Page 25
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
"Uncle Habib!" Meema ta faɗi out of excitement tare da nufa wajen da sauri.
Kasancewar shine a farko sai wanda ya ke magana da shi a ciki ta wajen window sai ta saka hannu ta rufe masa idanu da hannu biyu tare da faɗin,
"Guess who's here!"
Sansaraƙwai ya yi domin zuciyarsa ƙaryatasa ya ke a kan wacce yake zargin ita ce duk da the voice is familiar to him. Wanda ke gefensa kuwa sai kallon Meema ya ke yi without blinking.
"Kaita, don Allah wacece? Ka santa?" Habib ya faɗi yana kai hannunsa kan hannun Meema da ta rufe idanunta.
Wanda ya kira da Kaita sai a lokacin kawas da idanunsa a kan Meema tare da yin murmushi. Can kuma ya ƙara ɗago kai ya kalleta da kyau ya sakar mata murmushi. Ita ma murmushin ta masa tare da kashe masa ido ɗaya. Hakan da ta yi sai ya ƙara bashi dariya har sautin na ɗan fitowa.
"Iskanci! Ina tambayanta kana min dariya ko," Habib ya faɗi yana mai kama hannun Meema da kyau tare da juyo da ita.
"It's me!" Ta faɗi tana sakin dariya har sai da side dimples ɗinta ya bayyana.
"Ke!" Ya faɗi with surprised sosai a fuskansa yana nuna ta da hannu.
Gyaɗa kai ta yi tare da faɗin, "I'm real. Ni ce fa." Ta faɗi tana tsungulin hannunsa har sai da ya furta "auuch!"
"Ke da waye? Ina mamanki? Me kuka je yi a Dubai?" Ya jero mata tambayoyin.
"Ok, shift for me sai in baka labarin in details," Meema ta faɗi tare da zama a gefen Habibu da mamakin ganin ta cikin jirgi bai sake shi ba.
"Uncle ina faɗa maka ko, wata rana da safe, I can remember ranar Wednesday ne. Mummy da kanta ta yi min wanka, ta shirya ni cikin uniform sanna ta min breakfast ta saka min indomie with chicken a lunchbox ɗina sannan ta raka ni har gate na shiga school bus. Ashe dai ba school Bus ɗin makarantarmu bace. Wani ne ya ke driving Bus ɗin wanda wasu students suke sanya da irin school uniform ɗin makarantarmu. Ni dai da na shiga na ga ba ƴan school ɗin mu bane, shine na yi wa Bus driver ɗin magana amma da ya juyo sai ya fesa min wani abu a fuska and daga nan ban ƙara sanin komai ba sai gani na na yi a cikin wani ɗakin mai yawan mutane and I started crying loudly saboda they all look like monsters to me. They weren't wearing shirt. They were walking half naked and their eyes are red in colour. I was Soo afraid! Some of them were holding big guns and long sharpen knives. Jikina yana ta rawa sosai ina ihu. Sai ga wani babban mai ƙaton ciki ya shigo ya daka min tsawa sai da na yi fitsari a tsaye. Ya daura hannu a bakinsa tare da ce min 'ssshh! Ida kin ƙara mana ihu a nan sai na yanka miki wuya da wannan wuƙar da ke hannuna.' da sauri na saka hannu na rufe bakin ina girgiza kai. Shi kuma sai ya koma ciki inda ya fito. Haka suka bar ni ba su ba ni abinci ba kuma ina jin yunwa. Can da rana, wani ya kuma zuwa ya ce na miƙe tsaye, sai na miƙe shine su ka ɗauke ni a hoto. Wata mata ta zo hannunta akwai allura ta tsira min a hannu sai da na yi ihu. Bayan ta gama min allurar sai na fara ganin jiri. Komai ya dawo ina kallonsa huɗu-huɗu. Sai na fara ganin ɗakin zai faɗo a kaina. Daga ban kuma sanin komai ba. Washa gari ma haka suka min bayan sun saka ni a cikin wani ƙaton baho da ke cike da ruwan da ƙanƙara a ciki. Na sha wahala sosai kuma ko ruwa ba su bani ba sai wani abu kamar magani da kullum su ke bani ina haɗiyewa. A daran ranar na yi ƙoƙarin guduwa shine suka ganni suka buga min wani abu a ƙeyana. Ban kuma sanin komai ba sai a India. Mummy ta ban labari wai kidnapping ɗina aka yi kuma kashe ni suka so yi shi ne wani uncle kamar ka mai kirki ya cece ni ya kawo ni India saboda a Nigeria jikina bai sauƙi. Kuma da na warke sai muka tafi Paris tare mu kai five days a can, daga nan mu ka taho Dubai mu kai 7days shine yau za mu koma gida."
Hankalinsa ne ya yi mugun tashi, ba shi kaɗai ba hatta abokinsa Kaita sai da ya tsorata da labarin Meema.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! An kama su, kidnappers ɗin?"
Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "A'a, mum ta ce ba a kama su ba. Amma an ce babu abunda zai ƙara faruwa in Sha Allah. Kuma da kanta za ta riƙa kai ni school ta dawo da ni idan lokacin tashi ya yi."
"Kaita, ko ma menene zai faru, I'm willing to marry that woman and protect this little girl. Wallahi kamar ƴata ta cikina na ke jinta."
"Is she not together with her dad?" Kaita ya faɗi yana kallon sa.
"Maganar banza! Yanzu fa na ke baka labarin komai. Ita ce fa yarinyar and mamanta ce Zeenah," Habib ya faɗi.
Da sauri Kaita ya kallesa tare da faɗin, "You must be joking my friend. Are you telling me za ka auri karuwa just to look after her daughter? Wato za ka manta ko kai ɗin ɗan wani gida ne ko? And ya za ka yi da Amatul Kareem?"
Tun da Kaita ya kira Laushi da karuwa Meema ta kafe shi da idanu don wayau gare ta sosai ta san Habibu a kan mamanta ya ke magana. Wani irin haushi da tsanarsa ya darsu a zuciyarta kuma ta kafe shi da idanu babu ko kyaftawa.
"Ka san dai ina da halin da zan iya riƙe mata goma idan ana yi ko? Kuma ni mijin mace huɗu ne. Idan kuma ƙanwarka ka ke tayawa kishi sai inji."
Ɗaga kafaɗa Kaita ya yi tare da faɗin, "It obvious ka fi son karuwa a kan ƴar uwarka. Don Amatul kareem ba ƴar uwata ba ce ni kaɗai, ta wani gefen ma ka fini kusa da ita."
"Don Allah ka daina kiranta da ƙaruwa! Ban baka labarin nan ba don ta muzanta a wajenka. Asali ma na baka labarin ne domin kai ɗan uwana kuma close friend ɗina sabida agaji da neman shawararka ce kawai. And she's very wise," ya ƙarisa maganar yana nuna masa Meema da gefen idanu.
Bai kuma cewa komai ba sai magazine ɗin da ya ɗauka da ke kan cinyarsa ya hau dubawa. Habib kuma kallon Meema ya yi wacce ta ƙure Kaita da idanu. A kunne ya raɗa mata,
"Koma wajen mummynki kar ta duba bata ganki ba. Jirginmu na landing a ƙasa zan taho na same ku. Kuma dama saboda ku zan shigo Lagos amma da direct Abuja zan wuce."
Gyaɗa kai ta yi tare da tashi bayan ta gallawa Kaita harara wanda tsaf ya ganta don rabin hankalinsa na kanta.
"Shiyasa ya ke da kyau ka zaɓi uwa ta gari domin bawa ƴaƴanka tarbiya. Dama ina karuwa ina tarbiyar da zata iya bawa ƴar da aka haifa a bariki!" Faɗin Kaita bayan ya dawo da idanunsa a kan magazine ɗin daga kallon Meeman.
"Enough, Jawaad Kaita don girman Allah! Zagin ya isa haka. Wannan ƙaddararta ce, kuma kai ba baka wuce Allah ya jarabceka ba."
"Ba zan ga wannan jarabtar ba a rayuwata ba in Sha Allah! Allah zai cigaba da kare ni daga aikata zina har ƙarshen rayuwata," Kaita ya faɗi ba tare da ya kallesa ba.
"Ni ma ina maka fatan haka. Mu da muka taɓa yi kuma, Allah ya yafe mana ya sa mun tuba kenan har abada," faɗin Habib Girei.
Shuru duk suka yi na kusan kimanin mintuna goma sha bakwai kamun Kaita ya ajiye magazine ɗin da ya ke dubawa ba wai don yana fahimtar abunda ke ciki ba. Fuskan Meema ne kawai ke masa gizo, sai dai ya san ko da wasa hasashen da ya ke yi ba zai taɓa yuwuwa ya zamto gaskiya ba, amma duk da hakan fuskan ya tsaya masa a rai.
"Amma kai kana da ƙarfin guiwar tunkarar Abie da maganar auren karuwa?" Kaita ya jefawa Habib tambayar.
Kallonsa ya yi tare da faɗin, "Tabbas zan iya tunkarar Abie amma tare da taimakonka. Duk da na san sai an kai ruwa rana ko da za su amince."
"Ta wani ɓangaren Abie mai sauƙi ne a kan wannan fitinanniyar tsohuwar, musamman idan ta samu zugan mama Luba," faɗin Kaita.
"Ka san mama Luba ta wajena ce, maybe idan na kashe ta da daɗin baki ta fahimta. Ko kuma in samu Baffa Modibbo ya shige min gaba. Ka san na gaban goshin fitinanniyar tsohuwar nan ne. Idan ya ce, Yes! To fa Yes ɗin nan ne, haka idan ya ce No! To ko ana ha maza ha mata babu abunda zai canza zance sai wani ikon Allah."
Hannu Kaita ya miƙa masa tare da faɗin, "Goodluck, friend," yana janye hannunsa ya rufe fuskansa da magazine ɗin ya lunshe idanu ba wai don bacci ya ke ba.
Meema kuwa, tana zama ka Laushi na farkawa daga baccin da ya kama ta. Kallon Meema ta yi kasancewar a idanunta ta zauna tare da faɗin, "Daga ina kike Sarkin yawo?"
"I went to ease my self." Meema ta faɗi tana ƙara gyara zamanta.
Mayar da idanu Laushi ta yi ta rufe daidai lokacin da Meema ta ce, "Mum, uncle Habib is here in the airplane."
Buɗe idanu Laushi ta yi sosai tare da kallonta ta ce, "Wani Uncle Habib ɗin?"
"Uncle Habib dai da ya saya min chololate a hotel. Wanda ya ce miki 'Duk wannan rayuwar da kike yi, ko kuma in ce da muke yi tunda dole in saka kai na tunda ni ma matan na ke bi, baza mu taɓa so mu ga ƴaƴanmu suna yi ba. Don Allah ki kiyaye hakan." Meema ta faɗi.
Baki sake Laushi ke kallon Meema ganin yanda ta zayyano zancen da ita ta ma manta da shi.
"Ke, wallahi kar in ƙara ji kin maimaita wannan maganar ko in fasa bakinki! Ina shi uncle ɗin kareren na ki ya ke?"
Juyawa Meema ta yi tare da pointing ɗin Habib ɗin da ke bayansu. Haɗa idanu su ka yi da Laushi ya kashe mata idanu sai ta yi saurin ɗauke idanunta daga kallansa ta dawo da kallonta ga Meema tare da faɗin,
"Ki zauna a nan kar ki sake ki tashi, kin ji ni?"
Gyada mai Meema ta yi tare da faɗin, "Yes, mummy."
"Good!" Faɗin Laushi tare da mayar da idanunsa jikin window tana kallon clouds.
Kaita bai cire magazine ɗin fuskansa ba har sai lokacin da ya ji ana sanarwar a saka belt sabida jirgi zai sauka. Bayan ya gama saka na shi sai idanunsa ya sauka a kan Meema da ke ƙoƙarin saka belt amma ta kasa, mahaifiyar kuma tun da ta saka nata ta runtse idanu. A hankali ya miƙe tsaye, Habib ya yi saurin kallonsa tare da faɗin,
"Ina kuma za ka je Kaita? Kana ji fa ana announcement a saka belt Jirgi zai sauka."
Ƙala bai ce masa ba, sai ma wucewa da ya yi zuwa inda Meema ta ke tare da duƙawa ya saka mata belt ɗin tare da jan kumatunta sannan ya juya. Da wani irin kallo Laushi da tun zuwansa ƙamshim turarensa ya daki hancinta ta buɗe idanunta ta sauke a kansa. Meema kuma yana juyawa ta cire belt ɗin saboda haushin kiran mummyta da karuwa da ya yi. A idanun Habib komai ya faru. Wani murmushi ya yi ganin Meema ta kwace belt ɗin daidai nan wata ma'aikaciyar jirgi ta iso wajen tare da kallon Meema ta ce,
"Fasten your seatbelt, beautiful girl!" Ta faɗi hakane tana mata murmushi.
Kiciniyar saka ta shiga yi, har Laushi ta kai hannunta Meema ta yi nasarar saka belt ɗin.
"Good girl!" Ma'aikaciyar jirgin ta faɗi tare da shafa kan Meema sannan ta wuce.
Duk abunda ya faru a idanun Jawaad Kaita. Hakane ya tabbatar masa da maganar Habib na cewar Meema na da wayau don ya hango haushi da tsanarsa a idanunta kuma hakan bai rasa nasaba da maganganun da ya yi ɗazu. Don ko zuwan da ta yi ta rufe idanun Habib ta yi masa murmushi tare da sake masa fuska. Samun kansa ya yi da rashin jin daɗin katoɓarar da ya yi.
_Wai shin ni kaɗai ce Baffa Modibbo ya min kama da mahaifin Marwanat matar Alhaji Nura?_
( Punishment ɗinku kenan gajeran typing. Ban san mai gobe za ta haifar ba. Wata ƙila one readmore zan koma yi 🤷)
#Jawaad Kaita #Habib Girei #Laushi #Meema #Baffa Modibbo #Mama Luba #Abie #Fitinanniyar tsohuwa #Marriage #Drug Trafficking #My Destiny #Matar Sayyadee
*** [2/21, 6:36 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi! _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._