My Destiny (Ƙaddarata)

Page 20

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

"Zeenatu Ayuba Laushi! Kina tunanin zan ƙare rayuwata a magarƙama ko? To ƙaryanki wallahi! Ki fara ƙirgen ranakun farin cikinki daga yanzu. Domin wa'adin zamana a gidan yari ya kusa ƙarewa. Dama kuma na faɗa miki ba zan ɗauki adadin shekarun da alƙali ya ɗiba min ba. Zeenah sai na wulaƙanta ki a idanun duniya gaba ɗaya. Sai na saka labarinki ya zama abun kwatance a duniya. Yanzu haka ina cikin Prison amma na iya sakawa aka binciko min ke da kuma number ɗinki. Mai kike tunanin zan iya aikatawa idan na fito? Sai na kunyataki, na muzantaki ta yanda kare sai ya fiki daraja wallahi. Sai kin san cewa YASAAR ba abun yaudara da cin amana bane. Ba na yafiya sam a rayuwata!" Yana gama faɗin haka ƙit ya kashe wayar.

Wani irin mummunar zufan tashin hankali ya dunga tsiyayo mata tun daga tsakiyar kanta har fuskanta. Jikinta ya hau wani irin ɓari ta shiga nanata Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un har sau uku.

"Yasaar! Na shiga uku na lalace. Ya Allah ka rufa min asiri kar wannan bawan naka ya cutar dani," Laushi ta faɗi da mummunar tashin hankali tana zagaye-zagaye.

Habib ne ya yi saurin bin bayanta ganin yanda ta ruɗe. Salma nice da Ladi Katifa kuwa tsaye suka yi suna kallon Habib da ya bi Laushi fuskansa ɗauke da damuwa.

"Wai tsaya, ban gane ba. Wannan Saurayinki ne ko na Laushi? Ba shine wanda ya saya maki wannan wayar hannunki ba? Ina ce yanzu da muke hanya kika ban labarinsa. Har ce min ki kai kin yi mafarkinsa jiya," Salmanu ɗan daudu ya faɗi.

Ba tare da Ladi Katifa ta ba shi amsa ba ta duƙa kusa da Meema tare da faɗin, "Meema, jiya dawa-dawa kuka kwana a ɗaki tare??"

"Ni da mummy kawai muka kwana a ɗakin. Wannan ma wanda yazo jiya, ai bai kwana a ɗakin ba. Mummy ta ce in gaishe sa amma naƙi saboda ya sa mummyna tana cire kaya a gabansa yana taɓa ta. Na tsane shi, I hate him with passion!" Meema ta ƙarisa maganar da ɗacin rai.

Wani dogon numfashi Ladi ta ja tana kallon wani waje a duƙen, can kuma sai ta kalli Meema tare da faɗin, "To ya shigo ɗakin jiya sun hira da mom ɗinki?"

Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "A'a. Amma sun yi magana lokacin da suka fito nema na jiya da daddare."

Da sauri Ladi katifa ta kama hannun Meema tare da faɗin, "Mai suka ce?"

Ɗan ɗaga kai Meema ta yi tare da faɗin, "Akwai yawa maganganun da suka yi ai."

"Na san kina da wayau sosai. Za ki iya tunawa duka. Faɗa min kin ji!" Ladi Katifa ta faɗi cike da zaƙuwa.

"Kin san mai ya ce mata farko?" Meema ta faɗi kamar tana jawa Ladi Katifa rai.

A ƙage Ladi ta girgiza mata kai alamar a'a.

"Na san dai wannan mutumin da ya wuce ba mijinki bane. Amma don Allah wannan yarinyar ƴarki ce dagaske ta cikinki?" Meema ta faɗi.

"Sai kuma mai ya tambaye bayan wannan?" Ladi ta tambaya don ba abunda ta ke son ji kenan ba.

"Ki yi haƙuri don Allah. Don akwai tambayoyi sosai a bakina sai dai ban san ta yanda za ki fahimta ba," ya faɗi." Meema ta kuma faɗi kamar wacce ta ke recording.

(Jama'a gaskiyan Laushi ne da ta ce Meema na ƙura masu idanu tana rekodin maganganunsu😂😂)

"Ehen, sai kuma mai ya kuma ce mata?" Ladi ta faɗi.

"Wanene mahaifinta? Rabuwa kuka yi ko mutuwa ya yi? Mai yasa kike zaune a hotel yanzu? Kuma ya aka yi kika bar Meema ta fito cikin dare nan? Allah ne fa ya tsare domin nan garin Lagos ne kuma cikin hotel. Akwai mutane iri-iri ciki kuwa har da masu safarar ƙananun yara da kuma ƴan shan jini har da masu fyaɗe." Wannan karan har da kwaikwayon muryan Habib ɗin ta yi.

"Meema ba su karɓi Number ɗin juna ba? Ba ki ji ya tambayi Number ɗinta ba??" Ladi ta faɗi gabanta na faɗuwa.

Shuru Meema ta yi alamar tunani kamun ta sauke kai ƙasa ta ce, "Yauwa na tuna, cewa ya yi idan babu damuwa ki faɗa min inda kike da zama mana. Ko nan kike zama?"

"Sai ta ce masa me?" Ladi ta tambaya bayan ta kalli fuskan Salmanu ɗan daudu da ya taɓe baki tare da kama ƙugu.

"Cewa ta yi, A'a, ba nan nake da zama ba. Nan da 2days zan koma gidana a nan cikin Lagos. Sai dai fa bari na ɗan yi saurin taka maka burki, ba zan bari wani alaƙa ya shiga tsakanin mu ba saboda ƙawata. Don ita ce budurwarka."

Yanda Meema ke magana zaka rantse da Allah recoder ne a ƙeyarta. Don sanka-sanka take zaro zancen. Akwai ta da saurin ɗauke zancen. Za ayi ta magana hankalinta na wani waje. Amma da za a tsare ta ta maimaita abinda aka faɗi, anan ne za a sha mugun mamaki. Don tass za ta zayyano. Shiyasa ta ke ɗaukar first position a school don ƙaryane a yi karatu gobe a tambaye ta bata kawo shi tass ba.

Baki buɗe Salmanu ɗan daudu ke kallon Meema ya na tafa hannayensa. Can ya ce, "Ku hanƙadani ta baya in faɗa kan Katifa, ni Salma nice."

"A'a wallahi sai dai kan Laushi ba kaina ba," Ladi ta faɗi tana zazzaga masa harara.

"Ke, ba ke katifar nake nufi ba, katifar kwanciya nake nufi. Yo wannan zancen da Meema ke zayyanowa kamar ana raɗa mata a kunne ai dole ya gigitani haka, Ni Salmaaaa!" Ya ƙarisa maganar yana riƙe baki.

"Maman Meema, Maman Meema! Lafiya? Mai ke faruwa?? Wani abun ne ya faru?" Faɗin Habib ganin yanda gaba ɗaya Laushi ta rikice.

Hannu ta saka ta share hawayen dake gangarowa daga idanunta tare da faɗin, "Babu komai. Ba abu ne da ya shafe ka ba."

"Speak up ummu Meema, maybe I can help." Ya faɗi yana kallonta cike da wani shauƙin sirri zuciyarsa.

"You can't' do anything, please. Tunda na ce maka babu komai, kawai ka barshi a hankan," ta faɗi tana ƙoƙarin wucewa.

"Maman Meema!" Ya kira sunanta cike da tausayinta da ya rasa ko ne menene.

Cak ta tsaya amma bata juyo ba kuma hawaye bai daina zubowa daga idanunta ba.

"In case if you change your mind to share with someone, do not hesitate! Wannan ƙafadun ina ji a jikina an haliccesa domin ki ɗaura kanki a kai ki hawaye ni kuma in share miki," yana gama faɗin haka ya nufi inda su Ladi Katifa suke tsaye ita da Salma nice.

Murmushi yaƙe Ladi ta yi masa. Amma can cikin zuciyarta tana jin pain sosai don tunda take buga barikinta bata taɓa ganin mutumin da taji ya shiga zuciyarta farat ɗaya kamar Habibu. Sai dai ita kanta ta san abu ne mai matuƙar wuya yin takara da Laushi. Kallo ɗaya ta yiwa Habib ɗin ta hango wani bayyananniyar ƙaunar da yake wa Laushi.

A kunne Salma ya raɗawa Ladi Katifa, "A bayyane yake wallahi. Na ga soyayyar uwar Meema a idanunsa."

"Ni ma naga hakan," a bayyane Ladi ta yi maganar tana murmushi. Don yanda take jin Laushin a zuciyarta, zata iya barin mata Habibun. Amma har ga Allah ita tana sonsa.

"Ƙus-ƙus ɗin mai kuke yi haka?" Habib ya faɗi yana dariya don jikinsa ya bashi gulmarsa suke yi.

"A'a-a'a! Haza haramun, shiga abunda babu ruwanka. Wannan magana ce ta jinsi ɗaya. Mai ya kawo ƴan maza cikinta?" Salma nice ya faɗi yana rangwaɗa.

Laushi ne ta ƙariso wajen daidai lokacin da Habibu ke dariya saboda abunda Salma nice ya faɗi.

"Mu shiga daga ciki ko?" Ta faɗi tana mai kawas da fuska saboda kallon kukan me kike yi da Ladi Katifa ta mata.

"Na yi gaba domin canza auduga don jikina ya jiƙe sharkaf da baƙonmu na mata," Salma nice ya faɗi tare da yin gaba.

Dariya Habib ya yi tare da faɗin, "Ɗan iska!" Yana mai bin shafafan bayansa da kallo. Duk ya bi ya ƙobare saboda gantsare-gantsaren da yake yi ala dole shi mace ce.

"To mu mun shige daga ciki," Ladi Katifa ta faɗi tana kallon Habibu da ke kallon Laushi.

Mayar da dubansa ya yi zuwa ga Ladi Katifa tare da faɗin, "Mu yi waya anjima kamun ki bar nan, ni ma anjima kaɗan zan wuce Abuja. Flight ɗina is around 4:30. Kamun dai in wuce zan kira ki. Ka mun ku shige ga kayan Meema can a mota muje ku tafi da su don Allah."

Bin bayansa su kai har wajen mota sannan suka kwaso teddies ɗin da chocolate tare da ledan take away ɗin da ya sayo sannan su kai ciki.

Sai bayan duk sun zauna sannan Ladi Katifa ta kalli Laushi ta de da faɗin, "Wai me ke faruwa naga duk kin yi wani sanyi haka? Wanene ya kira ki a waya?"

Dogon ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce, "Ladi, Yasaar ne ya kira ni a waya!"

Waro idanu Ladi katifa da Salma nice suka yi tare da faɗin, "Wani Yasaar ɗin? Daga can gidan yarin ya kira k? Ko har ya fito?"

"Daga can ya kira ni. Kuma ya faɗa min maganganu ma su matuƙar tashin hankali da ban tsoro. Ya yi alkawarin sai ya muzantani, ya wulaƙantani a idon duniya tunda na ci amanarsa," Laushi ta faɗi.

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Yau mun shiga uku," Ladi Katifa ta faɗi. Salmanu ɗan daudu kuwa cewa ya yi,

"Ina ɗan iskan ya samu wayar da ya iya kiran ki shi dake gidan yari?"

"Malam nan Nigeria ne fa! Babu abunda ba za a iya ba," Laushi ta faɗi.

"Saboda wannan jimamin da kike ne kawai zai hana ni zabga miki rashin mutunci. Menene kuma malam kamar kin ga ƙato!" Salma nice ya faɗi.

Tsaki Laushi ta zabga don halin da take ciki ya wuce tsayawa sauraran iskancin Salmanu ɗan daudu.

"Ki kwantar da hankalinki babu wani abunda zai iya aikatawa. Ki sanarwar Sabo da kaza, na san zai maki maganinsa," faɗin Ladi Katifa.

"Ko?" Laushi ta faɗi tana kallonta.

"Ni ma dai hakan na gani. Shi kaɗai ne zan iya ci maki ubansa tun da shi kakansa ne akan harkar kwayoyi da makamai," faɗin Salmanu ɗan daudu.

"Makamai kuwa?" Ladi ta faɗi with shocked don Ladi bata faɗa mata har da safarar makamai ya ke yi ba.

Wani harara Laushi ta jefawa Salmanu a fakaice, sai ya yi saurin faɗin.

"Ke, kar ki tada mana hankali. Menene kuma safarar makamai? A ina kika ji an faɗi hakan? Ni nufi na shine ke riƙe da makaman kwayoyi a Nigeria."

Ajiyar zuciya Ladi ta saki tare da faɗin, "Ko da na ce! Da har hankalina ya tashi. Yanzu dai kawai Laushi ki ɗaga waya ki shaida masa komai zuwa anjima."

"Zuwa anjima kam zan kira shi. Don gaskiya na tsorata. Don na fi kowa sanin wanene Yasaar idan ya ƙullaci mutum," Laushi ta faɗi.

"Magana ta gaskiya ke ma laifinki ne. Ɗaiɗaikun mata ne ba a jibgarsu a bariki. Menene don dadironki ya jibgeki bayan kece kika ci amanarsa. Kuma daga baya bawan Allah ya dawo ya baki haƙuri har kun sasanta. Kawai ke kuma sai kika zagaye kika ci amanarsa, mummuna ma wanda ya yi sanadiyar sa zuwa gidan yari. Gaskiya ba ki kyauta ba," Ladi ta faɗi.

Taɓe baki Laushi ta yi tare da faɗin, "Caɓ! Haka nan mutum sadaki ya biya ya aure ni ba inyi ta masa biyayya kuma yana jibgata kamar ya samu ƴarsa. Ba zai yuwu ba sam. A bar ma maganar nan a ayi wata."

"To ai shikenan. Amma Ni ina da magana," faɗin Salmanu ɗan daudu har da ɗaga hannu sama," Salma nice ya faɗi.

"Ina jin ka." Laushi ta faɗi tana mai kai hannu baya domin ɓalle maɓallin bra.

"Wancen guy ɗin da ya fita da Meema, Saurayinki ne ko na Ladi Katifa?"

Wani kallon Laushi ta watsa masa tare da faɗin, "To baƙar munafuka! Yanda kika gan mu haka zaki kyale mu. Haɗa mu kike so yi? To ba saurayina bane saurayin Katifa ne."

"A'a wallahi Saurayinki ne. Kuma wanda ya isa ya haɗa mu faɗa. Mutu ka raba ni da ke ƙawata," Ladi ta faɗi.

"Wallahi saura kaɗan in watsa miki zagi! Idan ba ke yake so ba, mai yasa zai baki waya. Kuma ni jiya ya faɗa min ke yake so ai."

Murmushin takaici Ladi Katifa ta yi tare da faɗin, "We shall see."

Kau da maganar su ka yi dukansu suka hau wani hirar da ban bayan gama cin abincin da Uncle Habib ya sayo.

Ƙarfe uku daidai Habib ya kira Number ɗin Ladi Katifa ya ce ta same sa a waje.

Fita ta yi bayan ta yi masu bayanin fitar. Can parking lot ta nufa wajen motarsa kasancewar ya faɗa mata inda za ta same sa. Yana ganin zuwanta ya kai hannu ya buɗe mata mazaunin gaba. Shiga ta yi ta zauna ba tare da ta rufe motar ba.

"Rufe motar mana. Za mu ɗan fita daga waje ne," faɗin Habib.

Rufe motar Ladi ta yi. Shi kuwa ya kunna motar ya nufi gate, bayan ya miƙawa mai gadi card sannan ya fice. Gaba da hotel ɗin kaɗan ya yi parking a gefen hanya.

Kallonta ya yi na wasu ƴan sakwanni, ita kuma kanta na ƙasa tana wasa da zoben azurfan hannunta. Wani ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin,

"Ba ki faɗa min sunanki ba," yana kallon cikin idanunta ya faɗi hakan.

"Sunana Rakiya, amma anfi sani na da Ladi Katifa don ba kowa ya san sunana ba," Ladi Katifa ta faɗi.

"To ni dai Rukayyah ya fi min daɗi. Zan kira ki da Rukayyah, it is ok for you?"

Gyaɗa kai ta yi hawaye na zubowa daga idanunta, kuma bata damu da ta share ba.

"Why are you crying, Rukayyah? Ni ne na ɓata miki rai?" Ya faɗi yana nuna kansa.

Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Ko ɗaya. Na tuna ne da mahaifina. Shi kaɗai ne a kaf familyn mu mai kira na da wannan sunan. Allah ya masa rasuwa sukan shekaru goma sha biyu da suka wuce," ta ƙarisa maganar tare da ɓarkewa da kuka.

Shuru ya yi ba tare da ya hana ta kukan ba har sai da ta gaji don kanta sannan ya ce, "I'm sorry, Rukayyah. I'm very sorry! Allah ya jiƙansa da Rahama," faɗin Habib yana son tambayanta labarinta amma kuma da ya kalli agogo sai ya fasa hakan don ya san idan ya ce zai tsaya jin tarihinta to tabbas zai yi missing flight kuma idan har bai koma Abuja ba yau, baza su taɓa kwashewa lafiya ba da Mama Luba. Idan kuma aka koma wajen Musbahu Kaita, kashe sa zai yi da magana.

Gyaɗa kai kawai Ladi Katifa ta yi. Gyara zama ya yi tare da faɗin, "Ki yi haƙuri da abunda za kiji daga bakina. Na san cewa kina tunanin a kanki nake da interest jiya...."

Tun kamun ya ƙarisa ta yi saurin katsesa wajen faɗi, "No! Ba haka bane. Na san Maman Meema kake so, don idan kana son labarin zuciya to ka tambayi fuska."

Wani kunya ne ya ɗan kama shi amma sai ya dake ya ce, "Nagode sosai da kika fahimci hakan. Maganarmu ba za ta yi tsayi ba saboda jirgin da zan hau zai iya tashi in the next 1hour in Sha Allah. Abunda na ke so da ke shine, don girman Allah ki kula min da Laushi da yarinyar nan Meema kamun na dawo. Don zan iya ɗaukar wata uku ko huɗu kamun na shigo Lagos. Wallahi tallahi har cikin kwaryan zuciyata na ke kaunarta, kuma da aure nake sonta. Amma abunda nake son fara yi kamun ma na gabatar da kaina a gareta shine, cireta daga halakar da take ciki. Kin ga na farko, sana'ar da kuke yi, na biyu kuma shaye-shayen da take yi don kallo ɗaya na yiwa idanunta na fahimci hakan. Ni zan karɓi Meema hannu bibbiyu a matsayin mahaifinta duk da ba nine na haifeta ba. Har ke Rukayyah! Don darajar ubangiji mahalicci ki bar wannan rayuwar gantalewar. Ko ba muji tsoran Allah ba, ma guji cutar zamanin nan. Zan baki jari daga Naira dubu ɗari har miliyan ɗaya. Don girman Allah ki natsu ki aure. Idan na dawo in Sha Allah zamu tattauna sosai. Ungo wannan, ATMcard ɗina ne. Akwai 200k a ciki. Ku yi duk buƙatunku kamun na dawo. Za mu riƙa waya a kai a kai, kin ji?"

Gyaɗa masa kai ta yi tana jin wani irin ƙaunarsa na ƙara huda ƙirjinta. Gaba ɗaya sai taji kewan gida ya dawo mata.

"Ki taya ni yiwa Maman Meema da Meema sallama. Ku kula da kanku, sai mun yi yawa."

"Nagode Allah ya saka da alkhairi," ta faɗi trying very hard to control her tears tare da buɗe murfin mota ta fita ta rufo masa ƙofar.

"Rukayyah, kar ki faɗawa ƙawarki sirrin da ke cikin zuciyata. Amma kuma ki faɗa mata gaskiyan cewar babu komai tsakanin mu. Domin abunda take tunanin kenan."

"In Sha Allah!" Ta faɗi tare da juyawa ta wuce.

Shi ma be bar wajen ba har sai da yaga shigewarta cikin hotel ɗin sannan ya tada motar ya wuce.

Da gudu Ladi ta wuce bayan ginin upstairs ɗin hotel ɗin ta dunga kuka kamar ranta zai fita. Don Habib ya tsokano mata mikin da ya daɗe yana mata ciwo a zuciyarta. Ga kuma kyekkyeta mata zuciya da ya yi sai da ta gama saka rai da shi. Ta jima tana kuka kamun ta isa wajen pampon dake can nesa da wajen ta wanke fuska da kyau ta yanda baza a gane ta yi kuka ba sannan ta koma ɗakin.

"Ke, Ladi! Wannan irin jimawa hakan? Ko dai sai da aka shige owner's corner ne??" Salmanu ɗan daudu ya faɗi yana dariya.

Ita ma dariyar ta yi tare da faɗin, "Ki kula da titi Salma nice. Kin ga wallahi magana muka jima muna yi. Na faɗa muku wallahi ba saurayina bane. Ni ina ganin dai kamar Laushi ya ke so duk da bai faɗa min ba. Yanzu ma fa cewa ya yi in kula masa da Laushin da kuma Meema shi ya wuce Abuja."

"Yana ruwa tsundum wallahi!" Laushi ta faɗi tana mai buɗe ledan chocolate tare da ɓalla ta hau tauna.

"Uhm!" Ladi Katifa ta ce tare ɗaukar leda ɗaya ita ma ta buɗe ta hau tauna.

Kwana biyu su Laushi suka ƙara a hotel ɗin, wannan saurayin wanda ke wa Sabo da kaza aiki ya zo ya kwashe su ya kai su gidan da ya sayawa Laushin a Adenji Adele Street. Gida ne madaidaici mai ɗauke da ginin fourbedroom flat. Ko ina ya sha tiles. Parlourn yana da girma sosai. A parlourn kuwa manya-manyan set ɗin kujerune kalar maroon da wata shirgegiyar tv kamar majigi. A kwai dinning, sai ƙatoton kitchen mai ɗauke da store a cikin. Akwai ƙofa da zai fitar da kai ta baya a kitchen ɗin. Ɗakunan baccin ma manya ne kuma duka akwai furniture a ciki ban da guda ɗaya da yake a kulle don Sabo da kaza ne kawai ke da key din ɗakin. Akwai shuke-shuke da ya ƙawata gidan irin su; inabi (grape), apple, gwaiba, apple mango, tangerine, african Cherie (Agwaluma) banana da sauran su. Sai parking lot da aka ƙawata wajen duk da babu mota ko ɗaya a wajen. Sannan akwai shukokin ƙawata gida irin su, Sunflower da sauransu.

Ladi Katifa da Salma nice sai santin gidan suke. Washa gari Ladi da Salma nice suka kwaso kayansu duka kowa ya kama ɗakinsa. Ladi ta ɗauki daya, Salma nice ma haka, Laushi da Meema suma haka. Don Meema bata taɓa yarda ta kwana inda ba mamanta a wajen.

Har wani kwarya-kwaryan walima suka haɗa na tarewa a gidan. Satinsu ɗaya, Sabo da kaza ya turo wannan saurayin ya zo da mota ya ɗauki Laushi da Meema domin yi mata registration ɗin boko.

A wani makaranta mai suna Bright scholars aka yi enrolling ɗinta. Kuɗin komai aka biya don hatta school uniform su suka bata kala biyar don kowani rana akwai kalan kayan da yara suke sakawa. Makarantar na yaran masu kuɗi ne domin malamansu akwai turawa a ciki.

Bayan sun dawo gida, da yamma duk suna zaune a parlour, Salma nice na kitchen yana dafa masu abinci, wayar Laushi ya yi ƙara. Tana ganin sunan da ya yi appearing a screen ɗin gabanta ya faɗi don tun kiran da ya yi mata a hotel bai ƙara ba, har ta mance da lamarinsa don ko Sabo da kaza bata faɗa masa komai ba. Bata ɗaga ba har wayar ya katse.

"Ana kiran ki a waya fa," Laushi ta faɗi.

"Yasaar ne! Wallahi shine ya sake kirana da ɓoyayyiyar Number."

Dogon tsaki Ladi ta ja tare da faɗin, "wallahi idan kika sake ya fahimci wannan tsoron na ki, kin kaɗe domin da shi zai yi ta amfani dake. Dakewa za kiyi ki nuna masa ƙarya yake yi."

Nan take Laushi ta ji wani courage daidai nan Yasaar ya sake kiran wayar. Picking ta yi tare da karawa a kunne,

"Ke! Ni zan kira kiƙi ɗagawa kira immediately?"

"Ubana ne kai? Ko kuma uwata? Idan har ka sake kirana sai na wulaƙanta rayuwarka fiye da wulaƙancin da kake fuska yanzu haka. Wawa sakarai kawai!"

Wani irin two minutes silent ya yi kamun ya ce, "Kin shiga uku Zeenatu! Daga gobe zan fara nuna miki abunda zan iya ina daga cikin gidan yari," yana kawowa nan ƙit ya kashe wayar.

#Laushi #Zeenah #Ladi Katifa #Ruƙayyah #Habib Girei #Yasaar #Prison #Sabon gida #My Destiny #Matar Sayyadee

*** [2/15, 4:35 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi! _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._