Page 38
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
"Yallaɓai akwai mummunar matsala fa! Wallahi ga uwar yarinyar nan na kasa controlling ɗinta ni ɗaya, sai yi take kamar mai taɓin kwakwalwa don sai buga kanta take a bango jini na zuwa," faɗin Laminu waya kare a kunnansa, hannunsa ɗaya kuma riƙe da hannun Laushi.
Daga can ɓangaren Jawaad na jiyo ihun Laushin kamar zai fasa dodon kunnensa, wani irin rintse idanu ya yi yana jin jijiyoyin kansa na harbawa haka kuma bugun zuciyarsa na linkuwa, "Laminu, ka yi duk yanda za ka yi ka kaita asibiti mafi ƙwarewa a Lagos, ni ma gani nan zuwa zan biyo jirgi," yana gama faɗin haka ya katse wayar tare da fitowa daga ɗakin ya nufi ɗakin da shine mallakin Khairta amaryarsa.
Sai da ya ɗanyi jim! Kamun ya ɗaga hannunsa ya yi knocking, don tun shekaranjiya da aka kawo ta gidan magana bata shiga tsakaninsu ba sai ɗazu da safe da ya jefar da waya bayan gama waya da Laminu. Haka nan ya ji bai kyauta ba, don ko ba sosai tsakaninsu ita ɗin ƴar uwarsa ce ta jini, ba kuma zai so ai wa Khadija ƙanwarsa haka ba.
Shuru babu amsa bayan kusan second talatin da yin knocking ɗin. Hannu ya kuma kai wa ya yi knocking a karo na biyu, sai dai shima shurun ya ji. Hannu ya ɗaura a kan handle ɗin tare da murɗawa, aikuwa nan take kofar ta buɗe. Kutsa kai ya yi tare da shiga still bakinsa ɗauke da sallama.
Fes, ɗakin yake babu ko ɗigon datti sai ma tashin ƙamshin turaren bakhur yake. Kallon fari ƙal din makeken gadon da ya lailayu da zanin gado mai taushi kalar sararin samaniya. Sai da ya kwashi mintuna uku yana ƙarewa ɗakin kallo kamun ya jawo stool ya zauna yana jiran fitowarta jin ƙarar ruwa a bayi alamar wanka take yi.
Bai wani jima sosai ba ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fito tana goge kanta da ta jiƙa don yanzu ta yi wankan tsarki kasancewar itama ranar ɗaurin aurenta ta soma jinin haila. Duburburcewa ta yi ganinsa zaune a kan stool kuma ya zubawa farar fatar jikinta dake sheƙi irin na fulani, ƙoƙarin juyawa ta yi zuwa bayin don daga ita zai gajerar tawul da bai gai ko guiwarta ba.
"I'm sorry! Na shigo babu permission, tawo ki shirya bari na baki waje idan kin gama ki same ni a ƙasa," yana gama faɗin haka ya juya ya fice.
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi bayan ya fice ya kullo mata ƙofar. Cikin sauri ta soma busar da gashin kanta da hair drayer sannan ta kimtsa a gaggauce gudun barinsa ya yi ta jiranta. Kuma sosai ta ji daɗin ganinsa a ɗakin nata, don fisabilillah ita tun ba yanzu ba take matuƙar ƙaunarsa a zuciyarta.
Takun tafiyarta sa ya ji mai tafe da ƙamshin turaren jikinta ya tilasta masa juyawa yana kallonta cikin doguwar rigar sari ta indiyawa kalaar ja, sai ta lulluɓe kanta da mayafin, fuskanta ta yi kyau sosai duk da ba kwalliya ta yi can sosai ba. Powder ce da man leɓe kawai ta shafa. A kunyace ta ƙariso gabansa tare da durƙusawa ta furta, "Hamma, an tashi lafiya?"
Ɗagota ya yi yana mai sakar mata murmushi tare da faɗin, "Sau nawa za ki gaisuwar, Khairiyyah? Ai mun gaisa," ya ƙarisa maganar yana zaunar da ita a gefensa.
Rufe fuska ta yi da tafin hannunta tana murmushi, shi ma murmushin ya yi tare da faɗin, "You look very beautiful my amarya!"
Ƙara rufe fuskan ta yi da kyau tana dariyar jin daɗi.
"To a saka min abinci mana in karya, don so nake na ɗan fita, amma zan iya yin dare sosai. Da zai mu riƙa waya don kar kiga angon na ki bai dawowa ki ɗauka ko ya ɓace ne, kuma ki shirya yau zan camarcina tabbas," ya ƙarisa maganar yana kashe mata ido ɗaya.
Da sauri ta miƙe ta nufi dinning tana jin matsanaicin kunya ta rufe ta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta yi serving ɗinsa tare da furta, "Na kammala ka zo ka karya, Hamma."
Sai da ya yi murmushi sannan ya miƙe ya nufi dinning ɗin tare da jan kujera ya zauna sannan ya nuna mata wajen zama itama. Zama ta yi a kunyace ta re da ƙara matsar masa da plate din boiled plantain wanda akai wa sorce ɗin kwai da hanta da kayan lambu.
Fork ya ɗauka tare da yin basmala ya soma ci yana kallonta. Nuni ya mata da nata plate ɗin alamar ta ci, sunkuyar da kai ta yi ta soma cako plantain ɗin tare da kaiwa baki. Sun ci suna satar kallon juna.
Murmushi Jawaad ya kuma saki karo na babu adadi tare da aje fork ɗin ya ɗauki tissue ya goge baki tare da jan kujera baya ya miƙe tare da faɗin, "Bari na shiga na shirya na fito."
Gyaɗa masa kai ta yi, shi kuma ya wuce yayin da ita kuma ta hau gyara wajan da suka gama cin abincin.
Ɗakinsa ya shiga ya watsa ruwa a gaggauce sannan ya shirya cikin ƙananun kaya da ya yi masa matuƙar kyau. Agogo ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa sannan ya feshe jikinsa da furare ya ɗauki mukullin mota a kan mirror tare da wayarsa ƙirar android da bata jima da shigowa ba, sai wane-da-wane ma kake gani a hannunsa, shima ya ɗan jima da sayi amma sai jiya ya saka ta a caji, yanzun ma ya ɗauko ta ne saboda fasa sahibarsa da ya fi so a cikin wayoyi wato _Nokia!_
Bai same ta a parlour, sai ya juya ya nufi ɗakinta, sai dai bai yi taku huɗu ba su kai kiciɓis. Saurin ja da baya ta yi tare da faɗin, "Sannu da fitowa."
Hannunta ya riƙo tare da faɗin, "Kina burgeni idan ina ganin wannan kunyar ta ki ta gado, Allah miki albarka. Sai na dawo ki kular min da kan ki, kin ji?"
Gyaɗa masa kai ta yi hawaye na taruwa a idanunta wanda bata san ko na menene ba.
Ɗan yatsa ya kai ya sharce hawayen tare da faɗin, "Menene kuma haka? Ba fa kwana zan yi ba, imfact ba Abuja zan bari ba. Kuma anjima muna tare, In sha Allah. Kina buƙatar wani abu ne?"
Girgiza masa kai ta yi tare da faɗin, "A'a, Allah ya kiyaye ka, ya sa kaje duk inda za ka lafiya ka dawo lafiya," ta ƙarisa muryanta ba cracking alamar kuka take son fashewa dashi.
Janyota ya yi tare da rungumeta sosai sannan ya ɗago kanta ya sumbaceta tare da mata murmushi sannan ya kama hannunta har wajen motarsa. Sai da ya shiga ya tada sannan ya sauke glass tare da furta, "Ki tunani na, ni ma zan yi na ki. Sai na dawo."
Ɗaga masa hannu ta yi guntun hawaye na gangaro mata, girgiza mata kai ya yi sai ta yi saurin share su tana masa murmushi. Sai da taga ficewarsa daga gidan sannan ta juya ta koma ciki.
*HAFIZ INFORMER* Tashin hankalin da yake ciki ba mai misaltuwa bane, don ya tabbatar yanzu idan har komai ya fashe ya shiga uku ya lalace, don sai Babiyo ya ɗauresa har sai igiya yayi rara. Ɗaga idanu sama ya yi yana tuno maganganun sa suka tattauna da Baffa Ɓalerin da bai taɓa tunanin yana raye ba shi da iyalansa, kana ganinsa ka ga Babiyo domin babu inda ya baro Babiyon har baƙar zuciyarsa.
"Idan har kana buƙatar cigabar rayuwarka da rufuwar asirinka cikin Arɗo barkinɗo, to ina son duk wani moves na Mamiyo a tafin hannuna, idan na ce komai, to ina nufin komai. Duk wani abu da ta umarce ka da ka yi, to ka fara sanar min tukun, idan kuma ba haka ba, ka tanaji abunda za ka faɗawa Babiyo domin kare kanka."
Tuno maganar da suka yi ya saka ya fiddo wayarsa cikin aljihu da sauri ya shiga tura saƙo kamar haka; _Ba ita ce ta saka a kashe Abdul-Hameed ba, sai, dai Baffa Jibrila ne ya yi ƙoƙarin ɗaukar ransa! Yanzu haka ban san menene shirin Mamiyo na gaba ba, amma zan yi ƙoƙari in gano don ba ni kaɗai na ke mata aiki ba_
Cikin ƙanƙanin lokaci aka aiko masa da replay kamar haka; _Kai ƙoƙarin gano hakan cikin gaggawa._
Ajiyar zuciya Hafiz ya sauke yana danasanin haɗa kai da ya yi da Mamiyo don yana ji a jikinsa Allura ta kusa tono garma! Ɗauko hoton Meema ya yi a karo na babu adadi ya shiga kallonta kamar zai zaro ta daga cikin hoton, ya yin da ɗaya hannun nasa ke kallon hoton Laushi gabansa na ninninka faɗuwa.
_MAMIYO_ Watsi ta riƙa yi da duk wani abu da taci karo dashi tare da sakin wasu irin numfarfashin baƙin ciki da tashin hankali mara misaltuwa. Jajjayen idanuwanta ta ɗago tare da kallon ƴaƴanta ta furta da ƙarfi, "Na rantse da girman Allah ba zan taɓa sadudu ba, ba zan bari na faɗi a yaƙin da na soma shekarun sittin ba, sai na ƙarisa wannan yaƙi. Ku sani kune kawai za ku rage magadan dukiyar _Arɗo Barkinɗo_, na muku wannan alƙawari! Tana gama faɗin haka ta faɗa ɗakinta ta kullo ƙofa tare da kira wata number da ta yi saving da malam mai huluna sittin da shida. Ringin biyu ya ɗaga yana sakin wata malalaciyar murmushi.
"Malam, a yau ina a warware wannan ƙullin da na saka ka ƙulla, ina son tsohuwar zuma ta dawo tamƙar ranarta ta farƙo ko fiye ma da hakan. Ina son ganin kwakwalwar Abdul-Hameed a birkice, ina son ya rasa sukuni sannan ya kasa jin maganar kowa, ya daina ganin kowa da komai sai wannan yarinyar da na saka kai musu farra'u!" faɗin Mamiyo.
"Yan iya duk yadda kika umarta, amma kuma hakan na da matuƙar hatsari domin zai jawo wasu fitintimu da ɓacin rai har ma da rasa ran kuma......"
"Ka yi yadda na ce kawai malam! Ni ban damu ba ko yaƙi zai ɓalle a Nigeria in har burina da na daɗe ina ginawa kaina da ƴaƴana zai cika."
"Shikenan! Amma duk abunda ya biyo baya, ki kuka da kanki," faɗin malam mai huluna.
Kasancewar Mamiyo ba cikin hayyacinta take ba, sam ba wani fahimtar malam din ta ke sosai ba, burinta kawai Abdul-Hameed ya wulaƙanta sabida kar burin Babiyo ya cika na shirin mayar dashi minister ɗin da ya ke shirin yi.......
Hmmmmm🤔🤔🤔 to bari dai na yi shuru🤐
#Jawaad #Laushi #Meema #Abdul-Hameed #Mamiyo #Khairat #Hafiz informer #Baffa Ɓaleri #Minister #Ƙaddarata #Matar Sayyadee *** [7/30, 3:25 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`