Page 29
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya*
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
Aneurysm shine kumburin jijiyar dake ɗauke da jini daga zuciya ya kai shi sassan jikin ɗan adam.
Brain aneurysm kuma wata cuta ce da ke faruwa idan artery dake a ƙwaƙwalwa ya kumbura, wato raunannar jijiyar jinin kwakwalwa. Cuta ce wacce idan ta kai wani mataki take haifar da raptured brain aneurysm (Ma'ana fashewar kumburin ko ita jijiyar ƙwaƙwalwar da ke sadar da jini.) Raptured brain aneurysm na janyo matsanaicin naƙasu ga lafiya kamar su; matsanaicin ciwon kai na fitar hayyaci kuma mara misaltuwa, zuban jini daga cikin ƙwaƙwalwa, ƙwaƙwalwa ta yi dameji, doguwar suma, shanyewar ɓarin jiki har ma da mutuwa nan take.
Abubuwan da ke jawo cutar Brain aneurysm sune kamar haka; hawan jini, shan sigari, wiwi da sauran kayan hayaƙi, cutar magudanun jini wacce take aukuwa sakamakon kitse daya tattaru ya cushewa magudanun jinin, tashin hankali, gadon ciwon daga cikin family, tu'amali da hodar iblis, shan miyagun ƙwayoyi da sauransu. Amma bincike masana kimiyya ya nuna mafi yawancin abunda ke janyo cutar sune; hawan jini da tu'amali da miyagun ƙwayoyi, shaye-shayen kayan hayaƙi da hodar iblis.
Shi kuma Fusiform aneurysm; ba kasafai suke faruwa ba. Shi Fusiform aneurysm kumburin magudanar jijiyar jini ne a duka ɓangarorin jijiyoyin. Irin wannan anuerysm ɗin yana da mugun wahalar magani, amma kuma suna da wuyar fashewa. Shi Brain aneurysm wani waje ne kawai a brain yake kumbura, amma Fusiform aneurysm gaba ɗaya yake kumbura. Kuma Fusiform aneurysm Laushi ke ɗauke da shi.
Fitowa daga ɗakin Sabo da Kaza ya yi tare da tsayawa a bayan kujera yana kallon Laushi da ke bacci a wahale, Meema na gefenta ta zabga tagumi babu abunda ke zubowa daga idanunta sai hawaye masu ɗumi. Taɓe baki ya yi yana mai mayar da kallonsa gun Meema.
"Mai ya samu Mummyna? Mai yasa take ta buga kanta a bango? Ta taɓa irin haka a Paris har muka je asibiti. Kuma ka ce mana baza ta sake yi ba kuma ga gashi yau ta kuma yi " Meema ta jefa masa tambayar tana shassheƙar kuka.
Yafito ta ya yi da hannu, kamar baza ta tashi ba, sai kuma ta miƙe ta nufi bayan kujeran inda ya ke a tsaye.
"Mummynki za ta samu lafiya kin ji! Ciwon kai ne mai tsanani ya ke damunta. Kin san ta shiga damuwa mai tsanani lokacin da aka yi kidnapping ɗin ki. Hakan ne ya haifar mata da damuwar da ta saka mata matsanaicin ciwon kai. Amma idan ta huta za ta tashi wasai. Wannan ba wani ciwo bane na tashin hankali."
Hakanan Meema ta ji bata gamsu da maganarsa ba. Amma sai ta gyaɗa masa kai kawai hawaye na zubo daga idanunta.
"Zan fita inje in samo mata wani magani ta sha idan ta tashi. Ki kula da ita, kin ji?"
Gyaɗa masa kai ta kuma yi a karo na biyu tare da komawa gaban kujeran inda Laushi ke kwance ta ɗaura hannunsa a kan jikinta. Duk da Laushi bacci ta ke yi, amma lokaci-lokaci ta kan kai hannu kanta tana yamutsa fuska alamar kan yana matsa mata da ciwo ko a cikin bacci.
Sabo da Kaza na ficewa daga gidan a cikin motarsa ya ɗaga waya ya kira wata Number ya yi maganar mintuna biyu sannan ya yanke wayar. A ƙofar guess house ɗin sa ya yi parking ba tare da ya shigar da motar ciki ba ya fito ya yi amfani da key ɗin hannunsa ya buɗe gidan ya shiga ciki.
Ƙofar ɗakin ya yi knocking sau biyu, nan take Yasaar da shekaran jiya ya fito daga gidan yari ya taso ya buɗe masa ƙofar tare da matsawa ya bashi hanya ya shigo ciki. Sai da ya yi balance a kan kujera three seater sannan ya kalli Yasaar ya ce,
"Yasaar, wato abunda muke shirin aikatawa Laushi ba ƙaramin illa zai wa rayuwarta ba. Tabbas za ka ɗan samu relief akan abunda ta aikata maka. Wai ka san wani irin cuta take ɗauke da shi a ƙwaƙwalwarta kuwa?"
Girgiza kai Yasaar ya yi yana jiran ƙarin bayani daga wajen Sabo da Kaza da ke ɓaɓɓaka dariyar mugunta. Sai da ya yi dariyarsa ma'ishi sannan ya ce,
"Fusiform aneurysm ta ke fama da shi. Ina mai tabbatar maka ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya faruwa da ita; shanyewar ɓarin jiki, doguwar suma, ko kuma ƙwaƙwalwarta ta yi dameji. Infact za ta iya mutuwa ko wani irin lokaci. Kuma babban matsalar shine; masu irin ciwon nan sam basu buƙatar tashin hankali don hawan jini yana ɗaya daga cikin abinda ke haifar da ciwo."
"Wani irin ciwo ne wannan haka? Ban taɓa jin ko labarin sa ba," Yasaar ya faɗi yana kallon Sabo da Kaza with confusion.
"Fusiform anuerysm kumburi ne na duka magudanar jijiyar jinin da ke ƙwaƙwalwa," saboda da Kaza ya fadi murmushi bai bar fuskansa ba.
Wani irin ɓacin rai ne ya dabaibaye fuskan Yasaar. Cike da ƙunar zuciya ya furta, "Yanzu ke nan ba za ta yi tsawon ran da za ta ɗanɗani kwatankwacin baƙin cikin da ta saka ni ba? Kullum da hoton tagwainina na ke kwana a ƙirjina. Ɗan uwana bai ji ba bai gani ba ta yi sanadiyar mutuwar sa. Ba zan bari wannan ya tafi a banza ba. Idan har Laushi ta mutu da wuri, burina ba zai taɓa cika ba na wulaƙanta rayuwarta. Ɓan ƙaunar yarinyar nan ta mutu," Yasaar ya faɗi hawayen baƙin ciki na kwaranyo masa.
Dafa kafaɗarsa Sabo da Kaza ya yi tare da faɗin, "Kwantar da hankalinka, Yasaar. Ai ni ma ba zan bari haka ya faru ba. (sai ka ce rayuwarta a hannunsu ya ke🙄) zan riƙa amso mata magani kamar yanda doctor William ya bani shawara tun a Paris. Ka san tun a can da ciwon ya soma nunawa na kai ta asibiti suka faɗa min ciwon da ke damunta. Kuma ya faɗa min idan tana shan pills ɗin da ya faɗa min za ta riƙa ɗan improving, amma fa idan so ake ta warke duk da sun ce ba a taɓa warkewa gaba ɗaya, amma idan aka yi mata ɗaya daga cikin waɗanda za ta iya warkewa. Wato; Hunterian ligation, trapping, surgical bypass, and clip reconstruction techniques. Amma mafi yawanci sai an yi surgery kuma under risk ya ke."
"Ni dai wallahi ban so ta mutu. Allah yasa sai na gama gwarata kamar kwallo, kuma ta mugun wulaƙanta a duniya kamun ta mutu," Yasaar ya faɗi.
"Burinka zai cika," Sabo da Kaza ya faɗi yana bugun bayansa kaɗan tare da miƙewa ya shiga cikin wani ɗaki.
Yana shiga ɗaki wayarsa ta yi ƙara alamar shigowar saƙo. Fiddo wayar ya yi daga aljihu sai ya ga saƙo ne daga doctor William.
_She should take the following; Calcium channel blockers, Antiepileptics, Antihypertensives, Analgesics, Antiemetics, Antacids, and Stool softeners. Also she should avoid taking the following medicines; Cipro (ciprofloxacin), Levaquin (levofloxacin), Factive (gemifloxacin) and Avelox (moxifloxacin). These medications may increase the risk of aortic dissections or ruptures._
Yana gama karanta ya tura masa thanks tare da jefar da wayar a kan gado sannan ya faɗawa toilet.
Ɓangaren Laushi kuwa, wannan matsanancin ciwon kan ba ƙaramin uzzurawa rayuwarta ya ke ba ko cikin bacci. Meema kuwa ko gusawa daga inda ta ke ba ta yi ba tana nan ta zabga tagumi tana kallon Laushi. Wani lokacin kuma sai ta fashe da kukan musamman idan Laushin ta kai hannu bibbiyu ta damƙi kanta ta shiga jujjuyawa.
"Mummy, mummy, mummy can you hear me?" Meema ta faɗi tana kallon fuskan laushin da ya ɗan soma kumbura kaɗan.
Laushi kuwa bata ma san duniyar da take ba balle ta jiyo muryan ƴar ɗiyar tata. Miƙewa Meema ta yi ta kwasa da gudu ta shiga bedroom ɗin Laushin tare da ɗauko wayarta ta lalubo Number ɗin Ladi Katifa ta danna mata kira. Sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan Ladi ta ɗaga kiran tare da faɗin,
"Har an gama cin uwar sabadar kenan? Ya wuce ne?"
"Aunty Ladi ki zo da sauri don Allah, mummyna za ta mutu," da kuka Meema ta ƙarisa maganar.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Gamu nan zuwa ni da Salma nice yanzu," tana gama faɗin haka ta katse wayar.
Parlour Meema ta dawo ta zauna tare da riƙe hannun Laushi saboda wannan karan bugun kan take da ƙarfin tsiya. Yanzu hakan ma sai da ta saka ƙarfinta duka sannan ta iya riƙe hannunta kuma don har yanzu allurar anesthesia da Sabo da kazan ya mata yana aiki a jikinta, don a hakan ya rage mata raɗaɗin azabar ciwon kan da take fama da shi.
Cikin awa guda, Ladi da Salma nice suka shigo gidan hankali tashe lokacin allurar anesthesia ya soma sakin jikinta sai sai haukan buga kai da kujera take.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, ni Salmanu jikan Iya! Wannan wani irin ciwo ne kamar na hauka?"
"A'a dawanau ne na Kano ko kuma Barnawa a kanta. Ya muna masifar tashin hankalin nan za ka daɗa mana wani a kai! In Sha Allah, Laushi ba za ta taɓa hauka ba a kaf rayuwarta," Ladi ta faɗi tana kuka.
Kamar an tsikari Laushi ta tashi a razane tare da kwanɗama wani irin mahaukacin ihu tana buga kanta a jikin kujera, Ladi Katifa ta yi iya kacin ƙoƙarin wajen ganin ta riƙe ta kada ta jima kanta ciwo amma ta kasa. Hatta Salma nice sai da ya ajiye daudu a gefe ya saka dukkanin ƙarfinsa amma ya kasa riƙe Laushi.
Meema ganin haukan buga kan da mummynta take yi yafi na ɗazu lokacin da Sabo da Kaza ya ke nan sai ta hau kuka har numfashinta na wani irin ɗaɗɗaukewa. Sai jin faɗuwarta tim suka yi a ƙasa.
"Tabbat yada habi lahabin wa Tabba, Inna a'a ɗaina kalkauthar, Li'ilafi quraishin! Ya Allah kai kaɗai ne Lam yalid walam yulad, walam yakul lahu kufwan ahad, ka rufa mana asiri ka tashi kafaɗun wannan baiwar taka. Allah astagfirullah mun tuba billahil lazhi la'ilaha illahuwa. Allah kafi kowa sanin ni ɗin ba kowa bane face Salmanu jikan Iyan mai danko. Allah mun tuba ka yafe mana," faɗin Salmanu bayan ya ɗaga hannunsa biyu sama har da ƙwallarsa.
Ladi ruɗewa ta yi ita ma ta fashe da kuwa kuma ta rasa inda za ta nufa, wajen Meema domin bata taimako ko kuwa wajen Laushi da duk ta gama fashe kanta sai tsiyayar da jini yake.
"Salma fita ki nemo mana......."
Saurin katse Ladi da ta soma magana ya yi cikin kuka tare da faɗin, "Wallahi Allah ya isa kika kuma tura ni jinsin ƴan mata. Mai kuma ya haɗani da jinsin mata ni ba ƙirji da mazaune ba. Ko kin ganni da bireziya ne a jiki. A'a wallahi idan ma don wannan kallabin da ke ɗaure a kaina ne to billahil lazhi na cire shi na yar. Gobe-goben nan zan je kasuwa in nemo hula shafa kaji hadisi da kuma carbi in riƙe a hannu ina ja. Kar ki kuma kai ni jinsin mata!" Da iyakacin gaskiyarsa ya ke faɗin haka bayan ya cire duk wani abu da ya danganci mace a jikinsa ya wurgar a ƙasan ɗaki.
Da Ladi Katifa cikin hayyacinta take, to babu abunda zai hana ta dariya har da kwanciya a ƙasa saboda yanda gaba ɗaya Salmanu ɗan daudu ya firgice yana faɗin maganganu.
"Dalla fita ka nemo mana taxi kar ayi gawa biyu a cikin gidan nan!" Ladi Katifa ta faɗi da ƙarfi.
Har Salmanu ya ɗaga ƙafa ɗaya sai ga Sabo da Kaza ya shigo hannunsa riƙe da wata ledan mai tambarin wata babbar pharmacy da ke Lagos. Da kallo ya bisu kamun ya sauke idanunsa a kan Laushi da gaba ɗaya jikinta ya ɓaci da jinin da ke zuba a kanta.
"Tsayuwar me kuke yi kamar wasu sojojin gadi kuna kallon halin da take ciki kuma a hakan kuke kiran kanku abokanta?" Saboda da kaza ya faɗi cike da fushin da ba daga zuciyarsa ta fito ba.
"Yanzu muke ƙoƙarin kiran taxi domin kai ta asibiti," Salmanu ɗan daudu ya faɗi don ita Ladi kallo ɗaya ta masa saboda wani uban haushinsa da take ji.
"Ga magungunanta nan na sayo mata da allura. Ta taɓa haka lokacin da muka je Paris, so na kai ta asibiti sun faɗa min hawan jini take fama dashi mai saka matsanaicin ciwon kai saboda tashin hankalin rashi Meema da tayi har hakan ya saka jininta ya yi mugun hawa. Amma ya ce idan tana shan waɗannan magungunar za ta samu sauƙi, in Sha Allah!"
Ladi ta ɗan ji gamsuwa da maganganun Sabo da Kazan saboda ita shaida ce a kan halin rashin bacci da tashin hankalin da Laushin ta shiga a wancan lokacin. Don baza ta manta da irin kwayoyin, sigari da wiwin da ta yi ta bankawa cikinta ba.
Da taimakon Ladi da Salmanu har da shi Sabo da kazan, sannan ya samu nasarar danneta ya mata ɗuren magungunar da ya shigo da su sannan ya danna mata wata allurar. Nan da nan jikinta ya saki ta hau bacci. Da kansa ya kai ta bedroom ɗinta ya jawo ƙofar.
Lokacin da ya dawo parlourn har Ladi Katifa ta yi nasarar farfaɗo da Meema daga sumar da ta yi. Sai da babu abunda take sai kuka tana faɗin a kaita wajan mummynta.
"Ki kaita ɗakin ta ganta saboda hankalinta ya kwanta. Ni zan tafi kuma ƙasar zan bari. Ki zo na yi maki bayanin magungunar nan, duk lokacin da abun ya taso mata kina bata su In Sha Allah za ta dawo normal, ciwon kan kuma zai bari."
Tashi Ladi Katifa ta yi tare da riƙo hannun Meema suka nufi bedroom ɗin Laushin. Tura ƙofar ta yi a hankali sannan suka shiga ciki.
"Kin ga mummyn na ki bacci take yi, ta samu sauƙi ki daina kukan kin ji daughter?"
Gyaɗa kai Meema ta yi tare da faɗin, "I want to sleep beside her, please."
Gyaɗa mata kai ta yi, ita kuma ta tafi ta hau kan gadon tare da kwanciya a gefen Laushi ta shige jikinta sosai sannan ta ɗaura kanta a kan kafaɗar uwar.
Wani irin mugun tausayin su duk su biyun ya kama Ladi har sai da hawaye ya zubo mata daga idanunta. Ta jima tana kallon su kamun ta juya ta fice daga ɗakin ta rufo masu ƙofar ta dawo parlourn.
"Ina kuma ita Meeman ta ke?" Sabo da Kaza ya faɗi yana kallon Ladi.
"Tana can kwance gefen uwar. Ka san ita Meema akwai ƙulafucin uwa. Yanzu haka sai ka ga tafi uwar rama a kan halin rashin lafiyar da uwar take ciki," Ladi Katifa ta faɗi.
Ba tare da ya ce komai ba ya fiddo duka magungunar ciki ya shiga nuna mata yanda za ta ba Laushin. Wasu sai ciwon ya tashi, wasu kuma kullum safe da dare.
"Kin gane ko?" Sabo da Kaza ya fadi.
"Eh duk na gane. Wannan ka ce asha safe da dare, wannan kuma sai ciwon ya tashi. Wannan kuma kace duk za ta ci abincin ta saka a ƙasan harshenta.
"A'a fa, ba haka na ce a wannan na ƙarshen ba, cewa na yi kamun ta ci abinci ta saka. Misali saura mintuna talatin ta ci sai ta saka shi a ƙasan harshenta, life support ne."
"Ok, na fahinta yanzu." Ladi ta faɗi tana kwashe kwalayan magungunar tare da sakawa cikin leda.
"Ni na wuce," ya faɗi tare da nufa ƙofar ɗakin ba tare da juyowa ko sau ɗaya ba. Don har wani sauri yake kamar zai tashi sama..
"Salma, ni fa ban yarda da wannan mutumin ba fa," Ladi Katifa ta faɗi.
"Amma ke dai Allah shi ɗebe miki albarka! Wacece kuma Salma babu daɗin ji? Tuf! Maza tofar wallahi. Bar tura ni jinsin ƴan maza. Gandareran saurayi majiyi ƙarfi ne a gabanki," faɗin Salmanu ɗan daudu.
Waro idanu Ladi ta yi tana dariya tare da faɗin, "Yau kuma? Menene ya canza maka ra'ayi haka yau?"
"Dama ai daudu riga ce, da na cire shikenan na dawo gandareran ƙaton saurayi. Tuni, na cire shegiyar rigar na yasar a ƙasa. Kin ga, bar ni na mutu maza ƴan uwana su kai ni ba mata ba."
Wannan karan dariya Ladi Katifa ke yi har da zaman ƴan bori a ƙasa. Eh, lallai maza anji anani an tuba an koma ga Allah!"
"Annabi umar da annabi Abubakar uban Nana Aisha duk suma tuban suka yi, don da ba musulmai suke ba, zuwan manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya basu kalmar shahada suka amsa," Salma nice ya faɗi.
"Kai! Iya bakinka. Ba annabawa bane Sahabbai ne. Sayyidina Umar da Abubakar za ka ce," faɗin Ladi Katifa.
"Yauwa su, hakan ɗin nake son faɗi sai na yi mistin (Mistake). To kin gani. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne kawai bai taɓa laifi ba a wannan duniyar. Kuma billahi na karanta a hadisi lokacin Iyan mai danko tana tura ni makarantar allo kamun na yi murabus na ɗauki tsinanna rigar daudu na saka a jikina. Ni ya ma hadisin ya ke, yauwa na tuna _Wallahi inni la astagfirullaha, wa'a tubu ilaihi, Astara min saba'ina marrat (wallahi Ni ina naiman gafara Allah, kuma ina tuba a gare shi fiye da so saba'in a rana)._ Idan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da bai yi laifin komai ba har ya bar duniya zai nemi gafarar Allah da tuba zuwa gare shi, Ni ƙatoto mai tiƙeƙen zunubi ai sai sau dubu malala gashin tinkiya. A'a wallahi, bar ni na tuba zuwa ga mahalicina. Wallahi daga yau babu wata sallar jam'i da za ta ƙara wuce ni sai dai idan ban da lafiyar da jikina baza ta iya motsawa ba."
Jinjina kai Ladi Katifa ta yi ganin dagaske Salmanu ya ke tare da faɗin, "To, Allah ya sa dai tuban ba na muzuru bane.
Harararta ya yi tare da faɗin, "Baƙin ciki kike da wannan tuban nawa tabbas! To yau kamun rana ta faɗi sai na tofe ki da Li'ilafi quraishin ƙafa ɗari huɗu da uku, sannan in biki da ƙul'uhiya ƙafa dubu, wa'innahu Sulaimanu ƙafa casa'in don ga dukkan alamu jinnin baƙin hali ke tattare da ke, kuma ba zan dakata ba har sai na rufe da Alamtarakaifa ƙafa saba'in da takwas."
Dariyarta ne ya ɗauke ɗif tuno da abokin wasanta Mu'awiyah kasancewar shine da anyi abu zai ce to wallahi Alamtarakaifa ƙafa saba'in ya kama ku idan har kuna so Allah ya yafe muku.
*_Bari mu ɗan koma baya kaɗan muji wacece Ladi Katifa_*
Asalin cikakken sunanta shine Rukayyah Shafi'u. Ita ƴar asalin jihar Kano ce a wani ƙauyen da ake kira kunya. Ita kaɗai ce a wajan mahaifinta mai suna malam Shafi'u da mahaifiyarta Uzaibatu. Ta kasance abun so a wajen iyayanta kasancewar ita kaɗai Allah ya basu bayan tsawon shekaru goma sha biyu da aure.
Malam Shafi'u wani ƙaramin mai kuɗin ƙauye ne, domin ko a wannan zamanin gidansa ba a cin shinkafa ƴar Hausa duk da kuwa yana noman ta. Idan ya yi girbi sai dai ya sai da ya kyautar da na kyautarwa wa dangi. Yana da ƙannai biyu duka maza, Labaran da Mashakur. Dukkan su suna da mata da ƴaƴa don Mashakur ma ya riga shi aure don a cikin ƴaƴansa manya maza suna masa aikin gona.
Bai da ƙyashi ko kuma rowa. Hannunsa a buɗe ya ke ba ga ƴan uwansa kawai ba har da mutanan gari. Yana hidimtawa ƴan uwansa sosai saboda tamkar uba haka yake a wajensu saboda iyayan duka biyu ƙasa ta rufe idanun su. Amma duk da wannan hidima da yake masu har da iyalansu, basu ganin hakan ko kaɗan sai ma mugun halinsa da suke gani saboda hassada da ya rufe idanun su.
A duk sa'ar da Rakiya ta je gidan ƙannan mahaifinta, daga matansu har su kansu sun dunga zaginta da dungurinta kenan suna faɗin ga ƴar ƙaruna nan wacce gidansu ba a cin ƴar Hausa da taliyar murji sai ta leda saboda an ɗauki rayuwar ƙarya da ji da kai. Haka za ta koma gida tana kuka sannan ta faɗawa mahaifiyarta abunda aka mata, amma sai mahaifiyar ta gargaɗe ta akan kar ta saki ta faɗawa mahaifinta saboda a gaban idanunsa nuna wa suke ko ƴaƴansu na cikinsu ba sa ƙauna kamar yadda suke ƙaunar Rakiya.
"Haba Rakiya, ke dai kwanaki kaɗan ya rage maki ki tafi ki koma makarantarki ta bodin (boarding). Ki rabu da su wata rana sai labari. Kuma su ɗin iyayanki ne. Misali yanzu a ce babu mu, dole wajen su za ki koma."
Wannan magana ita Uzaibatu mahaifiyar Rakiya ta ke faɗa mata a duk lokacin da ta dawo tana kuka daga gidan ƙannan mahaifinta.
A can cikin garin Kano take zuwa makaranta kwana mai suna Rumfa College. A duk lokacin da za ta koma, sayayya malam Shafi'u ke mata da yawa dangin su, madara, sukari, cornflakes, sabulun wanka, wanki, kwai, milo, magi star, couscous da sauransu.
Idan ƙannan mahaifin nata suka koma gida haka za su bajewa matayansu irin hidimar da Shafi'u ya yiwa Rakiya da za ta koma makarantar da su a wajansu karuwanci ya tura ƴarsa.
Sosai Rakiya ta tsaya masu a rai kuma sun mugun tsanarta musamman makarantar da take zuwa wanda ya tsaya musu a rai saboda ƴaƴan su ba sa zuwa sai aikin talle kawai.
Lokacin Rakiya na Form 3 Allah ya ɗauki rayuwar malam Shafi'u sakamakon ciwon ciki na kwana uku kacal. Labaran da kansa ya tafi cikin Kano har makarantarsu Rakiya ya ɗauko ta. Tun a hanya ya faɗa mata mahaifinta ya mutu ba tare da wani lalama ba ko dabara ta yanda ko mutuwar za ta dake ta ba kamar yanda ya faɗa mata kwatsam haka ba. Har suka shigo Kunya kuka kawai Rakiya take yi.
Uzaibatu kuwa ko idanunta ba ta iya buɗewa saboda tsabar kukan da ta sha na tashin hankali. Kukan bai kuma zuwan mata ba sai da ta yi arba da ƴarta da ta shigo a gigice tana faɗin,
"Innarmu shikenan Baba ya tafi bazan ƙara ganinsa ba? Shikena babana gatana kuma mai sona ya tafi ya barni?"
Babu wanda bata saka kuka ba da wannan maganganun nata. Ta yi kuka kamar ranta zai bar jikinta don har zazzaɓi mai zafi sai da ta yi.
Bayan kwana uku da rasuwar, sai Labaran da Mashakur suka kanainaye a kan dukiyar malam Shafi'u gaba ɗaya. Duk inda suka je faɗi suke sune da dukiyar Shafi'u tunda bai da ƴaƴa maza. Ita dai Uzaibatu idanu ta kawo ta saka musu. Duk abunda suka ce ta bada dangane da dukiyar Shafi'u, ba su take. Idan ƴan uwanta suka hauta da faɗa, sai ta ce shin dukiyar zai dawo da rayuwar mijinta ne. Su je su da Allah. Dukiya dai anan duniya muka tarasu, kuma ana duniyar za mu bar su.
Kamin bakwai sai da Labaran da Mashakur suka tattare komai na dukiyar Shafi'u. Hatta abincin da za a ci basu bari ba wai yanzu dukiya ta magada ce. Ran ƴan uwan Uzaibatu ba ƙaramin ɓaci ya yi ba saboda ba ƙaramin tijara su Labaran suke ba a gidan.
Bayan kwanaki goma da mutuwar Shafi'u suka shigo gidan suna tijara akan ƴan uwan Uzaibatu sun yi yawa a gidan don haka su bar gidan don za suyi amfani da ɗakunan cikin gida ɗaki ɗaya kawai za su barwa mai takaba ta yi takaba, kuma tana gamawa itama ta kama gabanta. Dubu goma suka aje wai shine tumunin takabarta, bayan wannan ba ta da komai da ya danganci dukiyar Shafi'u. Na Rakiya kuma sun riƙe a wajansu za su adana mata har ta yi aure tukun.
Ba ƙaramin gumurzu a kai tsakanin dangin Uzaibatu da su Labaran ba. Daga karshe ƴan uwan Uzaibatu suka tattara suka tafi Ɓagwai dama kuma su ɗin ƴan can ne. Sai suka bar ƙanwar Innar Uzaibatun kawai domin ta taya ta zama.
Kamun Uzaibatu ta kammala takaba ba ƙaramin wuya suka ci ba domin abinci gagararsu take don ko kwano ɗaya su Labaran ba su kawo musu. Duƙiya kuwa sai watanda suke da ita, don dukkansu babu wanda bai ƙara aure ba a cikinsu. Don Mashakur ma a nan gidan shafi'un ya ajiye amaryar tasa.
Bayan kammala takaba, Uzaibatu ta so tafiya da Rakiya amma su Labaran suka daka tsalle suka ce basu san wannan zance ba. Babu inda Rakiya za ta je. Da ihu da kuka aka raba Uzaibatu da ɗiyarta. Jama'ar gari kuwa sai zagi da alawadai da su Labaran suke yi.
Bayan komawar Rakiya gidan Labaran, ba ƙaramin gana mata azaba suke ba, dama kuma maganar makaranta tun ranar ukun Shafi'u suka faɗa mata cewar ta sani ita da makamanta har abada. Wanda ta samu Allah ya masa albarka.
Girki, shara, wanke-wanke, ɗiban ruwa, talle duk Rakiya ke yin su. Gaba ɗaya kayanta sun kwashe sun bawa ƴaƴan su mata. Duk wannan ƙibar ya zube sai idanu. Kaya kala biyu kawai suka bar mata. Sai ta haɗa sati biyu ruwa bai ga jikinta ba sabida bata da wannan sararin. Abinci kuwa ƙanzo ne rabonta shi ma idan ta je wanke-wanke. Wani lokacin kuma Samira ta ƴar wajen baba Labaran ta anyata masa ruwa idan ta lura tana kankara. Mutum ɗaya ne mai tausaya mata shine Mu'awiya babban ɗan baba Mashakur. Shi ke kawo mata awara da wainar rogo a ɓoye duk sanda ya zo gidan.
Da azaba tai mata yawa wata rana ta roƙi ɗari wajen Mu'awiya, yana bata ta gudu tasha ta hau motar Ɓagwai ta tafi wajen dangin mahaifiyarta Uzaibatu. Sai dai ko barin ta shiga cikin gidan mahaifin Uzaibatun bai ba ya rakota da bulala har tasha ya biya mata kuɗin mota ya ce ta koma can dangin ubanta don shi da ya tashi bada auren ƴarsa, ita kaɗai ya kai gidan miji don haka ita kaɗai za ta dawo masa gida. Musamman ma da suka shawo kanta da kyar ta yi auren a cikin garin Kano, Gwale.
Haka ta dawo tana kuka lokacin dare ya yi. Mugun bugu Baba Labaran ya mata saboda sun ci nemanta kamar ƙafafunsu za ta tsinke har sai da wata ƴar talla a tasha ta faɗa masu ta ganta cikin motar ɓagwai.
Haka rayuwa ta cigaba cikin uƙuba a gidan su baba Labaran.
Lokaci guda labaran da Mashakur suka bawa Hayatu aurenta saboda zuwan wani mai rufin asiri a cikin ƙauyen domin auren ta. Su kuma yanda suka tsaneta haka suka tsani duk wani cigaban da zai zo mata.
Hayatu dai tataccen mashayi ne kuma irin ƴan iskan tashan nan. Babu wanda bai sansa ba a cikin garin kunya saboda taƙadirancinsa. A cikin sati guda suka ɗaura aurenta wanda ko dangin uwarta basu sani ba suka miƙa ta gidansa daga ita sai tabarma, tukunya ɗaya, kwanan ci da sha sai kofin silver guda ɗaya.
Wani baƙar azabar wahalar ce ta kuma yi mata sallama. Don Rakiya za ta iya rantsuwa sati ɗaya kawai ta yi a gidan Hayatu cikin natsuwa, amma bayan wannan ranakun shafin babin wahala da azaba ne ya buɗe mata. Don kuwa babu ranar da Hayatu bai jibgarta. Ga rashin ci da sha, ga azabar shaye-shaye da har a cikin ɗakinta yi yake ga kuma azabar uwar miji, ita ta daka ɗanta ma ya daka.
A haka Allah ya kawo mata rabon juna biyu mai matuƙar laulayi. Amma duk wannan azabar laulayin haka mahaifiyar Hayatu take gallaza mata da uban ayyuka, idan kuma bata gama da wuri ba ta gibgeta. A haka har ranar haihuwarta ta zo. Da rana naƙuda ta kama, tun tana daurewa a ɗaki har ta koma kiran surukar da ƙarfin naiman taimako amma surukar ta yi burus kuma tana jinta. Sai cewa ta yi duk wata mace haka ta ji, don haka ke za kiyi abunki ke ɗaya ba mai zuwa.
Tun Rakiya na gani dishi-dishi har ta ta yi ɗif, bata kuma sanin inda kanta yake ba, sai a cikin garin Kano a asibiti ɗaure da ƙarin ruwa. Wata Nurse ce ke faɗa mata satinta ɗaya bata san inda kanta yake ba, kuma waɗanda suka kawo ta sun ɗauki gawar babyn da ta haifa sun tafi bayan sun bar takarda saki. Kuma babu wanda ya biyo bayan ta. Nurse ɗin ce ma ta taimaka take kula da ita.
Rakiya ta yi kuka kamar za ta mutu. Wannan Nurse ita ta kaita gidanta ta yi kwana bakwai tana kula da ita. Bayan ta warware sai ta bata kuɗin mota ta ce ta tafi dangin mamanta. Sai dai ko da Rakiya ta tafi Ɓagwai abunda ya faru zuwanta na farko shi ya kuma faruwa. Wannan abun ne ya kangarar da zuciyarta ta ji ai gwara kawai ta shiga duniya. A cikin mota Allah ya haɗa ta da wata wacce ita ma duniyar ta shiga, bayan bata labarinta sai ta yi mata introducing sana'ar da take yi. Rakiya kuwa ta yi na'am. Daga nan suka nufi Lagos gidan Hajj Lanti, shekarunta biyu a can ta dawo Bauchi. Kuma anan ne suka haɗu da Laushi har suka kuma komawa Lagos.
#Laushi #Ladi Katifa #Meema #Sabo da kaza #Yasaar #Meemah #Fusiform anuerysm #Arɗo Barkinɗo Family #The game is about to start #My Destiny #Matar Sayyadee
*** [2/28, 6:59 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`