My Destiny (Ƙaddarata)

Page 23

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Hankalin Ladi da Salma ba ƙaramin tashi ya yi ba. Ga Laushi zube a sume a ƙasa, Meema cikin jini a cikin akwali. Duk sai suka rasa inda za su yi. Salma nice sai zagaye akwatin da Meema ke ciki ya ke yana kusa. Haka Ladi ita ma tana duƙe tana kukan.

Can dai Salmanu ya fita da gudu ya taro mai taxi suka dawo tare. Yana fitowa daga motar, motar Sabo da kaza na parking a ƙofar gidan.

"Kai lafiya?" Saboda da kaza ya faɗi yana kallon Salma nice da ya gama fita daga hayyacinsa yana kuka.

Duk yanda ya kai ga tsanar a tura shi jinsin maza, yau kam ko kula da an kira sa da kai bai yi ba. Bai ma kula Sabo da kazan ba sai shigewa da ya yi cikin gidan. Bin sa a baya Sabo da kaza ya yi, sai dai turus ya tsaya yana kallon Meema da ke cikin akwatin da Yasaar ya aiko da shi.

"Wannan yaron yana da matuƙar taurin kai wallahi! Allah ya sa ba kashe yarinyar nan ya yi ba," Sabo da kaza ya faɗi cikin zuciya.

"Ke! Yaushe ta dawo? Wa ya dawo da yarinyar nan? Haka aka mata? Tana da rai a jikinta?" Sabo da kaza ya watso wa Ladi tambayoyin.

Cikin kuka ta ce, "Turo saƙo ya yi shine duk muka fito muka ganta cikin akwati a wannan yanayin, don Allah ka taimaka mana."

Leƙawa waje ya yi tare da kiran Yahuza. Cikin saurin Yahuza dake cikin mota ya fito ya shigo cikin gidan. Da hannu ya masa nuni da Meema, shi kuma ya yi saurin nufa wajen ya duƙa tare da cicciɓota ya fito da ita. Hannunta da kanta lilo kawai suke alamar ta mutu.

"Wannan yarinyar babu rai a jikinta," Salmanu ɗan daudu ya faɗi tare da fashewa da kuka.

Ladi Katifa kuwa tsigar jikinta ne ya yi wani irin miƙewa saboda yanda maganar da Salma nice ya yi ya shigeta kamar an watsa mata ruwan ƙanƙara a lokacin hunturu.

Sabo da kaza wajen da Laushi ta ke a kwance ya nufa tare da cicciɓarta ya fita, suma suka rufa masa baya.

"Ki koma ki kullo gidan sai ku taho ke da wannan ɗan daudun a taxi. Ku taho Alpha clinic can muka nufa," saboda da kaza ya faɗi bayan ya saka Laushi a motar ya jinginar da ita a kujeran.

Zagayawa ya yi tare da zama gidan gaba tare da kullo ƙofa, Yahuza ya ja motar suka ɗau hanyar Alpha clinic. Tun a hanya ya kira likitan asibitin su kai waya, hakan ya sa suna isa a ka wuce da su emergency. Laushi gado aka bata bayan an ɗaura mata ƙarin ruwa. Meema kuma likitoci uku suka duƙufa a kanta suna ƙoƙarin ceto rayuwarta. Bayan tsayin awanni biyu doctor Shola ya fito daga emergency ɗin ya nufo inda Sabo da kaza ya ke,

"Mu je office, akwai abunda ya kamata ka sani."

Gyada kai Sabo da kaza ya yi tare da bin bayansa zuwa office ɗin nasa. Zama doctor Shola ya yi a mazauninsa, Sabo da kaza kuma ya zauna a kujeran da ke fuskantarsa.

"Ina jin ka, doctor. Me ke faruwa?" Sabo da kaza ya faɗi yana sauraran doctor ɗin.

Ajiyar zuciya doctor Shola ya saki tare da haɗe hannunsa biyu ya ɗaura guiwar hannayen a kan desk ɗin da ke gabansa tare da faɗin,

"Luckily, the little girl is alive. Amma ko mu likitoci mun yi mamaki da yarinyar nan ba ta mutu ba don a cikin babu wanda ya yi tunanin zai iya ceton rayuwarta kawai dai mun yi aikin mu ne. Duk wanda ya yi wa yarinyar nan wannan abu to wallahi ba shi da imani ko kaɗan don kashe ta ya so yi kawai! Mai wannan yarinyar da baza ta wuce 9 ba ta sani? Gaskiya raina ya mugun ɓaci. Wai ko kasan mai suka mata kuwa? Dole ne ma a duba ƙwaƙwalwarta don ganin ko ta samu matsala."

Ɗaga masa hannu sabo da kaza ya yi tare da faɗin, "Please, go straight to the point and tell me what is happening to the baby. Was she raped?"

Girgiza kai doctor ya yi tare da faɗin, "No, she wasn't. But a ƙananun shekarunta aka shaƙa mata Cocaine sannan an yawaita danna mata allurar bacci tare da shaƙe mata wuya wajan ɗura mata ƙwayar fita daga hayyaci. Kuma an yi amfani da abu an daki kanta da shi, ina tunanin ƙoƙarin guduwa ta yi shiyasa aka mata haka. Sannan anyi amfani da ruwan ƙanƙara a jikinta, wata ƙila tsumbulata su kai ko kwarara mata su kai a jiki. Wannan yarinyar sai dai addu'a kawai don da wuya ta tashi."

Miƙewa Sabo da kaza ya yi tare da ficewa daga office ɗin ya na tsinewa Yasaar albarka saboda ɓata masa aikin da yake son yi. Kai tsaye waje ya nufa ya kira wata Number ya dunga faɗa yana zage-zage kamar zai ari baki

Wani ɗaki aka kai Meema wacce aka saka mata Oxygen a hanci. Kwance ta ke kamar gawa, don idan ka kalleta ma za ka ɗauka gawar ce har sai idanunka sun sauka a kan computer ɗin da ke reading heartbeat ɗinta tukun za ka fahimci da rai a jikinta.

An hana kowa shiga ciki ya ganta sai ta window kawai mutum ke iya hango ta. Kuka wiwi Salma nice da Ladi Katifa suka riƙa yi lokacin da suka hango Meema kwance kamar gawa.

"Ko dai Meema mutuwa ta yi suke ɓoye mana? Kalle ta fa Ladi!" Salma nice ya faɗi yana jan majina.

Kasa magana Ladi Katifa ta yi, sai rawa da jikinta kawai ta ke yi.

Sabo da kaza bai ƙara shigowa cikin asibitin ba sai gab magrib lokacin Laushi ta farka sai kuka take tana faɗin ina ƴarta amma su Ladi sun ƙi faɗa mata saboda ba su so ta je ɗakin ta ga halin da Meema ke ciki.

"Kukan me kike yi?" Sabo da kaza ya faɗi yana mai ƙarisowa kusa da gadon da laushi ke zaune.

"Dan girman Allah ku faɗa min gaskiya idan Meema mutuwa ta yi kawai in ɗauki dangana," Laushi ta faɗi bayan ta kamo hannun Sabo da kaza ta riƙe gam.

Miƙar da ita ya yi tare da kama hannunta suka nufi ɗakin da Meema ke kwance kamar gawa. Neman zubewa a ƙasa Laushi ta soma yi lokacin da ta yi arba da ƴarta kwance kamar gawa.

"Meeemaaaah!" Ta faɗi cike da wani irin murya ta ƙaunar ƴa. "Meema haka aka miki? Duk laifina ne. Ni na jawo miki komai. Da ban ci amanar Yasaar ba da duk haka bata faru ba. Don girman Allah Meema kar ki tafi ki bar ni. Ke kaɗai kika rage min a duniyar nan. Wallahi ina ƙaunar ki ƴata. Ka ce mata ta tashi don Allah. Ki tashi Meema! Meema ki tashiiiiiiiiiii!" Ta ƙarisa maganar tare da zamewa a gaban gadon tana wani irin kuka.

Taɓe baki Sabo da kaza ya yi tare da faɗin, "The is just the movie trailer. The real scene is by the corner!" Duk a cikin zuciyarsa ya faɗi maganar yana dariya.

Duƙowa ya yi daidai kunnanta tare da faɗin, "It's alright, Zeenah. Everything will be fine in Sha Allah. Meema need only your prayers not your tears. In Sha Allah za ta tashi."

Share hawaye Laushi ta yi tare da faɗin, "Mai ya samu ƴata? Fyaɗe ya mata ko?"

"Mu je waje mu yi magana, it will be better don sun ce Meema ba ta ɓulatar hayaniya saboda condition ɗinta.

Miƙewa ta y ta fice shi kuma ya bi bayanta har zuwa kan kujeran silver ɗin da ta zauna. Zama ya yi a gefenta tare da faɗin, "Zeenah, kin ga sakamakon cin amana ko? To yanzu wa gari ya waya? Zunubin da kika aikata yana ƙarewa a kan ƴarki. Kin san kuwa wahalar da na sha kamun na shago kan wanda Meema ke wajensu? To bari ki ji, sai da na yi asarar miliyoyin kuɗi wajen bailing Meema don har hakan ya kusa taɓa sana'a ta don har wasu daga cikinmu sun fara zargin ko da saka hannuna kika ci amanar Yasaar. Yasaar ya wuce duk inda kike tunani. Kin jawo masu ɗunbin asara da tashin hankali lokacin da kika ci amanar Yasaar wanda har hakan ya jawo aka kashe twin brother ɗinsa a matsayin Yasaar ɗin wanda hakan ya saka ya yi alwashin sai ya ga bayanki. Mai gidan Yasaar kuwa, kin saka ya yi asarar Cocaines har na sama da dala billion tara! Kin kuwa san nawa ne dala bilion tara a kuɗinmu na Nigeria? Hmm, Zeenah kin yi ganganci wallahi."

Laushi cikinta ya yi wani irin murɗawar tashin hankali jin labarin da Sabo da kaza ya faɗa mata. "Yanzu kenan farautar rayuwata da ta ƴata za su riƙa yi??" Laushi ta faɗi.

Girgiza kai ya yi tare da faɗin, "Fiye da haka! Don da kashe ki suke ke son yi, tun daran ranar da kika aikata son zuciyarki za su kashe ki"

"To yanzu mai za su mana?" Laushi ta faɗi bayan ta kai hannunta ƙasan mararta da ya murɗa da uban ƙarfi.

"Wannan ba shine mai mahimmanci ba. Don na riga na rufe wannan case ɗin da kyar. Yasaar ba zai ƙara farautar rayuwatarki ke da ƴarki ba, amma kuma ki sani, idan kika saki kika kwatanta abunda kika yiwa Yasaar a kai na, a gaban idanunki zan kwakwule idanun Meema sannan in kwanta da ita a gabanki kamun in daddatsata in saka ki dafa naman jikinta da hannunki sannan in ciyar da ke naman ƴarki da wannan hannun nawa," yana gama faɗin haka ya miƙe.

Laushi kasa motsi ta yi don idan ta yunƙura, tabbas wannan karan idan ta kai ƙasa sai ta samu shanyewar ɓarin jiki. Har ya yi taku biyu, sai ya dawo da baya tare da duƙowa daidai kunnanta ya ce,

"Ba suyi wa ƴarki fyaɗe ba, amma sun kusan nakasta rayuwarta. Don sun shaƙa mata Cocaine sannan sun mata allurar barci mara iyaka tare da ɗura mata kwayoyin da ko ke sun fi ƙarfin ki bare yarinya ƴar shekara 9. Akwai yiwuwar ta samu taɓun hankali saboda dukan kanta da suka yi da wani abu," yana gama faɗin haka ya miƙe tare da saka hannu cikin aljihu sannan ya kuma faɗin,

"Abu mafi muhimmanci, ko Ladi kar ta san sirrina!" Yana gama faɗin haka ya wuce da sassarfa.

Laushi ta kai tsayin mintuna arba'in jikinta na rawa ta kuma kasa motsa ko ɗan yatsanta. Abubuwa ne kawai ke ta mata yawo a kwakwalwar kanta. Idan ta soma saƙa zance sai ta warware ta hau saƙa wani.

"Yasaar, Sabo da kaza!" Abinda ta riƙa faɗi kenan cikin zuciya har ya fito fili ta riƙa faɗi kamar wata zararra.

Wata nurse ta girgiza ta da ƙarfi ganin ta yi mata magana amma bata san tana yi ba har sai da ta girgiza tan.

"Yasaar, Sabo da kaza! Don girman Allah ki faɗa min gaskiya. YASAAR, SABO DA KAZA!!" Wannan karon da ƙarfi ta yi maganar tana zazzaro mata idanu kamar wacce ƙwaƙwalwarta ya taɓu.

Cikin sauri nurse ɗin ta ja da baya ganin kamar da mahaukaciya ta ke magana. Amma cikin zafin namar da ta jima tana buƙatarsa domin ta miƙe tsaye ta cafko nurse ɗinnan ta riƙe gam tare da faɗin

"Ki faɗa min! Na ce ki faɗa min gaskiya. Na ce maki Yasaar, Sabo da kaza!"

Ihu Nurse ɗin ta shiga kwararawa tana neman taimako daidai fitowar doctor Shola daga office ya ƙariso inda suke. Ai Laushi na arba da shi ta shaƙi wuyan farar labcoat ɗin jinsa ta shiga faɗin,

"Yasaar, Sabo da kaza! Yasaar, Sabo da kaza!!"

Da kyar aka kwaci wuyan doctor a hannun Laushi. Su Ladi kuwa suna can ɗakin da aka bawa Laushin gado basu san wainar da ake tonawa ba.

Da sauri doctor ya koma office ya kira Sabo da kaza a waya ya shaida masa abunda ke faruwa.

"Danna mata allurar barci gani nan zuwa yanzu ban yi nisa ba. Yanzu na fita daga asibiti," faɗin Sabo da kaza tare da yanke wayar.

Nurses maza uku da kyar suka iya jan Laushi zuwa wani ɗaki doctor Shola ya soma ƙoƙarin danna mata allura. Sai dai yanda ta ƙame jikinta kamar icce ya saka doctor Shola ya fasa yi mata don tabbas idan ya saka allurar a jikinta karyewa zai yi kuma akwai matsala.

Ana wannan kiciniyar Sabo da kaza ya shigo ɗakin da suke. Hanky ɗin da ke hannunsa ya danna a kan hancinta, cikin second biyu ta tafi luuuu gaba ɗaya jikinta ya saki. Da kansa ya saɓa ta a kafaɗa ya nufi motarsa da ita. Shi da kansa ya yi driving har zuwa can guest house ɗinsa, wanda tafiyar awa ɗaya ne daga asibiti. Saɓota ya kuma yi a kafaɗa bayan ya shigo da motar ciki ya kwantar a kan doguwar kujera mai cin mutum uku sannan ya nufi wani ɗaki ya shiga ya kullo.

A can asibiti kuwa, Ladi sun ji shiru Laushi bata dawo ba, sai suka fito domin duba ta. Sai dai duk inda suka duba babu ita babu alamarta har shi Sabo da kazan.

"Lallai idan abunda zuciyata ke raya min hakane? To tabbas Laushi ta tabbata tinkiya kuma ƙidahuma!" Ladi Katifa ta faɗi ranta a ɓace.

"Ke ina kike tunanin ta je?" Salma nice ya faɗi.

"Ina kuwa bayan hotel ita da Sabo da kaza domin iskanci!" Ladi Katifa ta faɗi.

Girgiza kai Salma nice ya yi tare da faɗin, "Ni kuma ban tunanin haka. Ai bariki ba hauka bace! Wata ƙila dai wani abun mai mahimmanci ta je yi duk akan laluran Meema. Ke baki ganin yanda hankalinta ya tashi a kan ƴar!" Salma nice ya faɗi.

Ladi za tai magana wayar hannunta ya hau ƙara. Da sauri ta kalli screen ɗin tare da faɗin, "Habib ne ke kira na. Kuma nasan Meema zai ce a ba."

#Meemah #Yasaar #Sabo da Kaza #Laushi #Habib #My Destiny #Matar Sayyadee

*** [2/20, 9:56 PM] Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi! _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._