Page 42
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
Washagari Abdul-Hameem da duku-dukun safiya ya bar garin Bauchi don jiya yi gaba ɗaya garin ya yi masa zafi da ƙunci kasancewar babu annurin zuciyarsa a garin.
Ƙarfe biyu a garin Abuja ta yi masa, taxi ya hau har cikin Arɗo Barkinɗo cikin ɓadda kama. A daidai ƙofar gidan mahaifinsa ya cewa taxi driver ɗin ya tsaya, bayan ya tsaya shi kuma ya fito tare da biyan sa sannan ya tura gate ya shiga cikin gidan da ya kwashi shekaru bai shigo ba sai yanzu kasancewar Babiyo ya kori iyayansa. Tsaf ƙatoton harabar gidan ya ke wanda ya ƙawatu da shuke-shuke irin su; gwaiba, lemon, grapes, apple mango, orange, sun flower, neem (dogon yaro) da sauran su.
Knocking ya yi a ƙofar parlour sannan ya tsaya domin jira a zo a buɗe masa ƙofar. Mintuna kaɗan sai ga ƙanwarsa Ikilima ta buɗe ƙofar tana mai washe baki tare da faɗin, "Hamma Hameed, jaɓɓama!" cike da farin ciki ta faɗi hakan don ta jima bata saka shi a idanu ba.
Murmushi ya mata, ita kuma ta bashi hanya ya shigo ɗakin yana kallon parloun da ya zame masa baƙo kamar bai yi rayuwa a ciki ba. Muryan Baffansa ya ji yana dariya daga cikin wani ɗaki da ke cikin corridor a nan parlour kuma nan parlour ɗin ya ke dumfarowa.
"Ah! Ikon Allah, ki ga ɗan halas ɗin Saudatu. Ai yanzu muke zancan ka ni da Nennen na ku," faɗin Baffa Belɗo yana murmushi, daidai nan wacce ya kira da Saudatun (Wato mahaifiyar Abdul-Hameed) ta ƙariso. Ɗan duƙawa Abdul-Hameed ya yi tare da kallon iyayansa tare da faɗin, "A ɲalli e jam? (Kun wuni lafiya)"
"Jam ɲalli! Ada selli? (Lafiya ƙalau, lafiya kake?)" duk suka haɗa baki wajen faɗin haka.
Ko kamun ya ba su amsa Ramadan mai bi masa ya fito daga nasa ɗakin tare da faɗin, "Ina bayan gida na tsinkayi muryanka, da sauri na fito domin ganin our up coming young minister," ya ƙarisa maganar yanaa dariya kuma duk cikin fulfulde ya yi maganar.
Hararar wasa ya maka masa tare da faɗin, "Yaushe ka dawo?"
"Tun ranar da aka nemi sheƙe min kai na dawo. Wannan kakan naka ne mai iko da mulki ya hana mu isa gare ka, ni har wajen aunty Halima na so in je amma Nenne ta hana ni ita da Baffa wai suna gudun zuciyar Babiyo." Ramadan ya faɗi.
Daƙuwa Baffa Belɗo ya yi masa tare da faɗin, "Uban nawa kake wa tsiya."
Shafa kai Ramadan ɗin ya yi yana dariya tare da zama kusa da Abdul-Hameed ɗin da ya tashi ya zauna a kan kujera.
"Hmm! Ɗan gatan Babiyo. Wato duk mazajen cikin estate ɗin nan AUREN CIKIN GIDA a kai masu sai kai kaɗai ne Babiyo ya zaɓo maka daga cikin jikokin abokansa, hmm this is selfishness. Kuma kowa ya sani tun yanzu, ni Bahaushiya ko inyamura zan auro, ehe!"
Wani daƙuwar ya kuma samu daga wajen Baffa Belɗo, Abdul-Hameed kuwa mutuwar tsaye ya yi bayan jin zaɓin da Babiyo ya masa daga bakin ɗan uwansa.
"Baffa, menene na ke ji haka daga bakin Ramadan? Shin dagaske ne Babiyo ya zaɓar min mata??" Abdul-Hameed ya faɗi gabansa na faɗuwa.
Washa baki Baffa ya yi tare da gyara zamansa a kan ɗaya daga cikin kujerun dinning sannan ya ce, "Kwarai kuwa, don Baffannika ba su jima da dawowa daga Kaduna ba, ɗiyar Governorn Kaduna da ya sauka ne. An ce yarinya ce kyakkyawa ga ilimi don yanzu haka ma professor a nan jami'ar Ahmadu Bello da ke zaria. Shekarunta talatin cif. Kuma ka san dai Babiyo ba zai yi maka zaɓin banza ba, mahaifiyarka lokacin da aka nuna mata ita a hoto bata yarda ta kai shekaru talatin da haihuwa ba domin kama ta yi da yarinya ƴar shekaru ashirin da biyar, kuma ƴar asali ce, fulani gaba da baya." Baffa ya ƙarisa maganar yana dariyar farinciki.
Abdul-Hameed kuwa ɗif ya yi yana jin wani mugun tashin hankali na tsattsafo masa na jin wannan baƙin labarin.
"Kin ga daɗi ya kashe shi ya kasa magana," Baffa ya kuma faɗi still dariya a fuskansa.
"Baffa ina da wacce na ke so!" Abdul-Hameed ya faɗi.
Ɗif ɗakin ya ɗauka kamar an aiko da saƙon mutuwa mai kashe jiki.
*COLOMBIA*
Baƙaramin bacci Meema ta yi a cikin jirgin nan ba, ƙarfe goma jirginsu ya sauka, sune na biyun fita daga jirgin hannunta riƙe a cikin na mutumin (Berry brown) da aka haɗa da shi kasancewar ya tashe ta daga baccin da take yi.
"Ina aunty Laushina?" Meema ta faɗi tana kallon fuskan wanda ke riƙe da hannunta.
"Yanzu za a zo da mota a kai mu inda take," ya ba ta amsa.
Gyaɗa masa kai ta yi gaba ɗaya jikinta a sanyaye sai bin garin ta ke da idanu, duk da dare ne sosai amma ko ina haske ne tarwai kamar rana.
Wata jibgegiyar jeep suka iske tana jiransu, ko da na cikin motar ya hango su, buɗe motar ya yi fuskansa ɗauke da murmushi tare da nufa inda suke ya rungume wannan mutumin tare da faɗin,
"You're welcome" cikin harshen spanish. Da sauri Meema ta kalle sa da mamaki don sarai ta ji abunda ya ce don ta iya yaren itama kasancewar an koya mata tun a can Lagos.
Kumatunta ya kama tare da sha kanta yana faɗin, "Very beautiful gal, what's your name?"
"Faridat Zeenatu Laushi," faɗin Meema tana kallon Adalberto.
Kasa pronouncing ɗin sunan ya yi, sai cewa ya yi, "from now on, your name is Lulu, I'll be calling you Lulu."
"But I like my name, it was uncle Salma that gave me the name, and everyone calls me with the name." Meema ta faɗi tana turo baki.
"estas en colombia ahora, tu nombre es Lulu (you're in colombia, your name now is Lulu)". Adalberto ya faɗa bayan ya ranƙwafo daidai tsayinta.
"Mi nombre es Meema y nadie puede cambiarlo (Sunana Meema kuma babu wanda zai canza shi)"
Da mamaki sosai Adalberto ke kallon ta jin yaren spanish a bakinta.
"Ba na faɗa maka Yasaar ya shirya maka ita fiye da yadda kake tsammani ba," wanda ya taho da itan ya raɗawa Adalberto a kunne.
Dariya suka kwashe da shi su duka. Hannun Meema Adalberto ya kama suka ƙarisa gaban mota. Matsawa baya Berry Brown ya yi tare da faɗin, "Meet me here tomorrow, my flight is 10o'clock."
Gyaɗa masa kai ya yi don ya hamimci ba zai bi su can inda yake ba. Saka Meema ya yi cikin mota sannan ya rufe tare da zagayawa mazaunin driver.
Wani ihu Meema ta saki tana dukan glass ɗin tare ƙwala kiran Berry Brown tana kuka ya zo ya kai ta wajen aunty Laushinta.
Shi kuwa Adalberto ko juyawa bai yi ba balle ya kalleta tare da rarrashinta. Ita kuma Meema bata bar kuka tana bubbuga glass ɗin motar ba
Tafiya su kai kusan na mintuna ashirin sannan suka shigo wani waje wanda daga waje kamar shago yake, iri wanda ake buɗewa daga ƙasan nan zuwa sama, daga cikin ba ƙarami girma wajen ya ke dashi ba domin motoci ne a aje masu yawa. Parking ya yi sannan ya kama hannun Meema ya fito da ita daga cikin motar tana tittirjewa. A nan ɗin ma mutane ne da yawa kowa na hada hada-hadarsa.
Wani ƙofa suka nufa tare da shiga wani sashen da ban wanda waje ne mai matuƙar girma d faɗi, a tsakiyar wajan wani ƙatoton keji ne wanda aka zagaye shi da wasu wayoyi, sannann wajen shigar an yi masa ƙofa tare da saka masa kwaɗuna ta yanda duk wanda zai shiga ciki ko fita sai an buɗe ta waje tukun zai samu damar shiga ko fitan. Cikin wajen kuwa ƙananun yara ne maza da mata sa'annin Meema da waɗanda suka girmeta, don a kwai masu 20years ma a ciki, sai dai mafiya yawansu yara ne ƴan 11, 12, 13 ba. Gaba ɗayansu cikin cikin shiga tamkar almajirai, don wasu ma kayansu a yayyage ya ke, duk sun yi tsuru-tsuru.
Suna isowa wajen wanda ke gadin ƙofar hannunsa riƙe da bindiga ya fiddo key tare da buɗe ƙofar, shi kuma Adalberto ya hankaɗa Meema ciki sai da ta faɗi wanwar a ƙasa sannan aka mayar da ƙofar aka kulle. Da sauri Meema ta tashi ta iya wajen ƙarfen nan tana jijjigawa da ƙarfi tana kuka tare da faɗin a zo a fitar da ita a kai ta wajen mamanta.
Mai tsaron ƙofar kuwa ganin ta dame sa, sai ya danna wani can abu a jikin bango, nan da nan Meema ta soma wani irin jijjiga alamar shocking ya kama ta, kashe wa ya yi ita kuma ta faɗi yaraf a sume.
A tare wata farar yarinya wacce baza ta wuce 11 to 12years ba ita da wani yaro wanda shi kuma ba 18years ba suka isa inda Meeman ta ke tare da kamo ta.
Meema ta kusa awa ɗaya kamun ta dawo cikin hayyacinta, da kuka ta farfaɗo sai dai yaron da suka taimaka mata mai suna Leonardo ya yi saurin toshe mata baki tare da faɗin, "Si gritas fuerte te golpearán brutalmente, son monstruos. Ten paciencia, todo estará bien. (Kar ki kuka da ƙarfi, su dabbobi ne za su miki mugun duka idan suka ji. Ki haƙuri komai zai wuce).
"Ni gida zan koma, wajen mamana zan je, I don't want to stay here," da hausa ta yi maganar sannan ta ƙarisa da turanci wanda hakan ne ya saka ya ɗan fahimci abunda ta ce sabida bai jin hausa don bai taɓa ma jin kalar yaren ba sai yau a bakinta.
"I'm Leonardo, and you?"
Da sauri ƴar farar yarinyar da ke kusa da wanda ya kira kansa da Leonardo ta ce, "And I'm Issabella" rare da miƙa mata hannu.
Juya musu bayaa Meema ta yi tana shassheƙar kuka, daidai nan su ka ji an buɗe wata ƙatuwar ƙofa da ke yamma da su. Gaba ɗaya mutanan wajen suka sandare, ƴan cikin cage ɗin nan kuwa wani irin tsi su ka yi kamar mutuwa ta gifta.
*Denmark* Gaba ɗaya ya rasa sukunninsa, ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai kaiwa da komowa ya ke a tsakanin theather room, yana addu'a. Can da yaga hakan ba mai yuwuwa bane, sai ya fita ya yi alwala tare da zagawa bayan asibitin ya yi sallah raka'a biyi tare da kwararo addu'o'i ga Zeenah akan Allah ya s ayi wannan aiki a sa'a.
After four hours doctors suka fito daga theather room ɗin suna magana da junasu, da sauri Jawaad ya nufe su yana tambayar su lafiyar Zeenah.
"Meet me at my office," shine abunda doctor wanda ya kasance ba indiye ya faɗi tare da wucewa da sauri.
Shi ma Jawaad ɗin rufa masa baya ya yi hankalinsa a mugun tashe. Zama ya yi a kujerar da ke kallon na doctor ɗin har yana kusan faɗuwa amm bai damu ba sai zubawa doctor ɗin idanu da ya yi.
"I'm sorry to tell you that the surgery wasn't succesfull." faɗin doctor.
"Ya Allah!" Jawaad ya faɗi da ƙarfi tare da ɗaura kansa a kan desk, wani zafafan hawaye na zubowa daga idanunsa suna ɗiga a kan desk ɗin.
Zagayowa doctor ɗin ya yi yana ɗan buga bayansa tare da faɗin,
"Ka kwantar da hankalinka, za ta samu lafiya, komai zai yi daidai," doctor ya faɗi cikin harshen turanci.
"Doctor, pleaseee! I don't want to loose her, she's my Happiness, my life, and my one and only queen. Doctor baza ka gane yanda nake ƙaunar wanna baiwar Allahn ba. Wallahi idan wani abu ya same ta babu farincikin Jawaad a cikin duniyar nan. Wallahi da ana cire ciwo a mayar da shi kan wani da a yau ɗin nan na cire ciwon da ke jikim Zeenah na mayar kaina, doctor please save my wifeee!" ya karisa maganar tare da fashewa da kuka ya mayar da kansa a kan desk ɗin.
Sai da doctor din ha yi calming ɗinsa sannan ya shiga yi masa bayani, "If the brain aneurysm expands and the blood vessel wall becomes too thin, the aneurysm will rupture and bleed into the space around the brain. This event is called a subarachnoid hemorrhage (SAH) and may cause a hemorrhagic (bleeding) stroke."
Da wani irin sauri ya ɗago tare da faɗin, "Doctor don't tell me she's now suffering from raptured fusiform aneurysm!" ya ƙarisa maganar yana kallon doctor gabansa na wani irin bugawa yana fatan kar doctor ya gasgata abunda ya ke tunani.
Jinjina kai doctor ya yi tare da faɗin, "Kumburin jijiyar magunar jinin ya fashe, kuma hakan na haifar da zuban jini sosai a cikin ƙwaƙwalwa da kuma shanyewar ɓarin jiki."
Mutuwar zaune kawai Jawaad ya yi yanaa kallon doctor without blinking har sai da doctor ya jijjiga shi.
"Menene abun yi yanzu?" da kyar Jawaad ya fuzgi numfashi ya faɗi hakan.
"Repairing a ruptured aneurysm requires surgery or endovascular treatment. Endovascular treatment means an aneurysm is treated from inside the artery. (Fashewar kumburin jijiyar magunar jinin yana buƙatar surgery ko kuma endovascular treatment daga cikin artery ɗin)"
"How long can she survive with a ruptured aneurysm? (Tsayin wani lokaci za ta iya rayuwa da fasasshiyar magudanar jijiyar jini)"
"A brain aneurysm rupture is fatal for approximately 50% of people within 3 months"
#Abdul-Hameed #Jawaad #Laushi #Meema #Raptured brain aneurysm #Colombia #My Destiny #Matar Sayyadee [7/30, 3:25 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`