My Destiny (Ƙaddarata)

Page 31

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya*

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Baffa Giɗaɗo babu abunda yake yi sai uban zufa duk da AC dake cikin masallacin. Amma kuma bakinsa a washe yake sai murmushin yaƙe yake ci.

Mitsi-mitsi da idanu Babiyo ya yi yana kallon Jawaad da aka miƙawa goro da sweet yaƙi amsa hankalinsa gaba ɗaya yana wajen Habibu da ke ƙoƙarin suma shi kuma sai goga hannunsa ya ke a tafin hannun Habib ɗin.

"Ka dawo cikin hayyacinka ɗan uwana. Daure har a bamu damar tashi, idanun Babiyo a kanmu da iyayanmu ya ke."

"Yau babu karatu sai jibi idan Allah ya ara mana rai da lafiya," Babiyo ya faɗi cike da ƙasaitarsa.

Bayan ƴan wasu mintuna, ladan ya kwaɗa kiran sallah, Babiyo ya miƙe ya ja su sallar Isha'i. Ta baya idan ba wai mugun sani kai wa Babiyo ba, za ka ɗauka ɗan shekaru talatin ne. Domin akwai ƙarfi a jikinsa har yanzu. Jikinsa a miƙe ya ke kuma kyam-kyam irin dai jikin Fulani. Ba ƙaramin mai juriya daga wajen estate ya ke iya jurewa ba duk lokacin da Babiyo zai ja sallah, don raka'a ɗaya kawai zai iya ɗaukar mintuna biyar ko shidda. Daki-daki ya ke karatun sallah kuma ba da sauri ba, wani lokacin idan ya karanta fatiha sai ya janyo Rahaman ko waƙi'a kuma sai ya dire ta.

A daddafe aka ida sallah da Habibu, don jikin nasa wani irin rurewa ya kuma yi.

Babiyo ne ya fara ficewa daga masallacin. Jawaad na ganin haka ya miƙe tare da ɗaga ɗan uwansa ya saƙala hannunsa a kafaɗansa ya fice da shi. Ta gaban Babiyo ya wuye ba tare da ya kalli inda ya ke ba. Wani irin girgiza kai Babiyon ya yi yana sakin malalacin murmushi tare da bin su da idanu.

Iyayan ma gaba ɗaya suka fito daga masallacin kowa kunshe da magana a cikinsa amma kowanne na tsoron bayyanawa. Abunda ya ba su mamaki kuma shine ganin Babiyo tsaye jikin motarsa. Da sauri suka nufe shi tare da durƙusawa sannan suka haɗa baki wajen faɗin,

"Allah ya ƙara maka lafiya mai amfani, Babiyo. Shin akwai wani abu da kake son umartan mu dashi ne? Magana ɗaya ta wadatar, Babiyo."

Wani irin murmushin jin daɗin yanda ƴaƴan nasa ke masa biyayya ya yi sannan ya yi gyaran murya tare da furta, "Duk ku same ni a gida, kai kuma Giɗaɗo ka taho da Halima. Amma kar ka saka a ranka na janye hukuncina a gare ka ne, a'a sam. Na yau ne kawai. Kuma ka yi min submitting documents ɗin wajenka zan yi signing in tura prensident office," yana gama faɗin haka ya shiga bayan motar da Hafiz drivernsa kuma informer ɗinsa ya buɗe masa.

Wannan ya juya ya kalli wannan, haka ya kasance tsakanin su kamun suka samu ƙarfin guiwar buɗe motocinsu suka shiga.

"Menene sakamakon binciken da na saka kai min?" Babiyo da ke riƙe da jarida a hannunsa ya faɗi.

"Idan ka bani dama, zan sauka gefen hanya sai in yi maka bayani dalla-dalla," cike da ƙanƙan da kai Hafiz driver/Informer ya faɗi maganar.

Gyaran muryan da Babiyon ya yi ne ya fahimtar da shi ya bashi damar yin hakan. Parking ya yi sosai sannan ya juyo gaba ɗaya tare da faɗin, "Ranka ya daɗe, duk na yi abunda ka umarce ni. Sai dai iya abunda na faɗa maka kwanaki, shi na sake zuwa dashi sai ɗan ƙarin bayanin kaɗan,"

Ba tare da Babiyo ya sauke jaridar ba ya ce, "Ina sauraran ka, ka tafi kan maganar kai tsaye. Ka fi kowa sanin ban son kwana-kwana da rashin gaskiya."

"Ranka ya daɗe na je har garin Bauchin na yi bincike. Sunan mahaifinta Ayuwa, mahaifiyar kuma Umaima. Mutanan arziki ne daga uwar har uban. Sai dai uban yana da riƙaƙƙen zuciyar da bai ragawa a cikin gidansa. Wasu sun ce hatta matar bata jin daɗin zama da shi. Ƴaƴansa babu wanda ya gagaresa sai guda ɗaya tal, Zeenatu wacce ta ɗauko masa cikin shege har hakan ya yi sanadin korar karen da yayi mata, wasu sun ce tsirara haihuwar uwa ya turo ta waje yana bugu yana tsine mata albarka. Ita kuma ƴar ta yi alwashin dagargaza sunansa a cikin garin Bauchi, kuma hakan ne ya faru don ka'in da na'in ta faɗa harkar karuwanci a nan Bauchin wanda silan haka ya saka sunan Ayuba ya ɓaci hatta sallah aka dai na binsa. Bayan tsayin shekaru ita yarinyar ta dawo da tsohon ciki domin sace sarƙar zinarin da ya saya don aje ƙaddara, tun a hanya ya samu labarin dawowarta shi kuma yana shiga gidan ya nufi madafi ya ɗauko wuƙa domin kashe ƴar, sai dai wajen kokuwa kwatar kai ita ƴar ta soki uban a ciki ta gudu ta tafi Lagos ita da ƙawarta mai suna Rukayyah wacce aka fi sani da Ladi Katifa. Sai dai a binkicena na biyu da na kuma yi, na samu labarin uban bai mutu ba, Allah ya yi da saurin shan ruwansa a duniya. Sai dai har yanzu a kwai wannan burin kashe ƴarsa a zuciyarsa. Ita kuma uwar gaba ɗaya ganinta ya ɗauke."

Wani two minutes silent Babiyo ya yi kamun ya rufe jaridar hannunsa ya ajiye a gefe tare da yin gyaran murya sannan ya ce, "Kai ka samu ganin uban yarinyar?"

Girgiza kai Hafiz ya yi tare da faɗin, "A'a ranka shi daɗe. Ban samu ganinsa ba domin baka ba ni wannan umarnin ba. Kuma shi malam Ayuban tun da wannan incident ɗin ya faru ya yi sallama da fitowa waje, kuma ya ma samu matsala a ƙafarsa ta hagu sakamakon hatsarin da ya yi bayan warkewarsa daga sukan da yar ta masa a ciki. Kariyar cinya ce, da sanda ya ke tafiya har yanzu."

Gyaɗa kai Babiyo ya yi tare da faɗin, "To ya zancen yarinyar da ta haifa? Ka tabbata dai ba ta da alaƙa da cikin gidan ko? Bi ma'ana ba jinin Habibu ba ce!"

"A'a sam ba ƴarsa ba ce, don ko da ta haifi yarinyar a gidan karuwa, basu haɗu da Habibun ba. Kwakwata haɗuwar su bata wuce ta wata biyu zuwa uku ba idan ma ya kai. Ita kuma ƴar shekarunta goma cif yanzu."

Jim Babiyo ya yi na wasu mintuna kamun ya ce, "Tada mota! Ni na san mai zan yi saboda kar wannan karuwar yarinyar ta kuma shiga rayuwar zuri'a ta."

Mintuna kaɗan ya kawo su cikin mansion ɗin Babiyo wanda tuni ƴaƴansa sun halarta don ga motocinsu nan a fake a harabar gidan. Da sauri Hafiz ya fito daga cikin mota ya buɗewa Babiyo ƙofa sannan ya koma gefe ya tsaya.

Taƙamar ce ta tashi, domin sai da ya kwashi mintuna biyar kamun ya fito da farar ƙafarsa ɗaya ya ajiye, nan ma sai da ya ɗibi wasu sakwanni sannan ya ziro ɗayar tare da fitowa daga ciki riƙe da kyakkyawar sandarsa wai launin ruwan gold. Cikin taƙama kamar baza a taka ƙasa ba ya nufi enterance ɗin parloun. Fuskansa ita ce securityn ɗakin, shiyasa yana kallon ƙofar ta buɗe. Wani wahaukacin parlourn mai ɗauke da fararan set ɗin leather seat mai kyau da santsi. Throw pillows ɗin kujerun kuma kalar green. Hatta labule kalar green and white ne kasancewar kalar da Babiyo yafi so kenan.

Mamiyo ce haƙimce a kan 2seater, wata yarinya fara kyakkyawa wacce ta kasance ƴar wajen ɗanta na uku tana mammatsa mata ƙafafu. Ganin shigowar Babiyo sai ta gaida shi cike da girmamawa tare da ficewa daga ɗakin.

Mamiyo da kanta ta miƙe ta nufi ƙaramin fridge ɗin da ke ɗakin ta ɗauko masa damammiyar furarsa da ta dama masa kasancewar kullum sai ya sha da dare kamun ya kwanta.

"Ki bar wannan furar sai zuwa anjima tukun, yanzu fita za muyi tare zan yi magana da yaran can. Hafiz zai shigo miki da goro da sweet na ɗaurin auren," faɗin Babiyo.

Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Mamiyo har sai da hakan ya bayyana a fuskanta, "Ma sha Allah! Har da shi Giɗaɗon an ɗaura aurensa?" Ta jefa masa tambaya.

"Eh, na ɗaura aurensa da ƴar wajen Idirisa, Mardiya!"

Ɗif farin cikin da ke kwance a fuskan Mamiyo ya gushe har ludayin hannunta yana ƙoƙarin faɗi ƙasa.

"Mardiya kuma Arɗo? Ina ce Karime muka yi da kai," Faɗin Mamiyo.

Miƙewa tsaye Babiyo ya yi tare da faɗin, "Da Mardiya da Karime duk ɗaya ne a waje na. Ki same ni a parlourn meeting yanzu!" Yana gama faɗin haka ya nufi wani ƙofa da zai kai shi har ɗakin da yake kamar fada.

Mamiyo bata iya cire idanunta a fuskan Babiyo ba har sai da ya fice daga parlourn wanda ko waigawa bai yi ba.

Wani irin duka ta kaiwa bango ranta na wani irin soyuwa tare da nufa fuuuu cikin wani ɗaki bayan ta yi banging ƙofar.

"Tun da yarintata ban yarda mulki da taƙamata ta faɗi ba, yanzu da na tsufa ma ba zan taɓa bari hakan ta faru ba!" Mamiyo ta faɗi tana zagaye ɗakin hannunta cikin ɗayan hannun tana naushi.

Waya ta ɗaga ta kira wani Number, ringing biyu daga ɗayan ɓangaren aka ɗaga cike da girmamawa.

"Hafizu, mai Babiyo ya ke shiryawa a ƙasa wanda ban da masaniya a kansa? Menene dalilinsa na bawa Giɗaɗo auren Mardiya a yau ɗin nan? Na san ka san komai, kar ka yi ƙoƙarin cin amanata domin ni na kawo ka cikin gidan nan, idan kuma ka yi kuskuran juya min baya, ba cikin gidan nan kawai za ka bari ba, duniya gaba ɗaya za ka bari!"

"Hajiya kin fi kowa sanin ba Babiyo na ke wa aiki ba, ke na ke wa aiki. Akwai abunda ya kamata ki sani wanda ni ma a cikin kwanaki uku rak na samu labarin kuma ba daga bakin Babiyo ba, daga wata majiya mai ƙarfi na ji. Akwai gagarumin matsala. Na farko dai, naga Ɓaleri ganin idanuna a cikin wannan estate na Arɗo Barkinɗo, na biyu kuma wanda ya kamata ki sani wanda ya fi na farko ɗaga hankali shine; Babiyo yana shirin fitar da babban ɗan Baffa Belɗo, Abdul Hameed matsayin ɗan takararsa neman kujeran minista na nan Abuja, kuma kin san duk wanda Babiyo ya ɗagawa hannu kamar ya ci zaɓe ya gama ko da kuwa kujerar shugaban ƙasa ce. Kuma akwai yiwuwar Baffa Belɗo ya dawo cikin Arɗo Barkinɗo saboda wannan abu, kuma kin san dawowar Baffa Belɗo kamar dawowar Ɓaleri ne. Kuma dawowar Ɓaleri daidai yake da tonuwar asirinki a idanun Babiyo da ɗaukacin jama'ar Arɗo Barkinɗo."

Wani tsawa da ya kusa toshe masarrafar jin Hafiz Mamiyo ta yi tare da faɗin, "Ƙarya ne wannan! Ɓaleri ya mutu shi da iyalansa. Da hannunka ka cire birkin motarsu, ko ba haka bane?"

"Kwarai da hannuna na cire, amma ina mai tabbatar miki na ga Baffa Ɓaleri cikin Arɗo Barkinɗo. Ya rufe fuskansa da rawani, amma ni na gane sa sosai don ko bargo ya saka ya rufe jikinsa a irin farin sanin da na masa, sai na gane shi. Wallahi shine, kuma iska ta ɗaga gefen rawanin na kuma hangi fuskansa. Sai dai abunda ya ban mamaki da ɗaure min kai, mai ya kawo shi cikin estate ɗin nan, kuma ya a kai bai mutu ba. A gaban idanuna motarsu ta kama da wuta wallahi."

"Hafizu, kar kai kuskuren wasa da wuta za ta ƙona ka wallahi! Amana ta ka ci ko?" Da ƙarfi ta faɗi hakan.

"Haba Hajiya, da amanarki na ci tsayin shekaru ashirin da bakwai ai ya ci ki gaskiya ta fito. Abunda ya faru da Belɗo ma bai fito ba, sai na Ɓaleri da ya yi shekaru ashirin da shida zuwa bakwai.

Mamiyo ba ta san ta silale ta zauna a kan gado saboda tashin hankali abubuwan biyu da Hafizu ya faɗa mata.

"Hafizu ka tabbata Babiyo ya tsayar da ɗan takara? Kuma ka tabbata Abdul Hameed Babiyo ya ke shirin fitarwa? Yaushe Abdul Hameed ɗin ya shigo ƙasan ban da labari?" Mamiyo ta faɗi.

"Ki yi haƙuri Mamiyo da rashin samun labarin nan da ban yi ba tuntuni. Wallahi a wasu majiyar ma cewa suke Abdul Hameed ɗin ya shigo ƙasar sati biyu yanzu, amma yana wani ɓoyayyan waje da Babiyo ne kawai ya sani. Don har Babiyon ya kai shi Abdul Hameed ɗin wajen wasu manyan jam'iyya domin ya san su, suma su san shi. Kuma shi ya ya ba Babiyo option akan idan yana son ya yi siyasa to dole sai Baffa Belɗon ya dawo cikin Arɗo Barkinɗo, kuma Babiyo ya amince da hakan."

Ƙit Mamiyo ta yanke wayar tare da fashewa da kuka mai cin rai. "Kenan shekaru sittin ɗin da na kwashe ina gina kaina da ƴaƴana zai tafi a banza? Hakan ba zai taɓa yuwuwa ba! Idan kuma aka matsa, to wallahi za ayi kukan mutuwa a cikin Arɗo Barkinɗo!"

🤔Ashe dai ba mutum ɗaya aka kora a cikin Barkinɗo ba! Ikon Allah sai kallo. Amma dai wannan Mamiyooooooooo akwai ƴal..........🤐

To wai readers ku taya ni tunani mana, wanene Belɗo kuma wanene Ɓaleri??????

#Mamiyo #Babiyo #Ɓaleri #Belɗo #Abdul Hameed #Habib #Jawaad #Laushi #Meema #Hafiz Munafiki #Betrayer #Hatred #Ƙaddarata #Matar SAYYADEE

*** 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`