Page 22
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
Da sauri Ladi ta taro ta ta idasa faɗuwa a jikinta. Cikin sauri Salma nice ya fice domin nema abun hawa don kai Laushi asibiti. Ita kuma Ladi a hankali ta aje kan Laushi a ƙasa tare da nufa cikin gida da gudu ta ɗauko ruwan leda ta fito.
Fasa ruwan ta yi tare da yayyafawa a fuskanta. Sai da ta kwashi sakwanni kamun ta farfaɗo tana wawware idanu.
"Ina Meema? Na shiga uku na lalace, Yasaar zai ɓata min ƴata. Ladi ku taimaka min na shiga uku," Laushi ta faɗi tana kuka sosai.
Ɗaga ta Katifa ta yi tare da faɗin, "Amshi wayar nan maza ki kira Sabo da kaza ki faɗa masa komai."
Amsar wayar ta yi tare da danna masa kira, sai dai ringing ya yi har ya katse bai ɗaga ba. Da ta kuma kira sai ta ji wayar a kashe. Ihu kawai Laushi ke yi tana kiran sunan Meema kamar Meeman za ta iya jin ta daga inda ta ke.
Turo ƙofa Salma nice ya yi tare da faɗin, "Alhamdulillah! Ta farfaɗo kenan? Har na kira mai taxi gashi can waje.
Zumbur Laushi ta miƙe tare da faɗin, "Muje police station!" Sai dai ko taku ɗaya ba su yi ba wayar Laushi ya soma ƙara. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Shine ke kira na wallahi."
"Ɗauka muji mai zai ce kuma yanzu," Ladi ta faɗi jikinta na rawa.
Ɗauka ta yi tare da karawa a kunne ta ce, "Yasaar na roƙeƙa da darajar ubangiji ka yi haƙuri kar ka cutar min da ƴata! Ka faɗi abunda kake so in yi wallahi zan yi ko menene amma don't involve my daughter, please," Laushi ta ƙarisa maganar tana kuka.
Wani dariyar basawa ya saki tare da faɗin, "Ban kira don in saurari magiyarki ba. Na kira ne in yi maki kashedi da babbar murya, wallahi idan kika saki kika kai report wajen ƴan sanda, na miki alƙawarin zuwa anjima da daddare gaɓoɓin jikin ƴarki za su fara miki iso. Don sai na yankata gunduwa-gunduwa na aiko miki da su ɗaya bayan ɗaya," yana gama faɗin haka ya yanke wayar kamar ya san shirin abunda suke yi na zuwan police station.
Wani irin jifa da wayar Laushi ta yi ta hau hargitsa kitson attachment ɗin kanta tana ihu tana faɗin, "Yasaar kar kai min haka! Ni ce na yi maka wannan laifin ba ƴata ba. Ka dawo min da ƴata ni ka ɗauke ni. Wayyo Allahna Meema."
Gama ɗaya Laushi ta gama haukacewa. Ita kuka, Ladi kuka, Salma ma kuka musamman da ta faɗa masu abunda Yasaar ya ce idan har suka kuskura su ka kai report a station. Mai taxi da ke waje, haka ya gaji da tsayuwa ya yi zage-zagensa ya wuce.
Haka suka wuni babu mai sallah a cikinsu sai kuka. Tsabar firgici ko ƙaran bugawar minti na agogo Laushi ta ji sai gabanta ya faɗi. Har ƙarfe ɗayan dare suna zaune a parlour idanu a kumbure babu mai jin ko gyangyaɗi bare su kwanta. Gashi ta kira layin Sabo da kaza ya fi sau shurin masaƙi ya ƙi shiga. Kamun safiya Laushi ta koma kamar zararra. Sigari kuwa ta sha ya fi kwali ɗaya. Wiwi ma ya ci ubansa. A yanda ta ke jinta ko giya aka ajiye mata zata kwankwaɗe ƴar banza. Idan idanun nan suka tafi luuu sai ta buɗe da sauri tare da kai wa wiwi wani irin zuƙa.
Ganin abunda na ta ya wuce na misali, sai Ladi ta tattara duk wasu kayan mayen gabanta ta rufe a kitchen. Idan ka kalli Laushi a wannan halin da take ciki dole ka zubar mata da kwalla. Ga tashin hankali ga rashin barci da rashin cin abinci kuma sai ɗirkawa kanta wiwi da sigari ta ke.
Haka suka ƙara kwana babu labarin Meema ba su san halin da take ciki ba, kuma yasar wunin ranar bai kira ba, haka Sabo da Kaza.
A rana ta uku Sabo da kaza ya kira Laushi a waya lokacin bata cikin hayyacinta don ko hannu ba ta iya ɗagawa saboda yanda ta yiwa kanta illa da kayan maye. Ladi Katifa ce ta ɗaga wayar. Shi kuma jin ba muryan Laushi ba yaƙi magana sai faman "Hello! Hello!!" Ladi ke faɗi.
Katse wayar ya yi yana jan tsaki, kuma dama Laushin ya ke so ya faɗawa gashi a airport, Yahuza (yaron da ke masa aiki) ya ɗauko sa suna hanyar zuwan gidan yanzu haka.
"Kai ni M.I hotel kawai. Zuwa anjima idan na huta zan yi driving kai na zuwa gidan," sabo da kaza da ke bayan mota ya faɗi.
Laushi ba ita ta dawo hayyacinta ba, sai gab magrib. Da ƙyar ta Sha tea ɗin da Ladi ta haɗa mata shima rabin kofi. Idanunta sun yi zuru-zuru. Ƙashin wuya sun mata sarƙa. Ta koma kamar wacce ta shekara tana ciwo.
"Ɗazu Sabo da kaza ya kira wayarki," Ladi ta faɗi tana miƙa mata wayar.
Da sauri ta karɓi tare da saukowa daga kan gadon tana dailing Number ɗinsa. Sai da ya kusa katsewa ya ɗaga tare da faɗin,
"Ina jin ki," a dake ya yi maganar saboda ya ji haushin ba wata wayar da ta yi ɗazu.
"Kana ina? Wallahi ina cikin tashin hankali. Tun shekaran jiya nake kiranka a waya bai shiga."
Kai tsaye ya bata amsa, "Ɗazu na dawo daga Brazil. Ya aka yi? Kuma wa kika ba waya ɗazu da na kira ki?"
"Na sha magani ne ban cikin hayyacina shiyasa ta ɗaga wayar, ban ma san ka kira ba sai yanzu. Wallahi ina cikin bala'in tashin hankali. Don girman Allah kana ina ne in zo in same ka?"
"M.I hotel. Ki zo ke ɗaya!" Yana gama faɗin haka ya katse wayar.
Cikin sauri ta cire rigar da tun shekaran jiya yake jikinta tare da saka wata doguwar riga mai kama jiki kasancewar roba ce. Ko tsayawa saka bra bata yi ba. Vail ta ɗauka ta yafa a saman kitson attachment ɗin kanta sannan ta saka takalmi tare da ɗaukar waya da purse da kuma hotunan Meema da Yasaar ya turo da su, sannan ta kalli Katifa tare da faɗin, "Bari na je na same shi yanzu. Ya shigo Lagos yana hotel," tana faɗin haka ta fice daga ɗakin ba tare da ta saurari abunda Katifa ke faɗi ba.
A daidai gate ɗin hotel ɗin mai acaɓa ya sauke ta. Ɗari biyar ta miƙa masa sannan ta shiga cikin hotel ɗin tare da fiddo waya tana laluban layinsa.
"Room E33 by your left!" Yaron Sabo da kaza ya faɗi. Ita har firgita ma ta yi don bata ga zuwansa ba sai maganarsa.
Ba tare da ta ce masa uffan ba ta nufi direction ɗin da ya faɗa mata don ta san Sabo da kazan ne zai ce ya jira ta a waje. Murɗa handle ɗin ƙofar ta yi sannan ta shiga kasancewar a buɗe ya ke.
Zaune ta same shi a tsakiyar gado daga shi sai short yana amsa waya. Alama ya mata da ta taho garesa. Babu musu ta nufe sa sai dai bata fahimtar abu ɗaya da yake faɗi saboda wani yare ya ke yi wanda ita bata taɓa jinsa ba.
Kamar ta wanka masa mari a fuska haka ta ji lokacin da ya jawo ta sosai zuwa jikinsa yana shinshinar wuyanta duk da waya ce a kunnansa.
Magana ce da ta ɗauke sa kusan rabin awa sannan ya gama tare da ajiye wayar yana kallonta.
"Zeenah, what's wrong na ga duk kin koma wata tsohuwa duk wanann kwalliyar babu shi?"
Kamar tana jira ta rushe da wani irin kuka sosai tana faɗin, "Na shiga uku ya ɗauke min farin cikina!"
Zaune sosai ya tashi tare da kai hannu ya shafa ƙirjinta duka biyun don shi a tunaninsa ko masu kwashe mamuka da asiri ne suka tafi mata da su, amma da yaji duk suna nan sai cewa ya yi,
"Ban gane ba? Gabanki aka shafe ko mai?"
Girgiza kai Laushi ta yi tare da faɗin, "Yasaar ne!"
Wani irin ƙura mata idanu ya yi yana wani tunani cikin zuciyarsa. Can ya ce, "Ban gane Yasaar ba! Mai Yasaar ɗin ya yi? Shi da ya ke cikin Prison."
"Meema ya sace. Tana wajensa yanzu haka. Kuma ya ce idan na saki na faɗawa ƴan sanda sai ya yi gunduwa-gunduwa da ita ya turo min da part-part ɗin jikinta."
Wannan karon saukowa ya yi daga kan gadon tare da faɗin, "Wannan shirmen banza da wofi ne! Ta yaya mutumin da ke kulle a prison zai iya yin hakan?"
Laushi ita ma miƙewa ta yi tare da faɗin, "Wallahi, tallahi shine! Don mun yi waya da shi. Kuma Yasaar yana da manya sosai a garin nan. Ko su za su iya taimaka masa. Na san wasu daga cikin sirrikun Yasaar sosai. Idan na faɗa maka sunan manyan mutanan da yake wa aiki a garin nan, za ka sha mamaki. Abunda ya sa ban taɓa cewa komai ba ko kuma in fallasa asirinsu, saboda babu ruwana don ba da su ne ke faɗa ma, da Yasaar na ke yi. Shi ɗin ma wulaƙantanin da ya yi ne ya saka na rama gwargwadon abunda ya min. Amma ni ba ruwana da tonawa iyayan gidansa asiri."
"Wannan dalilin ya sa kike raye har yanzu!" Faɗin Sabo da kaza cikin zuciya sai dai maganar zuciyar ta fito fili don da sauri Laushi ta ce,
"Mai ka ce? Ban gane ba". Ta faɗi hakane tana kallonsa.
"Eh mana! Shuru da bakin da kika yi ne ya saka ubannin gidansa ba su ɗau mataki a kanki ba. Da kin sake kin kira sunansu ko ƙoƙarin tona masu asiri, to yanzu haka zancen wata ake ba ke ba. Tuni za su saka a kashe ki kuma a cikin na kusa da ke zai aikata hakan. Ai ba sa wasa da sirrinsu ko kaɗan," faɗin Sabo da kaza.
"To ni mai zai kai ni wannan aikin. Ni dai don girman Allah na san kana da hanyoyin da za ka taimaka wajen kuɓutomin da ƴata kwalli ɗaya. Ka taimaka min don girma Allah."
"Tun yaushe Yasaar ya soma kiran ki?" Ya jefa mata tamabaya.
Nan ta bashi labarin komai har zuwa yaron da ya turo da hotuna da kuma kiran da ya mata last. Masifa ya hau ta dashi sosai a kan mai yasa tun lokacin da Yasaar ɗin ya kira ta ranar farko bata faɗa masa.
"Da tun lokacin kika faɗa min, wallahi da ba zai sake yunƙurin kiranki na biyu ba balle ya yi wannan ɗanyen aikin. Amma yanzu ba bata ɓaci ba, zai ci ubansa. Ban hotunan da ya aiko da su." Ya faɗi rai a ɓace.
Da sauri ta ɗauki hotunan da ta aje a kan gadon ta miƙa masa. Sai da ya gama ƙarewa hotunan kallo sannan ya ajiye a kan gadon bayan ya yi kwafa tare da saka kaya sannan a ɗauki hotunan ya saka cikin aljihun shaddar jikinsa sannan ya kalli Laushi tare da faɗin, "Muje na sauke ki a gida, Meema yau a gida za ta kwana ki kwantar da hankalinki."
A take ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi sai ta miƙe ta bi bayansa. A baya duk suka zauna ita da shi a cikin mota. Fuskan nan na shi a matuƙar ɗaure har suka isa ƙofar gate ɗin gidan Laushi.
"Ki je ki kwantar da hankalinki. Na tabbatar miki Meema gida za ta kwana. Kuma ina fatan babu Saurayinki cikin gidan don a nan zan kwana duk dare," ya faɗi yana kallonta.
Gyaɗa masa kai ta yi tare da buɗe murfin motar ta fita, Yahuza ya ja motar.
"M.S.P.K (Maximum Security Prison, KiriKiri, Lagos State.)" Abunda sabo da kaza ya faɗi kenan yana danna wayarsa.
Shi kuma Yahuza na jin haka ya dauƙi hanyar Prison ɗin. 54mimutes ya kawo su Prison ɗin.
"Ka jira ni a mota!" Faɗin Sabo da kaza tare da buɗe murfin motar ya fita ya doshi Prison ɗin. A ƙofar gate suka haɗu da wani jami'in gidan mai babban muƙami sannan suka shiga ciki a tare.
Tafiya suke yi suna shiga lungu-lungu kamun suka iso wani waje kamar kogo amma a bakin kogon gate ne mai ƙatuwar kwaɗuna a jiki.
Buɗewa jami'in ya yi da key ɗin da ke hannunsa sannan ya shiga, Sabo da kaza biye da shi a baya.
Su takwas ne zaune, ko wanne sanye da riga kalar sararin samaniya, ko wanne da Number ɗinsa a jiki. Kati suke bugawa. Sai dai tun lokacin da suka ka fahimci ana ƙoƙarin buɗewa suka dakata tare da zubawa wajen idanu. Yasaar na arba da Sabo da kaza, ya miƙe da sauri jikinsa na ɓari.
A fusace Sabo da kaza ya ƙarisa ya dunga ɗauke fuskansa da maruka hagu da dama. Sai da ya masa maruka shida sannan ya nuna sa da yatsa tare da faɗin,
"Ban taɓa sanin daƙiƙancin naka ya kai har haka ba sai yau! Ko ka san kuwa saboda ni har yanzu ka kasance da rai a jikinta? Da naga dama da tun lokacin da aka kama ka a airport zan saka a ɗauke min kanka da alburushi. Wato ka raina dabarata da wayau na shiyasa kake ɗaukar matakin da zai kai ka ya baro ko? Mai kake ci na baka ke zuba?" A fusace Sabo da kaza ke maganar.
Ƙirjin Yasaar ɗin ya bubbuga tare da faɗin, "Saura ƙiris, Zeenah ta zo hannunka. Daga wannan lokacin babu wanda ya isa ya dakatar da kai akan fansanka. Ni nan Junaidu inkiya Sabo da kaza, na tsaya maka. Kar kai ƙoƙarin ɓata rawarka da tsalle. Bar ni na yi amfani da ita na wannan lokacin kamun na ka turn ɗin ya zo. Kar ka kuma aikata irin wannan sakarcin. Ka saka a mayar da yarinyar!" Yana gama faɗin haka ya juya ya kalli jami'in da suka shigo tare ya ce,
"Daga yau kar a sake bashi waya har sai idan ni na buƙaci hakan," yana gama faɗin haka ya fice jami'in ya bishi a baya. Sai da ya kulle ƙofar sannan ya bi bayan Sabo da kaza.
Sai da ya rako shi har mota sannan ya leƙa ta window tare da faɗin, "Yallaɓai ya za ayi da wannan budurwar ta gida da ka ce a ajiye maka?"
Wani kallo sabo da kaza ya yiwa jami'in tare da yin murmushi sannan ya ce, "Sabo da kaza......."
Dariya jami'in ya yi tare da faɗin, "Bai hana a yanka ta! An gama yallaɓai. Yau sai dai uwarta ta haifi wani tunda ka gama cin moriyarta."
"Shiyasa na ke son aiki da kai, Labaran. Saƙonƙa zai biyo ka har gida." Faɗin Sabo da kaza.
Sara masa jami'in ya yi tare da ɗaga masa hannu yana murmushi har motarsu ta bar wajen.
_Bayan awa biyu_
Wayar Laushi ce ta yi ƙara alamar shigowar saƙo. Da sauri ta kai hannu kuma dama jigum suka yi su ukun suna jiran ta inda Meema za ta shigo.
"Saƙo ne daga ɓoyayyiyar Number kuma na san Yasaar ne. Wallahi tsoron buɗewa na ke yi." Laushi ta faɗi.
Ladi Katifa ce ta amshi wayar don hannun Laushi sai rawa ya ke.
_Tsiyarki na ƙofar gida a ajiye, amma ki sani wallahi Yasaar ba zai taɓa kyale ki ba sai ya mayar dake abun kwatance_
"Meema na ƙofar gida!" Ladi ta faɗi tare da yin hanyar waje da sauri, Laushi da Salma nice suka rufa mata baya.
Curko-curko suka yi ganin ƙatuwar akwati a ajiye a ƙofar gate ta cikin gida. Dukkansu babu wanda ƙirjinsa bai dukan tara-tara. Laushi jikinta babu inda bai rawa sai kallon akwatin take.
Ladi Katifa ce ta yi ƙarfin halin tsugunawa ta soma zage zip ɗin har ta buɗe gaba ɗaya.
Wani irin ja baya ta yi ganin Meema tsirara cikin jini kuma babu numfashi. Daga tsayen nan Laushi ta kife kif a ƙasa sumamma.
(Jama'a ashe sabo da kaza munafiki ne! 🤔)
#Sabo da Kaza #Yasaar #Laushi #Meema #Jami'i Labaran #M.S.P.K #My Destiny #Matar Sayyadee
*** [2/20, 9:56 PM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi! _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._