My Destiny (Ƙaddarata)

Page 44

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Sauri-sauri ta riƙa tafiya har ta fito kan titi kasancewar inda Aizaad ya kaita can cikin daji ne a cikin wani gida ƙwalli ɗaya tak.

Titin ma babu kowa a kai saboda sun bar cikin gari sosai. Wata mota ƙwalli ɗaya ta gani a bakin hanya, mai motar kuwa yana gefe yana fitsari. Laɓewa ta yi har sai da me motar ya gama abunda yake yi sannan ya nufi motarsa tare da buɗewa yana ƴan waƙe-waƙen zai shiga. Cikin sauri ya ɗaga hannayensa duka biyu sama alamar saranda saboda bindigar da Meema ta ɗaura masa a ƙeyarsa.

"Ban key ɗin motar" ta faɗi cikin yaren spanish.

Jiki na rawa ya miƙa mata key ɗin, ita kuma ta ture sa gefe tare da shiga motar ta tada a guje ta bar wajen, yayin da mallakin motar ya bi bayanta da gudu yana mata hannu a kan ta tsaya.

Sai da ta iso cikin garin Mexico sannan ta samu waje ta yi parking tare da buɗe wayar Aizaad da ta ɗauko ta shiga loda number ɗin Esmeralda. Bugu biyu Esmeralda ta ɗaga wayar, jin muryar Meema tar saki wani murmushi tare da faɗin, "I knew it! I know you can do it Lulu."

"I need to come back to Colombia!" Meema ta faɗi cikin harshen turanci.

"Diego zai zo same ki a inda kike!" Esmeralda ta faɗi tare da kashe wayar.

Cikin daƙiƙu sai ga kiran Diego a wayarta. Ɗaga kiran ta yi ta faɗa masa inda take tare da kashe wayar tana kaiwa da komowa.

A hankali ta soma hango hoton Issabella lokacin da ake yamutsa cikinta ana fiddo cocaine. Wani irin ihu ta saki tare da kaiwa tayar mota wani irin duka da boat din dake ƙafarta kamar shine Esmeralda. Sai da ta gaji don kanta sannan ta durƙushe a ƙasa ta saki wani irin tsumamman kuka tana hargitsa gashin kanta.

Memories ɗin da suka yi spending tare da Isabella ta riƙa tunowa a cikin idanunta, lokacin da aka sakaa ta a cage, kula da ita da ta riƙa, idan an dake ta ko taji ciwo da ita da Leo su ke kula da ita. A kanta har fasa kan Isabella da ƙasan bindiga Esmeralda ta yi. Don akwai wani set-up da Esmeralda ta ke haɗawa da kanta domin gwada wanda suke mata aiki. A cikin mutananta take saka wasu su yi shigar hukumar NLA su kama ka, idan har ka kira sunanta a take take fasa kanka da bindiga. Ta taɓa yiwa Meema hakan, amma duk irin duka da kan bindigar da ake wa Meema ta ƙi faɗin sunan Esmeralda wanda hakan ya saka Esmeralda ke ji da ita a cikin yaran aikinta duk ta sha gwada ta a abubuwa daban-daban.

Ita kuma Isabella ta na yin duk abunda za ta yi ta kare Meema daga uƙubar Esmeralda ɗin, don wani abun ma ita ke faɗawa Meeman wanda hakan ya saka take cin baƙar azaba a hannun Esmeralda ɗin.

Kuka Meema ke yi kamar ranta zai fita. Can kuma ta yi wani irin miƙewa tare da fiddo bindiga a bayan wandonta ta yi kicking tare da ɗaurawa a kanta ta rumtse ido sannan ta danna kunamar.

Ɗas-ɗas-ɗas! Ƙarar harbin ya hargitsa mutanan wajen yayin da Meema da Diego suka faɗi kasa kasancewar yana isowa wajen yaga abunda take ƙoƙarin yi ya cafki hannunta tare da kawas da bindigar zuwa sama. Kokuwa suka fara yi har hakan ya yi sanadiyar faɗuwar su ƙasa bindigar ta yi gefe suma su kai gefe.

Cikin sauri Diego ya ɗauke bindigar ganin Meema na ƙoƙarin kai hannu ta ɗauka.

"Baki da hankali ne!?" Ya faɗi a tsawace yana kallonta. "Kashe kanki kike so ki yi?"

Wani kuka ta fashe da shi tare da faɗin, "Issabella!"

"What happen ta Isabella?" ya bata amsa fuskansa na nuna tashin hankali.

"Ta mutu!" ta faɗi tare da haɗa kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka sosai.

Dafa ta ya yi tare da faɗin, "Lokaci ya yi da zamu daina bin umarnin Esmeralda, mu haɗe kai ni ke da kuma Leo mu kai ta ƙasa mu maye gurbinta."

Wani wawan kallo ta masa tare da faɗin, "Kai ne gurbin Esmeralda ke burge ka, ni abunda nake buri yafi gaban haka. Buri ɗaya gare ni a yanzu, shine komawa ƙasar Nigeria domin aikata cikan burina, daga nan ban damu da na mutu ko na yi rai ba."

"Ni kuma na miki alƙawarin idan har muka haɗa ƙarfi da ƙarfe da ke, zan taimaka miki ki koma ƙasarki," Diego ya bata amsa.

"Ba na buƙatar taimakon ka. Na fika sanin ta yanda zan bar ƙasar nan b sai da taimakonka ba. Esmeralda ce kawai matsala ta."

Wani murmushi ya yi tare da faɗin, "Na san kin fini sanin kwaso casa'in daga sirrin Esmeralda, amma ina so ki sani hannu ɗaya bai ɗaukar jinga. Mu haɗu mu uku, ko ba komai za mu taimaka miki."

"Nicolas na ke son na fara karɓowa daga hannun Esmeralda kamun na tosa asirinta a idanun duniya." Meema ta faɗi.

"Buɗe asirin Esmeralda ba abu bane mai sauƙi kasancewarta sananniya kuma shahararriya a Colombia, kar ki manta ita ce shugaba a ƙungiyar kula d haƙƙin ɗan adam, kuma tana foundation na marayu reshe-reshe a cikin colombia da take taimako sosai. Sannan kuma ta fito takarar gomna wanda sako tamanin ni da ke mun san ƙuru'unta ne."

Miƙewa Meema ta yi tare da faɗin, "Shekaruna goma sha uku a ƙasar nan, kuma kai ma ka faɗa da bakinka na san wacece ita ciki d bai, kuma na san rauninta. Zan yi amfani da rauninta domin amso Nicolas a wajen ta, na yi rantsuwa jinin Isabella ba zai taɓa tafiya a banza ba!"

Tana gama faɗin haka tai gaba Diego biye da ita a baya.

*NIGERIA (ABUJA FCT)* "Wato ko Munzali, ban taɓa ganin jarumi kuma tsayayye kamar sugaban ƙasarmu Barr Abdul-Hameed Muhammad Barkinɗo ba. Shugaba adali. Shekaran jiya fa ba ƙaramin abu akai ba a ƙasar nan, ya sauke minister kuɗi, na ilimi da kuma na harkar noma, likitocin asibitocin gwamnati kuwa ance ya kori fin hamsin saboda rashin kula da marasa lafiya, sai su tafi na kuɗi da suka buɗe suna aiki a can, ga uban tsada kuma. Ni dai wallahi ina bayan masu jinjina masa."

Wanda aka kira da Munzali ya ce, "Ai mutumin ya yi ne wallahi! Ni abunda ya fi burge ni ma shine yadda yake cin uban masu tu'amuli da miyagun kwayoyi. Da an kama ka dashi, life in prison (mutuwa za ta fito da shi daga magarƙama)."

"Au-au-au! Tsohon zance. Shin yanzu ba ka ji sabon dokan da ya fitar ba wanda ya jawo cece-kucen jama'a ba? To ai kuwa sabon doka da ya fitar a kan masu harkar shaye-shaye da safarar wiwi da sauran su shine kashe mutum nan take da an kama shi. Shine fa mutane su kai caaa har da waɗancan mutanan ƴan bani na iya wato human rait (human right) sun yi kane-kane har da zanga-zanga a kan su basu yarda da wannan tsari ba kuma basu lamunci a rattaba hannu a kai ba."

"Ahaaf! Ka ji ba. Ai shiyasa ga yaran nan namu ko ina ka shiga su za ka gani suna zuƙe-zuƙe duk sun lalace. Su ne sace-sace da sara suka. Duk me ke jawo hakan idan ba shaye-shayen ba. Wallahi wannan shugaban na ƙoƙari sosai. Dubi dai lokacin da yayi ministern habuja, Abuja tai tsaf da ita. Ni Allah yasa ma kar su kawar mana da shi ganin yanaa mana abun arziki musammam ma Arewa."

"Yi shuru muji, gashi an fara labari, saurari kanun labaran ka ji," ya faɗi yana ƙaro ƙarar rediyon.

_A labarin yau dai za ku ji cewar First Lady wato mata a wajen shugaban ƙasar wannan ƙasa tamu ta bayyana wani a kan shugabar ƙasarmu wato Barr Abdul-Hameed Muhammad Barƙindo wanda matasa suke masa laƙabi da *_Baban matasa kuma Dodonsu*_. Sannan a wani majiya mai ƙarfi sun tabbatar da cewar EFCC ta yi ram ministern man petur sakamaƙon ƙwamushe kuɗin gwamnat har dala miliyan ɗari da goma, sannan kuma shugaban ƙasa ya kuma jaddada maganarsa a kan cewar duk wanda aka kama sa shafarar kayan maye hukuncisa kisa ne nan take. Waɗannan sune kanun labaran ga cikakkun labaran._

_First Lady ƴa ga tsohon gwammar kaduna na dubu biyu da takwas kuma matar shugaban ƙasa mai ci a yanzu wato Hajiya Asma'u Sulaiman Gudidi, ta fito ta bayyana cewar mijinta Barr Abdul-Hameed yana da ƴa wacce ba a san inda take ba tun tana da shekaru sha ɗaya a duniya wanda yanzu hakaa shekarun ƴar da ɓacewa goma sha uku, sai dai ta ce wannan ƴa ba ƴarta bace, ƴa ce da ba aure aka haife ta ba. Kuma bayyana cewar wannan rubutu da ke ta yawo a social media wata uku bayaa akaan matarsa ta biyu gaskiya ne ba ƙanzon kurege bane. Tabbas matarsa wacce kuma ƴar uwarsa ce wato Hajiya Zeenatu wacce bariki ta bataa sunan Laushi cikakkiyar karuwa ce kuma ƴan kwaya ta bugawa a jarida. Hajiya Asma'u first lady ta ƙara da cewar idan har shugaban ƙasa yana son hukunci to ya fara ta cikin gidansa._

Ɗif ya kashe rediyon tare da kallon Munzali da ya buga tagumi yanaa sauraro ya ce, "Munzali ka ji shegiyar matar nan abunda ta ɓullo dashi kuma.......!"

Zaune take a kan lumtsetsiyar kujera mai cin mutum biyu, ƙafarta ɗaya a kan ɗaya tana karanta jaridar da PA ɗinta ta kawo mata tare da sakin wani shegen murmushin jin daɗi.

"Aikin ki ya yi kyau PA!" ta faɗi tana mai sauke ƙafarta ɗaya a ƙasa tare da zare glasses ɗin da ke maƙale a fuskanta.

Kamum ta furtawani kalma wayarta ta hau ruri.......

#Meema #Esmeralda #Aizaad #Asma'u First lady #Abdul-Hameed #The war #Family Saga #My Destiny #Matar Sayyadee [7/30, 3:25 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`