My Destiny (Ƙaddarata)

Page 37

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama 👆🏼 ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Wayarsa ce ta yi ƙara alamar shigowar kira, wani irin zufa ce ta yanko masa tun daga tsakar kansa har zuwa kafaɗunsa ganin sunan da ya bayyana jikin screen ɗin wayar, "Lahaula wala ƙuwata illah billah! Yanzu idan na ɗauki wayar nan mai zan faɗawa yallaɓai ni, Laminu? Assha! Ko waye wannan daya zo ya ɗauki ƴar nan har cikin makaranta, Ubangiji ka ɗebe masa albarka," Informer ɗin Jawaad ya faɗi yana mai cigaba da warce zufan da ke yankowa daga goshinsa.

Sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga hannunsa na rawa kamar mazari ya kara a kunnansa, "Assalamu alaikum, Yallaɓai."

"Wa'alaikassalam, Laminu. Ina kuma ka aje wayar yana ta ringing har ya kusa katsewa kamun ka ɗauki kiran, ko akwai wata matsalar ne, ka ɗauko uwar da ƴar?" muryan Jawaad ta daki dodon kunnan Laminu, wanda hakan yayi barazana ga zuciyarsa.

"Ƴal....Yallaɓ...Ƴallaɓa!" Laminu ya faɗi cikin in'ina, sai dai bai san lokacin da yayi ɗif ba sakamakon wata tsawa da Jawaad ya sakar masa wanda ya kusa tarwatsa masa masarrafar jinsa.

"Will you stop that nonsense and tell me exactly what's going on their!" Jawaad ɗin ne ya faɗi hakan a tsawace.

"Yallaɓai kai min aikin gafara da abunda zan faɗi yanzu!" ya faɗi a raunane tare da cigaba da faɗin, "Na yi nasarar ɗauko uwar, sai dai ƴar wani ya riga ni ɗauke ta daga can makarantar su, kuma ina kyautata zato waɗanda na gani suna bin bayan uwar ne."

Ɗif Jawaad ya yanke wayar tare da maka ta da jikin bango ta faɗo ƙasa a tarwatse har sai da Khairat matarsa dake kitchen ta fito da sauri saboda razanar da tayi.

"Lafiya Hamma Jawaad?" ta faɗi tare da isa wajen fasasshiyar wayar da ta tarwatse a ƙasa tare da tattaro ta.

Jawaad bai iya bata amsa ba sai huci kawai ya ke yi zuciyarsa na zafi tare da azalzalarsa akan ya bi jirgi yau ɗinnan zuwa Lagos domin aiwatar da aikin da kansa, Babiyo kuma ya daɗe bai yi abunda zuciyarsa ta raya masa ba.

Ɗagowa ya yi tare da kallon Khairta da jikinta ke rawa hannunta kuma riƙe da fasasshiyar wayarsa tana kallonsa. Ƙirƙirar murmushi ya yi tare da faɗin, "Suɓucewa ta yi a hannuna ta fashe, ki koma ki cigaba da abunda kike yi zan ɗan fita yanzu in dubo Hamma Abdul-Hameed a asibiti."

Gyaɗa masa kai kawai ta yi tare da miƙa masa fasasshiyar wayar sannan ta koma kitchen ɗin jiki a saɓule.

Shi kuwa Jawaad zare sims ɗinsa dake cikin wayar kawai ya yi tare da aje kwankwon ya fice yana mai gyarawa link ɗin hannun rigarsa zama. Cikin sassarfa ya nufi wajen motarsa ya buɗe tare da shiga ya tada ya bar cikin gidan bayan mai gadi ya wangale masa gate.

Cinna hancin motar ya yi direct zuwa Arɗo Barkinɗo specialist hospital kamar yanda ya faɗawa amaryarsa Khairat. Yana parking ya fito ya nufi hanyar da zata sada sa da cikin wards zuwa aminity inda Abdul-Hameed ɗin ke kwance, sai dai kiciɓis ya yi da Baffa Giɗaɗo bayansa kuma Mama Halima ce hannunta riƙe da wata kyakkyawar ƙatuwar kula.

"Kai Jawaad! Zo nan," Baffa Giɗaɗo ya yafito sa da hannu fuskansa a haɗe.

Ƙarisawa ya yi tare da duƙawa ya ce, "Baffa awallidjam...."

Daƙuwa Baffa Giɗaɗo ya maka masa tare da faɗin, "Ungo nan," cikin harshen fillanci.

Sunkuyar da kai Jawaad ya yi don ya san dalilin Baffa na daƙuwar da ya yi masa. Baffa Giɗaɗo kuma a zafafe ya soma faɗin, "Wato har kai da nake maka kallon kamar mai hankali ashe ba haka bane kai ma ɗin kamar ɗan uwan naka ke masu irin hankalin mazan shanu ko! To maza ka juya ka koma gidanka don Babiyo na ciki kusa da Abdul-Hameed, yana arba da kai da safiyar nan, Hamma Bobbo (Mahaifin Jawaad ɗin) ne zai amshi hukuncin abunda ka aikata tunda bai baku izinin fitowa ba. Don haka maza juya tun kamun wani tsautsayin ya fito da Babiyon. Kuma don girman Allah Jawaad ko gate ɗin ƙarshe kar ku je kai da ɗan uwanka har sai ranar da za ku bar ƙasar nan."

Gyaɗa kai Jawaad ya yi tare da faɗin, "In sha Allah," sannan ya mayar da idanunsa a kan mama Halima mahaifiyar Habib ya gaida ta sannan ya juya wanda ba haka ɗin ya so ba.

"Hello Yasaar! Buɗe gate maza gamu nan mun shigo layin tare da ita."

Yasaar da ke zaune ya ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya ya yi saurin miƙewa tare ficewa daga ɗakin ya nufi gate ya buɗe, daidai lokacin da abokin nasa ya danno hancin motar zuwa cikin gidan bayan Yasaar ɗin ya ɗan kauce masa.

Farin ciki ne ya mamaye zuciyar Yasaar lokacin da abokinsa ya cicciɓo Ladi ya fito da ita daga cikin motar.

"Kai ta ɗakin dake gaban wanda Meema ke ciki, kar ka haɗa su waje guda," Yasaar ya faɗi yana bin bayanabokinsa da ya nufi cikin gidan.

"Yauwa aje shegiyar nan kan kujerar ka ƙulle min ita da kyau, dole ma ta faɗa min inda Laushi take ko kuma ta rasa rayuwarta. Shiga kitchen ka kandmomin ruwan ƙanƙara cikin roba," Yasaar ya ƙarisa magamar tare da jawo wata kujerar ya zauna yana fuskantar Ladi Katifa kusa-kusa. "Ka tabbatar ta ƙullu da kyau?" Yasaar ɗin ya kuma faɗin ganin abokin nasa ya matsa daga bayan Ladi katifa kasancewar ya haɗe hannunta biyu ta baya ne ya ƙulle.

"Ai ko mu biyu sai munyi dagaske za mu iya kwance wannan ɗauri, Yasin!" Abokin ya faɗi.

"Yauwa, haka nake so. Yanzu kandamomin ruwa ka kawo min," ya faɗi yana mai ɗago fuskan Ladi wacce bata san inda kanta yake ba.

Jim kaɗan sai ga abokinsa hannunsa ɗauke da madaidaiciyar roba mai ɗauke da ruwan sanyi har wani naso yake yi, irin wannan ruwanne mai kashe haƙori saboda tsabar sanyi. Yasaar yana amsa bai yi wata-wata ba ya antaya a fuskan Ladi Katifa, a take ta wani ja uban dogon numfashi mai tafe da ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya. Sai da ta kwashi mintuna biyar kamun ta ɗago da kanta tana kuma sakin doguwar ajiyar zuciya tare da sauke fuskanta a kan na Yasaar wanda ya yi kicin-kicin kamar an aiko masa da saƙon mutuwa.

"Yasaaar!" Ladi katifa ta faɗi saman laɓɓanta idanunta jazurrr.

"Ina Laushi take?" Yasaar ya faɗi fuskansa babu ɗigon rahama.

"Ban sani ba, ban san inda take ba Yasaar," Ladi ta faɗi cikin mawuyacin hali.

"Wannan itace tambaya da zan miki na ƙarshe; ina Laushi take??" a kausashe ya yi mata tambayar.

"Ban sani ba, Yasaar. Wallahi ban san inda Laushi take ba!" ta ƙarisa maganar hawaye na sauko mata.

"Ɗauko min wannan ƙaramar akwatin," Yasaar ya faɗi yana mai kallon abokinsa.

Da sauri abokin ya juya ya fice daga ɗakin, jim kaɗan sai gashi da wani madaidaicin akwati mai kama da first aid box. Amsar akwatin yayi tare da buɗewa ya ɗauko wata kaifaffiyar almakashi ya riƙe da kyau yana kallon fuskan Ladi Katifa wacce tsoro da tashin hankali ya gama mamayeta. Murmushin mugunta ya saki tare da ɗako yatsarta manuni ya zura cikin almakashin still yana kallon fuskanta.

"Dama ta ƙarshe, ina Zeenatu Laushi take?"

Wasu maƙudan hawaye ne suka shiga kwaranyowa daga kurmin idanunta, bakinta na rawa ta furta, "Don tsarkin ubangiji, Yasaar kai min rai, wallahi ban san inda Laushi take ba."

"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'uuuuun!" Ladi katifa ta faɗi da ƙarfi sakamakon danna almakashin da Yasaar ya yi sai da yatsarta manuni ta fice fit gaba ɗaya, jini kuma ya shiga wani irin tsirtuwa a ƙasa. Nan-da-nan wani irin zufa ya shiga kwaranyo daga ko ina a jikinta, can kuma kanta ya rankwafo alamar sumewa.

"Gyaran wajan da jinin ya ɓata ka mayar da akwatin, wannan shine azabar da zan riƙa mata har sai ya rage babu yatsa ɗaya a hannayenta inhar taƙi buɗe baki ta faɗa min inda zan samu Laushi. Rufe mata baki da salatep, ni zan fita wajen passport ɗin yarinyar can. Ka kula da ita, idan tana jin yunwa ka bata abinci, sannan abu mafi mahimmanci kar ka kuskura taga wannan matar," Yasaar ya faɗi tare da jan kujera baya ya fice daga ɗakin.

Shi kuwa abokin kallon Ladi katifa kawai yake yana haɗiyar yawu domin gaba ɗaya dirin jikinta ya gama tafiya da imaninsa. Salafep ɗin ya manna mata a baki sannan ya shiga gyara wajan.

*Jawaad*

Kai tsaye gida ya dawo, ko bi ta kan Khairat dake gaban dinning tana masa sannu da zuwa bai yi ba, sai ma saurin shigewa ɗakinsa da ya yi ya kullo ƙofa. Sauri-sauri ya buɗe drawer ya ɗauko wata ƙaramar waya nokia 3310 ya saka layinsa a ciki ya dannawa Laminu kira, bugu buyu Laminu ya ɗauki kiran, "Maza-maza ka tafi ka ɗauke Zeenah a inda take ka wuce direct da ita inda na umarceka da ka kai ta. Meema kuma zan saka amin binciken inda take yanzu," yana gama faɗin hakaa ya katse wayar yana huci.

Laminu na gama karɓan umarni daga Jawaad ya kunna mota ya nufi hotel ɗin da Zeenatu take hankali tashe don bai san abunda zai taras ba acan na rashin hankalin daLaushi zata kasance ciki idan taga babu ƴarta tare dashi. Mintuna talatin ta kawo sa hotel ɗin sabida sharara gudun da ya yi. Parking ya yi sannan ya fito daga cikin motar ya doshi cikin hotel ɗin. Yana knocking Laushi ta buɗe da sauri tana wurga idanu ta inda za ta hango Meema.

"Ina ƴata? Ƴata tana ina bawan Allah? Wallahi Meemah ita ce farincikina, idan babu ƴata ba zan iya rayuwa ba. Don Allah ka faɗamin ina ƴata take?"

"Ki kwantar da hankalinki madam, In sha Allah za a ga ƴarki. Ƴallaɓai ya tura a yi bincike, nan da sa'o'i sha biyu ƴarki za ta dawo."

Wani iri ja da baya Laushi ta yi tana girgiza kanta kamun ta saki wani irin ihu ta riƙe kan da hannu biyu saboda wani duum! Da ya yi mata. Can kuma ta shiga buga kan da bango kamar yanda ta saba duk sa'ar da ciwota ya motsa (wato brain aneurysm {Raunanniyar jijiyar jinin kwakwalwa}).

Ku yi haƙuri d wannan please🤗

#Ladi katifa #Meemah #Laushi #Jawaad #Yasaar #Colombia #My Destiny #Matar Sayyadee *** 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`