My Destiny (Ƙaddarata)

Page 40

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

A firgice ya kuma zaburowa tare da kai hannu ya kamo iska yana faɗin, "Babu inda za ki je, muna nan tare dake. Na miki alƙawarin kasancewa tare da ke for better for worse, Zeenah wallahi ban taɓa son wata halitta a duniyar nan ba kamar yanda na ke ƙaunarki. Ki istibra'i, zan ɗauke ki muje a ɗaura mana aure mu tafi Maldives mu ci amarcin mu a can, babu wanda zai takura mana and I promise to protect you, Laushina!" ya ƙarisa maganar yana kaiwa iska sumba (Kiss).

Duk da can ƙasa yake maganar, amma sarai doctorn da ke kusa da shi sosai yana jin wasu daga cikin maganganun na shi. Allurar bacci ya tsira masa domin samun natsuwa sannan kwakwalwarsa ya hutu. Suna fitowa Babiyo ya tare su tare da faɗin, "Ya jikan nawa??"

Hannu Babiyo ya kama tare da washe baki yana faɗin, "Alhamdulillah, idan ya farka lau zai miƙe. Babu abunda ke damunsa yanzu. Kawai hutu ya ke buƙata for now."

Wani nannauyar ajiyar zuciya Babiyo ya saki tare da dafa kafaɗan doctor ɗin ya ɗan bubbuga alamar ya ji daɗi news ɗin sannan ya shiga ɗakin.

Da safe tururuwa a ka yi zuwa duba Abdul-Hakeem ɗin kasancewar Babiyo ya kira ya bada damar zuwa a gansa. Mamiyo ce ta fara zuwa jikarta biye da ita a bayanta, tura ƙofar ta yi ta shiga, sai dai tana shiga suna haɗa idanu da Abdul-Hameed ɗin da ya kai mug ɗin coffe bakinsa. Wani irin kallon tsana suka jefi juna da shi, ita ta yi saurin kawas da kai saboda wani irin bugawa da zuciyarta ya yi saboda wani kwarjini da Abdul-Hameed ɗin ya yi mata.

Wajen zama ta samu ta zauna sannan ta kai idanunta kan mutanan da ke cikin ɗakin da ke gaishe ta cike da girmamawa.

Ciki-ciki ta amsa idanunta ƙur a kan Jawaad da ke kusa da Abdul-Hameed ɗin yana danna wayarsa ba tare da ya nuna ya san da wanzuwarta cikin ɗakin ba, gashi kuma Babiyo bai cikin ɗakin haka ma iyayansu maza da mata. Ƙannai ne kawai maza da mata da wasu daga cikin yayyinsu.

Gyaran murya ta yi bayan ta kawas da kanta daga Jawaad ta mayar kan Abdul-Hameed tare da faɗin, "Ya jikin?"

"Alhamdulillah!" ya faɗi a taƙaice still yana kurɓan Cappuccino coffee ɗin da Jawaad ya haɗa masa.

Da kallo ta riƙa bin su su ukun, Jawaad, Abdul-Hameed da Habib da shima tun da ya ce mata ta tashi lafiya bai ƙara furta ko kalma ɗaya ba

"Do you have an idea on who did that to you?" Mamiyo ta faɗi har da wani karkace kai tana kallon Abdul-Hameed ɗin.

Sai a sannan Abdul-Hameed ya ɗago ya kalleta karo na biyu bayan ya miƙawa Jawaad cup ɗin cappuccino coffee ɗin da ya ke sha tare da sakin wani irin murmushi da ya saka zuciyar Mamiyo tsinkewa tare da lugude.

"Don't have the time to waste on finding the cowards! Abu mafi mahimmaci shine; Allah bai ba su nasara ba, kuma I believed tun d har ni ban curar da kowa ba kuma ban da intention ɗin zalunta wani, Allah ba zai bar wani mahaluƙi ya yi nasara wajen salwantar da rayuwata ba har sai idan lokaci na ne ya yi don baki na bai rabo da faɗin *A'uzu bi-kalimatillahit-Tammatillati la yujawizuhunna barrun wa la fajirun, min sharri ma khalaqa, wa zara'a wa bara'a. Wa min sharri ma yanzilu minas-sama'i, wa min sharri ma ya'ruju fiha. Wa min sharri ma zara'a fil-ardi wa min sharri ma yakhruju minha. Wa min sharri fitanil-laili wan-nahari. Wa min sharri kulli ɗariqin illa ɗariqan yatruqu bi khairin, Ya Rahman!* na yi imani da wannan addu'ar sosai, kuma na san ita ke daƙile maƙiyata. Kuma kwana dubu na ɓarawo ne, rana ce ɗaya tak ta mai kaya, kuma wannan ranar na zuwa soon, Mamiyo. You don't have to be worry about does da suke son ganin bayana. Na rantse da girman Allah na san yanzu haka ba su cikin sukuni da walwala, ni Abdul-Hameed Umar Barkinɗo murucin kan dutse ne kuma kainuwa datsen Allah!"

Wani irin two-minute silent Mamiyo ta yi tana bin Abdul-Hameed da idanu kamun can ta nisa tare da faɗin, "Hakane! Allah ya baka lafiya, let get going Nadiya," ta ƙarisa maganar tana miƙewa.

"Jiki fa Alhamdulillah, don ji nake kamar ban taɓa ciwo ba. Babu abunda ke damuna yanzu sai abunda na saka a gabana a yanzu, thanks for the visit," ya ƙarisa maganar yana murmushi.

Mamiyo kuwa, uffan ba ta ce ba, sai hannunta biyu da ta mayar baya tana jin zuciyarta kamar za ta fashe tsabar tafarsasar da take mata kamar za ta tsaga zuciyarta ta fito.

Suna shiga tsakiyar ɗakinta ta wani irin juyo tare da kallon Nadiya ta ce, "Mai ki ka fahimta a maganganun wancen ɗan iskan yaron da ke kwance a saman gado?"

Jiki na rawa Nadiya ta zube gaban Mamiyo tare da faɗin, "Ki min aikin gafara da abunda za ki ji ya fito daga bakina yanzu. Babu abunda na fahimta a maganarsa illa zargi da na gani a idanunsa da kuma maganganunsa mai kama da jirwaye."

Gyaɗa kai Mamiyo ta yi tare da faɗin, "fice ki bar nan yanzu!"

Da sauri Nadiya ta miƙe ta fice daga ɗakin gabanta na dukan uku-uku. Fitarta ba jimawa Mamiyo ta ɗaga waya ta kira ƴaƴanta.

AFTER 3DAYS Abdul-Hameed ya wattsake sosai kamar ba shi ba, sai dai akwai lafceciyar tabo a tsakiyar kansa tamkar na Aamir Khan a film ɗin Ghajini. Ya yinda a gefe guda malamin Mamiyo ya faɗa mata ta kwantar da hankalinta komai zai tafi kamar yanda take so. Ɓangaren su Jawaad kuwa, gobe ne kowa zai tafi ƙasar da Babiyo ya zaɓa masu su da iyalansu.

Abdul-Hameed kuwa, tunda ya farka daga ciwo wani shuɗaɗɗan abun da ya jima sa mance sa rayuwarsa ta dawo masa sabuwa fil, wani irin soyayyarta ne ke huda ilahirin sassan jikinsa tare da tashin hankali da damuwa da ya cunkushe masa na rasa dalilin da ya saka ya mance ta a rayuwarsa bayan ya san the last thing da suka tsara shine washagari zai zo ya ɗauke ta su tafi wani waje ya killace ta ta yi istibura'i sannan su yi auren su.

"Mai ya faru da ni haka? Mai ya sa na mance komai? Where are you Zee-Meed, ina kike Zeenata? How can i find you Laushina?" haka ya riƙa jerawa kansa waɗannan tambayoyin da bai da amsar su.

Wani irin miƙewa ya yi bayan Bauchi ya zo masa cikin rai. Wani lumshe idanu ya yi tare da faɗin, "I'm coming for you, Laushinaa!" yana gama faɗin haka ya lumshe idanunsa.

Ɓangaren Laushi kuwa, tun jiya jirginsu ya sauka a Denmark ita da doctornta na nan Lagos da Laminu. Jiran isowar Jawaad ɗin kawai suke yi wanda shima gobe zai taho. Tuni har an soma ba ta kulawar gaggawa.

Washagari har da Abdul-Hameed a kai wa su Habib da Jawaad rakiya har airport. Sai da kowanne ya jirginsa ya ɗaga sannan suka dawo gida ban da Babiyo da Abdul-Hameed da Hafiz driver don wani waje suka nufa.

Cikin dare Jawaad suka sauka a Denmark, bolt suka hau har zuwa lafiyayyan masaukinsu wanda ke ɗauke da ƙatoton parlour sai three bedroom da bayi a ciki. A cikin parlourn a kwai ƙatoton kitchen. Tsarin ɗakin sai cif-cif.

"Fresh up first, let me go get you something to eat, and make sure to pray" Jawaad ya faɗi tare da fita da sauri.

Da idanu ta bishi tana mai zama a kan one sitter, gaba ɗaya tun ranar da ya ce mata zai fita ya je ya dawo (ranar da ya je Lagos) ta kasa gane kansa duk da dama can ba wani sakewa ya ke da ita ba.

Bayan 40minutes ya dawo ɗauke da leda mai tambarin gidan wani abunci. Miƙawa mata ya yi bayan ya shiga ɗakin da yake da tabbacin tana ciki. Bata jima da idar da salla ba ta ji knocking ɗinsa.

"Zan fita in ɗan samo mana abunda za mu yi amfani da shi kin ga gidan ba komai, ki tabbatar kin kulle ƙofa am coming back in lessthan one hour."

Gyaɗa masa kai ta yi shi kuma ya juya ya fice. Kai tsaye asibitin da aka aje Laushi ya nufa don sun yi magana a waya da doctor 30minutes ago akan yana buƙatar ganinsa. Yana isa kai tsaye doctorn ya kai shi office ɗin doctor Alexandra don shi ke nemansa.

Wajen zama doc ya nuna masa bayan sun yi musabaha sannan ya soma yi masa bayani, "Mr, your wife need urgent Microsurgical clipping."

Da sauri Jawaad ya ce, "What's that doctor?"

Doctor ya ce, "Microsurgical clipping is a technique that cuts off the blood supply to a brain aneurysm to prevent it from rupturing or to control bleeding if a rupture has already occurred (Microsurgical clipping wani technique ne da ke katse tafiyar jini a raunanniyar jijiyar jinin ƙwaƙwalwa domin kiyaye fashewar kumburin jijiyar ko kuma jijiyar da ta riga ta kumbura ta fashe). You're wife is in serious pain! Ta yaya ka bari ta ke amfani da miyagun kwayoyi haka? Ta taɓa faɗa maka ba ta samun bacci kwata-kwata kuwa? I'm sorry to say this, ko akwai wani matsale a zaman auren ku?"

"You can start preparing for the surgery, will transfer the amout right away!" Jawaad na gama faɗin haka ya fice.

*YASAAR* Hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya ga ya damƙa Meema a hannun mutumin da zai miƙawata wajen Adelberto a Colombia tukun. Jirginsu na ɗagawa ya juyo domin dawowa gidan da ya ajiye Ladi katifa domin ya azabtar da ita har sai ta faɗa masa inda Laushi take. Ya buɗe mota kenan idanunsa ya hango wayar Ladi Katifa a kan kujerar baya, wanda ya faɗi lokaci da abokinsa ke ƙoƙarin saka ta a mota. Da sauri ya buɗe motar ya ɗauko wayar, arba ya yi da address ɗin da Laushi ta turowa Ladin akan ta zo ta same ta...........

#Jawaad #Abdul-Hameed #Laushi #Meema #Yasaar #Mamiyo #Colombia #Microsurgical clipping #My Destiny #Matar Sayyadee [7/30, 3:25 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`