My Destiny (Ƙaddarata)

Page 26

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Wani irin kaɗawa cikin Meema ya hau yi lokacin da jirgin zai sauka ƙasa. Ba ta saki wandon jikin mahaifiyarta da ta damƙa da ƙarfi ba har sai da jirgin ya tsaya cak sannan suka saki ajiyar zuciya daga Meema har Laushi.

"Mummy wallahi jirgi a kwai tsoro! Na ji tsoro sosai da za mu tashi, haka yanzu da za mu sauka," Meema ta faɗi tana waigawa bayanta kuma karaf suka haɗa idanu da Kaita. Wani irin ɗauke kanta ta yi tare da miƙewa ganin mutane na miƙewa suna fita.

Laushi hannu ta kai ta jawo jakar kayansu, lokacin tuni Meema ta yi gaba. Da sauri ta juya tana masa wani irin kallo sakamakon maganar da ya furta a kunnanta.

"Ita macen kirki kamar rufaffan sweet a cikin leda haka ta ke, duk namijin da ya san kansa mai kuma cikar ƙima da wadatacciyar tarbiya da asali da kuma nasaba bai taɓa ɗaukar buɗaɗɗan sweet wanda ƙuda da ƙwari masu cuta da marasa cuta suka gaba hawa kai suka shanye zaƙinsa. Don haka ki saka a cikin ƙwaƙwalwar kanki ta tunkiya, ɗan uwana ba zai taɓa ɗaukar datti kuma shara bola kamarki ba ya ajiye matsayin mata! You're not welcome in our family. I'm advising you to stay far away from my brother, you're not his type." Ya na gama faɗin haka ya kai hannu ya jawota nesa da jikinsa ƙadan tare da ɓalle botur ɗin shirt ɗinta da ke a buɗe wanda hakan ya bada damar ganin half shinny white brest ɗinta ta sama.

"And who the hell is your brother?" A fusace Laushi ta ce haka tana watsa masa harara saboda maganar ta soki zuciyarta.

"Ke ba ki isa ki raba ɗan uwana da iyayansa ba kamar yanda ke kika rabu da na ki iyayan saboda baki san darajarsu ba ki ki ka taho bariki har da riba ga ta can," ya ƙarisa maganar yana nuna Meema da baki wacce ta kusa ficewa daga cikin jirgin.

Bangajesa ta yi ta nufi wajen Meeman don gaba ɗaya hankalinta ya tafi wajen can ganin ta kusa ficewa daga jirgin. Duk da zuciyarta na ingiza ta a kan ta tsaya ta wanke sa soso da sabulu, amma baza ta iya ba saboda tafi ƙaunar ƴarta da hakan. Amma ta ƙudurta a ranta akwai next time.

Duk abunda ya faru Habib kansa na ƙasa bai san komai ba saboda yana ƙoƙarin fito da boxes ɗinsu. Ko da ya fito har Kaita ya kusa ficewa. Da sauri ya bi bayansa.

A can cikin reception suka haɗu da shi yana kallon Meema wacce ta ɗaga bottle wata tana sha, Laushi a gefenta tana gyara mata ribbon ɗin kanta da ya zamo.

"Tun ɗazu a jirgi na ke kallon ka sai satar kallon Meema ka ke yi, ta burge ka ko?" Faɗin Habib.

"Poor little girl!" Kaita ya faɗi yana hura iskan bakinsa tare da kai hannu ya amshi ƙaramin akwatin kayansa ya soma ja ba tare da ya amsa tambayar Habib ɗin ba.

"Ba za ka je ku gaisa ba? To ida baza ka tsaya ba, ka jira ni a waje yanzu zan taho."

"Tun da ga body guard ɗin ka ba. Meet me at baffa Modibbo's house idan ka gama shiriritar," ya faɗi tare da nufar enterance ɗin domin fita.

Habib wajen da su Laushi su ke ya nufa. Meema na hango sa ta washe baki tare da faɗin, "Mum, uncle Habib is coming!"

Juyawa Laushi ta yi tare da masa kallo ɗaya ta kawas da kai ta cigaba da gyarawa Meeman gashinta.

"Maman Meema!" Ya kira sunanta a hankali bayan ya iso wajen.

Bata ɗago ba, kuma bata amsa kiran ba. Baby hijjab ɗin da ke hannunta ta sakawa Meeman tare da kama hannunta sannan ta ja akwatin kayansu da ɗayan hannun na ta.

"Maman Meema, fushi kike da ni?" Ya faɗi bayan ya taho ya jera da su.

Cak ta tsaya tare da kallonsa ta ce, "Kai ne wanda ya faɗawa wancan banza ni budurwarka ce har ya samu damar faɗa min maganganun banza? Wallahi ya ci sa a hankalina na wajen Meema, da sai na faɗa masa maganar da har ya mutu ba zai manta ba. Bai san wacece Zeenah shi yasa!" Ta ƙarisa maganar da ƙwafa tare da kamma hannun Meema ta wuce fuuu.

Da mamaki Habibu ya ke kallonta yana tunani a zuciyarsa. Hannu ya kai ya taɓa goshinsa tare da faɗin, "Kaita, Why?" Sannan ya bi bayan Laushi da sauri da har sun fice daga reception ɗin.

"Maman Meema! Maman Meema!! Don girman Allah ki tsaya ki saurare ni. Haba maman Meema," faɗin Habibu yana bin su a baya.

Hannu Meema ta saka ta tsayar da taxi tare da buɗe murfin mota, turus ta tsaya ganin wanda ke zaune a bayan motar yana danna waya kamar bai san da inuwarta a wajen ba. Kuma shi ya umarci driver ɗin ya tsaya ganin Habibu ya fito. Dogon tsakin da ta ja ne ya saka shi ɗauke kai daga kallon screen ɗin wayar tare da watsa mata kallon da bata san lokacin da ta saki murfin motar ba.

"Get lost malama ƙarni da hamamin da ke busowa a jikinki na rashin wadatacciyar wankan janaba ya dame ni!" A hankali ya yi maganar ta yanda ita kaɗai ta ji mai ya ke faɗi.

Har sai da gabanta ya faɗi sannan ta kai hancinta jikinta cikin dabara domin gasganta abunda ya ce. Wasu hawayen baƙin ciki sirara ya zubo daga idanunta ta yi saurin kai hannu ta sharce tare da buɗe baki za ta yi magana amma sai ganin hannunsa ta yi ya janyo Meema cikin motar yana wani murmushi daidai ƙarisowar Habib wajen.

"Kaita! Dama baka wuce ba?" Ya faɗi yana mai turo kai ta window ɗin front seat.

"Na wuce tun ɗazu, kurwata ce a nan ɗin," ya faɗi tare da mayar da bakinsa daidai kunnan Meema da ke kiciniyar kwace hannunta daga gare sa domin fita daga motar.

"Shiga mu sauke ku a hanya sai mu wuce," Habibu ya faɗi yana kallonta.

Harara ta watsa masa tare da faɗin, "Ba zan shiga ba! Ko dole ne? Meema fito mu wuce!" Ta ƙarisa maganar tana kallon Meema.

"Baza ta fito ba! Idan baza ki shiga ba, ki wucewarki za ta biyo ki daga baya," Kaita ya faɗi maganar tare da shan mur kamar ba shi ya yi maganar ba.

"Kana hau..........." Saurin gimtse maganar ta yi tare da sunkuyar da kai gabanta na faɗuwa saboda wani irin kwarjini da fuskansa ya yi mata.

"My friend, get in kina ɓata mana lokaci!" Ya faɗi maganar kamar yana magana da ƴarsa.

Shi dai Habibu da kallo kawai ya ke binsu kuma har zuciya ya ji daɗin abunda ya yi don riƙe Meeman ne kawai zai saka ta ta shiga motar.

Kamar tsafi ta saki tsaki ƙasa-ƙasa tare da yiwa Habib kallon matsa min in shiga gidan gaba. Da sauri ya ja baya ita kuma ta shige gidan gaban shi kuma ya shige gidan baya inda Meema da Kaita suke ya zauna tare da rufo ƙofar.

"Ina za a sauke ku?" Habib ya faɗi amma ko juyowa Laushi bata yi bare ta bashi amsa.

Kaita kuwa ko bi ta kansu bai yi ba, sai ma magana da ya ke da Meema ƙasa-ƙasa tana bashi amsa. Shi kansa ya yi mamakin saurin sakewar da ta yi da shi duk da fushin da take yi da shi na zagin mahaifiyarta da ya yi, sai dai ya bar haka a matsayin gasgata ƙaryar da ya mata wajen kare kansa don ƙiri-ƙiri ta faɗa masa she hate him sabida ya zagi mum ɗinta.

"Mushin za ka kai mu!" Faɗin Kaita kamar ba shi ya yi maganar ba. Kuma hakan ya yiwa Laushi daɗi don bata so Habibu ya san inda ta ke da zama.

Sun ɗan yi tafiya sosai saboda akwai nisa daga airport zuwa Mushin ɗin.

"Wai dagaske gidan Baffa Modibbo za muje? Na ɗauka hotel za mu sauka gobe sai mu wuce Abuja." Habib ya faɗi.

"To sai ka sauke ai. Idan har zan hau jirgin daga Dubai zuwa Lagos bayan akwai daga can zuwa Abuja, ai kasan there's something very important da zan yi. Kuma ka san it been long da naga Baffa Modibbo. So I decided to flight all the way from Dubai to Lagos just to meet him. Idan ba za ka je, ba dole sai ka juya ka koma airport, na tabbata ba za a rasa jirgin da zai je Abuja yanzu ba," Kaita ya faɗi yana kallon Habib da ya juyo yana kallonsa.

"To ka je, Allah ya yafe maka!" Habib ya faɗi tare da mayar da kallonsa a kan titi.

"Ameen," Kaita ya faɗi yana kallon Meema da ke buga game ɗin snake a ƙaramar Nokia tochlight ɗinsa.

"Yauwa ka yi parking a wajen milk colour gate ɗin can, I'm dropping their." Kaita ya faɗi yana nuna wajen da hannu.

Parking driver ya yi, Kaita ya shafa kan Meema tare da faɗin, "Be a good girl, kin ji?"

Gyaɗa kai ta yi tare da miƙa masa wayar. Amsa ya yi tare da cire simcard ɗin wayar sannan ya buɗe hannunta ya saka mata wayar ya raɗa mata a kunne.

"Kiyi game da shi. Na bar miki a matsayin ban haƙurin haushina da kike ji."

Dariya ta yi side dimples ɗinta suka loɓa tare da faɗin, "Ai ban jin haushinka yanzu tunda ka bani haƙuri kuma ka ce ba da mum ka ke yi ba. Your apology is accepted, uncle........" Ta faɗi tana kallonsa alamar ya cika mata sunan.

Wannan karan ma a kunne ya raɗa mata, "Jawaad Huzaifa Kaita."

"Uncle Jawaad Huzaifa Kaita!" Ta maimaita sunan tana dariya.

Kumatunta ya ja sannan ya buɗe motar ya fita ba tare da ya kalli Habib ba bare Laushi da ke gaban mota. Boat ya buɗe ya ɗauki akwatinsa ya nufi gate tare da buɗewa ya shiga.

Habib shima fitowa ya yi tare da rankwafosa a window gaban mota sannan ya ce, "Don Allah maman Meema ki haƙuri. Anjima idan kun sauka zan kira Rukayyah sai mu yi magana ta wayarta. I'll come and see you later in the night, In Sha Allah! Allah ya huta gajiya," ya faɗi hakane tare da zagawa wajen driver ya ciro Nigerian currency ɗin da ke aljihunsa ya biya driver ɗin har da na Laushi sannan ya dawo ta window ɗin baya ya yi blowing kisses wa Meema tare da faɗin, "Will buy chocolate for you later, my daughter, bye."

Bye-bye ta masa ita ma. Driver ya tada mota bayan ya kalli Laushi tare da tambayarta inda suka nufa, ita kuma ta faɗa masa.

A daidai kofar gidan ya yi parking, bayan sun fito ya juya kan mota ya bar wajen.

Laushi ba ta faɗawa kowa yau za su dawo ba don surprice ta yi niyyar masu. Dutse ta ɗauka ta hau kwankwasa gidan don idan da hannu ne ba za su ji ba sai anjima ana bugu shiyasa ta yi amfani da dutsen. Jim kaɗan sai ga muryan Salma nice yana mita,

"Wanene kuma da sakaliyar la'asar ɗin nan? Haba! Yanzu haka kwashe-kwashen Katifa ne," ya ƙarisa maganar da tsaki.

Laushi gimtse dariyarta ta yi tare da matsawa baya kaɗan da ƙofar gidan daidai lokacin da ya buɗe ƙofar. Wani irin waro idanu ya yi tare da aje yatsarsa a ƙasa ya hau rawa da mazaunansa. Can kuma ya miƙe ya hau girgiza tare da faɗin,

"Ahayyye camassss! Jama'a don Allah ku tura ni ta baya in faɗa kan Katifa in dumuimuyi Laushi!" Fadin Salma nice.

"Sai dai uban Laushi," faɗin Laushi murmushi a fuskanta tana watsa masa harara.

Hannu ya kai ya kamo hannun Meema da ke ta kyalkyalewa da dariya tun sanda Salam ya buɗe ƙofar. Ɗaga ta sama ya yi yana jujjuyawa tare da faɗin,

"Tabbas akwai party a gidan nan yau. Wai kuwa Laushi kin san yau ne Meema ta cika shekaru goma cif a duniya? Kin haifi Meema biyar ga watan Satumba Alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da tara (05/09/1999)."

"Ban manta ba, tun a Dubai ta ke tuna min saura kwanaki kaza birthday ɗinta," Laushi ta faɗi.

"Ahh! Yau akwai cin uwar sabada. Yasin sai mun yi party," ya ƙarisa maganar tare da sauke Meema ya kama hannunta zuwa cikin gida.

"Ina Ladi? Ban ji motsin ta ba fa," faɗin Laushi bayan ta ajiye akwatin tsakar parlourn tare da zama a kan three seater.

"Kasuwa taje. Ni ma kuma zama bata ganni ba, na tafi haɗo kayan party. Daga can kuma gidan Hajja Lanti na nufa domin gayya. Ke akwai labari don Hajja ta zo nan mun ci uwar sabada da ita. Sai ihu da masifa take ta yi wai mun ci amanarta. Sai dai na dawo," ya faɗi tare da shigewa ɗakin da yake na shi a gidan ya canzo jallabiya tare da shafa man leɓe da turare ya kuma baɗa hoda a fuska kamar jinjirin jaki sannan ya gyara ɗaurin ɗankwalin da ya kima a kai kamar gwaggo shaɓu sannan ya ɗau kuɗi ya zuba a aljihunsa ya fito yana taunar cingam.

"Meema da ba dan gajiya ba da na ce ki taho mu tafi tare," Salmanu ɗan daudu ya faɗi.

Da saurin Laushi da gyangyaɗi ya soma ɗauka ta wattsake tare da faɗin, "Wai! A'a babu inda za ta. Har ka manta abunda ya faru kenan? To ai ko school ni zan kai ta in kuma dawo da abuna."

"Ban ga laihinki ba. Adana abarki. Ni na yi nan. Akwai abinci a kitchen idan kuna jin yunwa," yana gama faɗin haka ya fice yana rangwaɗa iwa mace.

"Ki shiga kitchen ki saka abinci idan kina jin yunwa," Laushi ta faɗi bayan ta miƙe tana hamma.

"Bana jin yunwa. Zan yi game a parlour."

Juyowa ta yi tare da faɗin, "Da me za ki game ɗin?"

Wayar da Kaita ya bata ta ɗaga tana nuna mata. A hankali ta ƙariso tare da karɓan wayar sannan ta ce, "Wa ya baki wannan wayar?"

"Wannan sabon uncle ɗin nan ne wanda muka haɗu da shi a jirgi kuma muka shiga mota ɗaya da shi. Tare suke da Uncle Habib, sunan shi......"

Katse ta Laushi ta yi tare da faɗin, "come on keep quiet! Uban wa ya ce ki karɓi abun hannunsa, shegiya mai kunnan ƙashi?"

Sosai Meema ta tsorata don ta mance when last maman ta yi mata tsawa haka da zagi.

"This should be the first and last time da stranger zai ba ki abu ki karɓa. Kin san sa ne don ubanki?"

Girgiza kai Meema ta yi tare da faɗin, "No, ma. We just met in the airplane."

"To don ubanki shine za ki amshi abun hannunsa? Idan kin ƙara za ki ga abunda zan miki, wawuya kawai. Kuma wayar fasa ta zan yi," tana gama faɗin haka ta shige cikin ɗakinta.

Kwalkwal Meema ta yi tana kallon bayanta har ta shige ciki. Kwanciya ta yi ruf da ciki ta hau kuka.

Salmanu ɗan daudu ba ƙaramin sayayya ya yi ba. Har da blouse ya sayawa Meema red colour mai kyau. Ya sayi cake da ballons da kuma gift. Daga nan gidan karuwai ya tafi ya yi gayyatar mutan gidan da ƴan uwansa ƴan daudu. Gab magrib suka shigo gidan har da Ladi wacce ba tafiyarsu ɗaya ba amma dawowarta kenan ita ma daga hotel kasancewar daga kasuwar ta yi saurayi suka wuce can.

"Ya naga ana ta shiga gidan, mai ya faru?" Ladi ta faɗi gabanta na faɗuwa.

"Na taɓa ki da alkhairi! Meema ce da uwarta Allah ya musu........."

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku na lalace!!" Ladi Katifa ta faɗi tare da ɗaura hannu a kai bayan ta katse masa magana.

"Ke! To Allah ya yafe maki kurakuranki. Mu dai kar ki kawo mana iskanci da tashin hankali a wannan rana ta farin ciki. Meema dai har jikokinta sai na gani In Sha Allah. Tana nan daram-dam-dam, maye sai dai ya ci kansa. Yanzu haka basday ɗinta za muyi. Suna ciki ita da uwarta Allah ya musu dawowa," Salmanu ɗan daudu ya faɗi yana fari da idanu.

Da gudu Ladi ta shige tana ihun kwala kiran Meema da Laushin. Meeman ce ta fito ta rungumeta don uwar tana ɗaka tana doko salloli biyun da ta rasa, wato azahar da la'asar ga magrib saura ƴan mintuna.

"Wayyo Allah ka rufa mana asiri kar ruwan sama ya mana fakap (fuckup). Allah kasa sai mun gaba zai sauko," faɗin kwalba uwar sharri har da ɗaga hannu sama saboda hadarin da ya soma haɗuwa.

Su suka yiwa tsakar gidan wajen shuke-shuken nan kwalliya kasancewar akwai wadatacciyar wutar lantarki a gidan sai wajen ya yi tarwai. Ƙaton desk suka aje a tsakiya tare da lulluɓe shi da wani yadi mai kyalkyali sannan suka ɗaura cake da shampen da fanta har da su viju milk.

Manya-manyan rediyo suka fito dashi su kai connecting sannan suka kunna waƙar P-squar. Laushi da idar da sallarta kenan ko addu'a ba tai ba ta cire hijjab ɗin ta cillar tare da hau rera waƙar tana rawa don _Do me_ yana daga cikin waƙoƙin P-squar da take so.

Zuwa ƙarfe bakwai kowa ya gama cakarewarsa da gayu har an ɗan yi yayyafi ya ɗauke sai gaba ɗaya suka fito daga ciki zuwa inda akai decorating suka hau taka rawa suna miming.

Meema ta yi kyau cikin jan blouse ɗinta da takalmi mai tsayi. Wajen yanka kai ma wannan karan Salma nice ya kawo baki ta yi kamar za ta saka masa ta sakawa Laushi a baki tana dariya. Bayan yanka kai aka hau rawa ana shaye-shayen wiwi, sigari da maganin tari. Ƴan daudu su Aunty Sadiya da aunty Munari an zage sai saɓar-saɓar ake a dole ga mata.

Wajen gaba ɗaya ya kacame da warin hayaƙi da kuma rawar banza kamar dai can gidan karuwan. Laushi kuwa ta yi ɗif da maganin tari da wiwi don har ta fita daga hayyacinta. Daga ita sai 3quater da wata riga da bata da maraba da vest. Kannan ya sha fixing sai layi take.

Gefe Meema ta koma tana kallonsu tana kuka kuma babu wanda ya kula da ita. Ta tsani ta ga mahaifiyarta tana cikin maye. Hannunta ta ji an damƙa sai ta yi saurin waigawa ta kalli wanda ya riƙe hannun na ta.

Hannun ya ɗaura mata a kan leɓe alamar ta yi shiru. Waro idanu ta yi a hankali ta furta, "You? How do you get in here?"

Bai bata amsa ba sai hannunta da ya ja zuwa gefen da babu haske sosai sannan ya ɗan ɗaga facing cap ɗinsa sabida ta gansa da kyau.

"Uncle Jawaad Huzaifa Kaita!" Ta ƙarisa faɗi tana ɗaura tafin hannunta a kan bakinta.

#Meema #Laushi #Jaawad Kaita #Habib Girei #Baffa Modibbo #Rashin tunani #Tarzoma #Tashin hankali #Girei vs Kaita #Matar Sayyadee

*** [2/23, 6:53 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi! _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._