muka barka a ɗaki."

Kafeta da idanu Habibu ya yi tare da faɗin, "Yaushe mu kai haka da ke, Aunty Laushi? Ni na ce miki budurwata ce? A'a, wani taimako za ta min domin samun wani abu mai mahimmanci a rayuwata."

Gaban Ladi Katifa wani irin bugawa ya yi lokaci guda tana kallon Habib babu ko kyaftawa. Yayin da Laushi ta saki baki ita ma tana kallon Habibun don ta san dai ko jiya sun yi magana ya nuna mata ladin ya ke so. To menene na kuma canza magana yanzu.

Juyowa Ladi Katifa ta yi tare da yiwa Laushi wani irin kallo daidai lokacin da wayar hannu Laushi ya yi ƙara, sai dai unknown caller taga an rubuta. Ɗagawa ta yi ta kai kunne, wani irin zaro idanu ta yi tare da ja da baya ta juya da sauri.

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihir!! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!!! Na shiga ni Zeenah, na shiga ukunaaaaa"

_Uhm! Wani bala'in ka ke son haɗawa oga Habibu? Wanene ya kira Laushi a waya ya firgitata haka? Har na fara jin zazzaɓi😬_

#Laushi #Ladi Katifa #Habib #Meema #Unknown caller #My destiny #Matar Sayyadee

*** [2/15, 9:21 AM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._