My Destiny (Ƙaddarata)

Page 45

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Kallon wayar ta yi tare da ɗan sakin tsaki ƙasa-ƙasa ganin mahaifiyarta ke kiran wayar. Ringing ya yi har ya katse bata ɗaga ba, yana katsewa wani kiran ya sake shigowa. Nuni Her Excellency Asma'u ta yi alamar PA ta ɗauki wayar. Cike da ladabi PA ta kai hannu ta ɗauki wayar tare da latsawa ta kara a kunne.

"Asma'u ashe ke dabba ce ban sani ba! Mijin naki za ki tonawa asiri a idanun duniya saboda kishin banza da wofi. To ki sani ba shikaɗai kika wulaƙanta ba har da ke kanki, domin duk wani baƙin fentin da ya shafe shi ya shafe ki!" tana gama faɗin wayar ƙit ta kashe wayar.

Da hannu Her Excellency ta yiwa PA alama da ta mata bayanin abunda mahaifiyar nata ta ce.

Rusunar da kai PA Samira ta yi tare da faɗin, "Ki gafarce ni your Excellency, bakina bai yi tsaurin da zan iya faɗin abunda mama ta ce ba. Maganganu ta yi cikin ɓacin rai kuma duk akan abunda ya faru ne na batun fitar da shirrin His Excellency."

Jinginar da kai ta yi jikin kujera tare da sakin murmushi sannan ta ce, "Kira taron ƴan Jarida." tana gama faɗin haka ta miƙe ta nufi wani upstairs da tsayawa faɗin tsaruwarsa ɓata baki ne.

Cikin abunda bai fi mintuna ɗaya ba, kira ya riƙa shigowa wayar Her Excellency Asma'u (First lady). Amma ta yi biris da kiran.

Zaune ya ke a katafaran office ɗinsa AC na ratsa shi. Jaridu ne kala-kala a gabansa da PA ɗinsa ya kawo masa. Wani irin murmushin takaici da kuma baƙin ciki ya saki bayan ya gama karata wani gajeran rubutu a cikin jaridar wanda aka yi da manyan baƙi.

_SHUGABAN ƘASAR NIGERIA WATO HIS EXCELLENCY BARRISTER ABDULHAMEED YANA DA WATA ƁOYAYYIYAR ƳA DA YA HAIFA DA KARUWARSA BA TARE DA AURE BA, AMMA DAGA BAYA SAI YA AURE TA DOMIN GUDUN TONUWAR ASIRINSA_

Wayarce ta yi ƙara, kallon screen ɗin ya yi, ganin wacce ke kiran sai ya saki lallausar murmushi tare da ɗaga kiran.

Shassheƙar kukanta ya soma dukan kunnensa, wani rumtse idanu ya yi tare da furta, "Zee-meed, you're not longer a baby" cikin wani voice ya yi maganar wanda ita ce kaɗai ke jin irin wannan sautin.

"Ssshhh! Stop crying babyna, komai zai wuce kin ji?"

Kamar yana gabanta ta shiga gyaɗa kai a hankali.

"Matar shugaban ƙasa guda tana kuka...... Noo I don't want to here that again, ni kaɗai nake son jin wannan sautin tare da wannan tsadddun hawayen suma kuma na shagwaɓa, ni kuma in bi ina lashe su."

Duk da kasancewarta cikin tashin hankali sai da ta murmusa.

"Ke da waye a inda kike?" ya tambaya yana gyara zama a kan kujera kamar babu abunda ke damunsa.

Kallon inda Ladi katifa ke zaune ta yi tare da faɗin, "Ni da aminiyata ce."

"Ki faɗa mata ta rarrasar min ke kamun na dawo yanzu. Ban so ki ƙara kuka ko kaɗan, and where are the kids?"

A hankali ta bashi amsa da, "Awwab na tare dani, Muslimat da Muhaysim suna wajen Nenne."

"That's very good. Ni ma gani nan bisa hanya, I love you!"

"Love you too!" ta faɗi tare da yanke wayar.

PA ɗinsa dake tsaye yana jiran ya kammala wayar da ko kalma ɗaya bai ji ba daga maganar Excellency ɗin ya yi saurin soma magana bayan ya ga ya ajiye waya a kan tebur

"Your Excellency umarninka nake jira yanzu nan domin kamo duk wani da ke aiki a wannan gidan jaridar da kuma gidan rediyon da suka fitar da wannan zancen banzan!" PA ya faɗi ransa a matuƙar ɓace.

Murmushi ya kuma saki a karo na biyu tare da faɗin, "Babu buƙatar haka PA. Ina son ka soke duk wani zama da zan yi a yau da koma wanene, zan shiga cikin gida!" yana gama faɗin haka ya miƙe.

"Your Excellency awa biyu kenan sirikinka wato tsohon gwamnar jihar Kaduna yazo domin ganawa da kai amma sakatariya bata bashi wannan damar ba."

"What!" faɗin His Excellency ransa a ɓace sannan ya cigaba da faɗin, "Kana hauka ne za ka bar surukina a waje for morethan two hours! "

Yana kawowa nan ya fita fuuu ya buɗe ƙofar tare da watsawa sakatariyarsa da ta yi sauri miƙewa tsaye wani irin mugun kallo sannan ya nufi surukinsa da ya miƙe tsaye alamar girmamawa ga Abdulhameed ɗin.

Rusunawa ya yi tare da faɗin, "Barka da zuwa sir, ban san ka nan ba. Mu shiga daga ciki." ya faɗi hakan tare da juyawa ya nufi office, baban matarsa biye dashi a baya har cikin office ɗin.

Suna zama gaba ɗayan su a tare suka kalli tanƙameman TVplasma ɗin da ke manne jikin bango. Ganin haka cikin sauri PA dake tsaye ya ɗauki remote ya ƙara volume.

Her Excellency Asma'u Sulaiman Gudidi ce tsaye gaban ƴan jaridu. Sanye take cikin wani arnen less da yasha ɗinkin doguwar riga bubu ya ji shuwaris stone sai walwali yake. Fuskanta manne da tafkeken glasses da ya ƙara fito da kyawunta kuma ya ɓoye shekarunta. Fuskanta ya sha make-up kuma ta yi kyau sosai. Gyalen nan a kafaɗa. PA ɗinta na bayanta tare da wasu matan suma kowacce taci gayu.

" _Dole ne a hukunta gidan rediyon da kuma jaridar da ke ƙoƙarin ɓata sunan mijina da kuma nawa. How on earth zan yi wannan furucin a kan mijina? Wannan abun ba daga ko ina ya fito ba sai daga wajen ƴan adawa ganin yanda mijina ya samu karɓuwa a wajan al'ummansa kasancewarsa adali kuma shugaba nagari. Kuma ina so jama'a su sani, ni Asma'u Sulaiman ban da hannu a cikin wannan magana da ta fito, rusheni ake son yi a wajen mijina? To mahassada ku sani ni da His Excellency mutuwa ce zata raba mu! Kuma a yau ɗinnan sai an kama duk wata jarida ko gidan rediyon da suka yaɗa wannan ƙanzon kuregen da sunana. Jama'a ina mai baku haƙuri!_"

Ta ƙarisa maganar tare da ɗaga hannayanta biyu sannan ta juya ba tare da ta amsa tambayoyin da ƴan jaridar ke watso mata ba, sai dai securities sun hana su isa gare ta.

"PA, ina son hotunan nan su yi yawo a social media a daren yau. Ina son mutanee su rikice da sukar His Excellency Abdulhameed har sai ya ji tamkar ya yi murabus daga kujerarsa. Ita kuma shegiyar haɗiyar zuciya na ke so ta yi ita da shegen tsumman tsohon nan da har yanzu na rasa uban mai ya ke jira bai gamaa ɗauka ba a cikin duniyar!"

_Bogata Colombia_

Suna sauka a airport kai tsaye suka hau shirin yaƙar Esmeralda. Dama tun a can Mexico su kai waya da Leonardo a kan ya same su a keɓaɓɓan wajen da suke haɗuwa idan suna son aiwatar da wani abun sirri. Suna isa wajen suka taras da Leo har ya iso shi da Mateo.

Da mugun sauri Leo ya isa inda Meema ta ke tare da rungumeta sannan ya yi kissing kumatu da goshinta tare da faɗin, "Are you okay?"

Gyaɗa masa kai ta yi tare da shiga wani ɗaki ta fiddo da wata taswira ta shimfiɗa a kan wani ƙaton tabur ɗin da suke packaging cocaine sannann ta shiga nuna masu hanyar shiga cikin gidan Esmeralda har zuwa bedroom ɗinta inda a nan ne suke son tattaro duk wata hujjar da ke nuna ita ɗin shahararriyar ƴar ta'adda ce.

Kasuwa su ka yi su huɗun, Meema za ta tafi gidan Esmeralda ɗauko sirrinta ita da Leo wanda shi ya yi insisting haka sabida ya bata kariya a cewarsa, Mateo kuma zai tafi makaranta ya ɗauko yarinyar Esmeralda da bata wuce shekaru takwas ba zuwa tara ba, Diego kuma zai kasance a wajen taron campaing da za ta yi a gobe misalin ƙarfe huɗu na yamma.

Gaba ɗaya sun gama tsara yanda za su tarwatsa Esmeralda tare da kwance mata zani a kasuwa a gaban jama'ar da ke mata kallon waliyyiya.

Kai tsaye suka nufi can inda suke haɗa cocaine, Meema na shiga da gawar Isabella suka ta fara cin karo cikinta a fafare. Wani irin ihu ta saki tare da rungumo gawar a jikinta tana wani irin kuka. Duƙawa Leo ya yi domin ɗago ta amma ta ture sa da ƙarfi tare da ƙara rungume gawar Isabella tana kuka da iyakacin zuciyarta. Kallon da su ka yi wa juna na ƙarshe ta riƙa kallo yana giftawa a idanunta wanda hakan ke ƙara tunzurata.

Alajendro ne ya iso wajen tare da cafko gashin Meema ya haɗa kanta da tebur sannan ya dumbuzo cocaine a hannunsa ya shiga shaƙa mata.

Wani irin gigicewa ta yi tare da soma gani dishi-dishi. Ihu mai ƙarfi Leo ya yi tare da cafkar wuyan Alajendro ɗin ya damfara a ƙasa sannan ya shiga buga kansa da bango.

Wani irin dambe suka shiga yi tamkar za su kashe juna. Sauran mutanan da ke wajen kuwa, babu wanda ya yi yunƙurin raba su sai ma ƙara zuga su da suka yi.

Duk da ciwon da ke hannun Leo sabida harbin da aka masa, hakan bai sa ya rasa cin galaba a kan Alajendro ba, don sai da ya masa jina-jina sannan ya zaro bindiga tare da kicking ya sai ta kwanyar Alajendro ɗin.

A dishi-dishin da take gani ta isa wajen tare da riƙe hannun Leo amma kuma kasancewar jikinta ya sake kuma ta soma fita hayyacinta, sai ta faɗa kansa luuuu. Cicciɓarta ya yi gaba ɗaya tare da kai ta ɗakin da ya kasance nata ne, ya shimfiɗar da ita a kan gado tare da ja mata bargo. Sai da ya tsaya yana ƙarewa halittarta kallo yanaa jin ƙaunarta na ratsa ilahirin jikinsa sannann ya juya ya fita tare da rufa ƙofar ya murza key ta waje sannan ya saka key ɗin a aljihunsa yanaa jin idan bai kashe Alajendro ba yau hankalinsa ba zai kwanta ba.

Yana isa inda Alajendro ya ke a kwance yana numfashi sama-sama, ya kama ƙafarsa ya shiga jaaa ƙiii ya kaisa jikin bango sannan ya kom kan tebur ɗin nan ya ciko hannunsa da cocaine ya shaƙ masa, ya kuma cikowa ya shaƙawa masa. Sai da yaga kamar zai mutu sannan ya kyale shi haka tare da fiddo bindigar da ya soke jikin wando ya sai ta a tsakiyar kan Alajendro sannan ya saki kunamar. Wani irin tsartuwa jini ya yi daga ƙoƙwan kansa, ko shurawa bai kuma yi ba.

Leo kuwa ji ya yi ya samu salama a cikin zuciyarsa ganin ya kashe wanda ya taɓa masa annurin zuciyar.

Sai da Meema ta kwashi awa bakwai kamun ta dawo hayyacinta, a hakan ma don jininta na da ƙarfi don ita sam bata shan cocaine, Isabella ce ma ke ɗan sha kaɗan-kaɗan. Su Leo kuwa ba a maganar su don sun gwanance wajen shanta.

Esmeralda ta ƙi ta gana da Meema, a cewarta sai ta gama da harkar campaing ɗinta tukun za ta waiwaye ta.

Washagari da plan ɗinsu suka tashi, Meema da Leo sun tafi gidan Esmeralda, Diego kuma ya jima a wajen da za ta yi campaing tare da saita sniper ɗinsa daidai inda Esmeralda za ta kasance a tsaye. Mateo kuma tuni ya ɗauko ƴar a makaranta.

Meema da Leo sun samu nasarar kwamusho hujjoji, yanzu jira kawai suke a soma taron.

Ƙarfe huɗu dot Esmeralda ta iso ita da ja kariyarta fuskan nan nata a washe sai ɗagawa mutane hannu take. Mutane kuwa suka hau shewa suna turereniya domin gaisawa da ita. Sai da ta gaggaisa da wasu sannan ta isa matsayanta ta shiga jawabin yaudara.

Wayanta da ke hannun ja kariyarta ne ya yi ƙara alamar kira ya shigo, ɗaga kiran ya yi ya ɗaura a kunnansa. Zaro idanu ya yi tare da isa inda take ya mata maganaa a kunne sannan ya nuna mata video ɗin da akaa turo; ƴarta ce Meema ta ɗaura mata bindiga a kai.

Excusing mutane ta yi da sauri tare da komawa gefe ta ƙara kallon video ɗin ranta na ɓaci. Nan take wani kiran ya kuma shigowa, wannan karan ita ta ɗauka.

Idanunta ta kai saitin da Diego ya ke ta haɗiye wani malulu sannan t furta, "Ki kawo min ƴata ki ceci rayuwarki!" cikim harshen spanish.

"Ke ce za ki kawo min Nicolas ki ceci taki rayuwar da na ƴarki." Meema ta bata amsa.

Ajiyar zuciya Esmeralda ta sauke tare da faɗin, "Shikenan, na amince. Ina zan zo na amshi ƴata?"

"Ke babu inda za ki, ki turo da Nicolas, ni kuma zan basu ƴarki cikin ƙoshin Lafiya."

Yanke kiran Esmeralda ta yi tare da yi wa mutane uku daga cikin bodyguard ɗinta magana sannan ta koma matsayarta ta cigaba da jawabi.

Body guard ɗinta kuwa kasancewar ta ce masu kar su yi anything stupid, su ba su Nicolas su karɓo mata ƴarta ita ta san mai za ta yi gaba. Hakaa ce ta kasance, sun yi musayar ba tare da an samu wata matsalaa ba. Hankalin Meema ya ɗan kwanta ganin Nicolas cikin ƙoshin lafiya.

Dagaa nan babu inda sukaa nufa sai hukumar NLA suka bayaar da duk wata hujja da ke nuna ɓoyayyiyar halin Esmeralda ɗin sannan suka kira Diego tare da ce masa ya janye. A daidai kuma lokacin Esmeralda ta yi umarni da a nuna tanƙameman sabon makaranta ta marayun da ta kuma buɗewa, sai dai maimakon hotom haka ya bayyana, sai hotonta ya bayyana lokacin da ta yi amfani da bindiga ta fasa kan wani jami'in NLA, daga nan video ya riƙa canzawa zuwa ta'addacin da take y kalaa-kalaa har da kashe jarirai da take yi tanaa sakawa ana fafe cikinsu a saka cocaine a ciki domin fitar dashi zuwa wata ƙasa.

Aikuwa mutane suka hau ihu suna tsalle domin cafkota. Tuni wajen ya hargitse da harbin bindiga dagaa ja kariyarta suna kashe mutane har sukai nasarar sakaa ta cikin mota suka ja motar. Sai dai basu yi tafiya mai nisa ba hukumar NLA suka zagaye su.

Bayan kwana biyu aka gabatar da Esmeralda a kotu tare hujjoji da ke nuna ta'addacinta. Take kotu ta yanke mata hukunci kisa ta hanyar sakaa mata hular lantarki a lantarke ta har sai ta mutu ita da muƙarrabanta.

Bayan sati ɗaya Meema, Leo, Diego da Mateo suka kai Nicolas gidan marayu. Ba ƙaramin kuka Meema tasha ba lokacin da yaron ya rungumeta yana tambayanta ina mamansa. Haka ta baro orphanage ɗin jikinta a mace.

Kallonsu ta yi gaba ɗayansu bayan ta rungume su ɗaya bayan ɗaya tare da faɗin, "I appreciate what you did to me. And I want you to know that I will never forget you. I'm saying good bye to your cus I'll be leaving to my country tomorrow. Will come back to you as soon as I finish my task."

Da wani expression Leo ke kallon ta tun da ta soma magana ko kyafta idanu bai yi ba.

Sauran kuma rungume ta suka sake yi ɗaya bayan ɗaya suna mata addu'a sannan suka wuce domin basu waje ita da Leo don duk sun san irin ƙaunar da yake mata.

Wani irin juyo da ita ya yi har sai da suka haɗe da juna tare da soma magana cikin yaren spanish "Me kike faɗa haka? Tafiya za ki yi ki barni?? Kin san irin son da nake maki kuwa, Lulu? Babu inda za ki je muna tare a nan. Ki manta da ƙasarki, kowa naki muyi auren mu. I promise you zan kula dake, zan baki soyayya wanda baki taɓa kawo shi a tunaninki ba, soyayya zan gwada miki irin wanda ba a taɓa irinsa ba a duniya, Lulu." yana kawo wa nan ya fiddo da wata kyakkyawar zobe a aljihunsa tare da duƙawa a kan guiwarsa ya kama hannunta tare da faɗin, "Will you marry me, Lulu?"

Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "I'm sorry Leo. Babu gurbin soyayya a zuciyata sai ɗaukar fansa! Ba zan iya aurenka ba. Kuma ko da ma babu buri a raina, addinina bai yarda na auri wani mutum mai saɓanin addinin da ba nawa ba!"

A matuƙar zafafe ya furta, "Ina ruwa soyayya da addini? Wani addini kike yi kenan? Kina sallah lokacin sallah, kina bin mu church idan za muje, na ɗauka kina yin haka ne saboda ɗaya muke duka. Ubangiji ɗaya muke bautawa, idan kin yi sallah, idan na je church duk wajensa addu'a da roƙo yake zuwa. Don haka babu bambamci tsakanin mu. Za ki yi addininki, nima zan yi nawa. Ƴaƴan da zamu haifa da ke idan kin ce duka addininki za su yi, ni ban da matsalaa, Lulu. I only love you, you alone Lulu. Please accept this ring" ya ƙarisa maganar yana hawaye.

Itama hawayen take yi, don ita kanta ta san Leo ba ƙaramin so yakee mata ba, amma sai dai ya yi haƙuri don babu abunda zai shiga tsakaninta da cika buradinta na kashe mahaifiyarta. Share hawayenta ta yi tare da faɗin,

"I'm sorry Leo, can't accept this ring. But I promise to come to you when I'm done."

Girgiza kai ya yi tare da faɗin, "Muje court mu yi aure, ni kuma na miki alƙawari ba zan karɓi virginity ɗinki ba har sai mun cika burinmu a Nigeria duk da ban san ko na menene ba. Let go get married, Lulu." ya faɗi yana matso da ita kusa tare da ƙoƙarin kissing ɗinta.

Kawas da kai ta yi tare da faɗin, "I'm sorry Leo!" tare da juyawa ta soma tafiya.

Kiran sunanta ya yi, juyowar da za ta yi taga ya nuna ta da bindiga tare da jan kunamar, "Ko ki amince mu yi aure, ko kuma in harbe ki!"

Matsowa kusa da shi ta yi tare da faɗin, "Fine, go ahead!"

Girgiza kai ta yi tare da mayar da bindigar a kansa tare da faɗin, "Da hannuna ba zan iya kashe masoyiya ta ba, gwara na kashe kaina. Ina sonki Lulu har ƙarshen numfashina............"

(Wai kana nuhin kashe kanka za kai Leo🤔🤔🙄)

#His Excellency Abdul-Hameed #Her Excellency Asma'u First lady #Laushi #Meema #Ladi Katifa #Leonardo #Hatred #Love #Sacrifice #What your sow is what you reap #My Destiny #Matar Sayyadee *** [7/30, 3:25 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`