Page 33
Baffa Giɗaɗo sai da ya ga sun ɗan yi nisa sannan ya juyo wajen motarsa ya shiga tare da kunnawa ya bi bayansu.
A cikin mota babu abunda mama Halima ke yi sai kuka, shi kuwa Abdul Hameed gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi saboda a duniya ya tsani kukan mace.
"Mama don girman Allah ki bar kukan nan, kin ji? Bari mu isa gida sai mu yi magana," Abdul Hameed ɗin ya faɗi bayan ya juyo ya kalleta kaɗan.
"Wani gida za ka kai ni? Idan ba wajen ƴar uwata ba ka fitar dani daga Arɗo Barkinɗo yanzun nan!" Ta ƙirisa maganar a hassale.
Murmushin gefen baki ya yi tare da faɗin, "Mama kina da inda yafi Arɗo Barkinɗon ne a wajen?"
"Zan ci mutuncin ka fa, Abdul Hameed. Idan ban da kowa wajen Arɗo Barkinɗo, ai ina da ƴan uwan uwa a Yola ko!"
"Kuma Mama har kike tunanin ƴan Yola za su baki shelter ba tare da umarnin Babiyo ba? Kin sa da say ɗinsa suke amfani. Shi ɗin tamkar sarkinsu ne. Ki haƙuri Mama don Allah. Ke ɗin mai haƙuri ce tun fil zal, don Allah kar ki canza," Abdul Hameed ya faɗi daidai lokacin da ya karya kwanar Giɗaɗo street.
"Wallahi Abdul Hameed, Babiyo duk ya canza. Duk da tun fil azal shi mutum ne mai zafi da kuma bada umarni mai tsanani, amma yanzu komai ya ninku kuma babu sila kamar Mamiyo. Wallahi matar nan idan bata tuba Fir'auna na samanta," faɗin mama Halima tana share hawayen da ya silalo mata.
Abdul Hameed bai ce komai ba, domin shi ne mutum na farko a duniya da zai bada labarin mugun hali da makircin Mamiyo.
Sai da ya daidaita parking sannan ya fito ya buɗe mata gidan gaba, tana ziro ƙafa motar Baffa Giɗaɗo na shigowa. Hamdala ya yi ganin tana ƙoƙarin fitowa daga mota saboda ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin tana ƙoƙarin barin gidan wanda hakan daidai yake da tsinke igiyar aurenta idan Babiyo ya samu labari. Buɗe murfin mota ya yi shima tare da fitowa ya nufo inda suke.
Mama Halima na ganin haka ta yi saurin cewa Abdul Hameed, "Ka tafi gida kawai, amma ka tabbatar gobe da safe ka shigo nan ka same ni!" Tana gama faɗin haka ta yi gaba da saboda bata san haɗuwa da Baffa Giɗaɗon don tabbas za su iya raba hali har gaban ƴaƴa abunda bai taɓa faruwa ba.
Ganin fuuu ta yi ciki, sai Baffa Giɗaɗo ya dakata kusa da Abdul Hameed tare da faɗin, "Allah ya maka albarka, Abdul Hameed da ka dawo da ƴar uwar mahaifiyarka gida. Ka cece ni kuma ka ceci aurena. Ina Hamma Belɗo da Nennen? Na matuƙar ƙosawa Babiyo ya bamu umarnin ganawa da juna. Na yi kewar ɗan uwana."
Ɗan sunkuyar da kai ya yi tare da faɗin, "Dama tun tuni suna cikin Arɗo Barkinɗo a keɓaɓɓan wajen da shi kaɗai ya san wajen. Ko ni ban san inda suke ba. Sai dai wani lokacin mu kan haɗu da su idan Babiyo ya so, amma sai ya fitar da su daga cikin Arɗo Barkinɗo tukun."
Jinjina kai Baffa Giɗaɗo ya dunga yi yana tunanin dalilin da yasa Babiyo bai yiwa mahaifin Abdul Hameed fata-fata kamar yanda ya yiwa Hamma ɓaleri ba, saboda ya san akwai lokacin da zai zo ya yi amfani da ɗansa wajen harkar siyasarsa shiyasa.
"Ka je gida ka da Babiyo ya samu labarin zuwan ka nan don ni ɗin ma ina cikin hukuncinsa ne. Domin ya ce kar na sake kusantar inda yake har na tsawon shekara guda, sannan ya dakatar dani daga zuwa Arɗo Barkinɗo Company limited na tsawon watanni shidda," Baffa Giɗaɗo ya faɗi.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Baffa, wai ya za muyi da Babiyo ne a kan wannan halin na shi na korar ƴaƴana daga cikin Arɗo Barkinɗo?"
"Sai addu'a da haƙuri tare da kiyayewa kawai! Ka je sai mun ji daga Babiyon, Allah ya tashe mu lafiya," Baffa ya faɗi yana jin ina ma yana da wata hanyar da zai iya daƙile Babiyon daga abunda yake aikawata wanda ya ke cutar da ƴaƴa da kuma wasu daga cikin jikokinsa.
"Sai da safen Baffa," Abdul Hameed ya faɗi jiki a sanyaye tare da juyawa domin nufa wajen motarsa.
Baffa Giɗaɗo yana amsa sai da safen da ya yi masa ya shige cikin ɗaki tare da turo ƙofa.
Babu kowa a cikin parlourn sai tv da ke ƙara kawai. Ƙarasawa wajen TV ya yi tare da kashewa sannan ya nufi ɗakin matarsa. Sai da ya yi sallama sannan ya shiga ciki.
"Baffa, welcome!" Gaba ɗaya ƴaƴansa mata suka faɗi bayan sun miƙe daga zaune a bakin gado kusa da mamansu.
"Welcome, daughters!" Ya faɗi lowering himself a inda Wasila ta tashi.
Gaba ɗaya sai suka fice daga ɗakin tare da turo ƙofar, kuma dama sun shigo ne domin jin abunda ya faru ganin mood ɗin mahaifiyar tasu lokacin da ta shigo. Sai dai ba su samu amsa ba har Baffa Giɗaɗon ya shigo ɗakin.
"Wai fisabilillah, Halima ba za ki min uzuri mu taru mu taushi junanmu ba, Haba Halima! Wallahi kin canza. Ni wannan ba Halimar da na aura shekaru talatin da ɗoriya ba. Na rantse miki da girman ubangijin Musa, Haruna, Nuhu, Yusuf da Muhammad ban san da maganar auren nan ba. Haba! A cikin wannan tashin hankalin da nake ciki har za ki tunanin ina da courage ɗin fuskantar Babiyo da zancen aure? Haba, ki duba mana!"
"Ni sam ba zancen auren bane yafi ɓata min rai ba, duk da zuciyata ta sosu ba ƙadan ba. Sa'ar Walida fa! Kamar ni inyi kishi da sa'ar ƴata. Wani irin kashi da fitsarin Mardiya ne ban ci ba a cikin gidan nan! An min adalci kenan? Yarinyar nan a wajena ta yi rayuwa tun tana da shekaru tara a duniya. Dama can Babiyo na da wannan shirin shiyasa ya ɗauke ta daga wajena last year ya mayar da ita wajen mahaifiyarta. Yarinyar da Mama take kira na duk da kuwa ni ɗin yayarta ce," tana kawowa nan ta rushe da kuka.
Shuru ya yi don ko shi abun ya zo masa bagatatan kuma banbarakwai kasancewar hatta shi Baffa Giɗaɗo take ce masa ba Hamma Giɗaɗo ba.
"Ki haƙuri don Allah Halima! So kike hawan jininki ya motsa? Wallahi babu yanda na iya da Babiyo, ban isa na yi masa jayayya akan hukuncinsa ba. Ke mai bani shawarar yi masa biyayya ne domin tsira ranar gobe. Shi ɗin uba ne!" Baffa Giɗaɗo ya faɗi cikin kwantar da murya.
"Baka ji abunda Babiyo ya faɗi ba a fadarsa? Baka ji irin faɗan da ya yi min ba? Kuma fa a gabanta ita da iyayanta, kuma sai ya yi kamar bai ga ita Mardiyar ba balle ya yi mata faɗa kamar yanda ya yi min. Ba ka tunanin hakan zai ba ta damar raina ni a gidan mijina uban ƴaƴana? Cewa fa ya yi wai in kama girma da mutuncina don idan ya samu wata ɓarna daga gare ni zai ɗau mummunar hukunci a kaina."
"Ke kuma sai kar ki bada wannan damar, Halima. Ke kin san ni ba zan taɓa bari Mardiya ta raina ki ba wallahi," ya faɗi yana riƙe hannunta.
"Don girman Allah ka raba mana gida, Baffan Habib!" Ta faɗi a marairaice.
"Ki yi haƙuri, ke ma kin san abunda ba zai taɓa yuwuwa bane. Nan unguwar ita ce unguwata. Bani da wani wajen ajiye Mardiya da ya wuce nan gidan wallahi."
"To ai shikenan! Allah ya ba mu zaman lafiya tare da kau da fitina," tana gama faɗin haka ta kwanta a kan gadon tana shassheƙar kuka.
Ɓangaren Abdul Hameed kuwa, babu abunda ke masa yawo cikin zuciya sai lamarin Babiyo. Shi sam bai ƙaunar harkar siyasar nan da yake so daura sa a kansa saboda bai san komai a ka ba kuma bai da burin sanin komai. Ya amshi bukatarsa ne saboda iyayansa da ke son yafiyar Babiyon domin dawowa cikin ƴan uwa su zauna tare da kuma ƙoƙarin karya alkadarin Mamiyo wacce ita ce silar komai domin ruguza masa iyalai saboda abun duniyar da Babiyon ya tara domin cin su ita da ƴaƴanta kawai. Babu wani motsinta da bai sani ba sai wanda ta ke ƙullawa a ƙarƙashin ƙasa wanda kuma ita ta barwa kanta sani har sai lokacin da Allah ya gama ara mata lokacin sannan ya tona mata asiri a idanun duniya.
Wayarsa ya ɗauka dake gefe kusa da shi tare da lalubo Number ɗin Jawaad ya danna masa kira.
Jawaad da ke can asibiti kusa da Habibu da bacci ya ɗaukesa mai nauyi saboda allurar baccin da akai masa, ya ji wayarsa na ruri. Fiddo wayar ya yi tare da latsa madannin amsa kira ya kara a kunne duk da sunan mai kiran bai fito a wayar ba kasancewar ba shi da Number ɗin Abdul Hameed ɗin.
"Assalamu alaikum, Jay ya kake?" Abdul Hameed ya faɗi cikin sanyin muryansa mai tafe da natsuwarsa.
"Hamma Hameeeed!" Jawaad ya faɗi da ɗan ƙarfi don it been long da ya ji muryansa. Su kasance tamkar ƴan uwa a cikin Arɗo Barkinɗo, shi Abdul Hameed ɗin da kuma Habib kamun Babiyo ya cire shi Abdul Hameed ɗin daga cikin su.
"Jay I need to talk to you, kana ina?" Abdul Hameed ɗin ya faɗi yana ɗan rage tafiyar motar.
"Ga ni a Arɗo Barkinɗo specialist hospital, Habib ne kawo an bashi gado," Jawaad ya faɗi.
"Subhanallah! Gani nan zuwa in five minutes," yana gama faɗin haka ya yanke wayar tare da ƙara gudun motar kasancewar asibitin na daga can cikin estate ɗin ne.
Mintuna biyar ɗin ya kawo shi cikin Arɗo Barkinɗo specialist hospital. Fitowa ya yi tare da kulle motar sannan ya nufi cikin asibitin cikin tafiyarsa ta natsuwa. Kai tsaye Amenity 1 ya nufa duk da kuwa Jawaad ba faɗa masa ɗakin ya yi, zuciyarsa ne kawai ta bashi ya nufi can. Yana tura ƙofa su kai idanu biyu da Jawaad ɗin da ke kusa da Habibu. "Alhamdulillah," ya ce cikin zuciya tare da ƙarisowa ciki.
Jawaad kuwa tun da ya kafe shi da idanu ya kasa ko kyafta idon yana ƙarewa kyakkyawar baƙar fatarsa da ke sheƙi kallo.
"Hey, dude! Ya da wannan kallon kamar za ka cinye ni?" Abdul Hameed ya faɗi.
Murmushi Jawaad ya saki tare da faɗin, "I really miss you, my Hamma Hameed!"
"Really miss you too, little bro!" Ya ƙarisa maganar yana taɓa kafaɗansa.
Bige masa hannu Jawaad ya yi tare da faɗin, "Don ka samu dakyar ina ce maka Hamma shine har da wani kira na little bro! To kar dai ka manta it's only 7months difference tsakanin mu," yana ƙarisa maganar cike da raha.
"Ko ma dai ina faɗowa ka faɗo, na girme ka," Abdul Hameed ya faɗi shima yana dariyar.
"So sannu sa'an sarki Babiyo! Na samu labari tare ku kai wasan ƙasa ma. Sannu kaka Hameed, Barka da zuwa," da dariya ya ƙarisa maganar shi kuma Abdul Hameed ya kai masa duka a baya.
"Mai ya samu Habib haka har da kwanciya a asibiti?" Abdul Hameed ɗin ya faɗi yana kallon Habibu da ke bacci fuskansa na kallon sama.
"Auren dole akai masa shiyasa ya gigice," faɗin Jawaad.
"Wani irin auren dole kuma? Ba da Amatul kareem aka ɗaura masa auren ba?" Abdul Hameed ya faɗin sounding a little bit confusion.
"Da ita fa! Kawai iskancinsa ne ya motsa, ka san halin ƙanin naka ai," faɗin Jawaad yana kallon Habibu da ya ɗan soma motsawa.
"Ko cikin bacci idan ana gulmarsa fahimta ya ke, dubi yanda yake motsi kamar tsutsar da aka matse," Abdul Hameed ya faɗi yana ɗaura hannunsa a kan goshin Habib ɗin.
"Kuma jikin babu wani zafi sosai," Abdul Hameed ɗin ya kuma faɗi.
"A'a, ya dai sauka ne. Amma ɗazu tsaf mutum zai iya gasa ɗanyen masara har ta soma ƙonewa ma," Jawaad ya faɗi shima yana kai hannu kan goshin Habib ɗin.
"Mazugal!" Abdul Hameed ya faɗi yana harararsa.
"To ai shikenan tun da baka yarda ba. Amma sincerely speaking yaron nan ɗazu jikinsa kamar garwashin wuta wallahi," Jawaad ya faɗi.
"Uban wanene yaron? Na wuce yaro yanzu tun da na ajiye iyali. Wata ƙila wata tara mai zuwa ku taho yi min barka!" Faɗin Habibu da idanunsa ke a rufe.
Haɗa idanu Abdul Hameed da Jawaad suka yi kamun Abdul Hameed ya yi saurin faɗin, "Ba na faɗa maka ba, ai Habib da idanu ɗaya ya ke bacci. Ɗan iska, kana nan kwance har ka hango wata tara masu zuwa ko?" Ya faɗi yana dariya.
Su ma gaba ɗaya dariyar suka saka har suna tafawa kamar kowanne su bai da damuwa, bayan babu wanda bashi da damuwar da ke maƙale yana cin zuciyoyin su.
"Hey, Allah ba ka kwana a asibitin nan, muna nan har ƙarfe ɗayan dare. Ruwan nan na ƙarewa gida muka nufo domin shirye-shiryen gobe. Kun san dai ku biyun nan angwayene ko? Don haka we have alot to do tommorow!" Abdul Hameed ya faɗi.
"Ministan Abuja mai jiran gado, to ka sani mu namu auren mai sauƙi ne wallahi. Wata ƙila ma kai yanzu haka da matarka wacce a kai muku aure tun wancen-wancen-wancen December ɗin baka sani ba. Kasan dai wanene Babiyo. Kai ne next target ɗinsa wallahi!" Habib ya faɗi.
"Bari, bari HB! Wallahi har ka saka naji wani rass kamar saukar aradu," Abdul Hameed ya faɗi har da riƙe ƙirji.
"Mai za a bari ɗin? Malam idan ma za ka fara duba yarinya a cikin Arɗo Barkinɗo ka fara wallahi, don yasin-yasin Babiyo sai ya maka aure kwanannan," Jawaad ya faɗi.
"To bakinku dai ya sari ɗanyen ƙashi wallahi," Abdul Hameed ya faɗi.
"To akai wa Baffa Giɗaɗo ma bare kai, shi da yake da mata da manyan ƴaƴa," Jawaad ya faɗi.
"Kai dai bari, wallahi auren Baffa Giɗaɗo ya ɗaure min kai matuƙa. Ina Baffa ina Mardiya sa'ar Wasila! Ni dai wannan abun bai min ba wallahi." Abdul Hameed ya ƙarisa da ɗacin rai.
Shuru Habibu ya yi don har da hakan ya ƙara maza zafin zazzaɓinsa. Don Mardiya kamar ɗiya haka take wajen mamansa. Kuma ya san abun zai mugun dukanta musamman abubuwan da Babiyo ya faɗi a wajen meeting.
"Ni fa na ƙosa wannan tsohon ya mutu ko mararmu ta saki mu samu damar yin bowali da kyau, haba! Wannan abu na Babiyo ya yi yawa," Jawaad ya ƙarisa maganar yana tsaki.
Murmushi Abdul Hameed ya yi tare da faɗin, "Na taɓa kuskuren faɗin haka a gaban Baffana, sai ce min ya yi wai sai na mutu da shekarun Annabi Nuhu a duniya kamun Babiyo ya mutu."
Wani irin dariya suka fashe dashi tare, Habib ya ce, "Ai kuwa da Babiyo ya shiga uku don da kansa zai riƙa zuwa masallatai yana kuka tare da roƙon mutane akan su roƙa masa mutuwa a wajen Allah."
"Idan jikin nasa ya iya motsawa kenan, don wallahi Shekaru sha biyar zuwa ashirin mutumin nan ya ƙara a duniya, tattarosa za a riƙa yi kamar tsumma ana saka shi a baro," Jawaad ya faɗi.
"Wai yanzu Babiyon ku kewa tsiya haka? To yana kallonku bisa computer ɗinsa daga gida," Abdul Hameed ya faɗi yana dariya.
Wani irin firar yaushe gamo ne ya ɓalle tsakanin su cike da nishaɗi suna tuno rayuwar ƙuruciya har ruwan da aka ɗaurawa Habibu ya ƙare jini ya soma haurawa. Da sauri Abdul Hameed ɗin ya kashe ruwan tare da cire masa canular suka fice daga asibitin ba tare da sun jira anyi discharging ɗinsa ba.
Kusan kwanan zaune su kai a gidan su Jawaad cikin ɗakinsa don ƴan gidan ma basu san da zuwan Abdul Hameed ɗin ba, don da Baffa Bobbo ya sani ba zai bar Abdul Hameed ya kwana gidan ba gudun ɓacin ran Babiyo tunda bai bada umarnin haka ba.
Washa gari da biki aka tashi a estate ɗin tsakanin ɓangarori uku; ɓangaren Jawaad, Habibu, da kuma Mardiya. Tuni kaya sun iso daga China don tuntuni Babiyo ya bada order kayan amare tun daga kan kayan furniture, kitchen utensils, bedsheets da curtains.
Ɓangaren amarya Mardiya kuwa, kwana ta yi kuka kamar ranta zai bar jikinta akan auren da Babiyo ya saka a ɗaura mata da wanda ta ke masa kallon Baffa ba Hamma ba. Har duka ta ci wajen baban ƙanin baban nata mai wanda shi ne na huɗu wajen iyayan su Babiyo kuma kamar ɗa haka yake wajen Babiyon don tun rasuwar iyaye Babiyon ke masa komai ba ma shi kaɗai ba har da sauran ƴan uwan nasa da suke uwa ɗaya dama wanda uba kawai suka haɗa. Kuma ya rike su da amana shiyasa suke masa kallon uba kuma basu iya musu dashi akan duk hukuncin da ya yanke.
Kamun zuwa ƙarfe huɗu, duk an gama shirye-shiryen kayan duk amaren guda uku. Jawaad yana can ciki kusa da Arɗo Barkinɗo Supermarket, wanda anan aka yanke fili flot aka gina masa gidansa mai tsananin kyau . Habib kuma layi huɗu ne tsakaninsa da gidan Jawaad ɗin wanda shima tsarin ginin gidansa iri ɗayan ne da na Jawaad ɗin. Mardiya kuma dama a can gidan Baffa Giɗaɗo aka kai nata kayan, sai side ɗinta yana ɗan nesa kaɗan dana mama Halima.
Su kansu ƴan kawo kayan Mardiyar ba ƙaramin kunya ce ta kama su ba lokacin da suka shiga cikin gidan. Kasa shiga sashen mama Halimar suka yi saboda kunya suke ji matuƙa da wannan abu da Babiyo ya aikata.
Ana saukowa sallar magrib aka haɗa kawunan amaren uku aka nufi gidan Babiyo da su domin yi masu nasiha tare da saka masu albarka.
Irin mahaukacin kukan da Mardiya ke yi ya ɗaga masu hankali har su kai parking a gefen titi tare da kiran mahaifinta a waya ko akwai wani abunda zai faɗa mata da zai sanyaya zuciyarta don muddun ta isa gaban Babiyo a haka ba ƙaramin tashin hankali da damuwa za ta jawo wa mutane ba. Don cewa zai yi ba a bata cikakkiyar tarbiyar da zata iya bin umarninsa da kuma karɓan duk abunda ya zaɓa mata da hannu bibbiyu ba. Kuma hakan na nufin yi wa iyayanta hukunci bisa abinda ta aikata.
"Mardiya yanzu abunda za ki min kenan? Asiri kike son tona mini? Idan Babiyo bai yi iko da ƴaƴana ba, da wa kike so ya yi? To shikenan, ki yi yanda kike so, Mardiya. Duk abunda Allah ya yi daidai ne. Amma ki sani duk hukuncin da Babiyo ya ɗauka a kai na, ke ce sila Mardiya. Nagode da wannan sakayyar," wannan shine maganar da mahaifin Mardiya ya faɗi lokacin da aunty Nana ta kara mata wayar a kunne.
Lokaci guda kukan na ta ya ɗauke ta shiga goge hawayen idanunta da ga hannunta biyu tana sakin ajiyar zuciya a jajjere. Ganin haka sai su ka ce wa driver ya ja motar su wuce.
A tsakiyar ainahin parlourn Babiyo suka ajiye amaren uku da fuskokinsu ke a lulluɓe. Babiyo kuma na kan 1seater fuskansa sanye da glasses yana kallo a makeken tv da ke ɗakin manne da bango. Bai mayar da idanunsa a kan su ba har sai da ya kammala kallon news ɗin da ake maimaita a tashar NTA.
"Ni ba magana ce zan yi mai tsayi ba, abunda na ke faɗawa iyayanku duk zan aurar da su, shi zan sake maimaita maku. Abunda zan fara jan hankalinku a kai shine, ai haƙuri, ai haƙuri kuma ai haƙuri! Domin shi haƙurin nan da na nanata sau uku, shine ginshiƙin zaman aure. Da iyayanku maza da mata da ni nan kaina da na yi shekaru fiye da sittin da aure, haƙurin nan shine ya kai mu har ga wannan lokacin. Bayan haƙuri kuma, sai in ƙara tunasar da ku akan yiwa mazajanku biyayya. Yi, na yi, bari, na bari. Kar ku yarda wata matsala wacce ba a fata ta ɓullo kuma binkice ya nuna daga gare ku ne. Idan har hakan ta kasance, kun fi kowa sanin wanene Arɗo Barkinɗo da kuma abunda zai iya aikatawa. Ke kumaMardiya nasiha ta a gare ki shine, ki kama kanki ki natsu a ɗakin aurenki, kar ki kuskura ko da wasa inji labarin kin yi wa Halima kallon banza saboda kina ganin matsayinku ɗaya da ita. Na san wacece Halima domin ubanta rainona ne. Ita ɗin yarinya ce mai matuƙar haƙuri da kawas da kai. Ban haɗa aurarku da Giɗaɗo domin ta gaza ba, a'a sam! Haka Allah ya rubuta tun farko ita ɗin ce uwar riƙon ki kuma daga baya ta zama abokiyar zamanki. Kuma na zaɓe ki ne saboda ganin natsuwarki da hankalinki. Kar ki kuskura ki yi amfani da damarki ta matar mijinta ki ce za ki wulaƙanta, ba zan ɗauka ba. Kamar yanda kike ƴata, haka itama take. Ke Amatu, in Sha Allah baza ku wuce sati ba, za ki bi mijinki ku tafi Sweden can za ku zauna har sai na nemi mijinki. Ke kuma Khairiyya, ke ma za ki bi mijinki ƙasar da zai je yin course na shekaru biyu kawai, bayan ya kammala kuma za ku dawo tare. Allah ya ba ku zaman lafiya!" Ya ƙarisa maganar yana miƙawa kowacce maƙudan kuɗi a cikin envelope wanda sadakinsu ne da kuma gudunmawarsa matsayinsa na kakansu.
Da hannu biyu suka amsa suna godiya. Mardiya dai sai danne kukan da ke neman cin ƙarfinta ta ke yi.
"Ku kai su cikin wajen Lauratu (Mamiyo)" Babiyo ya faɗi yana ƙara gyara zaman gilashin idanunsa.
A can ɗakin Mamiyo kuwa, zaune take a kan kujerar da ke parlourn ta hannunta riƙe da wasu ƙananan kwalaban turaruka. Guda biyu daga cikin, launinsu green ne, ɗayan kuma shi ba baƙi ba, shi kuma ba kalar ruwan toka mai duhu ba. Wayar ce kare a kunnanta tana magana da wani.
"Yanzu ka tabbata idan har ta yi amfani da wannan turaren a inda ka ce, mijin na shaƙa zai ji ya tsane ta ko?"
"Kwarai da gaske ni na faɗa miki wannan zancen. Kuma shi da gabansa ya miƙe in dai a ɗakin ya ke to har abada. Kuma duk abunda kika ce ba zai musa ba," faɗin wanda ke kan wayar.
"Ke nan ko bai kusance ta ba aka wayi gari kwarya a fashe, ba zai musa cewar bai kusance ta ba ko?" Ta kuma jefa masa tambaya.
"Tabbas kuwa hajiya. Sai dai idan bai shaƙi wannan turaran ba," ya faɗi yana dariya basawa.
Yanke wayar ta yi tare da ajiyar a kan kujera sannan ta saka ko wani turare a cikin wani ɗan akwati mai ɗauke da awarwaro da ɗan kunnen zinari. Kuma a daidai wannan lokaci akai knocking ɗin ɗakinta.
Da fara'a ta buɗe ɗakin tana masu maraba kamar abun arziki. Bayan doguwar nasihar zaman aure, sai ta umarci amaren kawai da su miƙe su bi bayanta zuwa cikin ɗakin baccinta. Gaba ɗaya suka miƙe suka bi bayanta.
Gyalen da suka lulluɓe jiki da shi ta saka suka warware, ta kan Amatul kareem ta fara, babu inda bata goga mata turaren ba. Tuni wani ƙamshi mai azababben daɗi ya gauraye ɗakin. Haka ta yi wa Khairat matar Jawad itama.
Da tazo kan Mardiya, sai ta buɗe ɗayan turaren ta goga jikin wani farar auduga mai taushi sannan ta soma goga mata. Tun gogawar farko kan Mardiya ya yi wani duum, nan da nan turaran ya soma hawa kanta taji kamar za ta yi amai.
Mamiyo kuwa sai da ta goga mata sosai a jikinta sannan ta miƙawa kowacce kyautarta kamun ta fito da su parlourn aka wuce da su gidajan.
_The Grooms_
Duk da auren ba haka suka so yazo masu ba, amma sun cakare babu wanda zai kalle su ya ce akwai wani abu a zuciyarsu. Su ukun nan sun yi anko cikin wata farar tattausar yadi mai layi-layi transparent don hatta singlet ɗin jikinsu ana gani. Yadin yana da matuƙar tsada da taushi. Abdul Hameed da ya kasance baƙi a cikinsu, yadin ba ƙaramin amsarsa ta yi ba ka ce shine angon.
"Kai! Wai Jawaad lafiyar ka kuwa? Sai ka ƙarar mun da turaren tukun za ka ji daɗi? Ni dai tun da na nuna maka turaran nan na shiga uku ai," faɗin Abdul Hameed tare da kai hannu ya fizge kwalbar.
"Oho dai, na dai fesa ma'ishi!" Jawaad ɗin ya faɗi yana masa gwalo.
A jikin Abdul Hameed Jawaad ya soma jin ƙamshin turaren *_DKNY Golden Delicious_*. Duk idan ka ji wannan ƙamshin to babu shakka Abdul Hameed ɗin ne a wajen. Shi kuma Jawaad sai Allah ya ɗora masa ƙaunar turaren, don wani lokacin takanas bayan ya yi wanka ya shirya ya ke tafiya gidan Baffa Ɓelɗo domin ya fesa turaren Abdul Hameed ɗin. Bayan Abdul Hameed sun bar Arɗo Barkinɗo ya yi neman turaren a Abuja, da wasu daga cikin ƙasashen da ya ke zuwa bai samu ba sai shekara ɗaya baya da ya je Sweden ya samo turaran a wani complex da yaje.
"Ungo ɗan wutan ciki! Kasancewar na san kana ƙaunar turaren na sayo maka shi matsayin gift na aurenka." Faɗin Abdul Hameed bayan ya saka masa a hannu.
Rungumesa Jawaad ya yi tare da faɗin, "That's why I love you my Hamma Hameed."
"To ni ina nawa kyautar?" Habib ya faɗi kana kallonsa kasan akwai sauran rashin lafiya a jikinsa musamman ma ɗazu da ya leƙa gidansu ya ci karo da ƙannansa sai rusa kuka suke da suka ji aurar da Babiyo ya yi wa Baffan.
"Ungo kai ma, ni muje in kai ku gidajanku joo. Kuma kun san dai sai mun fara zuwa wajen Babiyo."
Bayan few minutes suka kammala sannan suka hau mota zuwa gidan Babiyo. Yana nan parlourn zaune, sai dai wannan karon furarsa ya ke sha, Mamiyo na gefensa tana ɗan jefa masa zance zuciyarta wasai.
"Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu!" Gaba ɗaya suka faɗi kasancewar sun san halin Babiyon ya fi son cikakkiyar sallama.
Yana ɗaga kai da Abdul Hameed ya fara arba, hakan ne ya saka ya amsa sallamar fuska faɗaɗe da fara'a.
Zama su kai a ƙasa daidai wajen ƙafafunsa sannan suka gaishe sa shi da Mamiyo.
Mamiyo kasa amsawa ta yi sai kallon da ta bi Abdul Hameed ɗin da idanu tana jin kamar ta tashi ta shaƙar shi ya mutu nan take. Sosai ta yi nisa a tunaninsa don bata ji duk abunda Babiyo ya ke cewa ba, ta dai tsinci maganarsa na ƙarshe,
"In sha gaba ɗaya rana ita yau za ku bar ƙasa. Sai dai ku sani, dukkan ku za ku dawo idan lokacin kaɗa ƙuri'a ya yi domin ku zaɓi ɗan uwanku kuma abokinku, Abdul Hameed."
"In Sha Allah, Babiyo. Mun gode da nasiha, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma." Duk suka faɗi.
Da ameen ya amsa sannan su kai masu sallama, Mamiyo da kai kawai ta iya amsawa. Don idan ba gizo idanunta suke mata ba, sai taga kamar Abdul Hameed harararta ya ke yi.
Habibu ya fara saukewa a harabar gidansa tare da miƙa masa ledan kaza da yoghurt tare da faɗin, "Aci amarci lafiya!"
Sai da suka ɗan tsaya na mintuna biyar suka zaulayi juna kamun Abdul Hameed ɗin ya juya kan mota ya sauke Jawaad ɗin shima yana masa tsiya. Kai tsaye keɓaɓɓan gidansa ya nufa domin ya huta gajiya.
Parking ya yi tare da fitowa daga motar ya doshi cikin gida, sai dai bai yi ko taku huɗu ba yaji wani mahaukacin azaba a kyeyarsa sakamakon sauke masa wani murɗanɗan ƙarfe a wajen. Wani irin jiri ya soma gani ga jinin da ke zuba a ƙyeyarsa kamar an buɗe fanfo. Yaraf ya faɗi ƙasa yana shure-shure kamun ɗif ya tafi.
Wanda ya kwaɗa masa karfen kuwa, kansa ya zo ya tsaya tare da tattaɓasa domin tabbatarwa shin ya mutu. Jin babu numfashi sai ya saki wata dariya tare da janya gefe sannan ya bar gidan da sauri...
A can gidan Baffa Giɗaɗo kuwa, ana shigar da Mardiya cikin ɗakinta ta yi saurin faɗawa ban ɗaki saboda wannan turaren da Mamiyo ta saka ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya ke ba. Burinta kawai ta sake yin wanka domin wanke ƙamshin turaren ko za ta ji dama-dama....
_ZEENATU LAUSHI_
Ciwo ya hana ta sukuni. Duk da ba ta buge-buge amma kanta ji take kamar ba na ta ba. Gashi gidan yanzu ya zama tamkar na ƴan ta'adda, don kwana suke idan sun kawo kaya. Abu ya zama mata goma da ashirin. Yanzu za ayi abu da ita, yanzu ta manta shi kwata-kwata. Ga wani irin shuru-shuru da ta koma. Idan kuwa ka yi kuskuran buɗe ƙofa ya yi ƙara yanzu za ta fita hayyacinta. Ko ƙarar cokali bata son jin idan ana cin abinci don a cikin maɗiganta take jinsa. Tafiya, cin abinci da magana ya zama cikin takatsantsan saboda condition ɗin ta.
Meema kuwa, yaran spanish ɗin da ake koya mata ya soma zame mata tamkar yaran Hausa. Ta ɗan fara sakewa da Yahuza saboda kullum suna tare. Shi ke kai ta makaranta ya dawo da ita.
_YASAAR_
"Kana jina ko, ni wallahi gani nake Oga raina min wayau kawai ya ke yi. Daga ni har Zeenah amfani ya ke damu domin cika burinsa. To gaskiya an kawo ni karshe! Ban san mai yasa mutanen da na amince da su suke min haka a rayuwa ba. Don haka na gama yanke hukunci. Zan aikata abunda na ce maka zan yi, zan nunawa Sabo da Kaza ba shi kaɗai ya iya playing game ba, ni ma na koya daga gare shi. Don haka zan riga shi ɗauke Meema, ni Colombia zan tura ta wajen Adalberto ya tura min kuɗinta kawai, ita kuma uwar na san yanda zan yi da ita............"
#Abdul Hameed #Jawaad #Habib #Mamiyo #Babiyo #Baffa Giɗaɗo #Mardiya #Mama Halima #Sabo da Kaza #Yasaar #Meema #Colombia #My Destiny #Matar Sayyadee
*** Rahamanatu: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`