Page 21
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
"Wai me ɗan iskan ya ce? Wallahi kar ki nuna tsoransa. Kuma kema sai da na ce maki ki yiwa Sabo da kaza magana," Ladi Katifa ta faɗi.
"Cewa ya yi wai daga gobe zai fara nuna min abunda zai iya yi yana daga cikin gidan yari."
Mugun tsaki Ladi ta yi daidai fitowar Salmanu daga kitchen hannunsa riƙe da plate ɗin abinci guda biyu a hannunsa.
"Wallahi wannan mugun ɗan iska ne! Ina sha Allah babu abunda ya isa ya miki. Ƙaryansa ta sha ƙarya," Ladi Katifa ta faɗi duk ita ma can ƙasan zuciyarta tana tsoron Yasaar ɗin, kawai kwantarwa ƙawar tata hankali take.
"Wanene kuma yanzu?" Salma nice ya faɗi bayan ya ajiye Plate ɗin a gabansu.
"Ɗan iskan nan mana, Yasaar!" Ladi Katifa ta faɗi.
"Dan Allah ku tura ni ta baya in faɗa kan kat......"
Saurin katse sa Ladi ta yi tare da faɗin, "Kan uwar wa? Ka kiyaye ni Salma."
"Wallahi ban kiyayanki tunda kika tura ni jin su ƴan maza," ya faɗi yana mai mayar da kallonsa wajen Laushi.
"Kar ki wani damu da ɗan iskan. Ki haɗa shi da Sabo da kaza kawai ya ci miki uban shege kawai."
"Ni ma haka na ce mata," Ladi Katifa ta faɗi.
Waya Laushi ta ɗaga ta kira Sabo da kaza, sai da ya yi ringing kamar zai katse sannan ya ɗaga tare da faɗin, "Zeenah zan kira ki anjima. Yanzu ina wani muhimmin meeting ne a Akwa ibom. Gobe ni ma zan shigo Lagos ɗin, sai na kira," yana gama faɗin haka ya katse wayar ba tare da ya bata damar yin magana ba.
"Wai yana hanya gobe. Yanzu haka meeting suke a Akwa ibom, wai zai kira ni anjima," Laushi ta faɗi.
"To ai shikenan! Faɗuwa ta zo daidai da zama. Allah ya kai mu goben," faɗin Ladi.
"Wai ni kuwa ba gulma ba, shin kuna waya da wannan Habibun yake ko uban wa?" Salmanu ɗan daudu ya faɗi.
"Kai! Ai babu ranar da bai kira a waya wallahi. Kullum sai ya kira an bashi Meema a waya sun yi hira," faɗin Ladi Katifa.
"Meema ya ke kira, ko uwar Meeman?" Salma nice ya faɗi yana dariya.
"Wallahi daga munafuka sai ke Salma. To duka yake kira," Ladi ta faɗi.
"Ai Salma akwai gulma wallahi. To ya kira ni ya min me? Meema dai yake kira. Kasan jininsu ya haɗu," Laushi ta faɗi.
"Ai fa, jininsu kam ya haɗu." Salmanu ɗan daudu ya faɗi daidai nan Meema ta buɗe ƙofa ta shigo da sallama school uniform a jikinta.
"Assalamu alaikum, can I come in?"
"Iskanci! Sai bayan kin shigo ɗin ne kike faɗin haka?" Faɗin Laushi tana miƙa mata hannu alamar ta taho wajenta.
Da gudu Meeman ta nufo ta faɗa jikinta tare da faɗin, "Afternoon mom, afternoon aunty Ladi, aunty Salma afternoon!" Cike da farin ciki ta bisu ɗaya bayan ɗaya da gaisuwa.
"Afternoon Meema!" Ladi da Salma nice suka faɗi.
Laushi da kanta ta cire mata sandal ɗin ƙafarta sannan ta zare farar computer socks ɗinta. Za ta zage mata zip ɗin riga sai ta yi saurin riƙewa tana kallon Salma nice tare da turo baki. Zaro idanu Salma nice ya yi yana tafa hannu tare da faɗin,
"Ke duniya! Ke wannaan, to don gidanku ni ce nan na sulluɓeki tas lokacin da kika faɗo duniya. Me zan gani yau ni Salma nice?"
Dariya sosai Meema ta hau yi tare da faɗin, "Aunty Salma mai kika dafa mana, shinkafa da miya?" Meema ta faɗi tana kawar da maganar farko.
"Uwarki da miya na dafa gata nan ki ci," Salma ya faɗi tare da aunawa mata daƙuwa.
Wannan karan ba Meema kaɗai ba, har da Ladi Katifa sai da suka dara.
"Mom, let me change," Meema ta faɗi tare da miƙewa ta ɗauki socks ɗinta da sandal ta nufi ɗakin Laushi. Bayan few minutes ta fito sanye da blouse Kalar pink.
"Aunty Salma, I'm hungry!" Meema ta faɗi tana ɓata fuska.
"Gashi nan na zubo miki," Laushi ta faɗi tana mai tura mata Plate ɗin shinkafa da miya da kaza.
"Thank you Mom!" Meema ta faɗi tare da yi mata kiss a kumatu.
"Yauwa mom, kin san wani abu?" Meema ta faɗa bayan ta kai lomar abinci ɗaya a baki.
"Ba a cin magana idan ana cin abinci, ki gama tukun," Laushi ta faɗi tana nuna mata abincin.
Kallon juna Ladi da Salma nice suka yi. Salma nice ya yi caraf tare da faɗin, "Wannan caring ɗin fa yau, Hajiya Laushi! Ko yau mother's day ne? Ko kuma children day?"
Harara ta watsa masa tare da faɗin, "Mai kuke nufi ne wai? Na ga kamar so kuke ku ce ban ƙaunar ƴata ko?" Laushi ta faɗi.
"A'a, ke kika faɗin hakan da bakinki. Ai ko dabba ta san ƴaƴanta, kawai dai yau ne muka ga abun daban don bamu taɓa ganin haka ba sai dai Meema zan kazanki, ko kuma ki kai mata duka." Salma nice ya faɗi.
Taɓe baki Laushi ta yi tare da saka hannun a cikin abincin Meema suka shiga ci a tare.
Meema na gama ci ta sha ruwa sai ta kalli Laushi tare da faɗin, "Mom, wallahi na yi mafarkin babana jiya."
Gaba ɗayansu zuba mata idanu suka yi. Laushi kuwa, tsayin shekaru tara bata taɓa zaunar da Meema ta ƙare mata kallo don kawai ta hango kamanninta da kyau ko zata iya hasaso mahaifin nata ba sai a yanzu. Sosai ta ke kallonta, amma iya hasashenta ta kasa ganowa.
"Kin san fuskan babanki ne, Meema?" Ladi Katifa ta faɗi.
Girgiza kai Meema ta yi tare da faɗin, "Ban gani ba! Rufe fuskan ya yi da kyalle amma shima baƙi ne irina. Ina ta binsa muna zagaye wani ƙaton parlour ya fi wannan kyau sosai. Ya ce min idan na kama shi zai buɗe min fuskansa kuma zai ɗaura ni a wani kujera mai kyau da tsawo. Amma na kasa kama shi," ta ƙarisa maganar cike da ɗacin hakan.
Tsit ɗakin ya yi babu wanda ya iya ko tari. Dukkansu juya mafarkin Meeman suke a cikin zuciyarsu musamman Laushi.
"Mummy.…...." Meema ta faɗi amma da sauri Laushi ta katseta tare da faɗin,
"Enough! Je ɗaki ki kwanta kamun anjima ki zo ki homework."
A hankali ta miƙe ta nufi ɗakin Laushi ta kwanta tana tunanin mai yasa mamanta bata so ta nuna mata babanta.
"Wallahi Laushi ina jiye maki lokacin da yarinyar za ta mallaki hankalinta ta titsiyeki sai kin nuna mata mahaifinta," Ladi Katifa ta faɗi.
"Ina son Meema, Ina matuƙar ƙaunar yarinyar nan sosai. Har da dalilin wannan tambayar da nake gudu ya saka na saka mata tsoro da shakkana a ranta. Ban taɓa jin tsoron kalaman Meema kamar na yau ba. Wallahi Ladi na kasa hasaso mahaifin yarinyar nan. A Bauchi ya ke, a ina yake, Wallahi ban sani ba. Da na san haka zai iya faruwa, da ban yarda na ɗau cikin nan ba wallahi. Wannan Yarinyar ina ji a jikina ita za ta zame min tashin hankali. Wallahi ban taɓa dana sanin wannan rayuwar da nake yi ba, amma yau yarinyar nan ta saka zuciyata ta min rawa," Laushi ta faɗi jiki a sanyaye.
Babu wanda ya yi magana cikinsu har tsayin mintuna ashirin kamun Ladi Katifa ta ce, "Ina da shawara."
Kallonta suka yi su duka suna sauraranta.
"Why not mu duka mu daina wannan rayuwar da muke yi, kin ga ke kin samu wanda ya ke sonki tsakani da Allah, sai ki istibra'i ku yi aure. Na tabbata zai riƙe miki Meema kamar mahaifi."
Wani wawan harara Laushi ta watsa mata tare da faɗin, "Babu aure a agenderna, kin fi kowa sanin haka." Tana gama faɗin haka ta miƙe ta bi bayan Meema.
"To ke ina ruwanki? Jikinki ko nata? Idan kin ga ke za ki tuba, to ki tuba ba dole sai da Laushi ba," Salma nice ya faɗi.
Wunin ranar a ɗaki Laushi ta yi sa tare da Meema don ko da daddare Salma nice ɗin ne ya bi su da abinci. Washa gari, da wuri Laushi ta tashi don hana kanta shaye-shayen dare ta yi don kawai ta shirya Meema da kanta. Ita ta yi mata wanka ta saka mata kayan makaranta bayan ta yi mata breakfast da kuma wanda za ta tafi da shi school.
"Thank you Mom!" Meema ta faɗi lokacin da Laushi ta saka mata jakar bayan da Uncle Habib ya saya maka mai shape ɗin elephant.
"For what?" Laushi fa faɗi tana kallonta.
Maimakon Meema ta bata amsa sai ta mata kiss a kumatu tare da faɗin, "Bye mum, sai na dawo!"
A baya Laushi ta bita tana jin wani sabon ƙaunarta da kewarta har ta shiga school Bus tana ɗaga mata hannu. Har motarsu ta ɓace a layin Laushi ta tsaye a bakin gate. Sai da ta gaji da tsayuwa sannan ta juyo ta dawo ɗakinta. Zama ta yi tsakiyar gadon tare da rungume pillow, can ta sauko ta haɗa tea mai kauri ta sha kasancewar a kwai komai a dakin. Kwalbar codine ta ɗauko ta buɗe ta sha kaɗan sannan ta kwanta tare da jan bargo.
Laushi bata farka ba sai gab azahar. Saukowa ta yi daga kan gadon ta fito parlour. Ladi da Salma nice ta taras a parlourn suna buga kati.
"Meema ta dawo ne?" Ta faɗi tana kallonsu.
"Ƙarfe ɗaya ne yanzu da mintuna bakwai fa. Meema ai sai uku za ta shigo gidan nan," Salmanu ɗan daudu ya faɗi.
Bata ce komai ba ta nufi kitchen ta ɗaura ruwan wankan tare da ɗebo tuwon semo ɗin da ta gani a kitchen da zafinsa ta fito. Abincin ta ke ci amma lokaci-lokaci ta ke kai idanunta kan agogon bangon da ke ɗakin. Wani dogon tsaki ta ja da ya saka duk suka kalle ta.
"Lafiya kike zabga tsaki haka?" Ladi Katifa ta faɗi tana kallonta.
"Wallahi lokaci ne yau naga bai gudu kwata-kwata, na ƙosa Meema ta shigo. Ban san mai yasa ba wallahi tun ɗazu gabana ke faɗuwa," Laushi ta faɗi.
"In Sha Allah babu abinda zai faru, Meema za ta dawo Lafiya ƙalau," su Ladi suka haɗa baki suka faɗa.
"Allah ya sa," Laushi ta faɗi tare da tsame hannunta a cikin tuwon don ji take kamar tana tauna magani.
Ƙarfe uku na bugawa ta miƙe ta nufi gate ta buɗe ƙaramar ƙofar tana kallon hanya. Uku da mintuna goma amma babu school Bus ɗin su Meema. Nan da nan hankalinta ya yi mugun tashi don hatta cikinta wani irin ƙara yake yi. Rufo ƙofar ta yi tare da dawowa parlourn ta soma faɗin,
"Ladi kalli agogo, uku har da mintuna goma sha bakwai amma Meema ba ta shigo ba, na shiga uku! Allah ka rufa min asiri kar wani abu ya samu ƴata," Laushi ta faɗi tana kuka lokaci guda kuma tana laluban Number ɗin makarantar.
Ladi da Salma nice da jikinsu ya yi sanyi su ma suka miƙe don Meema bata taɓa kaiwa uku da mintuna biyar bata shigo ba. Wani lokacin ma ukun bai cika take shigowa.
"Hello! Ina magana da makarantar bright scholars ne?"
Daga can aka bata amsa da eh. Sai ta hau faɗin, "My daughter is not yet home, I called to confirm if she's still there in the school."
Daga can aka tambayeta sunan yarinyar nata, sai ta ba su amsa da, "Fareedat Zeenatu Laushi, she's in primary four."
"Ok. Give some minutes, will call you back," aka faɗa daga can tare da yanke kiran.
Kamun su sake kira Zeenah sai zagaye ɗakin ta ke gabanta na faɗuwa. Knocking ɗin kofar gate ɗin gidan aka yi sai duk suka fice da saurin suna fatan Allah ya sa Meema ce ta dawo. Sai dai Salma nice na buɗe Ƙofar wani yaro ya miƙo wata farar envelope da leda viva baƙa tare da nuna wata dark ash ɗin mota Civic tare da faɗin, "Wani a cikin motar can ya ce in kwankwasa gidan nan in ba Zeenah Laushi." Salma nice na amsa yaron ya wuce.
Ko kamun su yi wani yunƙuri motar ta wuce da uban speed ta bar unguwar.
Daidai nan hukumar makarantarsu Meema ta kira ta shaida mata kwata-kwata Meema yau bata zo school ba don ko Bus driver ɗin da ke ɗauko ta ya ce yazo yana ta horn har tsayin mintuna bakwai bata fito ba shi kuma ya wuce. Sakin wayar ta yi ya faɗi a ƙasa.
Hannun Zeenah har rawa ya ke wajen ƙarban envelop ɗin ta buɗe. Farar takardar da ke ciki ta zaro ta warware tare da soma karantawa a fili,
_Dama na faɗa miki sai na nuna miki ƙarfin ikona. Zeenah, wallahi sai na wulaƙantaki a duniya. Daga yanzu ki fara ƙidaya awannin da suka ragewa ɗiyarki a duniya! Kamata ya yi ko gode min ma domin zan raba ki da shegiyar ƴar da ba ƙaunarta ki ke ba. Amma ka mun nan, sai na kwanta da ita na ji bambamcin da ke tsakaninku na ji shin ita ma Laushin ce kamar ke! Ga saƙo nan cikin leda wanda zai tabbatar miki da maganata ba wasa bane._
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!!" Shine abunda Ladi da Salma nice ke ta faɗi.
Laushi kuwa kamar bishiya haka ta ƙame ƙam jikinta na kakkarwa. Ladi ta zazzage ledan domin ganin abunda ke ciki; hotuna ne guda uku, sai kayan makaranta Meema da lunch box ɗin ta. Duƙawa Ladi Katifa ta yi ta kwaso hotunan.
Hoton farko Meema ce da kayan makaranta ta tsuguna kanta babu barrett sai gashinta daya zubo ya lulluɓe mata fuska, na biyu kuma tsaye take tana kuka daga ita sai pant da vest ɗin da Laushi ta saka mata da safe, Na ukun kuma wata ce sanye da bulun doguwar riga tana tsira mata allura a kafaɗar hannu ita kuma ta wage baki tana ihu.
Luuuuu Laushi ta faɗi daga tsayen a sume.
_Hmm_ 🤔
#Meema #Laushi #Yasaar #Sabo da Kaza #Matar Sayyadee #My Destiny
*** [2/16, 7:43 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi! _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._