My Destiny (Ƙaddarata)

Page 34

by @matarsayyadee3

*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!*

```Dukkan godiya su tabbata ga Ubangijinmu, mahaliccinmu mai kowa mai komai da ya sa muka ga zuwan wannan wata da ta wuce (Ramadan) lafiya. Allah don girmanka da zatinka ka sa muna daga cikin ƴantattun bayinka. Ubangijin al'arshi, kai muke roƙo domin kai kaɗai ne muke wa laifi, muyi mu kuma ƙarawa, amma hakan bai hana idan mun ɗaga hannu mun roƙeka ka amsa mana. Kai kaɗai ne _LAM-YALID WALAM YULAD, WALAM YAKUL LAHU KUFWAN AHAD_! Albarkacin fiyayyan halitta (Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama) ka saka tausayi a zukatan shuwagabanninmu domin su tausaya mana a wannan rayuwa da muke ciki. Allah don Rahmarka, don zatinka, don ƙudirarka, ka yafe mana zunubanmu domin mun san duk abunda ke faruwa damu zunubanmu da ƙin bin dokokinka ne suka jawo mana komai. Allah ka shirya duk wanda bai kan hanyar da kake so mu bi, idan kuma ba masu shiryuwa bane, Allah kai ka san yanda za kai dasu. Allah duk musulman da suka koma gareka a cikin wannan watan mai albarka da ma waɗanda suka kwanta dama tun daga zamanin Annabi Adama har izuwa yau ka gafarta masu daga cikin gafararka, ameen!```

*BARKA DA SALLAH MUTANAN ARZIKI, 😍 DA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA! ALLAH YA MAIMAITA MANA*

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

"Dama ai ni na jima ina faɗa maka Sabo da Kaza amfani kawai ya ke da kai domin cimma manufarsa. To idan ba haka ba, yaushe zai baka damar ɗaukar fansarka? Kawai Yasaar ka yi abunda zai fissheka kawai don Sabo da Kaza yana gama amfani da kai zai yar da kwallon mangwaro ya huta da ƙuda ne wallahi!" Abokin Yasaar da suke waya ya faɗi hakan cike da zuga.

Numfashi Yasaar ya fesar tare da faɗin, "Shekara goma sha ina wa tsinannan aiki amma babu wani abunda ya tsinana min a rayuwa in banda Prison da ya jefa ni tare da bada ɗan uwana rabin jikina a ka kashe matsayin ni. Dole ne ma na ci amanar wannan ɗan iskan wallahi!"

"Kai ba ka ji sunansa ba, Sabo da Kaza fa! Ai hakan na nufin duk yanda kuke da shi hakan ba zai hana ya yi maka kafurci ba, wata ƙila ma ya zama ajalinka! To wallahi kamun ya farga ka tarwatsa shi kai," abokin Yasaar ya faɗi yana ƙara kunna shi.

"Bari, zan kira ka zuwa anjima da yamma!" Ya faɗi hakan tare da yanke wayar yana wani dogon nazarin ta yanda zai yi da rayuwar Laushi da na ƴarta Meema.

_Abuja_

Wani irin wankan fitar hayyaci Mardiya ta ke yi a cikin bayi da shower gel ɗin da ta gani ciki. Sai da ta kusa zuba kwatar goran a jikinta, bata samu natsuwa ba har sai da ta ji jikinta ya koma babu abunda ya ke sai ƙamshin shower gel ɗin nan sannan ta haƙura ta fito daga bayin. Jakar da Aunty Ladi ta shigo mata da shi ta buɗe tare da fiddo audugar mata kasancewar tana fashin sallah ta saka sannan ta mayar da kaya a jikinta.

Ɓangaren Mama Halima kuwa, ta daina kuka sai tagumin da ta zabga tana kallon ƴaƴanta mata da suka fita shiga tashin hankali da auren da Babiyo ya yiwa Baffansu. Baffa Giɗaɗo kuwa ya shige ɗakinsa ya turo ƙofa har da saka key saboda bai son zuwa wajen amarya.

Abun ya zamewa mama Halima goma da ashirin don idan har bai tafi ba, wani matsalar ce za ta sake ɓullowa idan Mamiyo ta shigo gobe da safe domin duba ratayayyar ƙwarya. Don da kanta ta ke zuwa dubawa ba aike ta ke yi ba.

Mama Halima ta yi bugun ƙofar har ta gaji, amma Baffa Giɗaɗo bai buɗewa. Ganin zaman parlourn ba zai fissheta ba ga ƴaƴa sun saka ta gaba da kuka, sai ta miƙe ta nufi ɗaki tare da rufo ƙofa ta ɗauki waya tare da turawa Baffa Giɗaɗo saƙo kamar haka;

_Baffan Habib, idan har ba so kake ka saka a kore mu kamar yanda aka kori Hamma Belɗo da Hamma ɓaleri ba, ka yi haƙuri ka fito ka wuce ɗakin amaryarka. Idan kuma so kake Babiyo ya yanke hukunci a kai na, fine! Don na tabbata baka manta kashedinsa a gare ni ba. Kuma idan har baka kwana ɗakin amaryarka ba a yau, hakan na nufin ni ce na hana ka a idanun Babiyo da Mamiyo da sauran da ke goya masu baya!_

Bayan kamar mintuna bakwai da tura masa saƙon, sai ta ji maganarsa a parlourn shi da ƴaƴansa. Rintse idanu ta yi tana hamdala cikin zuciya. Hawaye ne suka sillo mata lokacin da ta ji fitarsa daga ɗakin, dama ta riga ta san ba zai shigo ba saboda gudun ɓacin ranta. A daren dai barci ɓarawo ne ya kwashe ta.

_Mamiyo_

Mahaukatan maruka Mamiyo ta riƙa ɗauke Baffa Jibrila da shi cikin zafin rai da ɗacin zuciya.

Shi kuwa Baffa Jibrila sai wani irin huci ya ke idanunsa sun ƙada sun yi jazur tsabar yanda zuciyarsa ke tafasa.

"Wannan ai hauka ne da neman tona mana asiri a cikin Arɗo Barkinɗo! Ka yi hauka ne, Jibrila? Dukkan mu nan da kake gani kowa a tafashe ya ke! Mai yasa sam wani lokacin ba ka iya sarrafa kan ka ne? Ka san mai ka aikata kuwa? Allah ka sa wannan yaron bai mutu ba!" Baffa Mahmud wan Baffa Jibrila ya faɗi.

Mamiyo kuwa bayan ta gama kakkafta masa maruka sai ta shiga zagaye ɗakin hankalinta a matuƙar tashe don har zufa ɗigo mata ya ke duk da sanyin Ac ɗakin.

"Wannan yaron wani lokacin ji na ke kamar ba jinina bane! Daƙiƙi kawai ya na neman tona mana asiri. Wa ya faɗa maka kashe Abdul Hameed shine zai warware mana komai? Waye ya baka damar bin bayansa har ka aikata wannan ɗanyan aiki, Jibrila? Ka fini son ya mutu ne? Ko kuwa ka fini dabara, basira da kuma ƙwaƙwalwa ne?" Mamiyo ta faɗi a hassale.

"Ki min aikin gafara Mamiyo, na ɗauka abunda na yi zai sanya ki cikin farin ciki, ban ɗauka shirme na aikata ba!" Baffa Jibrila ya faɗi kansa a ƙasa.

"Sha-sha-sha!" Mamiyo ta faɗi bayan ta jefa masa wata uwar harara tare da ɗaukar wayarta a bakin makeken gadonta ta shiga lalubo Number ɗin Hafizu.

"Akwai matsala babba, Hafiz! Kana ina ne?" Mamiyo ta faɗi bayan Hafiz ya ɗaga wayar.

Hafiz da ke duƙe gaban Babiyo da ya yi kiransa suna tattauna wata magana ya furta, "A'a ban yi nisa ba ina wajen Babiyo, yanzu ya kira ni. Ku ci baccinku kawai idan na dawo zan ci nawa," ya ƙarisa maganar kamar da matarsa ya ke magana a kan wayar.

Mamiyo kuwa da jin haka ta katse wayar don bata da buƙatar fashin baƙi kasancewar ta fahimci ba zai iya wata magana da ita ba saboda suna tare da Babiyon.

"Yanzu haka Hafiz yana tare da Babiyo, amma na tabbata zai sake kirana nan ba jimawa. Zan saka shi ya yi clearing wannan matsalar da ke shirin kunno mana," Mamiyo ta faɗi tana mai saka mazaunanta a kan kujera.

"Ka tashi ka tafi wajan iyalanka, gobe idan Allah ya kai mu ma ƙarisa maganar," Babiyo ya faɗi yana kallon Hafiz da ke ta ƴan kame-kame.

Murmushin yaƙe ya yi tare da faɗin, "A'a ba ayi haka ba, Babiyo. Ba wani abu bane fa, ta ji shiru ne shine ta ke tambayata ina ina ne in dawo in ci abinci," da kame-kame irin na marasa gaskiya ya faɗi hakan.

Shi ma Babiyon murmushi ya yi tare da faɗin, "Uhm! Jeka kawai wajen matarka, Hafizu. Ai hakan ake son mace wajen kula da mijinta. Je ka ci abinci tare da iyalanka."

Ɗan sunkuyar da kai ya yi alamar girmamawa tare da faɗin, "Godiya na ke Babiyo, Allah ya ƙara girma."

Kai kawai Babiyo ya gyaɗa, shi kuma Hafiz ya miƙe da sauri ya fice daga parlourn. Mota ya buɗe ya shiga tare da tadawa ya bar Arɗo Barkinɗo Street. Sai da ya yi nisa da gidan sannan ya yi parking tare da dannawa Mamiyo kira.

Mamiyo na ganin kiran Hafiz ta yi murmushi tare da ɗaga kiran ta kara a kunne.

"Uwar ɗakina kin kira ina kusa da wannan tsohon, amma dabarata ta yi aiki don yanzu haka gani na fito daga gidan," Hafiz ya faɗi.

Kai tsaye Mamiyo ta tafi ga kan batunta, "Jibrila na neman ɓata mana aiki Hafizu, don ya bi bayan Abdul Hameed zuwa keɓaɓɓan gidansa ya bigesa da rodi a kai saboda rashin hankali."

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ya a kai ya yi wannan aika-aikar haka? Wayyo Allah ni kai na! Hajiya yanzu ya za muyi?" Hafiz ya faɗi a rikice.

"Abunda nake so da kai yanzu, maza-maza ka fita ka nufi gidan ka ɗauke sa ka kai shi Arɗo Barkinɗo specialist hospital, bayan ka kai shi sai ka kira Babiyo ka faɗa masa kana kan hanyan komawa gidanka sai ka ga motar Abdul Hameed ɗin wani na binsa a baya sai kai ma ka rufa masu bayan, sai ka ƙara da ce masa kana shiga ka gan shi kwance cikin jini kuma baka ga wanda ke bin sa ɗin ba," Mamiyo ta faɗi.

"Hakan za ayi, bari na tada mota, sai kin ji daga gare ni," yana gama faɗin haka ya katse wayar tare da tada motar ya figeta da sauri.

Kai tsaye gidan Abdul-Hameed ɗin ya nufa, a ƙofar gate ya yi parking tare da fitowa ya yi cikin gidan da sauri bayan ya ɗan waiga kudu da arewa. Tun daga farkon gidan ya ke kallon jini kasancewar tarr gidan ya ke da haske kamar rana saboda dogayen fitilun solar da suka ƙawata gidan. Gabansa ne ya yanke ya faɗi ganin babu alamar mutum a kaf filin gidan sai dai ga jini nan ya yi layi alamar ya fice daga gidan. Da sauri Hafiz ya juya tare da fita waje yana kallon ƙasa domin tabbatarwa, aikuwa ɓaro-ɓaro ya yi arba da ɗishi-ɗishin jinin Abdul-Hameed ɗin. Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi wanda ke nuni da tsoro da kuma tashin hankali.

Jim ya yi na kusan mintuna biyar kamun ya nufi mota ya buɗe ya shiga sannan ya lalubo Number ɗin Mamiyo ya danna mata kira. Ringing biyu ta ɗaga tare da faɗin,

"Hafizu, kar ka yi ƙoƙarin faɗa min abunda zai buga zuciyata cikin daren nan. Don alamu sun nuna ba ni tare da nasara a yau."

Ajiyar zuciya Hafiz ya sauke tare da faɗin, "Hajiya, babu Abdul-Hameed a cikin gidan nan sai jininsa da ya bari kawai. Alamu sun nuna ya bar cikin gida don na ga sahun ƙafafunsa da kuma jinin da ke zuwa a jikinsa har bakin gate ta waje."

"Inna lillahi wa'inna ilaihir! Wallahi da badan ina tsoron harshena a kan ƴaƴana ba, da yau babu abunda zai hana ni tsinewa Jibrila," tana gama faɗin haka ta katse kiran tare da mayar da hannunta biyu a baya tana zaga ɗakin.

Su kuwa ƴaƴan nata sai bin ta da idanu suke kowanne ƙirjinsa na luguden tashin hankali idan har asirinsu ya tonu a cikin Arɗo Barkinɗo. Don babu abunda zai hana Babiyo tsine masu tare da fatattakar su a cikin family na har abada.

Wayar hannunta ta kalla bayan wani tunani ya faɗo mata cikin ranta, cikin gaggawa ta kira layin Hafiz, bugu ɗaya ya ɗaga kiran.

"Yanzu-yanzun nan ka tafi Arɗo Barkinɗo specialist hospital ka duba min ko can ya tafi, kar ka yarda wani ya ganka. Idan can ɗin ya nufa, ka kira ka faɗa min sai kai tafiyarka kawai," tana gama faɗin haka ta yanke waya tare da kallon ƴaƴan nata ta furta,

"Dukkan ku ku wuce gidajanku, kar ku yarda ko a fuska matanku su fahimci wani abu bare kuma wani a cikin Arɗo Barkinɗo. Da safe kuzo nan akwai wata muhimmiyar magana da zan tattauna da ku."

Gyaɗa kai su kai gaba ɗaya, ɗaya bayan ɗaya suka fice daga ɗakin kowa da abunda ya ke saƙawa cikin zuciyarsa.

Ɓangaren Hafiz kuwa, nesa da asibin ya yi parking motarsa tare da fitowa bayan ya saka takunkumi (face mark) sannan ya doshi cikin asibitin. Yana tura kai ya dawo baya da uban sauri ganin Babiyo tsaye ƙyem a ƙofar emergency room yana kaiwa da komowa, Baffa Giɗaɗo, Baffa Modibbo, Baffa Bobbo da wasu da bai ga fuskansu da kyau ba suma tsaye hankulansu a tashe.

Tun da ya juya ko waigowa bai yi ba ya hau tsana uban sauri har ya isa wajen mota ya buɗe ya shiga. Nisa sosai ya yi da asibitin sannan ya kira Mamiyo ya shaida mata abunda ya gano a asibitin.

Wani wawan ajiyar zuciya Mamiyon ta saki tare da wani kasalallan murmushi sannan ta furta, "Ka je gida, aikinka ya kammala. Sai na neme ka da safe," ƙit ta yanke wayar.

"Ni Hafizu na shiga uku!" Ya faɗi a bayyane yana ƙurawa titi idanu tare da faɗa dogon tunani akan ganin da ya yi wa Ɓaleri a cikin Arɗo Barkinɗo, kuma tabbas ya san ba zuwan banza ya yi ba, don yanda ya yiwa Ɓaleri farin sani akan baƙar zuciyarsa wacce ya yo gatonsa gaba da baya wajen Babiyo, ba zai taɓa kyale ko yafewa duk wanda ya cucesa ko kuma ɓata masa suna ba. Sai dai kuma abunda ya bashi mamaki shine; ya san Ɓaleri tunda ya ce ya bar Arɗo Barkinɗo har abada a gaban idanun Babiyo wanda a yanda ƴaƴansa ke shakkarsa da tsoransa, ko cikin mafarki babu wanda ya taɓa kwatanta abunda Ɓalerin ya yi, to kuma abunda ya bashi mamaki shine, shin mai ya kawo Ɓalerin cikin ɓadda kama a Arɗo Barkinɗo, kuma mai ya taho yi? Tsahon shekaru goma sha sha bakwai zuwa sha takwas kenan da koran karen da Babiyo ya yi masa.

Wata zufan tashin hankali ce ta yankowa Hafiz ɗin duk da Ac da ke cikin motar, don har gangarowa take zuwa bayan kunnansa. Da kyar ya iya fuzgo hankalinsa waje guda ya nufi gidansa da ke nan cikin Arɗo Barkinɗo wanda Babiyo dakansa ya ware waje guda ya gina masa 2bedroom duk kuwa da ƙinsa da bare a cikin zuri'arsa.

Washa gari gagaruman abubuwa biyu ne suka faru a cikin Arɗo Barkinɗo wanda ya tada hankulan jama'a sosai; na farko, kai wa rayuwar Abdul-Hameed harin da aka yi wanda kaso tamanin daga cikin zuri'ar gidan suka amince akan abokan takara ne suka nemi ganin bayan Abdul-Hameed ɗin ganin tun ba a je ko ina ba jama'a su amshe sa hannu bibbiyu saboda yanda jaridu ke ta yawo da hotunansa da kuma jawabai akan kyawawan halayensa da kuma sanyin halinsa akan talakawa. Na biyu kuma fashewar kwarye a ƙofar ɗakin amaryar baffa Giɗaɗo wanda ya jawo cece kuce a tsakanin wannan family domin sosai faɗa da bala'i ya ɓalle tsakanin ƴan uwan amarya Mardiya da kuma ƴan uwan Baffa Giɗaɗo, don kowa na bin bayan nasa ne. Ƴan uwan amarya basu yarda da cewar Mardiya ba kai budurcinta ba, su kuma ƴan uwan ango, sun ce sam Baffa Giɗaɗo ba zai taɓa yiwa ƴarsu ƙarya ba.

Aunty Samira da tafi kowa zaƙewa, sai ɗura ashariya take don zargin Mama Halima take akan da saka hannunta da na mijin suka fasa kwarya don ya muzanta Mardiyan saboda bai ƙaunarta kuma bai da damar cewa a'a ga umarnin Babiyo shiyasa ya bijiro da wannan wulaƙancin musamman ma da shi har yanzu bai ce ƙala akan cece kucen ba, ita kuma ɓangaren Mama Halima suna ganin ta yi hakan ne saboda tsabar kishin an auro mata wacce ita ce ta raine ta da hannunta shiyasa suka haɗa baki da mijin domin warware auren cikin sauƙi kasancewar sun san doka ce a cikin Arɗo Barkinɗo duk wacce bata kawo budurcinta ba, za a saka mijin ya rubuta mata saki sannan a mayar da ita ƙauye ba za ta ƙara shigowa birni ba har ƙarshen rayuwarta.

Mamiyo zaune a katafaran ɗakinta babu abunda take yi sai girgiza ƙafa, fuskanta ɗauke da lafiyayyar murmushin da ke fitowa har ƙasan zuciyarta saboda plan ɗinta ya tafi a yanda ta tsara.

Shigowar Nadiya ɗaya daga cikin jikokinta ya saka ta ajiye ƙafar a ƙasa still murmushin bai gushe a kan kyakkyawar farar fuskanta da ta tsufa ba.

Ɗaura ƙafan Nadiya ta yi a kan cinyanta tana mammatsa mata kamar yanda ta saba a kowacce safiya irin wannan lokacin.

"Nadiya!" Mamiyo ta yi kiran sunanta ba tare da ta kalli fuskanta ba kuma murmushin nan na kan fuskanta har wannan lokacin.

"Na'am, Mamiyo," Nadiya ta faɗi respectfully.

"Idan kika kalle ni, da mai nake maki kama? Misali; idan aka ce ki fassara ni a cikin kalmomi mai za ki faɗi.

"Mace ke shu'uma, muguwa, makira, azzaluma, mara imani kuma mai san ganin komai ya zama sannan kowa ya ɗuka a ƙarƙashinta," Nadiya ta faɗi cikin zuciyarta kanta a ƙasa.

"Nadiya!" Mamiyo ta kuma kiran sunanta a karo na biyu kuma a kausashe.

Ɗan razana Nadiya ta yi tare da faɗin, "Afuwan, Mamiyo! Na faɗa kogin tunanin ta yanda zan fassara ki ne kamar yadda kika buƙata. Don ke ɗin babu wani halce da zai iya bayyanar da tsantsan mulki da haibarki a kaf faɗin Arɗo Barkinɗo. Ke ɗin sarauniya ce wacce ake shakka da jin tsoro fiye da yadda sauran ɗaukacin dabbobi ke jin firgici da maɗaukakin tsoron yayin da suka ji kukan ZAKI kawai. Babu wani mahaluƙin da zai iya gaba da gaba dake, idan na ce kowa kuwa ina nufin har da mai wannan katafaran Estate ɗin, wato Arɗo Barkinɗo (Babiyo), don ko shi yana shakkar ki."

Wani irin daɗi ne ke tsirga tun daga maɗigan Mamiyo har tafin kafanta. Koɗawar da Nadiya ta mata ya ratsa ta sosai kuma ta ji daɗin haka.

"Tashi ki shiga ɗakina, za ki ga wata sarƙar zinari a kan madubi, ki ɗauka na baki matsayin tukuicinki," Mamiyo ta faɗi.

Ƙam ta riƙe ƙafar Mamiyo tana ta koro godiya kamun nan ta miƙe ta shiga ta ɗauko sarƙar da nauyinta zai kai gram shida da ɗigo uku. Jiki na rawa Nadiya ta fito tana ƙara kwararo godiya sannan ta fice daga ɗakin.

A can Asibiti kuwa, Babiyo bai bar asibitin nan ba jiya sai da numfashin Abdul-Hameed ya daidaita wajajen ƙarfe biyun dare zuciyarsa na susa da kuma tunanin wani mara kwalli a idon ne da har ya iya takowa ya shigo har cikin Barkinɗo domin cutar masa da Abdul-Hameed ɗinsa. Sosai ya ɗauki alwashin bincike mai tsauri domin ɗaukar mummunar mataki akan koma wanene d ya yi ƙoƙarin kashe masa mafi soyuwa daga cikin jikokinsa maza.

Da sassafe kuma maganar fashewar kwarya ya riski kunnansa daga sashin Baffa Giɗaɗo. Wani irin rintse idanu ya yi yana jin ƙuna a cikin zuciyarsa jin wannan mummunar labarin. Zina yana ɗaga daga cikin mafi munin abunda Babiyo ya tsana a samu daga cikin zuri'arsa musamman ma ga waɗanda ya ɗaura yarda da aminci a kan tarbiyarsu. Wayarsa ya jawo a fusace tare da kira Mamiyo a waya.

Mamiyo da ke parlourn zaune tana jiran kira daga wajen Babiyon, kiran na shigowa ta yi saurin ɗaga kiran ta kara a kunnenta.

Babiyo ko amsa sallamarta bai tsaya yi ba, a kausashe ya furta, "A tattaro kowa da kowa, iyaye da yara su haɗu a fada!" Yana gama faɗin haka ya katse kiran.

_Lagos_

Kallo ɗaya kawai za kai wa Laushi gabanka ya faɗi in har ka mata farin sani a baya, don yanzu ta yi wani irin zabgewa ta lalace saboda cutar da ke neman haukata ƙwaƙwalwarta. Wani lokacin haka za ta yi abu kamar na mai hankali, wani lokacin kuma kamar haka-haka. So da dama tafi zama shuru ta ƙurawa wani waje idanu ko kuma ta kafe Meema ko Ladi Katifa da idanu tana hawaye. Idan kuma abun ya lafa, baza ka taɓa tunanin tana da wani cuta a ƙwaƙwalwarta ba sai dai uban rama da tayi don dogon hanci da manyan idanunta kawai kake hangowa a waje.

Ɓangaren Yasaar kuwa, ya gama haɗa plan ɗinsa wanda abokinsa Layos ke ba shi gudunmawa domin ganin bayan Sabo da Kaza. Don Yasaar ya lashi takobin sai ya nunawa Sabo da Kaza ya fishi sanin kan tsiya...

Yau da Laushi ta tashi da ƙarfin jiki domin cutar ta ɗan lafa mata. Sai dai gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake. Sauka daga kan gado ta yi tare da yaye duvet ɗin da ta lulluɓa da shi tare da kallon gefenta da Meema ke kwance tana bacci. Gashin da ya rufe idanun Meeman ta mayar dashi baya tare da kallon fuskanta na kusan tsayin mintuna biyar. Kanta ne ta ji ya mata wani duum har sai da ta kai hannu ta riƙe kan na wasu mintuna kamun ta kuma mayar da kanta kan Meema da girma ya fara zuwan mata. Don shekarunta goma sha ɗaya, watannin kaɗan ne babu. Tana da tsayi don ko a yanzu kaɗan ya rage ta kamo uwar, kyawunta sai daɗa fitowa ya ke. Komai na Meema mai matukar kyau ne. Da kallo ta bi tun daga kan Meema har ƙafafunta, gabanta ne ya faɗi sosai ganin irin dirin da Allah ya yi mata, don duk yanda ake koɗa kyawun dirin jikinta ta san idan Meema ta ƙara wasu shekaru biyu zuwa uku nan gaba, komai na halittar jikinta fitowa zai yi wanda kuma hakan faɗar mata da gaba ya ke. Idanun Meeman ta kalla ganin yanda zararan gashin giranta suka kwanto saboda tsayin su kamar artificial.

"Wanene kai? Kana ina don girman Allah??" Laushi ta faɗi a kan laɓɓanta tana kallon fuskan Meeman sosai.

A hankali Meema ta buɗe idanunta tare da faɗin, "Mummy, da wa kike magana??"

Hannu Laushi ta kai tare da shafa kanta sannan ta ce, "Ina kallon fuskanki ne ko Allah zai saka in ga kamannin mahaifinki a fuskanki har Allah yasa in gano shi."

Wani murmushin Meema da baccin ya ƙaurace a idanunta ta yi tare da faɗin, "Mum, ki kwantar da hankalinki. Ke kaɗai ma kin ishe ni, yanzu ban ma so in san wanene babana. Ko da can da nake damun ki saboda abunda kike yi ne da maza, wallahi mummy ji na ke kamar in cakawa duk namijin da ya taɓa jikinki wuƙa a nan," ta ƙarisa maganar tare da nuna ramin maƙoshinta.

Kallonta kawai Laushi ke yi without blinking. Tun Meema na da rai years, Laushi ta fahimci ita yarinya ce mai matuƙar wayo kuma bata mance duk wani abu da ta saka a ƙwaƙwalwarta. A yanzu haka idan Meema na tuno mata wasu abubuwan da suka faru tun tana da five years a duniya, abun matuƙar mamaki yake bata.

Shafa fuskarsa ta yi tare da faɗin, "Za ki yi lattin zuwa school, ki tashi ki wanka don yau ba aunty Ladi ko Uncle Salma bane za su kai ki, ni da kaina zan kai ki."

Gyaɗa kai Meema ta yi tare da sauka a kan gadon ta nufi bayin da ke cikin ɗakin. Da idanu Laushi ta bita har ta shige ta rufo ƙofa.

_Abuja_

Gaba ɗaya ɗakin a cike yake babu masaka tsinke kasancewar rabi da kwatan Arɗo Barkinɗo ne a cikin ɗakin don ma wasu ba garin suke ba sannan ƙananun yara daga masu shekaru sha biyu zuwa ƙasa ban da su a wannan taron. Amma tun daga kan baffanni, iyaye mata, ƙannai, yayyai da wasu daga cikin manyan jikoki duk suna wajen.

Tsit ɗakin ya ɗauka sakamakon isowar Babiyo hannunsa riƙe da golden stick ɗinsa kuma fuskansa a murtuke kuma a ɓace, wanda karyar duk wani mai shekaru hamsin zuwa ƙasa ya ce ya taɓa ganin bayyanar ɓacin ran Babiyo har ya nuna a fuska haka. Don shi ka'ida a yanayin zamansa ko gyaran muryansa ake fahimtar ɓacin ransa.

A bayansa Mamiyo ce, sai dai ita tata fuskan babu yabo babu fallasa, domin shi ba a ɗaure yake ba, kuma shi ba murmushi bane a samansa.

Babiyon ne ya soma zama akan kujerarsa ta sarautar Arɗo Barkinɗo ya wani karkace kaɗan tare da watsa hannayansa a saman hannun kujeran yana kallon kowa ɗai-ɗai da tsananin ɓacin ran da ya haddasa cikkunan mutane da dama da ke zaune a wajan murɗawar tsoro.

Zama Mamiyo ta yi a nata kujeran tana ɗan sakin murmushi a kan laɓɓanta don tabbas ta san yau a kwai tashin hankali ganin yanayin Babiyon da ko ita sau ɗaya ta taɓa ganin haka a iya zaman da suka yi, kuma ba ƙaramin hukunci ya yi ba a wancan lokacin da ya girgiza uban kowa da ke cikin Arɗo Barkinɗo.

"A buɗe taro da addu'a a taƙaice!" Faɗin Babiyo a kausashe wanda ya saka kusan su duka ɗagowa suka kallesa don kowa ya san Babiyo dai ya fi son doguwar addu'a.

Nan da nan akai addu'ar aka shafa kowa na jiran jin bayani daga bakin Babiyo da kuma irin hukuncin da zai aiwatar a yau.

"A jiya, ashirin da ɗaya ga watan Nuwamba, dubu biyu da takwas, an samu wani mara albarkan ya shigo har Arɗo Barkinɗo kamar yanda wasu suke tunani, domin cutar da jikana wanda da badan Allah ya yi yana da tsawon rai da kuma sauran shan ruwansa a duniya ba, da yanzu haka wani zancen ake yi. To ina son kowa da ke cikin ɗakin nan ya saurare ni da kyau! Wallahi, Tallahi, thumma Billahil azim ba zan kyale duk wanda ya yi wannan yunƙurin ba, walau a wajen Arɗo Barkinɗo ya ke, ko kuma a cikin Arɗo Barkinɗo kai ko a wata duniyar ya ke, sai na bincikosa kuma abunda zan yi......" Yana kawo nan ya wani cije leɓe tare da girgiza kai yana buga golden stick ɗinsa a ƙasa rai ɓace.

Baffa Jibrila gangan jiki da ruhinsa wani irin kakkarwa suka shiga yi don ji ya yi kamar kai tsaye Babiyo da shi ya ke magana. Duk da Acn da ke ɗakin wani irin zufa ya ke yi.

Mamiyo kuwa, duk ƙarfin zuciya irin nata sai da ta girgiza tare da tsoron kalaman Babiyon, don tunda ya furta, sai ya binciko kamar yanda ya yi alwashi. Hankalinta ne ya yi wani irin mugun tashi, duk wani farin ciki da ganin ita ce da nasarar da ta shigo da shi nan take ya yi fitar bindiga..

Dogon numfashi Babiyo ya ja tare da cigaba da faɗin, "Abdul-Hameed babu abunda zai same shi da izinin ubangiji, kuma ko ina da rai, ko ban da shi, in Sha Allah har shugaban ƙasar Nigeria sai ya yi!"

Dumm gaban Baffa Jibrila ya sake bugawa da ƙarfi, zuciyarsa har wani tsalle take yi kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito ganin kamar shaguɓe Babiyon ke masa.

Mamiyo kuwa tsabar yanda maganar Babiyo ya dake ta wani suman wucin gadi ta yi a nan zaune. Don ji ta yi kunnuwanta sun yi mata wani dummm, can kuma ta koma ji shuuuu a cikin masarrafin jinta kamar rediyon da aka daukewa wuta. Ta kusa mintuna uku tana jin haka kamun komai ya saisaitun mata har ta soma tsinkayan maganar Babiyo ta gaba.

"Abu na biyu kuma, tambaya nake son yi shin yaushe Estate ɗina ya zama dandalin tashin hankali da ƙananun magana? Shin na mutu ne, ko kuwa ban da amfani ne da har ke, Samira yaushe har wuyanki ya yi kaurin da za ki wanke ƙafafu ki tafin gidan Giɗaɗo kina ciwa matarsa mutunci?"

Jikin Aunty Samira rawa kawai ya ke yi ta kasa ko ɗagowa ta kalli Babiyon don sai yanzu dana sanin rashin mutuncin da ta yi wa mama Halima ya zo mata.

Mama Halima da ke gefe kuwa, babu abunda take yi sai hawaye. Haka ɓangaren amarya Mardiya ita ma da sai daga baya ta samu labarin sharrin rashin zuwanta gidan miji da duburci ya same ta. Shima aunty Aunty Samira ce ta saka ta a ɗaki tana bincikarta domin ta ji gaskiya. Anan ita kuma ta yi mata rantsuwar ko fuskan mijin ma bata gani ba balle har ya kusance ta. Hakan ne kuma ya tunzura Aunty Samira take ganin kamar shirin Mama Halima ce saboda kishi.

Jawaad kuwa kansa ya riƙe sosai yana jin takaicin wannan banzar al'adar tonon asirin sirrin auren da har yanzu aka kasa daina yi a cikin familynsa, don ya san tabbas sai Babiyo ya magantu a kai kuma a gaban waɗanan ɗumbin jama'ar.

Habibu kuwa tunda ya saukar da kansa ƙasa bai ɗago ba sai hawayen da ya ke ta tsiyayarwa ganin abunda ake son yiwa mahaifinsa da mahaifiyarsa kuma duk ta silarsa.

Baffa Giɗaɗo kuwa tagumi ya zabga yana kallon tiles ɗin da ke shimfide a ƙasa idanunsa sun tara hawaye yana jin zafin Habibu cikin ransa don gani ya ke duk shi ya jawo masa wannan abu gashi yau za a titsiyesa gaban yayyi, ƙannai, ƴaƴa, surukai da kuma wasu daga cikin ƴaƴan ƴaƴansa (Jikoki) da suka tasa. Shi kansa cike ya ke da mamaki ta yanda a kai kwarya ta fashe bayan shi ya san ko yatsan Mardiya bai taɓa ba, infact ma ko fuskanta bai gani ba a daren jiyan...........

(Wohoho! Ku gyara zama tare da kimtsawa don yanzu gwaramar zai soma. Wani shiri Yasaar ya yi a kan Laushi da Meema ne?🤔🤔🤫🤯)

#Babiyo #Mamiyo #Baffa Giɗaɗo #Baffa Jibrila #Amarya Mardiyya #Hafizu driver/informer #Abdul-Hameed #Habib #Jawaad #Laushi #Meema #My Destiny #Matar Sayyadee #Barka da Sallah *** [7/8, 8:43 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`