My Destiny (Ƙaddarata)

Page 30

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya*

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Hannu ya kai ya yi waving a fuskanta tare da faɗin, "Lafiya Katifa kika faɗa dogon tunani haka har da su kuka?"

Hannun ta kai ta share hawayen tare da sakin murmushin yaƙe ta furta, "Babu komai Salma."

"Allah kar kiga kina cikin ɗacin rai ki tunanin zan raga miki! Kar ki kuma tura ni jinsin ƴan mata. Tuni na cire kallabin da ɗaurin zanin na yar, haba!"

Murmushi ta kuma yi karo na biyu tare da faɗin, "To yi haƙuri Salmanu jikan Iyan mai danko."

"Now you're talking!" Ya faɗi yana rausaya da fari kamar dai mace.

Duk da kallabi da rigar ba zai yi wuyar cirewa ba, amma ɗabi'un matan da aka ɗauka aka ɗaurawa kai shekara da shekaru zai yi wuyar barin jikin.

"Wash! Kwankwasona, ni jikan Iyan mai danko. Basir duk ta gama cinye takashin wallahi. Mai kike cewa ɗazu ma?" Ya faɗi yana ƙoƙarin miƙewa.

"Kai da ka ke ƙoƙarin miƙewa kuma shine ka ke tambayar abunda na ce ɗazu. Ina za ka?" Ladi Katifa ta faɗi.

"Kitchen na nufa domin ɗaura mana girki. Wallahi yunwa nake ji sosai. Kuma uwar Meema idan ta farka za ta buƙaci abinci na sani," Salmanu ya faɗi yana nufar kitchen.

"Eh, haka ɗin na da kyau sosai. Ni ma yunwar na ke ji." Ladi Katifa ta faɗi.

Laushi bata farka ba har sai ƙarfe tara na dare don har Ladi da Salmanu tsoro ya kama su, sai dai jin tana numfashi sai hankalin su ya kwanta.

Meema kuwa ta tashi tuntuni, amma ta kasa matsawa daga kusa da uwar sai hawaye take kuma bini-bini sai ta kai kunnanta kan ƙirjin Laushin domin jin shin ƙirjinta na bugawa.

Lokacin da ta farka, kan ya mata mugun nauyi sosai, sai dai bai mata bala'in ciwo irin na ɗazu. Amma da zaran ta kalli ƙasa sai ta ji idanunta kamar za su faɗo ƙasa tsabar yanda su kai mata nauyi.

Meema ta taras a gefenta tana hawaye. Kallonta ta yi kamar wacce ta fara arba da ita a ranar.

"Mummy!" Meema ta faɗi tare da faɗawa kanta ta rungumeta ƙam tana kuka.

Hannu Laushi ta saka ta zagaye ta ƙwaƙwalwarta na tuno mata da abunda ya faru ɗazu da rana. Shuru ta yi tana tunanin tabbas ta taɓa iya wannan irin azababben ciwon kan nan a Paris har saboda da kaza ya kai ta aka mata hoton kai. Sai dai bai faɗa mata result ɗin hoton ba idan banda ce mata da yayi stress ne da damuwa ya jawo mata ciwo, sai kuma pills ɗin da ya bata ta sha, kuma tun da ta sha bata kuma jin irin ciwon ba har suka je Dubai suka gama kwanakin su suka dawo Nigeria. Irin wannan azabtacciyar ciwon kan da taji ko maƙiyinta ba ta masa fatan ya ɗanɗana.

"Mummyna, don Allah kar ki tafi ko ina ki barni. I can't live without you, mommah!" Meema ta faɗi tana ƙara ƙanƙame uwar.

Bayanta kawai ta ke bubbugawa ba tare da ta ce mata komai ba. Mafarkin da ta yi ne ya tuno mata karshe da mahaifiyarsu ta yi mata; _Zinatu, ni mahaifiya ce a gare ki kuma mai ƙaunarki, wacce take son cigabanki. Duk duniya babu wata mace ko ɗa namiji har da mahaifinku ban cire ba da zai gwada min ya fini son ku. Ina ƙaunar ki Zinatu. Sosai ba kaɗan ba, amma halinki ne ya ke sani jin haushinki da zuba miki idanu idan kina wasu abubuwan. Zinatu kowa rai ya yiwa daɗi barin mai shi ne. Yanzu fisabilillahi, Maryama da Sa'adatu basu burge ki? Sun natsu waje ɗaya babu ruwan su da shashancin ko kuma yin abunda Abie ɗinku zai hantare su. Kullum ƙorafinki shine ba a ƙaunarki cikin gidan nan. Kina ganin mutum zai haifi ɗa ya ce bai so? Ko bambamci da kika ga babanku yana nuna tsakanin sauran ƴan uwanki da ke, saboda halinki ne. Zan iya ƙirga sau nawa babanku ya saka hannunsa a jikin Maryama da Sa'adatu. Amma ke ban ga ranar da za ta hudo har ta faɗi ba a jibgeki a cikin gidan nan ba. Zinatu kina da shegen kwaɗayi da hangen na sama da ke wanda hakan ba ƙaramin illa bane a rayuwarki. Shi kansa mahaifin na ki da kika ganin kamar shi ya yankarwa kansa talauci, rayuwa ce ta mayar dashi haka. Amma da gatansa. Kawai yau da gobe ce, ku kun san haka don baku rasa ci, sha ko sutura ba. Yana iyakacin bakin ƙoƙarin sa a kan ku. Amma ke ɗaya kawai kina son caza mana ƙwaƙwalwa. Shin kin san irin ƙashin arzikin da Allah ya yiwa shi mijin da ya zaɓar miki? Don girman Allah Zeenah ki daure ki yiwa mahaifinki biyayya ki auren nan kamar yanda sauran ƴan uwanki suka amince. Kin ganni nan, na auri mahaifinku ne saboda biyayyar iyaye because I belongs to the family where good daughters never say no to their parents. My father wanted me to get married, and all a said is, if that will make you happy I'll say yes. And you all know it was never a happy marriage. Mahaifinku mutun ne mafaɗaci kuma mai zuciya tsiya. Yana da mugun taurin kai kuma ba ƙaramin abu ke saka zuciyarsa ta yi laushi ba. Don girman Allah ina roƙonki da ki kiyaye fushi da zuciyar mahaifinku, Zinatu. Zeenatu duk lokacin da na juya na kalle ku ku mata uku reras a gabana, sai na ji zuciyata ta tsinke. Bani da burin da ya wuce na ga na aurar da ku na miƙa ku gidan mazajan ku cikin mutunci. Ki taimaka min Zinatu, wallahi ke kaɗai ce ciwon kaina. Ban jin Maryama da Sa'adatu domin su ɗin masu tausaya min tare da jin maganata ne ni da mahaifinku._

Hannu Laushi ta kai ta share hawayen da suka ziraro a idanunta bayan ta gama tuno kalaman mahaifiyar tata a kunnanta kamar yanzu take mata magana.

"It been 10years now without you Mamana! Ba mutuwa kika yi ba amma ban da ikon zuwa inda kike saboda abunda na aikata! Wallahi tallahi ba intentionally na yi ba. Self-defense ne. Allah ka san komai kuma kana ganin komai." Laushi ta faɗi cikin zuciya tana hawaye.

"Ashe hake kike ji Mama? Ashe haka duk wata uwa take ji a kan ƴaƴanta? Ban san mai yasa ba kwanakin nan duk na kalle ki ƴata sai inji gabana yana mugun faɗuwa. Na haifeki ba tare da aure ba, na ɓata miki record. Ban taɓa tunanin wannan tabon da na miki zai dame ni ba. Ban taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo in soma nadamar abubuwan da na aikata ba. Ban taɓa zaman mintuna biyar na yi fashin baƙi a kan kalamanki ba ummi na. Ashe gaskiya kike faɗa mini."

Wannan karan hawayenta har sauka suke a wuyan Meema da ke rungume da ita.

A hankali Meema ta ɗago tare da kai hannu tana share hawanyen Laushin tare da faɗin,

"Stop crying mom, everything will be alright. You will get better soon, In Sha Allah!"

Gyaɗa kai Laushin ta yi tare da faɗin, "In Sha Allah, daughter."

Daidai nan Salmanu ɗan daudu ya shigo hannunsa riƙe da plate ɗin sakwara miyan egusi da ya ji stockfish da nama don Salma nice ba daga nan ba wajen girma ko wata macen albarka.

"Uwar Meema kin tashi? Ya jikin na ki? To ga abinci nan da zafinsa ki samu ki ci."

"Nagode, Salma. Kawo Meema ta ci don na san she must be hungry."

"Uwar Meema, ai haƙuri da wannan sunan don Allah. Kira ni da Salmanu ya fi daɗin ji wallahi," Salmanu ɗan daudu ya faɗi.

Laushi bata kula shi ba don she's not in the mood da za ta biye shi a yanzu kam.

"Je ki wanke hannunki ki zo muci abinci," Laushi ta faɗi tana mai miƙar da ita tsaye.

Sauka daga kan gadon ta yi tare da shiga bayi ta wanko hannu sannan ta dawo lokacin Salmanu ya bar ɗakin. A ƙasa ta samu Laushi riƙe da goshi saboda nauyi da kanta da kuma idanunta suka mata.

"Mummy, kan ne?" Meema ta faɗi muryanta na cracking.

Girgiza mata kai ta yi tare da faɗin, "No, am ok. Kawai idanuna ne suka min nauyi."

"Can I feed you, mum?" Meema ta faɗi bayan ta zauna kusa da ita.

Gyaɗa kai Laushi ta yi hawaye na ƙoƙarin zubowa amma sai ta yi saurin shanye su. Hannu Meema ta saka cikin kwanon ta gutsiro sakwaran sannan ta dangwala miya ta kai bakin Laushi. Buɗe baki ta yi ita kuma ta saka mata.

Laushi can't hold it bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba wanda lokaci guda jijiyoyin kanta ya harba. Hannu ta saka ta riƙe kan da ƙarfi tana kuka.

Da gudu Meeman ta fita daga ɗakin ta kira Ladi Katifa suka dawo ɗakin tare.

"Zeenah, kan ne? Bari na ɗauko miki magungunar ki." Ta ƙarisa maganar tare da fita da sauri.

Meema kuma zama ta yi gafenta tare da sauke hannunta ɗaya ta riƙe gam a hannunta. Jim kaɗan Ladi ta shigo da magungunan da kuma bottle water. Sai d ta ɓare tukun ta miƙawa Laushi ita kuma ta karɓa ta watsa a baki tare da binsa da ruwan goran. Zuwa can ta jinginar da kanta jikin gado.

Abincin da bata iya cinsa kenan ba, haka Meema don ita ma kasa cin sakwarar ta yi sanida Laushi bata ci ba. Da kyar dai ta sha custard ɗin da Ladi ta haɗa mata shima cokali biyar kawai ta yi.

Sati ɗaya kawai Laushi ta yi wani irin zabgewa. Ƙasusuwa sun mata sarƙa a wuya. Ta yi bye-bye da farin ciki da natsuwa. Cuta da tashin hankali ya yi mata knocking kuma ba tare da shiri ba ta buɗe ƙofa. Ɗaiɗakun rana ne Laushi ba ta azababben ciwon kan nan, bata taɓa samun natsuwa har sai ta sha pills ɗin da Sabo da Kaza ya bada a riƙa bata. Meema ma duk ta zabge saboda rashin lafiyar mummynta.

Sabo da Kaza kuwa ko a waya bai waiwaye su ba har sai da kwana bakwai ta cika sannan ya turo Yahuza ya ɗauki Meema a mota wata ranar Litinin da sassafe. Wani makaranta suka nufa a an cikin garin Lagos mai matuƙar kyau da tsaruwa kamar ba a ƙasar Nigeria ba. A nan aka sake enrolling ɗinta a primary 5. Kuma kullum Yahuza ke zuwa ya kai ta sannan ya dawo da ita.

Da farin ciki Meema ke faɗawa Laushi irin makarantar da aka kai ta, ita dai Laushi murmushi kawai take yi ganin Meema cikin walwalar da tun da ta fara ciwo bata yi shi ba.

Haka Meema ta kwashi sati biyu tana zuwa makaranta, sai dai ita bayan an tashi, Yahuza yana kai ta wata makaranta da ake koya mata yaren da bata taɓa jin irinsa ba a rayuwarta. Tun bata ƙaunar yaren kuma yana mata wahala har ta saba da shi don wata rana idan ta tashi da safe za ta gaida su Laushin da yaren ta ke gaida su.

Makamai kuwa ba a daina jibge su ba. Sai dai bayan kwana biyu ko uku, amintaccen Sabo da Kaza, wato Yahuza yana kawo wasu su kwashe bayan sun gama ciniki sun bada kuɗin.

*_Abuja_*

Daga Kaita har Habib babu wanda ke samun cikakken lokacin kansa don Babiyo ya matsa masu namba. Musamman ma Habib da ko ƙofar gate ɗin Arɗo Barkinɗo bai isa ya je ba. Bikinsu saura kwana huɗu rak. Idan kuka ga Habibu sai ya ba ku tausai don ko ta ina zafi ne a wajansa. Ta ɓangaren iyayansa, Baffa Giɗaɗo ko kaɗan bai raga masa kamar yanda Babiyo ya tsauwala masa. Ta wajen mama Halima da ta ɗan sauko ne kawai ya ke ɗan samun sauƙi. Mamiyo kuwa har baƙaƙen magana take faɗa masa idan ya je gaishe ta. Kai tsaye take zagin mahaifinsa tana aibata shi da mugayan suna.

Jawaad kuwa, Mahaifiyarsa ce da kanta ta zaɓa masa Khairat a matsayin matar da zai aura, kuma sosai Babiyo ya ji daɗin zaɓen don Khairat tana ɗaya daga cikin jikokinsa da yake ji da su.

Ana idar da sallar magrib a babban masallacin Juma'a na Arɗo Barkinɗo dake cikin estate ɗin, Habib ya yi yunƙurawa zai miƙewa, sai dai Jawaad ya yi saurin cafkar hannunsa tare da girgiza masa kai alamar kar ya tashi duk da kuwa ya ji zafin sosai a jikin Habibun lokacin da ya riƙe hannunsa. Da idanu ya yi masa nuni da Babiyo da ke ɗuke cikin wata arniyar dakakkiyar farar shadda ƙal ka ce yau take sallah.

"Zazzaɓi mai zafi nake ji sosai ɗan uwana. Kaina sara min yake kamar zai tsage ya rabe gida biyu," Habib ya faɗi ƙasa-ƙasa.

Shima ƙasa-ƙasa ya ce, "Babiyo ba zai maka wannan uzurin ba. Ganin kawai zai yi ka karya dokansa da gangan. Ka riga kasan ba ka da damar barin cikin masallacin nan har sai an kammala karatu an yi sallar Isha'i tukun."

"Zan iya kifewa in suma idan har ba gani na na yi a kan gado lulluɓe da bargo ba. Sanyin AC ya min yawa. Har cikin ƙashina nake jinsa," Habibu ya kuma faɗi.

Jinjina kai Jawaad ya yi tare da sakin hannunsa sannan ya ce, "Mu fita tare idan ya so sai a hukunta mu duka mu biyun."

Girgiza kai Habibu ya yi tare da faɗin, "Ba za ai haka ba. Idan kai hakan ka san wa za ka jawo wa hukuncin."

"Na sani muje kawai!" Jawaad ya faɗi yana ƙoƙarin miƙewa, sai dai daskarewa waje ɗaya ya yi sakamakon abunda ya ji cikin kunnuwansa wanda ya saka shi sakin baki da hanci yana kallon Babiyo da ke nesa da su.

"A soma siga!" Shine abunda ya faɗi kuma gaba ɗaya masallaci ya ɗauka saboda amsa kuwwar da ke jikin rigarsa kasancewar shi ke karatun bayan magrib ɗin.

"Shi ɗan uwana abunda kunnuwana suka jiye min daga bakin Babiyo haka ne?" Habibu ya faɗi bayan ya kamo hannun Jawaad.

Jawaad bai kai ga yi masa ƙarin bayani ba suka ji maganar Baffa Abubakar ɗan babban wan Babiyo na faɗin, "Jama'a ku shida Ni Abubakar Sadiq Arɗo na ba Huzaifa Giɗaɗo Arɗo auren Mardiya Idirisa Arɗo, akan sadaki naira dubu ɗari."

Da mugun sauri Habib da kansa ya kuma ɗaurewa ya kalli Jawaad tare da faɗin, "Ban fahimta ba ɗan uwana. Baffana kuma Babiyo ya ke ƙoƙarin ɗaura masa aure na biyu?"

"Ni Saifullahi Modibbo Arɗo, na amshi auren ɗan uwana Huzaifa Giɗaɗo Arɗo, jama'a ku shaida."

Wannan shine maganar da ta amsawa Habibu tambayarsa wanda ya saka kansa ya yi mugun ɗaurewa. Ba'a jima ba aka shiga ɗaura auren Jawaad da Khairat, suma ana kammala na su aka ɗaura na Habib da Amatul kareem.

Gaba ɗaya masallacin babu wanda bai ji shock ɗin auren Baffa Giɗaɗo da Mardiya wacce ita ma ƴar uwarsa ce kamar yadda mama Halima take ƴar uwarsa. Sai dai babu wanda ya isa ya tambayi dalili ko ya nuna rashin jin daɗin haka a fuska balle kuma ya furta.

Babiyo kuwa sai wani ƙasaita ya ke yana kallo kowa ɗaiɗai. Duk wanda aka bawa goro da sweet sai ya ƙare masa kallo domin ganin yanayinsa.

#Laushi #Meema #Babiyo #Jawaad #Habib #Baffa Giɗaɗo #Sabo da Kaza #My Destiny #Matar Sayyadee

*** [2/29, 6:47 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`