Page 24
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
"To ki ɗaga kiran mana kar ya katse," Salma nice ya faɗi yana kallon wayar hannun Ladin.
Ɗaga kiran ta yi tare da karawa a kunne ta furta cikakkiyar sallama.
"Ameen wa'alaikissalam, Rukayyah. Ina wuni ya aiki?" Faɗin Habib da ke ƙoƙarin fitowa daga cikin mota.
"Alhamdulillah, ya iyaye da kuma iyalan?" Ladi ta faɗi don bugun ruwan cikinsa domin ta ji ko yana da iyali.
"Suna nan lafiya, duk sun ce a gaishe ku. Ina mutuniyar tawa da kuma ƴata? Na ce sai na ji muryansu muyi sallama kamun na tafi," Habib ya faɗi yana sosa kunne da makullin motarsa.
"Tafiya za kayi ne? Ladi ta faɗi tana sauraran sa.
"Eh, ƙasar zan bari ma. Alhajinmu ne ya aike ni Sweden. Yanzu haka ma ina airport in the next 30minutes jirgin zai tashi," Habib ya faɗi.
"Ma sha Allah! Allah ya taimaka. Sai dai mutuniyar taka sun fita tare da Meema ba jimawa," Ladi ta faɗi saboda bata son tada masa hankali shi da zai hau jirgi.
Ɗan jim ya yi kamun ya ce, "Ta tafi da waya ne? Ina son magana da su kamun na wuce."
"Yau dai kam ka taki rashin Sa'a don ga wayar can jikin charger don jiya kwata-kwata basu bar mana wuta ba sai ɗazu suka kawo shiyasa bata tafi da wayar ba. Kuma ba ma nisa su ka yi ba. Nan da mintuna talatin za su dawo in Sha Allah."
Ajiyar zuciya ya yi tare da faɗin, "Jirgi sam bai jira da na jira na yi magana da su tukun kamun na wuce, amma ina sauka zan saka layin can ƙasar sai in kira ki haɗa mu da su."
"To babu matsala, Allah ya kiyaye hanya," Ladi ta faɗi. Da ameen ya amsa sannan ya katse wayar.
"Mai yasa kika masa ƙarya? Idan ya samu labari ba zai ji daɗi ba fa," Salma nice ya faɗi.
"Jirgi fa zai hau, kuma babansa ne ya aike sa. Haka nan sai in faɗa masa maganar tashin hankali! Ba zai yiwu ba."
"Eh, da wannan gaskiya. Amma naga ni cikin idanunki har yanzu kina son wannan mutumin ko?" Salmanu ɗan daudu ya faɗi yana kallonta domin ganin reaction ɗin ta.
"Hmm! Ba za ki gane ba Salma. Ba ki san komai a kan soyayya bane shiyasa. Farat ɗaya ya ke shiga zuciyar mutum, amma yana ɗaukar shekaru kamun ya fita. Wani ma da shi za a burne ka."
Dafa ta Salma nice ya yi tare da faɗin, "In Sha Allah ke ma za ki samu na ki soyayyar wanda zai iya komai a kanki cikin kuwa har da rintse idanu da toshe kunne. Ke da barikinki ma ba mai muni bane kamar na Laushi kuma duk da haka ta samu mai sonta da aure kamar Habibu!"
Janye kafaɗunta ta yi tare da faɗin, "Hmm, Salma kenan! Mu bar wannan maganar kawai," ta faɗi hakane tare da nufa ɗakin da Meema ta ke ta tsaya ta window tana hangenta.
Har a kai sallar Isha'i babu Laushi babu alamunta. Nan fa hankalinsu ya soma tashi. Ga Meema har wannan lokacin ba a faɗa masu komai a kanta. Gashi wayar Laushi na hannun Ladin bare su kira su ji inda ta ke. Can wani dabara ya faɗowa Ladi, sai ta kwashe number ɗin Sabo da kaza ta danna masa kira, sai dai har ya gama ringing ba a ɗaga ba. Ta kira sau ɗaya, biyu uku no answer. A na huɗun sai ta ji switchoff. Ba ƙaramin ɓaci ranta ya yi ba, kuma zuciyarta ta gama yarda Laushin iskancinta kawai ta tafi.
A can guest house ɗin Sabo da kaza kuwa; bayan ya shiga ɗakin nan, bayan mintuna uku ya dawo Laushi barci ta kwasa kamar gawa don sai ƙarfe goma da mintuna tara ta tashi kasancewar ya danna mata Midazolam injection. Ko da ta miƙe, kanta ne ya mata wani irin nauyi. Hannu bibbiyu ta saka ta riƙe kan da yake jujjuya mata. Ta jima a zaune kamun ta soma kallon ɗakin saƙo da lungun tana son tunano ina ne nan ɗin, kuma a daidai wannan lokacin Sabo da kaza ya fito daga ɗaki.
Da kallo kawai ta dunga bin sa kamar taɓaɓɓa, shi kuma ya ƙariso da jiƙaƙƙen hannunsa alamar alwala ya kammala ba jima. Hannun ya ɗaga ya yarfa mata a fuska tare da faɗin, "Why the look?"
Wani irin miƙewa ta yi tare da faɗin, "Where is my daughter? Where's Meema? Mai yasa za ka min haka? Mai yasa za ka haɗa kai da Yasaar ku cuce ni? Na san tare kuke? Mai na muku? Don girman Allah kuyi haƙuri ku fita daga rayuwa!" Da wani irin raunataccen kuka ta faɗi hakan.
Kujera ya nuna mata tare da faɗin, "Zauna."
Harara ta maka masa tare da faɗin, "ba zan zauna ba, Sabo da kaza!"
"Bai fa hana a yanka ta!" Ya faɗi yana shafa gemunsa tare da murmushi a lokaci guda.
"Me fa? Ban gane ba," ta fadi tana kuma harararsa.
"Sabo da kaza, bai hana a yanka ta! Ko baki fahimci hausar bane? To jinan; abunda ake nufi shine, duk sabo na da mutum bai hana ni cin ubansa ko kuma turasa inda ba a dawowa ko da kuwa ɗan uwana ne in dai akan sana'ata ce. Kin fahimta?"
Ƙasa ta zube a kan guiwowinta tare da kama ƙafafunsa ta shiga faɗin, "Na roƙeƙa da darajar iyayanka ka kyale mu ni da ƴata. Idan kana so zan iya rantse mata da alƙur'ani mai girma akan bazan taɓa furta sirrinka ga kowa ba. Dan Allah!"
"Ta shi ki zauna, Maman Meema," ya faɗi cike da muryan yaudara.
Da sauri ta ɗago domin sunan da ya kira ta da shi mutum ɗaya ya tuno mata da shi, wato Habibu.
Tashi ta yi ta zauna amma jikinta bai daina rawa ba. Don wani mugun tsoron Sabo da kazan ne ya shige ta lokaci guda.
Zama ya yi kusa da ita tare da saƙalo hannunsa ya ɗaura a kan kafaɗunta sannan ya matso da ita jikinsa sosai ya hau shinshina wuyanta zuwa kunnanta sannan ya saka yatsa ya mayar da kitson attachment ɗin kanta na gaba zuwa bayan kunnanta tare da faɗin,
"Ban ga laifinki ba da tsoro ya bayyana a tattare da ke haka ba. Sannan ban ga laifinki ba idan kin yi zargi na don ko ni ce a matsayin zargin da zan yi kenan. Amma abunda nake so ki sani kuma ki yi tunani da kwakwalwarki shine; idan har ina da alaƙa da Yasaar, menene zai saka na amince da ke har na saya maki gida na kuma ɗauke duk ɗawainiyarki da ƴarki. Sannan lokacin da Yasaar ya ɗauke Meema, ba zan taimaka miki ba wajen ceto ba, sai dai ma in haɗa hannu mu kashe ta. Ke kin san ba fin ƙarfina kika yi ba, asali ma da ni kike taƙama a garin Lagos. Idan cutar da ke na ke son yi ba sai na yi wannan kwane-kwanen ba, ko a nan da na kashe ki na bunne ki kuma babu wanda zai sani har duniya ta naɗe. Ni damuwa ta da ke kawai ki riƙe min amanata, idan har kika mun haka babu wani abu da zai haɗa mu da ke na tashin hankali."
A hankali sannan jiki a sanyaye ta ce, "To ni mai yasa zan ci amanarka? Ko shi Yasaar da na masa haka, shi ya fara cin zarafi na. Duk da ni ɗin karuwa ce, hakan ba yana nufin a riƙa cin zarafin jikina bane. Yasaar a cikin jama'a a kuma gaban ƴata ya min tsirara yana dukana. Abun ya min ciwo kwarai da gaske. Hakan ne ya saka zuciya wacce bata da ƙashi ta tunzura ni na yi masa cunen jami'an tsaro suka kama shi dumu-dumu da Cocaines, amma wallahi tallahi da ba dan haka ba babu abunda zai saka na ci amanar sa."
Murmushi ya yi tare da kwanto da kanta kan ƙirjinsa sannan ya ce, "To ki kwantar da hankalinki, ni babu abinda zan miki ke da ƴarki. Kuma zan zame maku garkuwa. Ba zan taɓa bari wani abu ya faru da ku ba. Meema kuma, in Sha Allah za ta tashi. Ni ma zan yi iyakacin ƙoƙarina ko da kuwa hakan na nufin fitar da ita waje ne."
"Nagode sosai, amma don Allah ka daina tsoratar da ni da irin maganganun da ka min a asibiti ɗazu," ta faɗi tana kallon fuskansa.
Gyaɗa kai ya yi tare da faɗin, "In Sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba. Ki saki jikinki dani."
Gyada kai ta yi tare da faɗin, "Muje ka mayar dani asibiti. Hankalina ba zai taɓa kwanciya ba sai na ganni kusa da ƴata."
Hancinta ya ja tare da faɗin, "Ai ni da na ɗauka baki son ƴar ai," ya ƙarisa maganar yana dariya.
Waro idanu ta yi tare da faɗin, "Wace uwa ce za ta haifa ƴa ta ce bata so? Caɓ! Ina ƙaunar abata Wallahi."
Dariya ya kuma yi tare da miƙewa ya ce, "Ni kuma da har ina harhaɗa kan ƴan kuɗaɗena in baki ki sayar min da ita."
Dariya ta yi sosai tare da faɗin, "Caɓ! Ai ko uban da ya haife ta ne ya zo ba bashi zan ba wallahi."
"Kin san uban kenan?" Ya watsa mata tambayar yana kallonta.
Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Wallahi ban sa shi ba."
"Allah ya kyauta to. Ki kimtsa bari na watsa ruwa na fito sai mu wuce asibitin," ya faɗi yana nufa ɗakin da ya fito.
"Wanka kuma? Ba alwala ka yi yanzu ba?"
"No, wanka na yi ban shafa mai ba. Wai kin san kuwa ƙarfe nawa?" Ya faɗi bayan ya ɗan juyo.
Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Ƙarfe nawa don Allah?"
"It's after 10 yanzu!" Ya faɗi yana mai zan hannun rigar shaddar jikinsa domin ganin agogo.
Da wani irin sauri ta miƙe tare da faɗin, "Na shiga uku na lalace! Don girman Allah mu koma asibiti. Wayyo, su Ladi na can na jira na."
"Ok, bari na ɗauraye jiki Sharp-sharp sai in fito mu wuce." Yana gama faɗin ya shige ciki.
Sawa da Marwa kawai tai ta yi har ya fito da ɗakin shanye da wasu kaya. Wannan ƙananan ƙaya ne a jikinsa, jeans da t-shirt sai P-cap ɗin da ya saka a kai da glasses. Sai kayan suka ɓoye shekarunsa. Key ɗin mota a hannunsa da wayarsa ya ce, "Muje ko."
Tuni har ta fice daga ɗakin tare da isa wajen mota. Kai ta ɗaga sama tana kallon yanda garin ya yi dinɗim da duhu.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku ni Zeenah!! Dare ya yi sosai wallahi," ta faɗi tare da ɗaura hannu a kai.
Sabo da Kaza yana ƙariso wajen ya buɗe mota da sauri tare da shiga. Ita ma cikin saurin ta buɗe gidan gaba ta shiga.
A wani restaurant ya yi parking tare da faɗin, "Bari na sama maki abinci ko!"
Girgiza kai ta yi da sauri tare da faɗin, "A'a ni kam mu tafi kawai. Ƴata nake son gani."
"Ai ko ke baza ki ci ba, waɗanda ke asibitin za su buƙaci abincin ko! Bari yanzu zan fito duk da na san ke ɗin ma yunwar kike ji," yana gama faɗin haka ya buɗe motar ya fice ya shige ciki da sauri.
Laushi kuwa tun da ya shiga ciki ta ke zabga tsaki tana kallon agogon motar da ya nuna sha ɗaya saura kwata. Zuwa can sai ga shi ya fito da manyan fararan ledodi guda uku. Ajiyar zuciya ta yi don ɗan fitar da ya yi na ƴan mintuna sai ta ga kamar ya kusa awa guda.
Buɗe bayan motar ya yi tare da ajiye ledojin sannan ya rufe ya buɗe mazaunin driver ya shiga tare da tadawa suka nufi asibitin. Karfe sha ɗaya da mintuna biyar suka shigo harabar asibitin. Da sauri ta ɓalle murfin motar za ta fita ya yi saurin riƙo hannunta tare da faɗin,
"Shikenan yanzu ni kaɗai zan kwana babu mace kamar ki kusa dani? Gaskiya i will miss you. Ko in jira ki ganta ne sai mu tafi gobe da asubar fari in dawo dake?"
Wani harara ta watsa masa tare da fizge hannunta ta ce, "Gaskiya ba ka da tausayi! Yanzu fisabilillah, ƴata na kwance a asibitin ne zan bi ka muyi iskanci?"
Shafa kai yayi tare da faɗin, "Kawai tsokana ce domin jin abunda za ki ce. Ɗauki ledan abincin ki shiga dashi sai na shigo gobe," ya ƙarisa maganar tare da sakar mata hannu.
Buɗe bayan ta yi tare da kwasan ledojin sannan ta rufe ta nufi ciki ba tare da ta ƙara juyowa ta kallesa ba.
Da sauri-sauri kamar za ta tashi sama ta yi ta tafiya har ta isa ɗakin da Meema ta ke. Sai dai an kulle gam, babu wanda zai iya shiga sai dai ya hange ta ta cikin window. Ta kusa mintuna talatin a wajen tana kallon Meema tana hawaye kamun ta juya ta nufi ɗakin da aka bata gado ɗazu domin duba su Ladi Katifa don ta san definitely babu inda za su tafi a wannan hali da Meema ke ciki. Ilai kuwa tana buɗe ƙofa su kai idanu huɗu da Salmanu ɗan daudu da ke hamma saboda muguwar yunwar da ya ke ji. Wani wawan harara ya maka mata tare da jan dogon tsaki ya juya baya.
"Ke kuma tsakin me kike haka? Ko duk na yunw.........." Ba tare da Ladi Katifa ta ƙarisa maganarta ba ta ja wani dogon tsakin da yafi na wanda Salma nice ya yi sannan ta koma ruf da ciki ta kwanta a kan gadon da Laushin ce ke kwance a kai lokacin da suka zo asibitin don har yanzu akwai sauran ruwa maƙale a jikin ƙarfe.
"Ku yi haƙuri don Allah. Na san dole kuyi fushi dani. Ba da gangan na bar ku da wunya ba. Wallahi tun da muka fita ni da sabo da kaza zuwa ɗakin Meema take ɗazu na ga halin da take ciki ban kuma sanin inda kai na yake ba sai gidan Sabo da kaza. Ban jima da tashi ba, shine ya ajiye yanzu. Ku yi haƙuri ga abincinku nan," ta ƙarisa maganar tare da ajiye masu ledan a kan wani ɗan drawer dake kusa da petient bed.
A zafafe Ladi Katifa ta miƙe zaune tare da faɗin, "Ban taɓa tunanin ke wawuya wacce bata san inda ke mata ciwo bace sai yau. Ƴarki! Wacce ta fito daga cikinki za ki wulaƙanta haka! Kin ban mamaki Zeenatu. Yanzu a wannan halin da ƴarki ke ciki har jijiyoyin da ke sadar da shawa'arki ta iya motsa miki ki ka tafi ki ka bi gantalallan Saurayinki da ni kwata-kwata bai kwanta min a rai ba ku ka je kuna iskancinku tare da shaye-shaye ko! To ya yi kyau. Kin kyauta Laushi."
"Wani irin maganar banza ce wannan, Katifa? Ni da ke wa ya fi son Meema? Kar ki manta ta jikina ta ratso ta fito a gaban idanunki. Duk duniya akwai wacce ko wanda zai nuna wa Meema soyayya ce da tafi tawa? Ya zan faɗa miki abunda ya faru amma ki ƙi yarda da magana ta! Wallahi, tallahi idan na kwanta da wani ɗa namiji yau ɗin nan, Allah ya ɗauki raina yanzun nan ko kuma gobe mota ta yi kwatsa-kwatsa da kwanyata!" Ta ƙarisa maganar cike da wani irin zafin rai da ƙunar zuciya.
Ajiyar zuciya Ladi ta sauke don yanzu kam ta yarda da ƙawarta. Hatta Salma nice da bai furta ko ƙala ba, shi ma ya yarda da abinda Laushin ta faɗi.
"To amma ina kika je haka kika kai dare? Gaba ɗaya hankalinmu ya tashi wallahi. Duk mun ɗauka kina tare da Sabo da kaza a hotel shiyasa ranmu ya ɓaci," Ladi ta faɗi da sanyin murya.
"Muna tare da shi, amma wallahi babu abunda ya haɗa ni da shi. Asalima ban san lokacin da ya fitar dani daga asibitin nan ba. Last abunda zan iya tunawa shine; zayyano min halin da Meema take ciki da ya yi. To tun daga wannan lokacin ban kuma sanin inda kaina yake ba," faɗin Laushi bayan ta zauna gefen Ladi.
"Mai suka ce ya faru da Meeman? Ba dai fyaɗen ya yi mata ba ko?" Ladi da Salma nice suka haɗa baki suka faɗi.
Sai da Laushi ta sharce hawayen da suka gangaro mata sannan ta basu labarin abunda Sabo da kaza ya faɗa mata akan halin da Meeman ke ciki.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! In Sha Allah babu abunda zai samu kwakwalwar Meema. Meema za ta warke! Ai likita ba Allah bane," faɗin Ladi tana kuka sosai.
Salmanu ɗan daudu kuwa mutuwar zaune ya yi bayan sauraron duk abunda Laushin ta faɗi. Can ya ɗaura hannu a kai ya kwanɗama wani ihu tare da faɗin,
"Wayyoo ni kaina! Wayyo Allahna! Wayyo ni Salmanu jikan iya!" (Finally! Yau dai Salmanu ya kira kansa da namiji. 🤚😂🤚😂😂
Haka su kai ta kuka babu mai lallashin wani. Can dai Ladi Katifa ta ce, "Gaskiya Laushi, tunda ke ce uwar yarinyar nan ki zo ki zauna cikin daren nan ni da Salma nice mu tsefe miki kanki tasss ki wanka musulunci sannan ki alwala ki duƙufa nemawa yarinyar sauƙin ubangiji, muma kuma za mu taya ki. Sannan kuma idan so samu ne, tunda gobe Litinin ki tashi da azumi. A cikin watannan gaba ɗaya ki kiyaye saɓon Allah domin samun damar Allah ya amshi addu'arki don ance addu'a da tsinuwar uwa tamkar yankan wuƙa haka yake ci."
"Wallahi maganari gaskiya ce. Gobe-goben nan zan fita na yanko mata yadikan hijjabai kala biyar, kuma ba zan shigo nan da su ba sai a ɗike. Idan komai ya daidaita sai ki cigaba da sharholiyarki," faɗin Salmanu ɗan daudu.
Ita dai Laushi bata ce komai ba. Duk yanda suka yi da ita a cikin daren nan haka take bi. Bayan sun ɗan taɓa abinci, sai suka hau tsefe kanta wanda ya ɗauke su har biyun dare don Ghana weaving ne kuma ƙanana. A haka ma don su biyu ne kuma suna da saurin tsifa.
"Yauwa to Alhamdulillah! Yanzu sai ki shiga daga cikin bayi ki wankan tsarki sosai, sannan ki ɗauro alwala ki fara sannan da wannan gyalen na Ladi na ga yafi naki ɗan girma kamun dai zuwa goben," Salma nice ya faɗi yana ɗaga fashminan Ladi Katifa.
Shiga bayin laushi ta yi tare da yin wankan tsarkin sannan ta fito ɗaure da towel gashinta na ɗigan ruwa.
"Ni da zan baki shawara ki ɗauka da cewa zan yi ki haƙura da wannan kitson ƙarin da kike yi tunda tubarakallah kina da suma sosai. Gashi kitson nan da kike yi duk ya cinye miki gaban gashi," Ladi Katifa ta faɗi.
Ita dai Laushi ko ƙala bata ce ba. Ta koma kamar wata salaha mai tsoran Allah.
"Ki ce Ash Hadu Allah Ilaha Illallahu Wa Ash......."
"Kai dallah rufewa mutane baki! Ridda ta yi da kake ƙoƙarin bata kalmar shahada kamar wata tubabbiya?" Ladi Katifa ta katse Salma nice.
"Haba ke kuwa Ladi! Irin wannan ɓarna da a ka yi shekara da shekaru ana yi, ai har sai a fita daga musuluncin ma ba a sani ba," Salma nice ya faɗi.
"Oh Allaaah! To Allah kyau. Ai sai ki karɓi kalmar shahadar ki koma cikin musulunci," faɗin Ladi Katifa.
Laushi bata saurare su ba ta saka rigar da ta kira tare da rolling fashminar Ladin ta tada sallah bayan ta shimfiɗa gyalenta a ƙasa. Gaba ɗaya duk sai ta jita wata kala don baza ta taɓa iya tuna when last ta saka goshinta a ƙasa ba da sunan gaishe da Allah. Sai ta ji wani irin kunya da nauyi ya kamata kamar Allah na gabanta tana kallonsa.
Babu abunda ta manta game da karatun sallah don sun samu horo sosai a wannan fannin a wajen abban na su wato, malam Ayuba.
Tun su Ladi na kallonta suna irga raka'a bibbiyu da take yi har barcin ya kwashe su. Laushi kuwa ko runtsawa bata yi ba har a kai kiran asuba wanda ta manta yanda ake jin kiran sallar a kunnanta. Addu'a ta yiwa Meema sosai bayan ta gama maimaita kiran sallah kamar yanda addini ya umarta.
Sai da gari ya yi sanke taar sannan Laushi ta tashi ta nannaɗe gyalenta tare da fita daga ɗakin ta nufi ɗakin da aka kwantar da Meeman, luckily sai ta gansa a buɗe sai ta yi saurin shiga har tana cin tuntuɓe.
Meeman dai na nan kamar jiya, banda zuciyar babu abunda ke motsi a jikinta.
"Allah don girman zatinka, ka tashi kafaɗun yarinyar nan ba don halina ba. Ya Allah kar ka dubi girman laifina a gare ka, na san ni mai zunubi ce. Allah don girman ka, don ƙaunarka ga fiyayyan halitta, don tsarkakakkun sunayanka guda casa'in da tara, don zatinka, don tausayinka, don alfarmarka ya ubangiji ka tashi kafaɗun wannan yarinyar da bata san komai ba," ta ƙarisa maganar tana mai haɗe hannayenta guda biyu sannan ta kai goshinta ƙasa ta yi sujada tare da fashewa da raunataccen kuka mai taɓa zuciyar mai sauraro.
Ta jima da kanta a ƙasa bata ɗago ba kuma bata bar kuka ba har sai da Nurse ɗin da ke kula da Meeman ta shigo ta ɗago ta.
"Ki yi haƙuri, za ta tashi in Sha Allah!" Nurse ɗin ta faɗi bayan ta dafa kafaɗunta.
Gyaɗa kai kawai Laushi ta yi tare da kama karfen gadon tana kallon Meema wacce idanunta ke arufe.
"Ku min haƙuri in zauna kusa da ƴata don Allah," ta faɗi bayan ta kalli Nurse ɗin.
"Babu matsala in dai baza ki hayaniya ba!" Nurse ɗin ta faɗi.
"Ba zan yi ba in Sha Allah!" Laushi ta faɗi tana jin daɗin sabon damar zama a ɗakin don ta riƙa kallon ƴarta.
Karfe tara Sabo da kaza ya kawo masu breakfast sannan ya yi sallama da Laushi a kan zai je Togo, tafiyar gaggawa ta same shi, sai dai ba zai wuce kwana uku zuwa huɗu ba. Sannan ya bata kwarin guiwa a kan in Sha Allah Meemah za ta tashi. Nan da sati guda idan kuma bata farfaɗo daga doguwar suman da doctor ya ce ta yi ba, to zai masu visa su tafi India a duba ta kawai.
Abun dai kamar wasa Meema ta kwashi sati guda bata farfaɗo ba a wannan asibitin. Ko ɗanyatsanta bai motsi. Laushi ta yi wani irin ramewa. Kuma a cikin sati ɗayan nan ta koma kamar sabuwar halitta domin sallah bai wuce ta, haka azumi don azumin Annabi Dawood ta koma yi idan ta yi yau gobe baza ta yi ba sai jibi.
Dama tun a rana ta biyar Sabo da kaza ya dawo daga Togo, kuma tun a can ɗin da ya samu labarin jikin Meema bai improving, sai kawai ya shiga ƙoƙarin yi masu passport. Ranar da ya diro ranar passport ɗinsu ya diro, private jet suka bi suka tafi India, Meema, Laushi da kuma Sabo da kaza.
Suna isa doctor huɗu suka rufa mata, tasa-tasai kuwa anyi mata sun fi goma, anyi hoton ƙwaƙwalwa guda uku. Kuma Alhamdulillah bayan kwana biyu result ya fito. Don tun kamun result ya fito Meema ta farfaɗo daga dogon suman da ta faɗa, sai dai ko da ta farfaɗo da ihu da kuma fizge-fizge ta farfaɗo har sai da aka mata allurar bacci.
Doctor ya kira Sabo da kaza da Laushi office ya masu bayanin cewar Meema bata samu matsalar komai a kanta ba ban da buguwa, doguwar suma ta faɗa sakamakon gana mata azabar da aka yi da kuma allurar da aka mata da ta fi ƙarfin ƙwaƙwalwarta. Don ma dai kaɗan ne aka mata, amma da ya wuce hakan da tabbas ƙwaƙwalwarta sai ya taɓu. Kuma wannan fizge-fizgen da take yi tsorata ta yi da kuma firgici shiyasa. Amma nan da wasu ƴan kwanaki duk za ta bari idan har aka kwantar mata da hankali aka nuna mata soyayya da kulawa har ta manta wancen abun da ya faru.
Wani irin sanyin rahama da daɗi Laushi ta ji jin babu wani mummunar cuta da ta samu ƴarta.
Satin Meema ɗaya a India ta warware, sai dai basu dawo Nigeria ba sai da suka biya ƙasashe biyu, wato Paris da Dubai. Meema ta samu farin ciki da mahaifiyarta da bata taɓa samu ba a rayuwarta ba. Domin ta ririta kamar kwai. Sun ɗauki hotuna babu adadi. Irin kulawar da Sabo da kaza ya basu ita da ƴarta ya saka gaba ɗaya ta sakankance da shi har ta mance da ibadar da ta soma, duk da dai sallar ana yinta, amma wani lokacin a ƙurarran lokaci, amma kuma karuwanci an koma ruwa tsundum da shaye-shaye. Idan ka ga Meema da uwarta sai ka musu kallo biyu domin fatar nan tasu ta yi kyau sosai musamman baƙar fatar Meema da ke shinning.
Daga Dubai jirgin Nigeria Meema suka biyu don a can suka bar Sabo da kaza kasancewar daga nan Dubai ɗin ba Nigeria ya taho ba, Angola ya nufa domin taho da wasu makamai da kwayoyi.
A cikin jirgi Meema gaba ɗaya tsoro ya kama ta don ko zuwansu India tana cikin coma bata san yanda yake ba. Da za su Paris kuwa har amai sai da ta yi. Bata samu natsuwa ba har sai da jirgin ya daidaita a sama sosai.
"Mummy, zan yi fitsari!" Meema ta faɗi bayan ta kalli Laushi da ta jinginar da kai tana bacci kamar tana ɗakin uwarta. Duk ita ma wannan shine karo na uku da ta shiga jirgin, zuwansu India, Paris da kuma Dubai.
Ganin mahaifiyar bacci ta ke sosai, sai ta miƙe ta soma kallon mutanan da ke cikin jirgin har wata ma'aikaciyar jirgin ta hangota ta nufo inda take tare da faɗin,
"Beautiful baby, how may I help you?"
"I want to ease my self," Meema ta faɗi tana kallonta.
Hannunta ta kama ta kai ta har bayin da ke cikin jirgin sannan ta koma wajen zamanta. Bayan mintuna kaɗan Meema ta fito ta soma tafiya domin komawa wajen zamanta. Sai dai me, kamar ance ta juya sai ta hangi Uncle Habib zaune yana magana da wani mutum da ke gefensa............
#Meema #Laushi #Sabo da Kaza #Habib #Drug Trafficking #Brain aneurysm. #My Destiny #Matar Sayyadee
***
🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi! _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._