My Destiny (Ƙaddarata)

Page 35

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya*

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Zuciya sosai ta ciyo Babiyo ganin ya aje ayar magana amma kuma Samira babu alamu na yin magana a tattare da ita, jikinta ne kawai ke tsuma kamar ɗan taurin da ake bugawa kirari da kiɗan gangi.

Ƙwafa mai sauti Babiyo ya saki tare da furta, "Tunda haka kika zaɓa na tada min hankali a cikin zuri'a, to na baki daga yau zuwa gobe, ki tattara kayanki ki wuce Yola, ko kuma ki bi Tukur ku wuce tare da Zubaida (Ɗiyar Baffa Modibbo kuma ƙanwar Marwanatu) tunda ita ma taƙi zaman aure kuma ta hana wasu su zauna a nasu gidajen."

Bakin Aunty Samira rawa yake yi kamar wacce ke rayuwa a dusar ƙanƙara, so take ta buɗe baki ta nemi yafiya, amma ta san muddin ta yi hakan ta kuma jawowa kanta bala'i da masifa wanda zai shafi har da mahaifinta wanda ƙani yake a wajan Babiyo ɗin, uba ɗaya amma uwa kowa da tasa.

Aunty Zubaida kuka take sosai rakuɓe da jikin kakarta, mahaifiyar Baffa Modibbo kuma matar Babiyo. Sai dai duk da kasancewarta matarsa, tamkar sakakka haka take cikin gidan ita da ɗayar matan, don gwara ma ita akan ɗayar kasancewar ita ko maganarta ma ba a ji kuma ba kowa ke zuwa inda take ba, hakan kuma umarni ne daga Mamiyo wacce ta yiwa Babiyo fanfo akan haka, shi kuma ya amince sakamakon haushin ɗanta ɗaya tilo da yake ji, wato Ɓalerin da ya kora a gidan shekaru sha da suka wuce.

Kallon da Babiyo ya watsowa Baffa Giɗaɗo ne ya saka hantar cikinsa ƙadawa ya sunkuyar da kai gabansa na faɗuwa yana fatan Allah yasa indai tambaya ce game da budurcin Mardiya, ayi sa a keɓance ba a gaban wannan ɗunbin jama'ar ba. Sai dai kash! Addu'arsa bata karɓu ba sakamakon jeho masa tambaya da Babiyon ya yi wanda ya ji saukar sautin har cikin ƙoƙwan kansa tamkar aradu ce ta faɗo masa.

"Menene gaskiya game da zancen kwaryar da ka fasa? Shin Mardiya ba ta je da budurcinta ɗakinka bane?"

Ba shi kaɗai da akai wa tambayar ba, mama Halima, Habib, Jawaad, surukansa, hatta ƴaƴansa mata da kuma wasu daga cikin jikokin wani irin duum suka ji tare da wani irin kunya da takaici da ya lulluɓe su, musamman ma Habibu da yake jin kamar ya ruga da gudu ya fice daga ɗakin taron.

Mardiya kuwa kuka mai narka zuciya ta saki tana jin ina ma ƙasa ta buɗe ta shige ciki ta huta da wannan tereran banƙadar da za ayi mata da wanda take masa kallon uba ba miji ba.

Mamiyo kuwa wani gyaran zaman ƙasaita ta yi don ta riga ta san Baffa Giɗaɗo ba zai musa akan Mardiya bata zo da budurcinta ba kasancewar tana da tabbacin ya shaƙi tutaren da ta goga a jikin Mardiyan lungu da saƙo a jikinta.

Babiyo kallon gefen da ya jiyo sautin muryan kukan Mardiyan ya yi yana jin wani takaicin na turniƙesa tare da fatan Allah ya sa ba dagaske bane abunda ake zarginta da shi, don idan ya tabbata gaskiya ne, shi kaɗai ya san irin hukuncin da zai yi. Mayar da kallonsa wajen Baffa Giɗaɗo ya yi yana jiran ƙarin bayani daga gare sa.

Girgiza kai Baffa Giɗaɗo ya yi tare da faɗin, "Ba gaskiya bane abunda ake yawo dashi a cikin Estate ɗin nan. Ni ko hannun Mardiya ban taɓa ba a jiyan balle har in san budurwar ce ko akasin haka."

Wani irin zillo Mamiyo ta yi tare da sakin wani bahagon tarin da ya zo mata a bazata sakamakon jin zancen da ba tai tsammanin jinsa ba a cikin masarrafar jinta. Dakyar tarin ya tsaya don sai da ɗaya daga cikin jikokin da ke ɗakin ta yi saurin isa ga dispenser ta tsiyayo mata ruwa a glass cup tare da miƙa mata. Tass ta sanye ruwan tana rarraba idanu. Sai da ta saisaita kanta tukun ta soma magana kasancewar gaba ɗaya wajen zubo mata idanu a kai har da ƴaƴanta,

"Wannan wani irin zancen banza ne? Wa ka ke son mayarwa abokan wasanka a nan? Ya za ka fasa kwarya da hannunka, sannan ka zo kana faɗa mana ko hannun Mardiya baka taɓa ba! To uban wa ya fasa kenan? Kuma menene amfanin abunda ka aikata?" Da huci ta ƙarisa maganar.

Babiyo da ya ɗauke idanunsa a kan Mamiyo tun san da ta soma maganar, wani irin murmushin ne ya suɓuce masa har sai da hakan ya bayyana wanda ya saka gaba ɗaya ɗakin suka wani irin ɗauke numfashin mamaki don babu wanda bai ga hakan ba shimfide a saman fuskansa wanda abu ne mai matuƙar wuya hakan.

Kan Baffa Giɗaɗo a ƙasa ya kuma maimaita abunda ya faɗi cike da tabbaci. Mamiyo ta buɗe baki za ta kuma yin magana, Babiyo ya ɗaga mata hannu alamar bai son jin komai daga gare ta.

Wani irin tsaam ta yi, domin hakan wani abu da bai taɓa faruwa ba a kaf tarihin zaman fadar Babiyon.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Na ji daɗi kwarai dagaske jin wacce na ke da tabbaci a kan tarbiyarta ɗari bisa ɗari, hakan ya ke. Wannan abu ya sanyaya min zuciya har ya saka na janye hukuncin da na zartar a karo na biyu a rayuwata; na farko dawowar Belɗo cikin gidan nan, na biyu kuma yafewa Samira akan abunda ta aikatawa Halima na rashin kunya. Na yafe miki Samira, amma ki je har gida ki nai mi yafiyar Halima akan rashin kunyar da kika mata idan an tashi daga zaman nan."

Aunty Samira ji ta yi kamar an tsoma ta a aljanna, nan da nan ta shiga kwararowa Babiyo godiya da kuma addu'ar tsawon rai.

Mamiyo kuwa ji ta yi ƙwaƙwalwarta na neman fashewa, hankalinta ya mugun tashi sosai ganin cikin ƙanƙanin lokaci komai yana neman rincaɓe mata.

"Daga yau, a yanzu kuma, ban so na ƙara jin wata magana dangane da fashewar kwarya har abada. Duk wanda ya taso da ita kuwa..........Hmm! Ba zan ce komai ba, na san dai kowa ya san irin hukuncin da zan iya yankewa. Ayi dogon addu'a ga Abdul-Hameed da ke kwance a kan gadon asibiti," faɗin Babiyo murmushi ɗauke a fuskansa.

Cikin sakonni ɗakin ya ɗauki sauntin Jawaad yana koro addu'a kamar yanda Babiyo ya faɗi. A cikin addu'ar kuwa, ya haɗo har da wanda ke neman rayuwar Abdul-Hameed ɗin da kuma duk wanda ke son ya ga ya tarwatsa Arɗo Barkinɗo na jiki da na nesa.

Sosai Mamiyo ta sha jinin jikinta, lokaci guda ƙiyayyar Jawaad ɗin ya kuma sukar zuciyarsa ita da ƴaƴanta.

Bayan kammala addu'a, duka ƴaƴan Babiyo suka nufo sa yana shafa kawunansu tare da saka masu albarka suna ficewa daga ɗakin.

Jawaad da Habibu kuwa, kai tsaye suka wuce asibiti don basu samu labarin abunda ya faru ba sai da asuba da suka fito masallaci sallah. Bayan an idar da sallah ne Babiyo ya sanar. Hankulansu ba ƙaramin tashi ya yi ba da jin hakan.

Ko da suka isa asibitin, kwance suka taras dashi yana kallon sama an saka masa na'urar numfashi, ƙeyarsa kuma wani tafkeken ɗinki ne an rufe da bandage.

Habib da yafi Jawaad nuna rauninsa a zahiri, tuni ya soma zubda hawaye yana la'antar duk wanda ya yiwa aminin nasa haka. Jawaad kuwa idanunsa ne sukai jajir laɓɓansa na motsawa ganin halin da ɗan uwansa ya ke ciki. Su ɗan jima a asibitin kamun kowannen su ya nufi gidan amaryarsa cikin motocinsu.

Ɗilin! Ƙarar shigowar saƙo ya shigo wayar Jawaad. Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar dake cikin bonet tare da shigo inbox ɗin.

_Assalamu alaikum Oga, ga ta nan yanzu muka ga ta fito cikin wata makaranta ita kaɗai. Yanzu haka ina bibiyarta a baya. Sai dai kuma tun fitowarta na lura da wasu suna bibiyarta ita ma, kuma sam ban yarda da su ba. Umarninka kawai nake jira._

Wani irin taka burki Jawaad ya yi tare da silalewa gefen titi ya faka sannan ya dannawa wanda ya turo maka da saƙon kira. Bugu biyu ya ɗaga kiran.

"Har yanzu ana bin ta ɗin ne? Ka yi duk yanda za ka yi ka saka ta shiga motarka, kar ka kuskura wani abu ya same ta!" Ya ƙarisa maganar da ɗan tsawa.

"Yanzun nan kuwa, dama umarninka na ke jira," yana gama faɗin haka ya katse kiran tare da ɗage tinted glass window sama ya shiga bin bayan Laushi.

Motar da take bin bayan Laushin na gab da shan gabanta, shi kuma ya taka motarsa da ƙarfi ya riga su shan gabanta tare da buɗe murfin gaba ya furta cikin sauri,

"Shiga da sauri ki rufo ƙofar!"

A razane ta ɗan ja baya, amma ganin yanda motar bayansu ta ja wani mahaukacin burki, sannan kuma ta yi arba da fuskan Yasaar bata san lokacin da ta afka cikin motar da sauri ba ta rufe murfin motar shi kuma ya ja motar a ɗari da hamsin.

Ganin haka Yasaar ma ya taka tashi motar da uban gudu yana bin bayansu. So ya ke ya fito da bindiga ya yi harbi amma babu dama don hakan zai iya jawo hankula har asirinsa ya tonu.

Wani irin duka ya kaiwa steri da ƙarfi ganin sun ɓacewa ganinsa. Sai kawai ya juya kan motar ya koma makarantarsu Meema domin ɗauko.

"Idan kin san wata, to baki san wata ba. Zan yi amfani da ƴarki kuma rauninki, dole ki fito a duk inda kika ɓuya!" Faɗin Yasaar.

Abokinsa da ke gefensa ya girgiza kai tare da faɗin, "Ka yi wani abu yanzun nan idan ba haka ba wallahi asirinka ya gama tonuwa idan har ta koma gida ta kira Sabo da Kaza. Kuma hakan idan har ya ji kashinka ya gama bushewa. Wallahi kashe ka zai yi!"

Tsaam Yasaar ya yi yana wani nazari a zuciyarsa. Can kuma ya saki murmushi tare da faɗin, "Zan yi amfani da salon yaudarar da ta yi min har aka cafke ni na yi zaman gidan yari tare da rasa tagwainina abun ƙaunata. Yanzu zan tura jami'an NDLEA gidan bayan na basu bayani akan abubuwan da ake aikatawa, sannan inyi wa Sabo da Kaza cunnensa har inda yake duk da na san ba za a jima ba zai kuɓuto, amma kuma zan cusa wata mummunar ƙiyayyar Zeenatu a zuciyarsa. Ba zai taɓa kawo ni ne na munafuncesa ba, Zeenah ce za ta zama first suspect ɗinsa. Kuma ba zai taɓa kyaleta ba. Ka ga kenan na jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya," yana gama faɗin haka ya yi wasu ƴan danne-danne a waya na kusan mintuna goma sannan ya juya kan mota zuwa makarantarsu Meema.

A cikin motar Informer ɗin Jawaad kuwa, mugun gudu suka sharara kamar za su bar garin Lagos sannan ya yi parking a gefen hanya ya kira Number ɗin Jawaad.

Laushi kuwa gaba ɗaya ta ruɗe, hankalinta ya yi mugun tashin da ciwonta ya kusa motsawa. Hankalinta kacokam ya koma kan ƴarta Meema, don ta san halin Yasaar, tunda bai same ta ba, kan ƴarta zai koma.

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ƴata!! Na shiga uku. Meema, don girman Allah malam mu koma in ɗauko ƴata, zai cutar min da ƴata wallahi. Ƴata ita ce rayuwata! Ita ce duniyata, ita kaɗai ce dangina. Don Allah ka mayar dani in ɗauko ƴata," faɗin Laushi tana kuka sosai.

Gaba ɗaya a kunnan Jawaad ta yi maganar saboda ya ɗaga kiran Informer ɗin nasa kenan ya jiyo sautinta tana wannan maganar.

"Bata wayar," Jawaad ya faɗi yana mai kumshe idanu don kukanta har cikin zuciyarsa ya ke jinsa.

Miƙa mata wayar Informer ya yi tare da faɗin, "Amshi, za ayi maki magana."

Saurin warce wayar ta yi tare da karawa a kunne ta soma faɗin, "Yasaar, na roƙeƙa da girman ubangiji kar ka cutar min da ƴata. Ƴata ba tai maka komai ba, ni ce na yi maka laifi. Zan zo gare ka ka hukuntani amma kar ka cutar min da ƴata."

"Nutsu!" Jawaad ya faɗi a hankali yana lumshe idanunsa. Ya na iya hango tsagwaran tashin hankali da damuwar da take ciki a muryanta.

Cak ta tsaya da kukan jin saukar muryan da ba na Yasaar ɗin ba. Wani irin ajiyar zuciya tashin hankali ta saki tare da faɗin, "Da wa nake magana? Wanene kai? Ku su waye?? Yasaar ɗin ne ya turo ku? Ƴata! Ina ƴata take?" A hankali ta ƙarisa maganar tare da sumewa a jikin kujera.

Da sauri ya tara hannu tare da caɓe wayar da ke ƙoƙarin faɗuwa ƙasa saboda sake shi da ta yi ya ƙara a kunne tare da faɗin, "Yallaɓai ta suma fa!"

"Kuna ina yanzu?" Jawaad ya faɗi da tashin hankali a muryansa.

"Ga mu a bakin babban hanyar fita daga Lagos."

"Ka sauke glass ƙasa domin iska ya shigo, sannan ka juya ka nemi ƙaramin masauki ta waje-wajen Lagos ɗin sannan ka koma can makarantar ka ɗauko yarinyar. Zan kira ka zuwa anjima bari na ƙarisa gida yanzu na kimtsa. Ni ma zan biyo jirgi na taho Lagos ɗin yau in Sha Allah!" Yana gama faɗin haka ya katse kiran.

Sauke glass ɗin ya yi kamar yanda Jawaad ya umarta sannan ya kunna matar ya juya. Ya ɗan yi tafiya sosai sannan ya taras da masaukin baki dake kan hanya. Har cikin harabar ya yi parking sannan ya fita ya yi booking ɗaki.

Lokacin da ya dawo wajen motar, Laushi ta farfaɗo daga suman da ta yi, sai dai sai rizgar kuka take yi tana faɗin ƴarta.

Zagayawa ya yi ya shiga mazaunin driver ya zauna tare da fuskantarta ya ce, "Ki kwantar da hankalinki, in Sha Allah yanzun nan zan koma in ɗauko maki ƴarki. Babu abunda zai same ta. Yanzu ki sauka mu shiga ciki in nuna miki ɗakin da za ki zauna sai in koma can in ɗauko ta."

"Mu tafi tare don Allah! Wallahi hankalina ba zai taɓa kwanciya ba har sai na ga ƴata tukun. Ba ka san wanene Yasaar ba, wallahi zai iya yin komai domin ya ga ya cutar dani. Na shiga uku ni Zeenah! Sam bariki ba tai min riba ba, ga shi yanzu na jefa mu ni da ƴata a cikin halaka. Wa ya san ko ma jinin mahaifina ne ke bibiyata," ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka.

Tausayinta ne ya kama shi, ɗan gyaran murya ya yi tare da faɗin, "Babu yanda za ayi mu tafi tare, kin san dai ke ma farautar rayuwarki ake yi. Don haka ki haƙuri ki zauna anan ɗin, ni kuma in Sha Allah zan dawo miki da ɗiyarki."

Ba don ta so ba ta amince don ta san tabbas Yasaar ba zai taɓa hutawa ba har sai ya ga ita da ƴarta a hannunsa. Pass ɗin da zai bashi damar ɗauko Meeman ta bashi, don ko zai mutu baza a bari ya ɗauki Meeman ba sai da shi.

Bayan ya kai ta masaukin tare da yi mata order ɗin abincin da ya san ba lallai bane ta iya cinsa, sannan ya kama hanyar cikin Lagos ɗin domin ɗauko Meema.

_Yasaar_ Yana juya kan mota bai tsaya ko ina ba sai makarantar su Meema, kasancewar ya san sai da pass ake ɗaukar ko wani ɗalibi, tun kwana biyu kamun yau ya nemi sample na pass ɗin ya buga exactly irin sa tare da sunan Meema a jiki. Shiyasa ko da ya isa bai sha wahalar samun Meeman ba bayan ya sharara masu ƙaryar uwar tana fitowa daga makaranta yayin kawo Meeman ta gamu da hatsari mai muni kuma yanzu haka tana asibiti bata san inda kanta yake ba, shiyasa ya zo tafiya da Meeman.

Sosai shugabar makarantar ta nuna jimami a kan haka tare da tausayawa Meeman, don ita ma ta san irin ƙauna da shaƙuwar da ke tsakanin Meeman da mahaifiyarta, musamman ba dai Meema don duk labarinta ba ya wuce mummyna kaza, mummyna kaza.

Har wajen motar Yasaar classroom teachern su Meema da shugabar makarantar ta rako Meema da ke wa Yasaar kallon ban sanka ba, sai dai ta yi shuru ne kawai ganin pass ɗin da zai bada damar ɗaukarta wanda mummynta ne kawai ke da shi a hannunsa, sannan kuma da cewar da aka mata mummyn ce ta ce a ɗauko ta, sai dai ba su faɗa mata ƙaryar da Yasaar ya sharara masu ba gudun kada hankalinta ya tashi.

Bayan ficewarsa da kamar mintuna ashirin da biyu, motar Informer ɗin Jawaad ya yi parking a ƙofar gate ɗin makarantar tare da fitowa daga cikin motar ya nufi gate ɗin ya kwankwasa. Mai gadi ya buɗe tare da tambayarsa lafiya, sai ya ce masa ya zo wajen shugabar makarantar ne. Hakan da mai gadi ya ji, sai ya buɗe masa ƙaramar ƙofar ya shiga.

Kai tsaye office ɗin shugabar makarantar ya nufa, cikin sa a kuwa ita kaɗai ce a ciki. Sai ya nemi izinin shiga ya shiga ciki. Da hannu ta yi masa nuni da wajan zama a ɗaya daga cikin kujerun da ke gaban teburin da ta aje hannunta biyu a kai fuskanta faɗaɗe da murmushi.

Sai da ya zauna sannan ya gaishe ta cikin harshen turanci. Cike da sakin fuska ta amsa sannan ta tambayesa abunda ke tafe da shi.

Dogon bayanin da ya mata akan abunda ke tafe dashi ne ya saka wani siririn zufa ya soma biyo bayan kunnanta zuwa wuyanta har cikin rigarta duk da kuwa Ac da ke aikin cikin kantameman ofishin. Hankalinta bai ƙure tashi ba, sai da ta ga ya ajiye mata plastic pass ɗin Meeman a kan teburinta. Ɗauka ta yi ta shiga ƙarewa pass ɗin kallo hankalinta na tashi kuma a lokaci ɗaya ta shiga ruɗu da kokwanta shin wani pass ne a ciki na gaskiya, wanda Yasaar ya kowa ko kuwa wannan da ke riƙe a hannunta.

Shi kuwa ganin irin kallon zargi da rashin amincewar da take masa, sai ya gyara zama tare da faɗin, "Domin tabbatarwa, ki duba file ɗin ɗalibar taki ki ɗauko Number ɗin mahaifiyar sai ki kira domin ki tabbatar."

Sosai shugabar makarantar ta ji daɗin wannan idea ɗin. Cikin sauri ta soma duba numbers ɗin files dake cikin wani dogon drawer har ta kawo kan na Meema ta ɗauko ta dawo ta zauna tare da kwashe number ɗin a wayarta ta danna kira. Ringing biyu Laushi ta ɗaga ganin kira daga makarantarsu Meeman.

"Madam ke ce kika turo wani ya zo ɗaukar ƴarki a makaranta yanzu? Gashi nan a gabanmu yanzu haka," shugabar makaranta ta faɗi cikin harshen turanci bayan kammala gaisuwar da suka yi.

"Eh, ni ce. Don Allah ku bashi ita yanzu, don rayuwar yarinyar bai ciki tsaro," Laushi ta faɗi cikin sauri.

"Jesus Christ!" Faɗin shugabar makarantar bayan ta miƙe tsaye, kasancewarta Christian.

Cikin tashin hankali Informer shima ya miƙe da sauri yana kallonta.

Laushi kuwa da ihun Jesus Christ ya sauka a dodon kunnenta, duk da bata san ainahin abunda ke faruwa ba, jikinta ne ya hau wani irin tsuma, nan da nan kanta ya sara, zazzaɓi mai zafi ya shiga rufe jikinta...........

(Hmmmmmm🤔🤔🙆)

#Meemah #Laushi #Yasaar #Sabo da Kaza #Jawaad #My Destiny #Ƙaddarata #Matar Sayyadee *** [7/8, 8:43 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'uerr Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`