Page 41
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko ko kuma zuwa wuri kaza , ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
Wani irin murmushi Yasaar ya yi tare da rufe gidan bayan, hannunsa riƙe da nokia tourch light ɗin Ladi Katifa. Gaban mota ya buɗe ya zauna a mazaunin direba sannan ya yi wa motar Key ya nufi can gidan da ya aje Ladi Katifar domin ta yi masa jagora zuwa wajen Laushi. Tun a kan hanya ya ke ta kiran layin Layos abokinsa amma no answer. Kira biyar ya yi masa amm ba a ɗaga ba. Dogon tsaki ya ja tare da aje wayar ya yi focusing a kan fuƙin da ya ke yi fuskansa ɗauke da murmushin jin daɗin ya kammala da matsalarsa. Wayarsa ce ta hau ruri, kallon wayar ya yi sai ya ga number ce da bai sani ba, kamar ba zai ɗaga ba sai ya yi wani tunani ya ɗaga kiran ya yi shuru ba tare da ya yi magana ba.
"Ina magana da Yasaar ne!" muryan mace ta daki dodon kunnasa.
"Eh, shine! Ina fatan lafiya?" yasar ya jefa mata tambaya.
"Sabo da kaza ya ce in faɗa maka ka nemi ajiyarka a duk inda ta ke ka cika buradinka fiye da yadda ka ke kissimawa a zuciyarka." tana gama faɗin haka ƙit ta kashe wayar.
Wani irin bushewa da dariya Yasaar ya yi tare da faɗin, "Wa ya isa ya ja dani ya zauna lafiya! Tarkona ya ɗanu. I'm coming for you Zeenah." yana gama faɗin haka ya fizgi motar da ƙarfi.
Ba ƙaramin zagaye su kai ba cikin garin Abuja shi da Babiyo yana nuna masa mahimman wajaje sannan kuma yana ƙara gabatar da shi wajan wasu manyan ƴan siyasa duk don ya samu ilimin siyasa da kuma gogewa. Sai la'asar lis suka dawo Arɗo Barkinɗo. Still tare suka jera har cikin tanƙameman ɗakin Babiyon suna tafiya suna taɓa hira a kan siyasa.
Bayan sun ɗan jima suna hirar sai Abdul-Majeed ya gyara zama tare da faɗin, "Da izinin ka Babiyo ina neman alfarmar a sahale min zan ɗan je in duba two of my friends a nan Abuja kuma za mu ɗan zaga gari da su zuwa gobe."
Shuru Babiyo ya yi na ƴan mintuna don har Abdul-Hameed ɗin ya cire ran jin komai daga wajensa sai ya tsinkayi muryansa yana faɗin, "Ka san dai ana farautar rayuwarka ko? Ban so wani abu ya same ka ba zan iya juran haka ba."
"In sha Allah zan kula, Babiyo. Cikin ɓadda kama zan fita ba tare da sanin kowa a cikin estate ɗin ba haka ma wajen estate In sha Allah," Jawaad ɗin ya faɗi yana fatan amincewar Babiyo don ji ya ke babu wani abunda zai hana shi zuwa Baushi gobe sai mutuwa.
"To Allah ya tsare min kai, Young Minister in advance," Babiyo ya faɗi yana shafa kan Abdul-Hameed, kuma gaba ɗaya haka ya faru ne a kan idanun Mamiyo da ke laɓe tana sauraran su.
Wani murmushi ta saki bayan Abdul-Hameed ɗin ya miƙe ya fice daga ɗakin. Ita ma juyawa ta yi a hankali tare da barin wajen.
Wani shegen murmushi Babiyo ya saki bayan ya kalli wajen labulen, don tun tsayiwarta ya fahimci wacece a wajen. "Time shall tell!" abunda Babiyo ya faɗi kenan cikin zuciyarsa tare da miƙewa ya shiga ɗakin karatunsa.
Washa gari karfe goma Abdul-Hameed ya je ya yiwa Babiyo sallama sannan ya koma ya canza shiga kamar yanda ya faɗawa Babiyo sannan ya bar gida ya nufi tasha ya shiga motar Bauchin Yakubu shi ɗaya tal domin drop ya ɗauka, sai dai abunda bai sani, Hafiz na biye da shi a baya bisa umarnin Mamiyo.
Ƙarfe uku suka isa Bauchi, ɗaki ya fara kamawa a hotel sannan ya fito ya tari a daidaina domin zuwa gidan karuwai inda a nan ne ya fara ganin Laushi. Sai dai hakaa ya yi ta yawo cikin differenrt adaidaita sahu ba tare da ya gano layin da gidan ya ke ba, daga ƙarshe ya koma tafiya a ƙafa cikin layuka yana tamabayan mutane. Wasu su yi masa kallon banza wasu kuma su zage shi wasu kuma su ba su san wani gidan karuwai ba.
Sai isha'i ya dawo masauki yana jin wani irin damuwa da tashin hankali, ji ya ke idan bai sami Zee-meed ɗinsa ba zai iya shiga matsanaicin tashin hankali da damuwa na har abada, domin Zeenah ita ce muradinsa, farincikinsa, natsuwarsa, jin daɗinsa kai infact komai na sa.
"Laushina kina ina? Hameed ɗinki yanaa ta bulayin naiman ki, don Allah kar ki wahalar da zuciyata ki bayyana a gare ni," faɗin Abdul-Hameed ya tsurawa mirror idanu kamar a ciki zai ga Laushin.
Ringing ɗin wayarsa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin rayuwar da suka yi shi da Laushi na tsayin watannin huɗu kawai, wani irin soyayya su ka zuba mai tsayawa a zuciya. Tana matuƙar ƙaunarsa haka shima yana matuƙar-matuƙar ƙaunarta tun ranar da ya fara arba da ita. Duk ya san idan zuri'arsa suka san yarinyar da ya ke mu'amala da ita ba ƙaramin matsalaa bane a tattare da shi, amma shi yana jin ko da sama da ƙasa za ta haɗe shi ba zai taɓa iya rabuwa ko ja da baya a kan soyayyarta ba. Wani irin soyayya su ke wa juna mai wuyar fasaltawa. Don shi gani ya ke ko waɗanda tarihi ya ke bada labarinsu a kan soyayya (Wato Laila Majnun da Romio da Juliet) ba za su gwada masa soyayya ba in har a kan Zee-Meed ɗinsa ne.
Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ɗaga da sauri ganin Babiyo ne ke kira, shaf shi ya mance ma za a iya nemansa musamman ma Babiyon.
"Abdul-Hameed, kana ina ne? Lafiyarka lau kuwa?" Babiyo ya faɗi cike da damuwar ganin har pass eight amma babu shi a Arɗo Barkinɗo.
Murmushin ƙarfin hali ya yi tare da faɗin, "Yanzu na ke shirin kiran wayarka dama, lafiya ƙalau na ke tsoho mai ran ƙarfe. Babu abunda zai samu Abdul-Hameed ɗinka. Sa dai ai min afuwa zan kwana wajen Sardauna, yanzu haka ma ina ɗakinsa. Ban so na fito cikin daren nan ne har wani ya gane ni ko kuma a bibiyeni."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Babiyo ya saki tare da faɗin, "Ka kula da kanka Abdul, sannan ka tabbata ka dawo gida da wuri."
"In Sha Allah," ya faɗi tare da aje wayar a kan mirror kasancewar Babiyo ya yanke kiran daga nashi ɓangaren.
Bayan ya yi sallar isha'i ruwan zafi kawai ya sakawa cikinsa shi ma babu madara sannan ya kuma saɓar hanyar neman gidan karuwa. Wannan karan an nuna masa gidan karuwai fin biyar, amma duk inda ya je ya ce Laushi ya ke nema, sai su ce masa su ba su san wata mai suna haka ba, daga ƙarshe ya koma haɗawa har da sunan Ladi Katifa amma nan ma ba a dace ba.
Sai wajajen sha ɗaya na dare wani ya kai sa wani tsohon gidan karuwai a wani unguwa, a nan ne da kyar aka haɗa shi da wata bayan ya biya naira dubu biyar ta kai shi wajen magajiyar gidan karuwa da su Laushi suka zauna. Har gidanta suka je a wannan daren, da kyar ta saurari Abdul-Hameed shi ma sai da ya bata kuɗi masu kauri sannan ta faɗa masa an tashe su a unguwar sa suke an kuma rusa gidan an yi katuwar kantin kayan masarufi a wajan, amma kamun haka su Laushi da Ladi katifa sun bar nan kusan da shekaru huɗu zuwa biyar sun koma Lagos da zama a wani gidan karuwan. Sai dai ita bata san a Lagos ɗin a wani gidan karuwai take ba. Sannan ta ƙara masa da ƙarin bayani a kan kisan da Laushi ta yiwa mahaifinta bayan ta ɗau sarƙar zinarinsa, wannan dalilin ne ma ya saka suka gudu lagos ɗin ita da ƙawarta kuma da tsohon ciki.
Ba ƙaramin gigicewa Abdul-Hameed ɗin ya ji ba da wannan labarin, musamman tsohon cikin da aka faɗa masa tana ɗauke dashi ya mugun tsaya masa a rai, batun kisan mahaifinta kuma shi sam bai amince da hakan ba. Godiya ya mata sannan ya bar gidan da ƙudurin duk inda Laushi ta ke a garin Lagos sai ya nemo ta ko da hakan na nufin zai karaɗe gidan karuwan da ke Lagos ɗin ne kaf!
#Abdul-Hameed #Laushi #Lagos #Babiyo #Mamiyo #Hafiz informer #My Destiny #Matar Sayyadee *** [7/30, 3:25 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`