My Destiny (Ƙaddarata)

Page 27

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Gyaɗa mata kai ya yi tare mai da idanunsa wajen da su Laushi suke na ƴan sakwanni sannan ya dawo da kallonsa zuwa ga Meema tare da faɗin, "Ki shiga ciki, kar ki ƙara fitowa wajen nan kin ji."

Rau-rau ta yi da idanu tare da faɗin, "Mummy ta yi shaye-shaye. Ba na so na tafi na barta sai dai idan za ka kai min ita ɗaƙinta."

Sosa kai ya yi yana kallon Meema, can kuma ya miƙe tare da faɗin, "Stay here, Kar ki je ko ina ki jira ni a nan."

Gyaɗa masa kai ta yi, shi kuma ya nufi filin rawar bayan ya janyo facing cap ɗinsa ta yanda ba mai iya ganin fuskansa.

Laushi babu abunda ta ke sai layi don a make ta ke sosai. Hannunta ta ji an damƙa da ƙarfi aka fizgota sannan aka soma janta.

"Kai! Wanene kai? Me yasa ka ke jan hannuna? Cika ni dalla can," cike da muryan maye ta ke faɗin haka tare da ƙoƙarin turjewa duk da babu ƙarfi a jikinta.

Ɗaga hannu ya yi zai wanke fuskanta da mari, sai kuma ya fasa ganin Meema na kallo wajen yana tsoron kar ya sauke yatsunsa akan fuskan mahaifiyarta tana kallo. Maimakon haka, sai ya kalli gefe da gefen kamun ya ɗagata cak ya ɗaura a kan kafaɗarsa sannan ya yafito Meema da hannu. Da sauri ta nufo wajen. Ita ta yi masa jagoranci har zuwa ɗakin Laushin. A tsakiyar gadon ya kwantar da ita yana sakin dogon tsaki ganin gaba ɗaya rabin jikinta a waje ya ke. Bargon da ke kan gadon ya jawo ya lulluɓa mata sannan ya juya ya kalli Meema da ke bayansa tare da faɗin,

"Ki zauna a nan kar ki kuma fita, kin ji?"

Gyaɗa masa kai ta yi tare da faɗin, "Thank you uncle Jawaad."

Murmushi ya mata sannan ya juya. Har ya kai ƙofa sai ya juyo tare da yafito ta ya mata magana a kunne sannan suka tafa ya fice yana murmushi.

Washa gari ƙarfe bakwai Laushi ta farka tana miƙa tare da hamma. Ganinta tsakiyar gado sai ta hau mamaki tana son tuna abunda ya faru a wajen birthday partyn Meema.

"Waye wannan?" Ta faɗi hakane tana shinshina jikinta don tun jiya da Jawaad ya shigo ɗakin ya dabaibaye da ƙamshinsa.

"Kai ba shi bane. Ba yanda za a yi ya kasance shi ɗinne. Bai san gidan nan ba. Ina ga kawai wasu ne a cikin kwashe-kwashen Salma nice mai irin ƙamshim nan." Ta faɗi tana mai bawa kanta kwarin guiwa tare da sauka a kan gadon ta fito.

Babu kowa a parlourn, sai dai kaca-kaca ya ke da tarkacen jiya na party. Kitchen ta shiga ta haɗa tea sannan ta dawo ɗauki ta rufe mug ɗin tare da shiga toilet ta wanko baki sannan ta fito ta hau shan tea ɗin amma rabin tunaninta ya tafi a kan ƙamshin turaran da taji.

_Daren Jiya_

Jawaad na fitowa daga gidan ya nufi ƙofar gate kai tsaye ya fice daga gidan ba tare da ya ƙara yiwa ƴan partyn kallo ɗaya ba. Tafiya ya ɗan yi a ƙafa zuwa bakin titi. Taxi ɗin na nan a fake a gefen titin. Buɗe gidan gaba ya yi ya shiga tare da kallo Fashola drivern da ya ɗauko a airport ɗazu, kuma dama shi ne ya bashi umarnin ya tabbatar ya sauke su Meema a gida sannan ya kira sa ya faɗa masa location ɗin bayan ya bashi Number wayarsa.

Tura gate ɗin gidan Baffa Modibbo ya yi tare da shiga ci. Sai da ya ɗan ɗauki second biyar kamun ya kwankwasa ƙofar ɗakin. Raihan ce ta taso ta buɗe tare da ja baya kaɗan ta ce, "Sannu da zuwa ya Jawaad."

Kai kawai ya gyaɗa mata tare da saka kai cikin parlourn. Duk suna zaune, Baffa Modibbo, Inna ƙarama, Umma, Aunty Zubaida da kuma Habib da ke danna laptop ko kallonsa bai yi ba.

"Ina ka shige, Jawaad? Tun ɗazu ɗan uwan naka ke ta neman ka kuci abinci. Kuma ya kikkira wayarka baka ɗagawa," Baffa Modibbo ta faɗi.

"Ko an samo min kishiya bayarabiya ne?" Inna ƙarama ta faɗi tana dariya.

Shi dai Jawaad bai ce ƙala ba sai murmushin da ya ke yi. Sai da ya zauna kusa da Inna ƙarama sannan ya kalli Baffa Modibbo tare da faɗin, "Djam hirri"

Baffa Modibbo ya bashi amsar a taƙaice, "Djam ni wallah" tare da cigaba da duba jaridar hannunsa bayan ya gyara gilashin fuskansa.

Kallon Aunty Zubaida ya yi tare da faɗin, "Su Hajiya Zuby yaushe a gari? Don ɗazu ban ji ɗuriyarki a gidan ba.

Wani irin ɗagowa Baffa Modibbo ya yi a fusace ya soma zazzaga bala'i cikin harshen fullanci. Baki sake Kaita ke kallon Baffa Modibbon. Kamar haɗin baki caraf sai Inna ƙarama ita ma ta amshe faɗan ta shiga zazzagawa Aunty Zubaidan.

"Wai auren wa aka kashe ne, Baffa?" Habib ne ya yi tambayar yana mai kashe laptop ɗin tare da ajiyewa a hannun kujera.

Nuna ta da hannu Baffa Modibbo ya yi tare da faɗin, "Wannan ƙatuwar babbar banzar ce ta zuga Marwanat ta soki mijinta da wuƙa a kan kishin banza da hofi. Allah ya taimaka wuƙar bai shiga cikinsa ba yana raye har yanzu. Ina faɗa maka ma ƙaramin tashin hankali suka saka mu ba, ni ba don Inna ƙarama da ta saka baki ba, wallahi babu abunda zai saka na sa hannuna a cikin lamarin da mutuncina ba. Dakyar mahaifin Nura ya janye ƙarar da aka shigar a kotu duba da yaran da ke tsakanin shi Nuran da Marwan, da yanzu zancan da nake maka Marwa na garƙame a prison. Marwanat fa ita ce har gidan karuwa don yin faɗa da karuwar miji ita da ƴan iskan ƙawayanta. Wallahi wannan abu ya min ciwo sosai!"

Da idanu Jawaad ke bin Baffa kamun ya mayar da dubansa ga aunty Zubaida tare da faɗin, "Ashe baki da hankali ban sani ba?"

"Baffa wallahi sai da na ce mata kar ta soke su, amma bata ji....." Ba tare da Zubaida ta ƙarisa maganar ba Baffa ya wulwulo jaridar hannunsa saitinta tare da faɗin,

"Tashi ki bar parlourn. Kuma wallahi na sake na kira Hamma Tukur ya faɗa min wani iskancin kika aikata a Yola shiyasa kika dawo min nan ko......" Bai ƙarisa maganar ba sai jijjiga kai da ya yi.

"Inna ina ita Marwan?" Jawaad ya faɗi yana kallon Inna ƙaramar.

Da baki ta yi masa nuni da wani ɗaki tare da faɗin, "Baffanta ya kulle ta a ciki ba shiga ba fita. Abinci ma shi da kansa ke buɗe ƙofar ya tura mata sannan ya fito. Kusan kimanin watanni uku kenan tana kulle a ciki."

Tsam Habib ya tashi don sun fi close da Baffa Modibbo tare da tsugunawa a gabansa ya ce, "Baffa don Allah ka ban dama na shiga ɗakin na yi magana da ita."

Girgiza kai Baffa ya yi tare da faɗin, "Babu abinda za ka ji daga gare ta sai takaici. Ka kyaleta kawai. Hakan shine daidai da ita. Saura wancen babbar banza. Ni kaɗai na san shirina a gare ta. Ƙaryar hauka take."

"Don girman Allah Baffa ka ban damar. Magana kawai zan yi da ita," Habib ya faɗi yana ƙara kwantar da murya.

Hannu Baffa ya saka a aljihu tare da wurgo masa key ɗin ɗakin a kan jikinsa. Da sauri ya ɗauka ya furta, "Miyetti Baffa," da murmushi a fuskansa sannan ya nufi corridor ɗin da zai sada sa da ɗakin da Marwanat take ciki.

Miƙewa Jawaad ya yi ya bi bayansa. Da gefen idanu Baffa Modibbo ya bisu da idanu har suka shige corridor ɗin.

"Malam menene ne na biyo bayana kuma? Ka san haushinka nake ji ko?" Faɗin Habibu yana hararar Jawaad.

"Akwai wuƙa a kitchen," Jawaad ya faɗi tare da kwace key ɗin hannun Habib ɗin ya shiga ƙoƙarin buɗe ɗakin da Marwanat ke ciki.

Murmushi Habib ya yi tare da gyara tsayuwa yana jiran ya buɗe ƙofar ya shiga. Sai dai me, Jawaad na shiga ya turo ƙofar ya rufe tare da murza key ta shi.

Waro idanu Habibu ya yi tare da faɗin, "wallahi Jawaad babban ɗan iska ne. Ni da tambayar abu shi da kwacewa har da turo ƙofa. Lallai!" Ya ƙarisa maganar yana knocking ƙofaf.

Harɗe hannu Jawaad ya yi yana kallon Marwanat da ta rakuɓe a lungun ƙarshe bangon ɗakin. Ta rame ta fita hayyacinta sannan ta koma kamar wasa tsohuwa kuma gaba ɗayanta bata wuce 26-27 ba.

"Yanzu ke abunda kika yi kin kyauta kenan? Kin ɓatawa mu Fulani record wallahi. Ɗiyar Fulani ba a santa da wannan haukan da rashin kamun kai ba. Da mutuncinki, iliminki da hankalinki ki taka ƙafa ki tafi gidan karuwai don faɗa da budurwar miji!"

Wani irin kuka Marwanat ta fashe da shi tare da faɗin, "Yaya Jawaad shin yanzu babu mai fahimtata ne? Babu wanda zai fahimci yanda nake ji a cikin zuciyata! Wallahi ji nake kamar in kashe kaina da kaina. Why I'm a even alive?" Ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka.

Takawa ya yi gabanta tare da faɗin, "Akwai hanyoyin kashe kai da dama a cikin ɗakin nan ai. Idan kuma ke ba ki gansu ba Ni bari na nuna maki su." Ya yi taku baya kaɗan tare da buɗe ƙofar bayin da ke ɗakin ya shiga ya ɗauko Jik ya ajiye a gabanta. Sannan ya koma kan madubin da babu komai a wajen sai insectiside (maganin kwari) nan ma ya ajiye mata tare da duƙawa gabanta ya ce,

"Duk wannan kina buɗewa kika tuttulawa cikinki, ina mai tabbatar miki za ki samu abinda kike so. Idan duk ba suyi miki ba, ga fan nan sai ki jawo stool ɗin gaban madubin can ki ɗaure fan ɗin da kyau sai ki rataya a wuyarki ki ture stool ɗin, za ki ga aiki da cikawa. Idan kuma shima wannan ɗin bai maki ba, zan fita sai in taimaka miki da wuƙa tunda kin fi kwarewa ta wannan fannin."

"Haba yaya Jawaad, Ya kake ƙarawa ciwon gishiri! Kai da nake tunanin za ka tausaya min. Ko da yake da dai yaya Habibu ne shi zai fahimce ni." Ta faɗi tana shassheƙar kuka.

Taɓe baki ya yi tare miƙewa ya maida hannunsa baya tare da juya mata baya ya soma magana,

"Kin san meyasa ba zan taɓa jin tausayinki ba?" Ba tare da jiran jin amsarta ba ya cigaba, "Saboda ke ɗin wawuya ce mara tunani! Ina sane da rashin mutuncin da kike aikatawa Nura mijinki. Bawan Allahn nan ya nuna miki shi ba zai iya rayuwa ta mace ɗaya ba. Ya zaunar da ke ya miki nasiha a kan ba wai kin gaza bane shiyasa zai ƙara aure ba, shi ya kasance irin mazan nan ne da basa iya rayuwa da mace ɗaya. Maimakon ki girmama buƙatunsa, a'a sai ki kai watsi da shi bayan bai rage ki da komai ba, asali ma yana matuƙar sonki wanda hakan ya saka ki kai amfani da rauninsa wajen azabar dashi. Babu irin ɗibar albarkar da baki wa Nura ba wanda ƙalilan ne a cikin maza masu iya shanyewa. Kin rushe masa aure ya fi biyar sannan kin ƙi bashi cikakken farin ciki a gida, kuma still a daƙiƙin tunaninki sai yaƙi neman matan banza ko? Duk abunda Nura ya aikata da saka hannunki, kuma yanzu wa gari ya waya? Ke! Gashi kin kasance a cikin gidan ubanki a ƙuntace, babu auren Nura a kanki kuma ƴaƴanki sun miki nisan da ganinsu ya gagare ki. Kin ga zuciya da kike ganinta, wallahi ƙaramar tsoka ce mai kai mutum ga halaka idan har ka kasa sarrafata ka bari ita ke sarrafa ka. Ina amfanin yunƙurin kisan kai? Yanzu dai kalle ki, kina ganin akwai namijin da zai amince ya aure ki bayan ya samu labarin ta'addancin ki? Tur! Da halinki, Marwanat!"

Kuka sosai take yi kamar za ta shiɗe, duk wani ɓangare na zuciyarsa yana tausayinta, amma bai nuna mata hakan ba don so yake ta fahimci girman kuskuren da ta aikata. Hakane ma ya sa yaƙi bari Habibu Sarkin tausayi shigowa don zai ɓata masa aikinsa.

"Wallahi, tallahi na yi nadamar yunƙurin kisan da na yi. Kuma wallahi ba shi na je kashewa ba. Tsautsayin ne ya faɗa kansa," Marwa ta faɗi.

Juyowa ya yi tare da kallonta sannan ya ce, "Ke nan da ita karuwar kika samu baza ki yi wannan nadamar ba ko?"

Gyaɗa kai ta yi tare da faɗin, "Wallahi ko yau na yi arba da tsinanniyar nan da ta yi sanadin kashe min aurena, sai dai a ɗau gawar ɗaya daga cikinmu, ko ni ko ita!" Ta faɗi maganar daga cikin zuciyarta.

Jinjina kai Jawaad ya yi tare da faɗin, "Da sauranki, tabbas!" Yana gama faɗin haka ya juya ya nufi ƙofa tare da murza key ya fita. Buɗe hannun Habib da ke ƙofar ɗakin ya yi tare da saka masa key ɗin sannan ya nufi parlourn.

Har zai wuce ɗakin da za su kwana sai ya dawo daidai kujeran da Habibu ya tashi a kai ganin wayar Habib ɗin a kai. Hannu ya kai ya ɗauka tare da shiga contact ɗinsa ya shiga scrolling numbers. Yana arba da Number ɗin da yaga an yi saving da Maman Meema da emojin heart ya yi deleting. Har zai ajiye wayar sai ya tuno da maganar da Habibu ya yi ɗazu na zai kira ta da wayar Rukayyah. Number ɗin Rukayyah ya yi searching ya shiga ya yi editing ya saka wata tsohuwar layinsa da ya daina aiki ya yi saving. Sannan ya yi creating wani Number da is not active ya yi saving da Maman Meema da emojin heart kamar yanda Habib ɗin ya yi saving da farko sannan ya ajiye wayar ya wuce ɗaki.

Habib ya jima a ɗakin Marwanat suna magana. Duk da yaji haushinta a wasu abubuwa da dama kuma ya mata faɗa, amma ya tausaya mata kuma kwantar mata hankali bayan ya bata shawarar ta cigaba da addu'a tana sallar dare, in Sha Allah idan da sauran zama tsakaninta da Nura tunda tana sonki, sai a iya sasantawa tunda shima yana da nashi laifin a wasu wajajan. Sannan ya ƙara da faɗin zai roƙi Baffa Modibbo ya sassauta mata.

Yana fitowa ya kai wa Baffa Modibbo key ɗin sannan ya nufi wajan wayarsa ya ɗauka ya fice daga parlourn kasancewar kowa ya bar parlourn har Baffa. Sai da ya fita gate sannan ya lalubo Number ɗin Maman Meema ya kira. Jin wayar ta ƙi shiga sai ya mayar da akalar kiran zuwa Number ɗin Katifa.

```The Number you're trying to call does not exist, please check the number and try again.```

Wani murmushin kun raina min wayau ya yi tare da furta, "You must be joking, MTN!" Tare da sake kiran layin.

Wannan karan mamaki ne ya kama shi sosai jin abunda suka sake maimaitawa.

"Ke! Tataya? Ko sake Number ta yi ne?" Ya watsowa kansa tambayoyin da bai da amsar su.

Bai haƙura ba ya dunga kiran layin kamar zararre but still the same abunda MTN suke ce masa kenan. Sai ya koma idan ya kira layin Laushi, sai ya mayar da kiran zuwa layin Ladi Katifa har sha ɗayan dare amma babu labari. Haka nan ya ja sakakken guiwarsa ya koma ciki da niyyar gobe da sassafe ya sake kira, idan bai shiga ba, sai ya bazama nema da kansa.

Daren ranar barcinsa ragagge ne don duk juyi sai ya yi tsaki. Idan kuma ya farka sai ya jawo wayarsa ya kuma danna kiran duka layukan biyu amma still bai shiga. Jawaad na jin duk wani motsinsa amma ya yi kamar bai san da ruwansa a ɗakin ba.

Sosai daren ya yiwa Habib nisa don ƙosawa ya yi gari ya waye, sai dai bai san Jawaad ɗin ya shuka masa tsiya ba tun jiya. Don tuni ya yankar masu tikitin jirgi, karfe takwas jirginsu zai tashi daga Lagos zuwa Abuja. Kuma ya sanar da Baffa Modibbo bayan ya shirya masa ƙaryan Baffa Chubaɗo ya ce goma ta musu a Abuja saboda meeting ɗin da za ayi da na family a gidan Babiyo. Hakan ya sa Baffa Modibbo ya ce da kansa zai kai su airport ɗin gobe.

Washa gari kuwa, tun bakwai da ƴan mintuna Baffa ya azalzala masu da su fito akwai nisa daga nan inda suke zuwa airport. Mamaki ne ya kama Habibu sosai ya shiga tambayar Jawaad mai za suyi da sassafen nan a airport.

"Mai zai hana ka fita ka tambaye sa da kanka!" Jawaad ɗin ya faɗi yana gyara zaman belt ɗin wandonsa.

"Na roƙeƙa da girman Allah ka faɗa min mana Jawaad," ya faɗi da damuwa a fuskansa ganin Jawaad ɗin na gyara akwatinsa.

"To, Baffa Chubaɗo ne ya yi kiran gaggawa a kan goma ta yi mana a Abuja saboda meeting ɗin da za ayi a gidan Babiyo. Hakan ya saka zai aje mu a airport."

Ragwajab Habib ya zauna a bakin gadon tare da riƙe kai don har ga Allah ya so zuwa ganin Laushi yau ɗin nan domin ya shaida mata sirrin zuciyarsa kamun ya tafi yaƙin amincewa daga familynsa. Kuma yasan cewa ƙaryansa yaƙi amsa kiran Babiyo.

"Wai jiran uban mi kuke haka? Tare za mu tafi fa. Don yanzun nan Giɗaɗo ya kira ni a waya ya shaida min taron kuma ni ma ana son gani na a can ɗin." Faɗin Baffa Modibbo.

Da sauri Habib ya miƙe, don Jawaad har ya kai ƙofa. Akwatinsa ya ja suka nufi ɗakin Inna ƙarama wacce da ita za ai tafiyar. Umma da su Marwanat kawai za a bari a gidan.

"Ai mu tafi kawai ma gaisa a cikin mota, jirgi bai jira sai dai a jira shi," faɗin Inna ƙarama tare da bin bayansu.

Ɓangaren Laushi kuwa, wannan ƙamshi ya tsaya mata a rai sosai. Duk mintuna sai ta ji gabanta na faɗuwa. Hakan ya saka gaba ɗaya ta kasance suku-suku. Meema kuwa ko da wasa bata faɗa mata zuwan Jawaad Huzaifa Kaita gidan ba don ya gargadeta da hakan. A daren ranar Sabo da Kaza ya mata waya tare da shaida mata anjima da daddare za a kawo kaya ta sallami kowa a gidan ya kasance daga ita sai ƴarta. Hakan kuwa aka yi. Ladi Katifa da Salma nice suka tafi gidan Hajja Lanti. Salma ya kwana a ɗakin Sadiya ɗan daudu, Katifa kuwa a daren customer ya zo ta tafi kwana gida.

Da daddare wasu maza kusan su goma gaba ɗaya fuskokinsu a rufe suka shigo gidan tare da manya-manyan makawai, Cocaines, tabar wiwi da kuma kwayoyi. Sai da suka jera komai a wannan ɗakin da tun tarewarsu a rufe yake. A gaban Laushi su kai komai sannan suka jawo ɗakin suka rufe.

*_Abuja_* Estate ne guda mai suna *_Arɗo Barkindo Family_*. A cikin wannan estate wanda ya kasance unguwa guda, akwai gidaje sama da ɗari biyu. Kowani layi yana da sunansa. Akwai irinsu; Giɗaɗo Street, Ɓaleri Street, Gaabɗo Street, Barkinɗo Street, Modibbo street, Belɗo Street da sauran su. Ko wani sunan layi, mai sunanne da iyalansa a cikin gida. Kuma gaba ɗaya ƴan uwan juna ne don ƴaƴan mutum ɗaya ne wato Arɗo Barkindo. Ko wani gida a estate ɗin irin tsarin gininsa ɗaya ya ke da na ɗan uwansa. Suna da wani irin ƙabilanci da nuna soyayya ga na su kawai. Su ɗin idanu ne wanda basu san baƙo (ma'ana bare) a cikinsu. Fararene sol, asalin Fulanin Yola.

Wani ƙatoton gida wanda shi kaɗai ya fita daban da sauran gidajan cikin estate ɗin saboda ya fi kowani gida tsaruwa a ciki. Gidan ne tamkar gidan wani hamshaƙin sarki ko kuma bafullace.

Motoci ne a harabar gidan nan wanda yawansu ya fi gaban a ƙirga su kowanne na wane wannan.

A cikin wani mahaukacin parlourn mai matuƙar girma kamar fada, mutane da za su kai hamsin a ciki kuma duk maza kuma dattijawa. Sai wani tsohon farin sol ɗin bafullace wanda zai iya kaiwa tamanin da ɗoriya zaune a kan wata kujera irin ta sarauta hannunsa riƙe da wata kyakkyawar farar sanda a hannunsa. Gefensa a kan irin kujerar da yake zaune, wata farar kyakkyawar farar tsohuwar bafulatana ce mai isa da taƙama itama.

Tsohon nan yana da masifar kwarjini domin da wuya ka iya kallon cikin idanunsa ka masa magana. Wasu ma cewa suke idan ko da tsautsayi suka kalli idanunsa gani suke ya koma kamar idanun zaki.

Kallo ɗaya za kaiwa yanayin zamansa ka fahimci yana cikin matsanaicin fushi. Don shi ba ka isa ka kalli fuskansa ka faɗi yanda yake ba. Sai da ka fahimta a yanayin zama ko kuma gyaran muryansa.

Arɗo Barkindo kenan wanda wasu daga jikin ƴaƴansa da jikokinsa suke kira Mamiyo wasu kuma su ce masa Babiyo.

Kowa daga cikin ɗakin nan gabansa bugun uku-uku ya ke suna fatan Allah yasa ba ɗaya daga cikin ƴaƴansu ko jikokinsa bane ya tafka wani babban laifin da yasa a kai masu wannan kiran gaggawan.

Da wani irin ƙasaita da isa Babiyo ya ɗago ya zubawa ƴaƴansa da wasu daga cikin jikokinsa idanu tare da faɗin, "A buɗe taro da addu'a!"

Nan da nan aka buɗe taron da addu'a mai ɗan tsayi saboda irin addu'ar da Babiyon ke buƙata kenan.

Gyaran murya ya yi wanda ya saka cikkuna mutanen da ke zaune a wajan da yawa ya kaɗa.

"Modibbo!" Babiyo yai kiran sunan Baffa Modibbon da tun da muryan Babiyo ya sauka a kunnansa ya ƙada har ji ya ke kamar zai zagaya.

"Na'am Babiyo!" Ya amsa har da rusunar da kai jikinsa na rawa.

"Zaman barikin ne ya saka ka kasa baiwa ƴarka cikakkiyar tarbiya har ta iya taka ƙafa ta tafi gidan karuwa? Sannan kuma ta nai mi kashe mijinta da wuƙa ta hanyar caka masa a ciki ko?"

Wani irin zufa ce ta shiga kwaranyowa daga goshin Baffa Modibbo, gashi babu damar musu bare kare kai. Idan kuma ka yi shuru babu amsa haka yana nufin tsantsan nuna rashin biyayya ne ga shi Babiyon.

"Ai min aikin gafara, Babiyo!" Ya faɗi still kansa na ƙasa.

Kaɗa ƙafa Babiyo ya yi tare da rausayar da kai ya mayar da kallonsa izuwa kan Baffa Giɗaɗo ya ce, "Mai Habibu ya ke jira har yanzu ba a tsayar da ranar bikinsu da Amatul kareem ba? Ko kuma yawon bin karuwa ya fiye masa auren ne?"

Lokaci guda zuciyar Habib da ke kusa da Jawaad ya yi wani irin tsinkewa ya faɗi. Duk da yasan kakan nasa da bin ƙwaƙƙwafi da bincike, bai taɓa tunanin zai binciko har ya gano yana bin mata ba. Don bai taɓa yarda ya nai mi mace a garin Abuja ba.

Baffa Giɗaɗo kuwa jin abunda Babiyo ya faɗi game da halin da Habibu ɗin ya jefa kansa, sai da ɗan ƙaramin fitsari ya kufce masa don ya san dole Babiyo ya yi hukunci a kan haka kuma hakan na nufin shi ma ta shafe sa.

"Babiyo duk abunda ka ce shine daidai. Ai hukuncinka kawai muke jira na yanke ranar auren tsakaninsa da Amatul kareem ɗin. Sannan don Allah ina neman alfarmar ai min afuwa kar a hukuntani akan mummunar ta'addancin da Habibu ya ke aikawa, sam babu hannuna a ciki."

Wani ajiyar zuciya ƴan ɗakin suka aje don sun san Baffa Giɗaɗo ya taro match babu kwallon bugawa saboda sam Babiyo bai lamuntar ya yi magana ka nemi kare kanka don ya fi ka sanin kana da hannu a laifi ko babu.

Ajiyar zuciyar da ƴan uwansa su kai ne ya dawo dashi hayyacinsa a kan taɓargazar da ya yi.

"Kai kuma Bobbo, ba ka isa da ɗanka Jawaad bane da har yanzu ka zuba masa idanu ya kasa fidda matar aure?" Babiyo ya faɗi zuciyarsa na tafarsa da abunda Habibu ya ke aikawa na ɓatawa suna gidansa da kuma abunda mahaifin Habibun ya aikata yanzu na kare kansa da ya yi. Don a wajan Babiyo ka kare kanka a gabansa daidai ya ke da ka kira sa mara adalci.

"In Sha Allah yau ɗin nan zai fidda matar aure sai a haɗa da bikin Habib ɗin duka." Faɗin mahaifin Jawaad.

"Hakan na da kyau!" Babiyo ya faɗi cikin ƙasaita sannan ya mayar da idanunsa a kan mahaifin Habibu wato Baffa Giɗaɗo ya ce,

"Ka zaɓi ɗaya; ko ka bar cikin zuri'a ta kai da iyalanka, ko kuma ɗanka ya fita daga lamarin karuwar da yake da burin aure wacce ta haifi shegiya a garin Lagos, wacce ta kashe mahaifinta kuma ta ke shaye-shaye, ya yi aure da Amatul kareem su bar ƙasar nan kar su ƙara waiwaya sai idan ni ne na buƙaci hakan, ko kuma na cire ka daga sahun ƴaƴana."

Sai a wannan lokaci tsohuwar nan ta buɗe baki tare da faɗin, "Kamar yanda na yankewa Ɓaleri hukunci shekaru tara baya, haka a yau zan yankewa Giɗaɗo kuma ina son kowa ya shaida hakan."

A ruɗe kowa ya ɗago yana kallonta. Da sauri Habib ya faɗi a kan ƙafafuwanta ya riƙe tare da fashewa da kuka ya soma faɗin,

"Ku min aikin gafara. Kar ku yankewa mahaifana hukunci bisa laifina. Na yi alƙawari wallahi, tallahi daga yau a yanzu haka na fita daga harkan Zeenah har abada. Babu ni babu ita. Kuma na amince ko gobe a ɗaura aurena zan bar ƙasar.......

(Na dage na yi readmore da yawa, saura ku ban kunya.)

#Arɗo Barkindo Family #Habib #Jawaad Kaita #Baffa Giɗaɗo #Baffa Modibbo #Babiyo #Laushi #Heart break #Emotion #My Destiny #Matar Sayyadee *** [2/24, 6:56 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`