Page 28
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
Wani murmushin ƙasaita Babiyo ya yi tare da kallon Habib ɗin da ke riƙe da ƙafar Mamiyo yana hawaye. Ya jima yana kallonsa kamun ya mayar da idanunsa a kan Mamiyo ya gyaɗa mata kai. Ita kuma ta saki ajiyar zuciyar ƙasaita tare da faɗin,
"Ka tashi ka ceci iyayanka daga faɗawa fushina. Sai dai duk da haka sai an yanke masa hukuncin ƙasa sarrafa ɗansa. Kaf zuri'ar gidan babu mazinaci sai kai, don haka your parents will pay for what you did!"
Baffa Giɗaɗo babu abunda ya ke sai share zufan da ke tsattsafowa daga goshinsa duk da AC da ke ɗakin har huɗu.
"Ba ni son sake ganin fuskanka ko sauraran muryanka Giɗaɗo a cikin wannan sashen har na tsawon shekara ɗaya. Sannan na baka suspension ɗin wata shidda, kar inji labari ko motarka ta gitta ta `Arɗo Barkindo Global Company Limited`."
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Shine abunda Baffa Giɗaɗo ya dunga maimaitawa cikin zuciya kamun ya zube gaban Babiyo ya ce,
"Godiya na ke da wannan hukuncin, Babiyo. Haƙiƙa kai adalin uba ne. Nagode da wannan sassauci da rangwamen da aka min wajen yanke min hukunci. Allah ya ƙara girma, lafiya da tsawon rai."
Gaba ɗaya ɗakin babu wanda bai ji tausayinsa ba sai dai babu wanda ya isa ya nuna hakan idan yana son tsira da nashi aikin da kuma kasancewa a cikin Arɗo Barkinɗo Family.
Ba tare da Babiyo ya kalli Baffa Giɗaɗo ba ya yi gyaran murya wanda hakan ke nufin ya tashi ya koma mazauninsa.
Cikin saurin Baffa Giɗaɗo ya miƙe ya koma ya zauna zuciyarsa a cunkushe.
"Kai kuma Modibbo, saboda ka raina ni, ba ka ganin mutunci da girmana kuma bariki ta canza ka shiyasa da ƴaƴanka su ka aikata ɓanna sai ka nemi binnewa a cikinka har ka iya tura ita Zubaida da ta kasa zaman aure Yola wajen Tukur saboda ni ban raye, ko kuma ba ni da wajen zaman da zan iya ajiye ta. Sannan shi Nuran ya saki Marwanat, amma ka kasa zuwa nan ka sanar dani saboda ka isa ka tumbatsa. Ka taka matsayin da kake iya yanke hukunci a gidanka ba tare da sani na ba. To hatta ƙarar da iyayan shi Nuran suka shigar na san da shi. Kuma kar ka yi tunanin saboda kai suka janye ƙarar nan. Ni ne nan na aikawa shi uban Nuran da ya zo ya same ni. Kuma ya zo har gida ya nemi yafiyata na ɓata sunan zuri'a ta da ya ke shirin yi a kotu. Da idanunsa ya yi kuka a nan a duƙe gabana sannan ya ba ni tabbacin Nura zai mayar da matar ɗakinta amma na dakatar da shi daka yin haka. Kuma dama tun farko na ba su auren Marwanat ne saboda su ɗin tsatson Fulani ne, amma idan ba haka ba, ko mutuwa za ta yi saboda sonsa baza ta aure shi ba."
Faɗuwa a gaban Babiyo Baffa Modibbo ya yi tare da faɗin, "Kai min aikin gafara, Babiyo. Wallahi ban aikata komai domin nuna isa ko don in ɓata ranka ba. Asali ma na yi duk saboda gudun ɓacin ranka wallahi. Don girman Allah da darajar tsoffi kai min aikin gafara. Hakan ba za ta sake faruwa ba Babiyo," har da ƴar kwallarsa ya ke wannan maganar.
"Ka tabbatar ka turo Marwanat da Zubaida nan idan ka koma Lagos!" Faɗin Babiyo a dake.
Wani sanyin rahama ne ya ziyarci Baffa Modibbo saboda hakan da Babiyo ya ce yana nufin ya amshi ban haƙurinsa, kuma hakan bai rasa nasaba da haɗa shi da Allah da kuma iyayansa da ke kwance a ƙasa da yake matuƙar so da girmamawa a duniya da ya yi.
Kallon mahaifin Jawaad Babiyo ya yi tare da faɗin, "Bobbo, ka faɗa ɗanka ya tafi gidan Macchiɗo ya duba matar aure, In Sha Allah wata mai kamawa za a haɗa ɗaurinsa da na Habib. Sannan ka faɗa masa zai tafi course na shekaru biyu a Denmark, kuma tare zai tafi da matarsa don haka ya tabbata ya tafi inda aka tura sa duba matar don tare da matarsa zai bar ƙasar. Shi kuma Habib Sweden zai koma da zama gaba ɗaya har sai na neme sa tukun zai dawo Nigeria. Na gama magana, a rufe mana taro da addu'a!" Yana kammala faɗin haka ya rufe idanu kamar mai bacci.
Bayan kammala dogon addu'ar, ɗaya bayan ɗaya suka shiga ɗukawa a gabansa tare da taɓa samar ƙafarsa, shi kuma yana shafa kawunansu tare da faɗin, "Allah ya muku albarka!"
Baffa Giɗaɗo ne farkon shiga motarsa ya fice daga gidan ba tare da ya tsaya tattaunawa da sauran ƴan uwansa ba kamar yanda suka saba duk suka fito daga wajen Babiyo. Kai tsaye motarsa ya shige ya figeta tare da nufa hanyar Giɗaɗo street zuciyarsa na masa zafi akan abunda Habibu ya aikata da ya zawo masa fuskantar ɗanyan hukunci daga wajen Babiyo.
Mai gadi da sauri ya taso ya wangale gate saboda irin mahaukacin horn ɗin Baffa Giɗaɗo ya dunga dannawa kamar zai cire masa kunne. Ko daidaita parking bai ba ya fito daga cikin motar yana tafiya dif-dif kamar wanda zai huce takaicinsa a kan ƙasan.
Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi tare da shiga ciki babu ko sallama. Gaba ɗaya ƴaƴansa da matarsa Halima suna zaune a parlour suna jiran dawowarsa don jin labarin meeting ɗin gaggawan da Babiyon ya kira tare da fatan Allah ya sa ba wata matsala bace ta faru daga cikin gidansu. Ba su kaɗai ba duk wasu iyalan ƴaƴan Babiyo haka suke fama da zullumi duk lokacin da Babiyo ya kira meeting.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Mama Halima ta faɗi ganin yanayin mijinta wanda hakan na nufin an samu matsala daga gare su.
"Mai ke faruwa? Yaran nan sun yi wani abun ko?"
Kyawawan fararan ƴan matan da ke ɗakin duk suka miƙe tsaye gabansu na faɗuwa suna fatan Allah ya sa ba Babiyo ya laƙa masu wani laifin ba. Don su irin soyayyar nan da wasa kaka ba sa yi da Babiyon, wasun su ma haushinsa suke ji saboda hana su rawar gaban hantsin da ya ke yi saboda al'adarsa da ɗabi'unsa. Da sun ɗan kuskure sun yi wani abu zai fasa taƙama da isa yana fankama tare yanke masu ɗanyan hukunci a nashi faɗin wai sun yi ƙoƙarin ɓata masa suna.
"Habib ya kashe ni, Halima! Habib ya tona min asiri da ɓata min suna a cikin estate ɗin nan. Ni Habibu zai wulaƙanta? Ni? Hmm!" Ya ƙarisa maganar yana safa da marwa tare dunƙule hannunsa yana naushin ɗayan.
"Mai Habibun ya aikata?" Faɗin mama Halima wacce mugun tashin hankali ya gama bayyana a fuskansa, don jikinta har rawa ya ɗauka.
"Wai Habib ke neman matan banza a waje! Mai nawa Habibu a rayuwa da ya min wannan abu? A ce a cikin zuri'a ta za a samu wannan ɗanyan aikin! To gashi nan ya ja min fushin Babiyo. Babiyo ya ce kar na sake zuwa inda ya ke har na tsawon shekara guda kuma ko muryata bai don ji, sannan ya dakatar dani da zuwa _Arɗo Barkinɗo Global Company Limited_ har na tsawon wata shidda!"
Luuuu Mama Halima ta yi za ta faɗi ƙasa, Baffa Giɗaɗo ya yi saurin taro ta tare da zaunar da ita a kan kujera. Ƴan matan kuwa kuka kawai suke jin abunda Habibu ya aikata kuma hukunci ya ƙare a kan mahaifinsu.
Kuka Mama Halima ta saka wiwi tana faɗin, "Anya kuwa investigator Babiyo ba a haɗa bakin da shi don kawai a ɓata mana suna a cikin Arɗo Barkinɗo Family? Ni ban yarda ɗana zai aikata haka ba. Kai ba mazinaci bane, haka ni ma haka. Kuma ɗan mu ba zai taɓa zama mazinaci ba. Wannan bita da ƙulli ne kawai don a wulaƙanta mu, kuma wannan shirin Mamiyo ne don kai ba ɗanta bane. Haka ta saka a kai biris da Ɓaleri a cikin wannan zuri'a. Wallahi ita ke rura duk wani abu a zuciyar Babiyo. Mai yasa ba a taɓa kama ƴaƴanta na cikinta da wani laifi ba sai ƴaƴan kishiyoyinta. Ka taɓa jin ance yau ga laifin Hamma Tukur, Hamma Lawal, Hamma Mahmud ko kuma Hamma Jibrila? Sai ku tunda ba ku da galihu mahaifiyarku ƙasa ya rufe idanunta! Ga dai Inna Jume can ita ba aurarra ba kuma ba sakakka ba a wajan Babiyo. An jingina ta a gefe ta zama wata mara amfani. Mamiyo ce matan so, matar gaban goshin Babiyo. Shiyasa ta ke cin karanta babu babbaka. Wallahi Allah ya.........."
"Ke, Halima!" Ya daka mata wani tsawan da ba ita kaɗai ba hatta ƴaƴana da ke zaune a parlourn sai da suka firgita.
Sai kuma ya sassauto da muryansa tare da faɗin, "Ki iya bakinki, Halima. Ki rufa min asiri don girman Allah!" Harda haɗe hannunsa waje guda don a yanda suke tsoran Babiyon gani suke a duk inda suke yana ina saka Camera kuma yana kallonsu.
Rausayar da kai mama Halima ta yi tana tsiyayar da hawaye baƙin ciki.
Lawisa ce ta miƙe ta ɗaga labulan window tana hangen motar Habib da ya shigo cikin gidan ya yi parking. Sakin labulan ta yi tare da faɗin, "Baffa ga Hamma Habib ɗin ya zo."
Miƙewa daka kusa mama Halima ya yi tare da tsayawa a tsakiyar parloun namansa har wani tafarfasa ya ke saboda ɓacin rai.
Tamkar munafiki haka Habib ya yi sallama tare da murɗa ƙofar ya shigo ciki. Kai tsaye inda mahaifinsa ke tsaye ya nufa tare da zube guiwowinsa a ƙasa a gabansa tare da faɗin, "Kai min aikin gafara, Baffa. Na san na cutar da........"
Baffa Giɗaɗo bai bari ya idasa ba ya dunga ɗauke fuskansa da mari hagu da dama. Shi kuwa Habibu tsayar da fuskan ya yi sosai domin mahaifin ya ji dadin kakkafta masa marukan ko hakan zai saka ya ɗanji sanyi a ransa na abunda ya jawo masa.
Mama Halima ce ta tashi dakyar ta riƙe hannun Baffa Giɗaɗo tana kuka tare da faɗin, "Haba Baffansu! Zai iya samun matsalar kunne fa. Wannan marin ya yi yawa haka akan abunda zargin sa ake ba wai ya amsa laifin bane."
"To gashi nan a gabanki da kike ɗaure masa gindi sai ya faɗa miki ya aikata ko bai aikata ba!" Ya faɗi a fusace.
"Hammadi, kalli cikin idanuna ka ƙaryata min abunda ake jinfanka dashi."
Kasa kallon mahaifiyar ya yi cikin hawaye ya shiga faɗin, "Ku yafe ni Baffa, Mama ki yafe min don Allah. Wallahi sharrin shaidan ne. Na yi alƙawari zan bi duk wani umarni na ku har ƙarshe rayuwa."
Da kallo kawai mama Halima ke bin Habibu da ya amsa laifinsa a gabanta. Girgiza kai ta shiga yi tana faɗin, "Wannan ba Hammadina bane. Hammadina ba zai taɓa kusantar zina ba. Sam ban yarda ba, saka a ka yi ka amsa laifin da baka aikata ba. Taso muje ɗaki ka faɗa min komai Hammadina."
Hannunta ya riƙe da hannu biyu ya shiga faɗin, "Mama nine, Hammadinki ne. Ki taya ni roƙon Ubangiji ya yafe min laifin da na aikata. Dagaske na aikata duk abunda aka tuhume ni da su, amma na yi alƙawarin ba zan sake ba."
Daga tsaye mama Halima ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume. Hankali tashe ya yi kanta sai da Baffa Giɗaɗo ya riga shi. Wani tsawa ya daka masa tare da nuna masa waje. Shi kuma ya cicciɓota ya nufi ƙofa sauran ƴaƴansa mata suka rufa masa baya. Jiki a matuƙar sanyaye gami da tashin hankali Habibu ya mike ya bi bayansu zuwa Arɗo Barkinɗo specialist hospital da ke cikin estate ɗin.
Taimakon gaggawa aka bawa mama Halima tare da ɗaura mata ƙarin ruwa sannan suka mata allurar bacci saboda jininta da ya hau 180/80.
Baffa Giɗaɗo ya hana Habibu ko tsayuwa kusa da window ɗin ɗakin da aka ajiye Mama Halima.
Jawaad ne ya yi parking a harabar tafkeken asibitin ya fito daga cikin motar ya shiga ciki. Tsaye ya hangi Habib ɗin da ya matuƙar ba shi tausayi ya haɗe kai da bango.
"Girei!" Ya yi kiran sunansa a hankali don Habibu ya yi nisan tunanin da bai san zuwan Jawaad ɗin ba.
"Ka ga abunda na jawo wa kaina ko, Kaita! Na je na aikata abunda ya shafi iyayena sa basu ji ba basu gani ba. Yanzu kalli halin da na jefa mahaifiyata mai ƙaunata. Kaicona da aikata Zina."
"Tuba ga Allah abu ne mai sauƙi. Wato shi ne a nemi gafarar Allah da harshe da zuciya sannan gaɓɓai su daina aikata zunubi ko laifin da ake tuba daga gare shi, Allah Madaukaki Ya ce: "Kuma wanda ya aikata cuta ko kuwa ya zalunci kansa, sannan ya nemi Allah gafara, zai samu Allah Mai gafara ne, Mai jin kai." Don haka idan har ka yi taubatan nasuha, Allah zai yafe maka don shi mai yawan gafara da jinƙai ne. Iyaye kuma, ɗan lokaci kaɗan za ka ba su In Sha Allah za su sauko daga dokin fushin da suka hau."
Jinjina kai Habibu ya yi idanun nan kaɗa sun yi jazur.
"Ina zuwa, bari naga jikin Maman," Jawaad ya faɗi tare da nufa ɗaƙin da mama ke kwance.
Yana turo ƙofar su kai idanu huɗu da Baffa Giɗaɗo. Wata uwar harara Baffa Giɗaɗo ya watso masa tare da nuna masa ƙofa bayan ya ce, "Ya turo ka ne mu idasa kashe ta? To fita! Hausawa sun ce abokin ɓarawo, ɓarawone."
"Allah ya huci zuciyar Baffa Giɗaɗo," Jawaad Kaita ya faɗi tare da juyawa ya fice ya jawo ƙofar.
"Ya koro ka ko?" Faɗin Habibu yana kallonsa jiki a mugun sanyaye.
Gyaɗa kai Jawaad ya yi tare da zama a gefen Habibun sannan ya ce, "Ban san mai yasa iyayanmu su ka nunawa wannan tsohon uban power haka ba da yake juya rayuwarmu kamar waina. Nan gama theater zai saka a yi mana sannan a maƙala bididdigi ta yanda ba zai riƙa ganin duk motsinmu yana daga zaune ba sai ya sha wahala wajen tura mana mutane suna kallon rayuwarmu ba. I'm tires of this old man. Idan kuma muka yi ƙoƙarin bijirewa, sai iyayanmu su daƙile mu waje mana barazana da mummunar kalma. Da rayuwarmu a hannun Babiyo ya ke da mun shiga uku, don da ya kashe mu tun December."
Habibu bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba saboda maganar ƙarshe ta Jawaad ɗin.
"Au dariya ma na baka? Lallai! To yanzu haka idan ka ji ihun da Baffana ya riƙa min ka ce rufe ni da duka zai yi. Faɗi ya ke ka wuce gidan Baffa Macchiɗo yanzu-yanzun nan na faɗa maka. Haba! Ni fa ban buƙatar wannan auren zumuncin wallahi."
"Kuma haka nan za kayi ba. Gwara kai after 2years bayan kammala course ɗin da Babiyo zai tura ka za ka iya dawowa kusa da family, ni kuwa sai Allah. Gashi na ɗaukarwa kaina alƙwarin da wataƙila shine sanadin rayuwata....." Sai ya juyo gaba ɗaya tare da fuskarta Jawaad tare da cigaba da magana, "Ɗan uwana kuma babban aminina, ina so ka sani, wallahi, tallahi burina a kan Zeenah shine yin jihadi domin canza rayuwar dabbobin da take yi. Wallahi tunda na ɗaura idanuna a kanta na ji haka nan ina jin tausayinta mai tsanani, ban tabbatar da haka ba sai da na haɗu da ƴarta. So nake In ceto wannan yarinyar domin idan har ta girma ta ga irin rayuwar da uwar take yi ita ma shi zata ɗauka. Ba ta san uban ƴar ba, ta rantse min da Allah baza ta iya nuna shi ta ce shine mahaifin Meema ba saboda bata san adadin mazan da tayi mu'amala da su ba," yana kawowa nan Jawaad ya wani irin rintse idanu yana jin tsigar jikinsa na wani irin mimmiƙewa ransa na mugun ɓaci.
Habib ya cigaba, "Burina in Maman Meema rayuwa mai kyau, in raba ta da wannan shashancin sannan in saka ta yi istibra'i sannan na yi mata jagora har wajen iyayanta ta nemi gafararsu ta zauna a gabansu. Daga nan ni kuma sai na gabatar da ita a cikin Arɗo Barkinɗo duk nasan abune mai matuƙar wuya su amince. Wannan shine burina ɗan uwana. Amma yanzu ba zan iya cika hakan ba. Ina jin matsanaicin ƙuna a zuciyata saboda hakan."
"Allah zai baka ladan niyya aminina! Amma baka jin abunda Babiyo ya faɗi a kan ita yarinyar ba?" Faɗin Jawaad yana jin matsanaicin tausayin abokin na shi.
"Me kenan?" Faɗin Habib yana kallonsa.
"Ta kashe mahaifinta! Wata ƙila dalilin da yasa ta gudu daga gida ta shiga bariki kenan." Jawaad ya faɗi.
Da sauri Habib ya gyaɗa kai tare da faɗin, "Zuciyata ba ta zargin haka. Kawai maganar Babiyo ne don iyayanmu su sake fusata."
"Amma kuma Babiyo bai taɓa faɗin abunda bai da tabbaci a kai," Jawaad ya faɗi.
"Ni dai zuciyata ba tai na'am da wannan zancan ba. Aminina, don girman Allah zan roƙeƙa wani taimakon mai wuya kuma mai hatsari, duk da na san za ka iya kira na da mai son kai ko kuma ka yi tunanin ina son jefa ka a matsala. Amma ina so ka sani, wallahi idan kai ne a matsayina wallahi zan iya maka wannan alfarmar."
"Faɗi maganarka kai tsaye aminina, ban tunanin akwai abunda ba zan iya maka shi ba a duniyar nan in har bai fi ƙarfina ba," Jawaad ya faɗi yana damƙe hannun Habib ɗin da ya ɗaura a saman na shi.
"Abokina zan bar maka aikin da ko fara shi ban yi ba domin kai ka aikata min don girman Allah." Habib ya faɗi.
Kallon yi min ƙarin bayani Jawaad ya masa yana kallonsa cikin ido.
Jinjina kai Habibu ya yi tare da faɗin, "Na san kwata-kwata baka ƙaunar maman Meema, amma don girman Allah ka taimaka min ka saka min ita a hanya ta bar wannan sana'ar da take yi, ka cika min duk wani burina a kanta. Ka kaita gaban iyayanta ta natsu har Allah ya fito mata da miji ta yi aure."
Kallon ba ka da hankali Jawaad ya yi masa tare da zare hannunsa cikin na Habib ɗin sannan ya ce, "Daren ranar da muka sauka a Lagos, ni ne nan na goge numbern Zeenatu a wayarka na sauya maka da wata Number, ta ƙawarta kuma na sauya maka da tsohuwar layina da ke ƙasa. Ka san mai yasa?"
Baki sake Habib ke kallon Jawaad jin abunda ya ce. "Amma wallahi kai daga kai sai ɗan iska! Yanzu fisabilillah abunda kai min ka kyauta?" Faɗin Habib ransa ya ɗan sosu da abunda Jawaad ya masa.
"I'm sorry! Na yi hakane domin in cece ka daga irin haka da ya faru saboda sanin condition ɗin mama da kuma yanda Baffa Giɗaɗo zai haukace akan haka saboda ka riga ka faɗa min plan ɗinka a kai. Ni kuma na riga na san ga wacce ka tsayar za ka aura kuma har kun daidai ta kanku. Kuma idan Babiyo ya samu labarin kai kanka ka san abinda a kai wa Baffa Belɗo na koran kare daga cikin Arɗo Barkinɗo."
Shuru Habib ya yi na ƴan daƙiƙu kamun ya saki malalacin murmushin takaici tuno da Baffa Belɗon sannan ya ce, "Kai min alƙawari za ka cika min burina, Kaita, idan kai min haka zuciyata za ta natsu har in iya sauke nauyin da ya rataya a kaina a kan Amatul kareem gudun faɗawa halaka da fushin ubangiji. Don idan kaƙi tabbas zuciyata baza ta taɓa zama waje ɗaya ba kuma baza ta natsu ba har abada. Na san ka Kaita, You never go back on your words."
Jawaad ya jima yana kallonsa kamun ya saki wani ajiyar zuciya sannan ya ce, "Allah ya dafa min wajen cika burukanmu!"
"Burukanmu?" Habib ya faɗi da mamaki.
Basarwa Jawaad ya yi tare da faɗin, "Eh mana, tunda ka saka ni ɗaukar alƙawarin da ban shirya ba. Kuma burinka ai nawa ne in dai mai kyau ne."
Dukan ƙafaɗansa Habibu ya yi sannan ya ce, "But you must be very careful! Ka san dai halin wannan tsohon mai gani har hanji."
Dariya su kai gaba ɗaya kamar babu abunda ke damun su sannan suka tafa.
_Laushi_
A daren da aka kawo kayan nan da mugun fargaba ta kwana ganin manya-manyan makami har da su boma-bomai. Kuma a nan mazajan duka su goman suka kwana.
Maƙalƙale Meema ta yi saboda sosai samarin suka bata tsoro gashi babu wanda fuskansa ya ke a buɗe. Ko magana da body language suke amfani kuma ba wai don basa iya magana ba. Kwanansu takwas a gidan ka mun suka tattara suka koma inda suka fito. A ranar da suka wuce Sabo da Kaza ya diro gidan. Key ɗin da ke wajansa ya yi amfani da shi ya buɗe ya dudduba kayan sannan ya fito ya kulle ɗakin.
"Wannan yarinyar ya kamata ta koma makaranta. Akwai wani makarantar da nake son canza mata, Yahuza zai riƙa kaita yana ɗauko ta don na lura wancan bata da wani tsaro."
Jiki dai a sanyaye Laushi ta ce, "Nagode sosai da taimako."
"Ke dai ki tabbatar sirrina bai fita ko ina ba! Ki same ni a ciki yanzu, saurin nake ban da isasshen lokaci kuma a buƙace nake da ke."
Haka nan Laushi ta samu kanta da faɗin, "Ina al'ada fa!" Ta faɗi hakane ba wai don gaskiya ne abinda ta faɗi ba.
"Muje ko ƴan dabaru kya min!" Ya faɗi tare da shigewa ciki.
"Kai!" Ta faɗi irin ba haka taso ba. Gashi Meema na ciki tana bacci. Har ta yi taku biyu ta tsaya cak tare da riƙe kanta hannu bibbiyu ta kwatsatsa wani irin ihu sakamakon wani mahaukacin sarawa da kanta ya yi.
Da gudu Sabo da Kaza ya fito daga ɗaki Meema a bayansa wacce farkawarta kenan ta jiyo ihun mamanta.
Wani irin juyi Laushi ke yi a tsakar ɗakin, can ta nufi wajen bango ta riƙa buga kanta da bangon da mugun ƙarfi kuma da sauri da sauri. Meema ruɗewa ta yi ta saki ihu tana kuka itama tare da ƙoƙarin riƙe Laushin amma sai ta yi wani irin jifa da ita ta cigaba da buga kanta da bangon har kan ya fashe yana tsartuwar jini.
Juyawa Sabo da Kaza ya yi da sauri ya shiga ɗakin nan da makamai ke ciki ya fito da wata zungureriyar allura ya tsira mata a kafaɗa.
A hankali ta shiga tsagaitawa daga buga kanta da bangon har ta tafi luuu zata zube ya taro ta ta faɗa jikinsa. Cak ya ɗagata ya kwantar a kan 3sitter sannan ya ware fankar ɗakin.
Meema kuwa jikinta babu inda bai rawa sai kuka take yi kamar zata shiɗe ganin Laushi ta koma ba ta motsi ga jini yana zuba daga kanta.
Tashi Sabo da Kaza ya yi tare da shigewa ɗakin makamai ya kullo ƙofa sannan ya dannawa wata Number da ya yi saving da doctor William kira, ringing huɗu ya yi, Doctor William ya ɗaga wayar. Bayan gama sauraran maganar Sabo da Kaza doctor William ya shiga faɗin,
"A brain aneurysm also known as a cerebral aneurysm or intracranial aneurysm - is a bulge or ballooning in a blood vessel in the brain. An aneurysm often looks like a berry hanging on a stem. Experts think brain aneurysms form and grow because blood flowing through the blood vessel puts pressure on a weak area of the vessel wall. This can increase the size of the brain aneurysm. If the brain aneurysm leaks or ruptures, it causes bleeding in the brain, known as a hemorrhagic stroke. A ruptured brain aneurysm occurs in the space between the brain and the thin tissues covering the brain. This type of hemorrhagic stroke is called a subarachnoid hemorrhage Brain aneurysms are common. But most brain aneurysms aren't serious, especially if they're small. Most brain aneurysms don't rupture. They usually don't cause symptoms or cause health problems. In many cases, brain aneurysms are found during tests for other conditions. However, a ruptured aneurysm quickly becomes life-threatening and requires medical treatment right away. If a brain aneurysm hasn't ruptured, treatment may be appropriate in some cases. Treatment of an unruptured brain aneurysm may prevent a rupture in the future...."
"What type of brain aneurysm is she suffering?" Sabo da Kaza ya katse shi ba tare da ya ida bayani ba.
"She's suffering from Fusiform aneurysm." Ya bashi amsa.
"What's the causes of Fusiform aneurysm?"
"High blood pressure, Smoking, Alcohol abuse, Atherosclerosis, Trauma, Family history of aneurysms, Cocaine or amphetamine use."
Ƙit sabo da kaza ya kashe wayarsa ba tare da kuma cewa komai ba.
"_Menene kuma Brain aneurysm?🤔_ (Za ku ji bayani da Hausa a next page In Sha Allah. Na san wasu da dama basu taɓa jin sunan ciwon ba ma.)
#Brain aneurysm #Laushi #Meema #Jawaad Kaita #Habib Girei #Arɗo Barkinɗo Family #Babiyo #Mamiyo #Mama Halima #Alƙawari #Rayuwa da Mutuwa #My Destiny #Matar Sayyadee
*** #Baffa Giɗaɗo [2/26, 5:29 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`