My Destiny (Ƙaddarata)

Page 43

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Rintse idanu Jawaad ya yi tare da jinginar da kansa a kan kujerar da yake yana jin dama yana da ikon cire ciwo a jikin ɗan adam da a yanzu ya cire na Zeenah.

"Ku yi mata aikin, Allah ya bada nasara," yana gama faɗin haka ya miƙe ya fice daga office ɗin idanunsa jazur.

ABDUL-HAMEED Da wani irin tashin hankali suke kallonsa tamkar wawa furucin da ya yi. Da sauri Nanne ta ƙarisa gabansa tare da fashewa da kuka sannan ta ce, "Ka rufa mana asiri Hameed, ka rufa mana asiri mu cigaba da zama cikin ƴan uwanmu kamar kowa. Idan kuma ka fiso mu cigaba da yawo a gari ka yi yadda kake so, ka faɗawa Babiyo cewar baka son zaɓinsa. Sai dai ina son ka rubuta ka ajiye, wallahi idan har ka nuna ƙin amincewarka a kan wannan zaɓi da Babiyo ya maka, to ka nemi wata uwar ba ni ba, na yafewa duniya kai! Kuma ban yafe maka ba idan har ka kuma kallon inda yarinyar da kake ikirarin kana sonta. Shi har son da kake mataa yafi wanda kake wa iyayanka ne da har za ka zaɓe ta fiye da farin cikin mu? To bari na sake maimaita maka da babban murya, ban yafe maka ba idan ka kuma kula yarinyar nan!"

Wani irin tsaam Abdul-Hameed ya yi tare da jin kamar an sauke masa guduma a tsakiyar ka. Ajiyar zuciya ya riƙa saukewa a-kai-a-kai jikinsa na wani irin rawa kuma bakinsa na motsawa yana faɗin, "Shikenan! Shikenan!!"

"Wannan maganar taki ta yi tsauri, ban so ki sake maimaita irin wannan ɗanyen hukuncin. Ban amince maki ba akan kowanne daga cikin ƴaƴana ki maimaita masa irin wannan furucin da ki kai wa Abdul-Hameed. Tashi ka je zan neme ka zuwa anjima" ya ƙarisa maganar yana kallon Abdul-Hameed.

Idanunsa a rufe ya miƙe tare da barin parlourn ya koma can bayan gida ya haɗa kai da bishiyar Neem ya hau zubar hawaye kamar fanfo.

"Na tabbata a yanzu gangan jikina ne kawai zai zama a raye idan babu ke Zee-Meed, na tabbata farinciki ya yi ƙaura a tare dani daga yau da Nanne ta gina katangar rodi tsakanina da ke. Duk inda kike ina fatan kina cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ke da abunda kika haifa, Zee-Meed. Don tabbas na san abunda ke cikinki nawa ne!"

✈COLOMBIA✈ Hannunta riƙe Marlboro cigarette tana zuƙarsa tare da fesar da hayaƙin zuwa samaa. Sanye take cikin riga da skirt na suit, skirt ɗin daidai guiwarta, gashin kanta kuma ta yi parking ɗinsa a ƙarshen ƙeyarta jelar ta zubo bayanta. Bakin nan nata raɗam da jan janbaki. Ita baza ka kira ta da siririya ba, haka ma baza ka kira ta da mai ƙiba ba. Ƴar tsaka-tsakiya ce.

Jefar da guntun tabar hannunta ta yi tare da take sa a ƙasa sannan ta harɗe hannunta biyu tana yiwa cage ɗin da ke cike da yaran nan wani irin kallon ƙasa-ƙasa kamun ta yi nuni da hannu alamar a fito mata da Meema.

Cikin sauri wanda ya kawo Meeman ciki ya nufi wajen cage ɗin, shi kuma mai tsaron cage ɗin ya yi saurin buɗe masa ƙofa. Cike da tsoro waɗanda suke cikin cage ɗin suka soma ja da baya wanda ke nuna alamar tsoro. Shi kuwa kai tsaye wajen Meema ya isa tare da cafkar gashinta ya damƙo sannam ya soma janta tana kuka har gaban Esmeralda sannan ya dunkufar da ita a kan guiwowinta.

Hannu Esmeralda ta saka tare da ɗago fuskan Meema ta yi mata kallon mintuna biyar, Meema kuwa itama kallon ido cikin ido ta yi mata.

Sakin fuskar ta yi tare da kallon Adalberto ta furta cikin yaren spanish, "Sabes cómo se llama? (Shin ka san sunanta?)"

"su nombre es lulú (Sunan ta Lulu)" Adelbarto ya faɗi cike da girmamawa.

Jinjina kai Esmeralda ta yi tare da juyawa ga bodyguard ɗinta ta amshi wata jakar kuɗi ta jefa masa, cikin sauri ya caɓe yana godiya tare da washe baki.

Magana ta yi musu cikin yaren spanish tare da komawa ita inda ta fito. Mai tsaron ƙofar nan kuma ya yi saurin isowa ya ɗaga Meema tare da mayar da ita cikin cage ɗin ya kulle.

Satin su uku a cikin cage ɗin, sai dai kawai idan lokacin cin abinci ya yi a jefa masu bredi a kuma kulle cage ɗin. Tun Meema na kuka har hawayanta suka bushe. Kuma kullum Issabella da Leonardo suna a tare da ita. A hankali ta fara sakin jiki da su har ta faɗa masu labarinta na cewar sato ta aka yi har makaranta aka kawo ta nan ɗin, suma kuma suka faɗa mata duk waɗanda ta gani a cikin cage ɗin nan sato su aka yi domin harkan cocaine da kuma wasu harƙallolin irin su karuwanci da sauran su. Sai dai su shidda Esmeralda ta bada umarnin saka su a makarnata, shi Leonardo ɗin, Diego, Alajendro, Mateo, Carlos da kuma Isabella akan wani ƙudiri na ta. Isabella ce kawai ƙarama a cikin su, amma sauran mazan gaba ɗaya sa'annin Leonardo ɗin ne saboda su sun kai 18years. Yayin da Isabella bata wuce 11-12 ba.

Kullum sai sun bata labarin Esmeralda da kuma irin azabtarwar da take wa duk wanda ke ƙarƙashinta da ya yi yunƙurin tona mata asiri gurin hukumar NLA ko kuma mutum ya yi ƙoƙarin guduwa.

Watan su ɗaya a cikin wajen, su ba aikin komai ake saka su ba, haka su ba a bar su sun koma ga iyayensu ba. Meema har ta saba da su sosai sai dai fa kullum cike take da kewar mamanta.

Sai dai akwai wata rana da ta tashi hankalin kowa da ihu akan ita gida zata wajen mummynta. Ba ƙaramim duka taci ba amma bakinta ya ƙi yin shuru. Hakan ya saka Esmerald ta saka aka kai mata ita har can cikin inda take. Tafi awa biyu a ciki kamun ta fito idanuta jazur don jikinta har rawa yake yi. Sai dai duk tambayar da su Leo su ke mata bata faɗa musu abunda ya wakana a ciki ba. Amma kuma gaba ɗaya rana da kuka ta raya shi, don ko bacci ya fizgeta haka zata miƙe a zaburd tare da ƙanƙame jikinta tana kuka tare da faɗin, "Na tsane ki! Na tsani duk wani abu da ya danganceki. I dont want to see your face ever again."

Ranar da Meema ta cika wata ɗaya da sati biyu, Esmeralda ta saka aka fito da ita tare da su Leonardo. Leo na ganin haka ya raɗa mata a kunne cewar makaranta Esmeralda za ta saka ta, ilai kuwa haka ce ta faru, makaranta Esmeralda ta saka kuma aji ɗaya da Isabella wato grade6 (Jss1).

Sai dai kyakkwar warning akai mata akan babu ruwanta da faɗawa kowa labarin Esmeralda idan ba haka ba, kasheta za ayi.

Ba makaranta kawai aka saka Meema ba, har da wata makarantar koyon faɗa da kuma koyon harbi. Meema na enjoying makarantar koyon faɗa da harbin nan.

Satittika sun wuce, watanni suma sun zo sun wuce, haka shekaru. Domin yanzu shekarun Meema uku a ƙasar Colombia, kuma girma ya bayyana a jikinta don yanzu tana cikin na sha biyar, don an kawo ta ƙasar Colombia tana 11-12.

Faɗa da kariya babu wanda Meema bata iya ba, haka fannin harbi, idan aka cire Leonardo ita ce ta biyu a harbi. Don ko idanunta a rufe suke idan ta saita waje sai ta samu. Haka fannin makaranta akwai ƙwaƙwalwa. Duk wani girma na jikin ɗiya mace ya bayyana a jikinta, hatta period tana da sha huɗu cif ta fara yinsa. Akwai wani irin mugun shaƙuwa tsakaninta da Leo, Isabella da Carlos. Sannan kum babu jituwa ko kaɗan tsakaninta da Alajendro (Ina fatan baku manta Alajendro wanda ya kashe mijin Isabella ba a page 9).

Isabella da Carlos kuwa wani irin soyayya suke wa junansu tankar za su haɗe zuciyoyinsu guda. Kowa ya san da wannan soyayyar ta su har da Esmeralda kasancewar abu ne da bai ɓoyuwa a gare su.

Ɓangaren Leo ma haka take domin yana matuƙar ƙaunar Meema sai dai bata bashi fuska ba hakan ya sakaa ya mayar da maitarsa ciki, sai dai kuma duk inda ta saka ƙafa yana wajen kamar bindinta.

A kuma wannan lokacin Esmeralda ta fito da manufarta a kansu su bakwai har da Meema. Dama su mazan sun saba da yi harkan cocaine ɗin duk da dai ba su kai manya-manyan masu mata aiki ba.

Aikin farko da Esmeralda ta saka Meema ta yi, ƙim yi ta yi sai ma tashin hankalin kowa da ihu da ta yi akan ita gida zata wajen mummynta. Ba ƙaramim duka taci ba amma bakinta ya ƙi yin shuru. Hakan ya saka Esmerald ta saka aka kai mata ita har can cikin inda take. Tafi awa biyu a ciki kamun ta fito idanuta jazur don jikinta har rawa yake yi. Sai dai duk tambayar da su Leo su ke mata bata faɗa musu abunda ya wakana a ciki ba. Amma kuma gaba ɗaya rana da kuka ta raya shi, don ko bacci ya fizgeta haka zata miƙe a zaburd tare da ƙanƙame jikinta tana kuka tare da faɗin, "Na tsane ki! Na tsani duk wani abu da ya danganceki. I dont want to see your face ever again."

Tun kuma daga wannann ranar Meema ta ɗauki wani irin mugum taurin zuciya da na kai. Ta kuma ninka ƙwazonta a komai, don ko Leo bai isa a yanzu ya nuna mata ƙwarewa a kan harbi ba. Fanni gudu kuwa, idan Meema ta falle ƙura kawai ke tashi. An taɓa haɗa su faɗa da Leo sai da ta kai shi ƙasa, duk da su Isabella sun ce ya kyaleta ta ci galaba a kansa ne kawai don yana sonta.

_After 4years_

Leo shine jagoransu akan duk wani harkan Cocaine, Meema (Lulu) ta zama cikakkiyar budurwa kuma kyakkyawa sosai ta bugawa a jarida duk da kasancewarta baƙa. Babuirin dabara na shiga da fitar da cocaine da Lulu (Meema) bata sani ba, hatta yanda ake sarrafashi ta sani don suna daga cikin masu yinsa.

Akwai wani kwangilar dala million hamsin da aka baiwa Esmeralda akan kai cocaine ƙasar Maleyshia. Meema aka ba aikin ita da Leo da wasu mata, sai di rashin lafiyar da ta soma mai zafi ya saka aka mayar da tafiyar kan Isabella akan idan ta dawo za ta yi signing gamee da auren da suke son yi ita da Carlos ɗin don da da farko ƙi ta yi.

Yarirai har shida Esmeralda ta saka aka kashe sannan aka kwashe kayan cikins tsf sannan aka dola cocaines ɗin a cikin ko wani jariri sannan aka ɗinke. Ko wacce ta goya matsayin ɗanta suka hau jirgi suka kai Malayshia ba tare da wata matsalaa ba suka dawo. Dawowarsu ba jimawa aka ɗaura auren Carlos da Issabella a coci...

Bayan sati da auren Carlos da Isabella muka tafi wani gari a nan ƙasar colombia domin kai saƙo, kuma wannan ranar ce muka fara haɗuwa da kai.

Meema na kawo nan da bashi labarin ta miƙa masa hannu alamar tana buƙatar ruwa, ruwan ya miƙa mata ta karɓa ta sha. (Kar ku rikice readers, kar ku manta a page 10 Meema wacce ake kira da Lulu a ƙasar colombia labari take bawa wanda ya biyo su tun daga airport labarin yanda ta kasance a nan har ta soma safarar cocaine. Sannan ku sani Meema bata san labari komai dangane da mahaifiyarta ba tun bayan sace ta da Yasaar ya yi, na kawo labarin Laushi bayan sace Meema ne don komai ya tafi daidai)

Bayan ta ajiye cup ɗin, ya kalleta tare da faɗin, "Kamun ki cigaba da ba ni labari, ina so ni ki faɗa min abunda Esmeralda ta faɗa miki lokacin da ta saka aka kaii mata ke lokacin da kika nuna ke kawai gida za ki."

Wani murmushi mai ɗaci tare da tafasa zuciya Meema ta saki kamun ta buɗe baki da niyyar yin magana sai kuma ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

Bai yi ƙoƙarin hana ta ba har sai da ta gaji don kanta sannan ta ce, "Bam taɓa tunanin rashin ƙaunar da mahaifiyata ta ke min ya kai har ta iya sayar dani wa waɗannan mutanan ba sabida kuɗi. Video Esmeralda ta nuna min na mahaifiyata tana ciniki na ita da Adelbarto. A ƙatuwar jaka aka biya ta kuɗina da ta sayar, wannan dalilin ne ya saka nake mata aiki tuƙuri don taci alwashin ba zata sake ni ba har sai na biyata kuɗin da mamana ta karɓa a hannunta wanda zai ɗauke ni shekaru goma sha biyu ina mata aiki, kuma duk ranar da ta samee ni da cin amana a take za ta fasa kwanyata da bindiga! Hakane ya saka na dage tuƙuru domin in fanshi kaina in koma ƙasa ta in nemi duk inda mahaifiyata take in ɗauki rayuwarta da waɗannan hannayan nawa."

Da idanu Aizaad kawai ya ke bin Meema yana karanto tabbacin maganarta cikin kwayan idanunta saboda yanda su kai mitsi-mitsi suma fitar da wani wutar ƙiyayya da kuma fansa cikin su.

Kamun ya ankara Meema ta miƙe da wani irin azama tare da shaƙa masa wani abu a saman tebur, nan da nan kuwa jikinsa ya saki gaba ɗaya. Kwantar da shi ta yi tare da ɗaukar wayarsa da ke kan teburin ta sakaa cikin wandonta, sannan ta zare bindigar ƙugunsa nan ma ta soke a bayan jeans ɗinta sannan ta fice cikin sauri..........

Hmmmmm🤔 I'm speechless

#Meema/Lulu #Aizaad #Esmeralda #Abdul-Hameed #Laushi #Colombia #My destiny #Matar Sayyadee [7/30, 3:25 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`