Page 32
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya*
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
Sai da ta saisaita kanta sannan ta fito daga ɗakin tana cika da batsewa tare da nufi ƙofar da Babiyo ya bi wanda shine zai sada ta da fadan Babiyon. Da taƙama kuma ba tare da ta kalli kowa ba, kuma hannunta duka a baya ta iso kan kujeran kusa da na Babiyon ta zauna.
Gaba ɗaya suka shiga kawo gaisuwa wajenta, amma ko kallon basu ishe ta ba sai hannu da ta ɗaga masu kawai.
"Mai ya daɗar da ke har haka kika bar ni zaune ina jiran ki kamar ɗanki?" Cike da ƙasaita ya faɗi hakan wanda kuma ita kaɗai ta ji abunda ya ce.
"Ai min afuwa, Arɗo. Na zaga ne shiyasa na jima ban iso nan ɗin ba," Mamiyo ta faɗi.
Ba tare da ya kuma ce mata ƙala ba ya mayar da dubansa ga ƴaƴa da wasu daga cikin jikokinta ba ya furta, "A buɗe taro da addu'a."
Bayan doguwar addu'a, Babiyo ya ce, "Alhamdulillah! Dukkan godiya su tabbata ga Allah Ubangiji da ya ara mana rai muka shaida waɗannan aure da aka ƙulla a yau ashirin ga watan Nuwamba dubu biyu da takwas. Allah ya sa albarka a cikin zaman su ya kawo masu zuri'a ɗayyiba ya kuma kau da fitina da shaiɗan la'ananne."
Gaba ɗaya suka amsa da ameen ban da Mamiyo da ta ce ciki-ciki, "Allah ya wargaza auren."
"Abu na biyu da zan ce a wannan zama shine; kowa dai ya san an ɗaura auren Giɗaɗo da ƴar wajen ɗan uwana Idirisa wanda ni ne na yi zaɓin da kaina!"
Wani irin bugawa zuciyar mama Halima ya yi alokaci guda tare da saurin ɗaga idanu ta kalli Baffa Giɗaɗo wanda kansa ke a ƙasa. Kuka take san fashewa da shi amma ta daure kada hakan ya zame mata magana ita da ƴaƴanta har ƙarshen rayuwarsu.
"Na ɗaura auren ne a bisa dalilin rashin kyakkyawa da ingantacciyar tarbiyar da ita uwar gidansa, Halima ta kasa baiwa ƴaƴanta. Abun ya mini ciwo kwarai da gaske! Wai ace kamar ni Arɗo a cikin zuri'ata za a samu fasiƙin da ke yawon banza yana zina da matan banza ba wai don ya rasa arzikin ko kuma matan da zai aura ba. A saboda wannan dalilin na wanke ƴa a cikin ƴaƴan ƴan uwana wacce na amince da tarbiyarta na ba shi Giɗaɗon domin ta saka shi a miƙaƙƙen hanya shi da ƴaƴansa," ya ƙarisa maganar yana kallon Mama Halima da ta mayar da idanunta ƙasa tana ta danne kukan da ke ƙoƙarin kufce mata.
"Ke, Halima! Ga yar uwarki nan ki riƙe ta da hannu biyu. Ke ce babba kuma uwar gida, don haka ki kama girmanki ki kuma riƙe mutuncinki, don ki ka saki na ji wani ɓatanci daga wajenki, baza ki sameni da hukunci mai sauƙi ba."
"In Sha Allah za ka same ni mai biyayya ga umarninka, Babiyo," faɗin Mama Halima muryanta na rawa.
"Ma sha Allah! Sai abu na gaba, Ina son shaida muku na fidda ɗan takara daga cikin jikokina a wannan karan. Don tafiyar ta matashi in Sha Allah, don haka na duba cikin jikokina masu jin magana da gudun ɓacin raina na zaɓo Abdul Hameed na tsayar matsayin ɗan takarar Ministan Abuja. Sannan kuma mahaifinsa da mahaifiyarsa, na janye maganata a gare su, na dawo da su cikakku kuma halastattun zuri'ar Arɗo Barkinɗo."
Wani irin ɗif ɗakin ya yi na wasu mintuna biyar. Masu shararo zufa irinsu Hamma Tukur, Hamma Lawal, Hamma Mahmud da kuma Hamma Jibrila sai hannu suke kaiwa kan goshi suna sharcewa.
Da gefen idanu Jawaad da yazo taron da kyar ya ke kallonsu yana wani murmushin gefen baki don sosai ya ji daɗin zaɓin Babiyon.
Mamiyo kuwa, fararan kwayun idanunta sai yawo suke a kan ƴaƴan nata da ke sharan zufa. Ranta wani irin sosuwa ya ke yi kamar ana caka mata mashi a ƙahon zuciyarta.
"Jawaad da Habibu su sani, rana ita yau za su ɗaga zuwa ƙasashen da na umarce su da su tafi, amma gobe kowanne a cikinsu zai tare da matarsa."
Sai a wannan lokacin Mamiyo ta ɗago tare da faɗin, "Ina fatan babu wacce ta mance da al'adarmu ta Fulani a cikin ku? Don haka za mu rataya kwarya a ƙofar ɗakin ko wani ango, da sassafe kuma za mu tura domin ganin sakamako. Idan har kwarya tana nan yanda take a rataye a kowani gidan ango da aka rataya, hakan na nufin amarya kamilalla ce kuma jinin Arɗo Barkinɗo, bima'ana cikakkiyar mace wacce bata taɓa aikata mafi munin zunubi a wajen Allah da kuma cikin wannan zuri'ar ba, wato Zina! Idan kuma mun samu kwarya a fashe, to hakan na nufin yarinya ba ta kai budurcinta gidan miji ba!"
"A rufe taro da addu'a, kuma a saka Abdul Hameed a cikin addu'a a kan Allah ya bashi nasara!" Yana gama faɗin haka ya rufe idanu.
Bayan doguwar addu'a, Babiyo ya tashi ba tare da ya yiwa inda Mamiyo ta ke kallo ɗaya ba ya wuce ko albarkan da ya saba yiwa ƴaƴan na sa bai yi ba. Ita kuwa taƙama da baƙin ciki ya hana ta tashi ta shige ciki, kuma waɗanda suke ciki ba su isa su fita ba tare da Mamiyo ta bar ɗakin ba.
Haka su kai ta zama jugum suna jiran Mamiyo ta tashi. Jawaad kuwa ganin Mamiyo ta ƙi tashi, ga Habibu da ke ta makyarkyatar sanyi saboda zazzaɓin da ya saka shi a gaba, kawai gani su kai ya miƙe tare da ɗago Habibu da jikinsa ya saki gaba ɗaya ya ratayo shi suka fice daga ɗakin. Da idanu Mamiyo ta bi Jawaad da shi tana jin matsanaicin ɓacin rai da takaicin abunda ya aikata yanzu na nuna rashin girmama a gare ta.
Baffan Jawaad kuwa wani harara ya ke bin Jawaad ɗin da shi kamar ya fizgosa ya dawo da shi baya ganin yana son jawo masa jidali. Shi kuwa Jawaad babu wanda ya kalla a cikinsu har ya fice daga ɗakin riƙe da Habibu.
Dawo da kallonta izuwa Mahaifin Habibu da Jawaad ta yi tare da faɗin, "Kuna kallon rashin tarbiyar da ƴaƴan ku suka nuna a gare ni, amma kuka kasa magana saboda ba ni ce na haife ku ba ko? To ni zaman mutunci da amana na yi da iyayanku!"
A tare Baffa Giɗaɗo da Baffa Bobbo suka zube a gaban Mamiyo tare da faɗin, "Ki mana afuwa Mamiyo! Ke ɗin uwa ce a gare mu kamar iyayan da suka haife mu. Wallahi ko cikin mafarki ba mu isa mu bawa ƴaƴanmu damar raina ki ba, yanzu haka ma gudun ɓacin ranki ne ya hana mu ɗaukar mataki."
Baki ta taɓe tare da miƙewa bayan ta kalli ƴaƴanta na cikinta wanda ke nuni da tana buƙatar ganinsu, sannan ta shige ciki.
Jawaad bai tsaya ko ina ba sai asibitin Arɗo Barkinɗo. Nan da nan aka amshi Habibu tare da bashi gado sannan aka ɗaura masa ƙarin ruwa a hannun bayan sun yi masa allurar bacci.
Mama Halima kuwa, ba ta yarda ta haɗa hanya da Baffa Giɗaɗo ba, a ƙafa ta riƙa tafiya duk da ta san akwai nisa sosai daga Arɗo Barkinɗo Street zuwa Giɗaɗo street. Gashi kuma har yanzu jikin na ta ba wani warwarewa ya yi sosai ba.
Horn ta ji ana dannawa amma ta yi biris duk da kuwa ta san mai horn ɗin. Parking ya yi tare da fitowa ya nufe ta da sauri tare da shan gabanta ya shiga faɗin,
"Haba Halima! Haba maman Habibu!! Zafi biyu za ki ƙara min?" Ya faɗi a marairaice.
Wani irin baƙin ciki ne ya turniƙeta, ta buɗe baki za ta yi magana kenan ta fashe da kuka saboda yanda zuciyarta ke mata azabar zafi.
Hannunta ya riƙe tare da faɗin, "Wallahi, tallahi billahil azim ban san komai ba game da wannan auren. Ji kawai na yi ana sigar ɗaurin auren. Ki haƙuri don girma Allah ki shigo mota muje gida kin san fa ba ki da isasshen lafiya."
A zafafe ta ce, "Ni fa na zo ƙarshe, baffan Habibu! Wannan wani irin mulkin kama karya ne haka? Mu bamu tsira ba, ƴaƴanmu basu tsira ba, haba! To ka sani, idan ɗana ya mutu kai, mahaifinka da matarsa ne sila kuma ba zan taɓa yafe maku ba!"
Tass! ya wanke fuskanta da mari sannan cikin tsawa da ɓacin rai ya shiga faɗin, "Baki da hankali ne? Ko don kin ga ina lallaɓa ki? Don ke kaɗai Allah ya halicce ne? Na faɗa miki wannan auren ban san da shi ba, kuma ke ma kin san ko giyan wake nake sha ban isa na bijirewa umarnin Babiyo ba! Da bakinki yau Halima kike zagin Babiyo? Ai idan da mutunci ko da ace Babiyo ba wan mahaifinki bane, tunda ya haife ni, Ni kuma na auro ki kya girmama shi matsayinsa na suruki a gare ki. Balle kuma Babiyo shine wanda ya saki nono ya barwa mahaifinki."
"Shekarun mu talatin da biyar da aure, ko baƙar magana mai zafi bata taɓa shiga tsakanin mu ba duk da kuwa aurena da kai auren haɗi ne, amma yau da girmana a kan titi ka ɗaga yatsunka ka sauke su a fuskanta saboda na faɗa maka gaskiya! To ka sani ka kakkaɓe aurenka a yau ɗin nan. Kuma ba zan daina faɗi ba, idan ɗana ya mutu sai na yi Shari'a da Arɗo!" Tana gama faɗin haka ta yi gaba.
"Halima! Halima!! Ke, Halima!!!" Haka ya riƙa faɗi yana bin ta a baya hankali a mugun tashe don ya san idan ya yi gigi Halima ta tafi, ba lallai Babiyo ya bari ta dawo ba.
A hankali ya ke tafiya a cikin motarsa ya sauraren ƙira'ar sudais da ya zame masa jinin jiki wajen sauraro. Tun daga nesa ya hangi Baffa Giɗaɗo da mama Halima da ke magana wanda duk wanda ya kalla ya san ba lafiya ba. Kasancewar akwai haske tarwai a estate ɗin kamar rana, shi yasa kallo ɗaya ya gane su.
Parking ya yi ganin Mama Halima ta yi zuciya tana tafiya, shi kuma Baffa Giɗaɗo yana bin ta a baya yana kira. Da sauri ya fito daga cikin motar ya sha gaban mama Halima tare da faɗin,
"Barka da dare mama," ya faɗi maganar ne tare da ɗan risinawa daidai ƙarisowar Baffa Giɗaɗo nan ma ya kuma gaida shi.
"Abdul Hameed!" Mama Halima ta faɗi kamun ta fashe da kuwa mai ƙarfi? "Ina Nenne? Ina Hamma Belɗo? Ina su Aysha, Saudat, Rahma, Ramadan da Shu'aib? Kai ni wajen Nenne na Abdul Hameed," kuka sosai ta ke tare da riƙe hannunsa.
Kyafta masa idanu Baffa Giɗaɗo ya yi alama ya saka ta a cikin motar ya kai ta gida.
Hannunta Abdul Hameed ɗin ya kama tare saka ta cikin mota sannan ya rufe tare da komawa kusa da Baffa Giɗaɗo ya ce, "Gida zan kai ta ko can wajen Nenne?"
"No, Kar ka kai ta wajen Nenne hakan zai iya janyowa mu fuskanci hukunci wajen Babiyo don bai bada wannan umarnin ba. Kai mata dabara kawai ku je can gidana," Baffa Giɗaɗo ya faɗi.
Juyawa Abdul Hameed ya yi bayan ya amsa masa tare da buɗe motar ya shiga ciki.
_Don Allah ku yi haƙuri da wannan ni kai na ba nan na so tsayawa ba, amma gobe za ku samu mai tsayi._
#Abdul Hameed #Jawaad #Habib #Babiyo #Mamiyo #Election #Mamiyo's children #Mama Halima #Ƙaddarata #Matar Sayyadee
*** 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`