Page 46
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
Meema ta san rashin hankali da kuma haukar son da Leo ke mata zai iya sakawa ya yi komai, cikin har da kashe kansa. A raunane ta furta, "Drop the gun, Leonardo I'm begging you."
"Do you love you, Lulu?" ya jefa mata tambaya still bindigar na kansa.
"I love you Leo! I love you with all my heart Leonardo." Meema ta faɗi tana kusanto shi.
"Then let go to court and get married!" shima ya bata amsa yana kallonta.
Bata ce masa komai ba har sai da ta ƙariso kusa dashi tare da janye bindigar da ke kansa ta cire duk alburusan da ke ciki sannan ta watsar tare da kama hannunsa suka soma tafiya.
Buɗe gaban mota ta yi ta saka shi ciki sannan ta zagaya ta shiga mazaunin driver. Juyowa ta yi ta kallesa tare da faɗin, "Za muyi aure kamar yanda kake so, amma da sharaɗi guda biyu."
Hannunta ya damƙa da sauri tare da faɗin, "Na amince! Na amince Lulu."
Jinjina kai ta yi tare da faɗin, "Na farko, you won't be able to get to my body until I come back from Nigeria, secondly I'm going to Nigeria alone with out your accompany."
Kallonta ya ke without blinking na kusan tsayin mintuna biyu kamun ya furta, "Do not betray me, Lulu. I can't live without you."
Shafo fuskansa ta yi tare da faɗin, "You can count on me, dear. Let go time is going!" ta ƙarisa maganar tare da tada motar.
"With this dress? No! You have to change and look very beautiful. Ohh my God I'm I dreaming? Leo is about to get married to the most beautiful lady in the world, indeed I'm the luckiest person on the earth!" ya ƙarisa maganar har da ihunsa yana kaiwa dashboard dukan farinciki.
Meema na tuƙi a hankali tana kallonsa ta gefen idanu tana murmushi. Ita kanta ta san tana son Leo.
Leo ya kasance dogo kuma ja, don shi ba fari bane ɗau haka. Idan ka hangashi cikin fararan mutane ma za ka iya kiransa chocolate colour. Kyakkyawa ne sosai. Bai da makusa sai na kasancewarsa aljihun baya (ma'ana ba musulmi ba).
A ƙofar wani ƙaton shagon make-up ta yi parking tana kallonsa tana murmushi.
"Go go the court and arrange everything, will call you if I'm done here to come and pick me." ta ƙarisa maganar tare da buɗe murfin motar ta fita.
Shima fitowar ya yi tare da zagayowa inda take ya saka hannu ya jawo ƙugunta har sai da ƙirjinta ya haɗu da nasa. Kallon ido cikin ido suke wa juna kamun a hankali ya furta, "I love you, Lulu" tare da kai baki zai mata kiss amma sai tai saurin saka tafin hannu ta rufe bakinsa sannan ta ja baya tana masa dariya.
Gyara tsayuwa ya yi yana shafa kai. Juyawa ta yi ta nufi cikin shagon. Da idanu ya bi ƙerarran ƙugunta da kamar ita ta zana kanta har ta.
Har za ta shige shagon ya ƙwa kiran sunanta, tana juyowa ya hura mata kiss tare da faɗin, "Te amo (ma'ana ina son ki)".
"Te amo" ta faɗi itama tare da hura mata kiss sannan ta shige shagon.
Lokacin da aka gama mata kwalliya ita kanta tsayawa ta yi tana kallon kanta cikin madubi. Sanye take cikim wataa arniyar fara ƙal ɗin wedding gown wanda ke ja har ƙasa. Gaba rigar net ne mai kyau wanda hakan ya bawa rabin ƙirjinta bayyana. Bayan rigar kuma igiyoyine aka haɗe waje ɗaya suka bada wani waves. Fuskan nan nata ta sha make-up da ya ƙara fiddo da kyawunta. Gashin kanta anyi mata wani irin style wanda aka mata kitso guda ɗaya amma daga tsakiya aka fara ɗaukosa irin hannu biyun nan aka saki jelar har tsakiyar bayanta sannan kuma suka ƙawata ƙan da wasu duwatsu masu kyalkyali da ya ƙara fito da kyawun gashin. Hannunta sanye da doguwar shantly sock irin na amare.
Make-up artist ɗinnan sai ɗaukarta hoto take a waya tana yana kyawunta.
Waya ta ɗaga ta kira Leonardo, bugu ɗaya ya ɗaga tare da shaida mata yana hanya shi da su Diego.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso wajen, make-up artist ɗinnan ita ce ta fito da Meema. Mutuwar tsaye Leo ya yi domin ba ƙaramin kyau ta masa ba, duk da shima ba ƙaramin kyau ya yi ba. Sanye yake cikin suit baƙaƙe, na cikin kuma ja, sai wata kyakkyawar rose flower dake aljijun coat ɗin. Kan nan nashi sai shinning yake. Su Leo ma irin shigar da ke jikinsu kenan, sai dai rigar ciki ce kawai ta bambanta dom tasu fara ce.
Shi da kansa ya ƙarasa ya kamo hannunta ya yi kissing sannan ya ƙarisa da ita wajen motar da tasha kyau da ballons white and red. Tattaro rigar ya yi ya saka cikin motar sannan ya koma ɗaya bangaren ya shiga buɗe gidan baya ya zauna kusa da ita. Diego kuma ya buɗe gidan gaba ya shiga ya tada motar. Mateo kuma ya biyo su a ɗaya motar.
Da sauri Meema ta kallesa ganin sun yi parking a church, "Why church? Ba court za muje ba?"
Hannuta ya riƙo tare da kissing sannan ya shiga yi mata bayani, "Ba zai yiwu mu yi auren court a yanzu ba, don sai mun yi presenting abubuwa da dama wanda hakan zai iya jawo a fahimci mun yi aiki da Esmeralda kuma hukumar NLA kashe mu za suyi."
Gyaɗa kai ta yi alamar ta fahimta. Shi kuma ya buɗe motar ya fita tare da zagayawa inda take ya buɗe motar ya riƙo hannunta tare da fito da ita suka nufi cikin church ɗin, su Diego biye da su a baya.
A nan suka samu pastor shi kaɗai cikin church ɗin yana jiransu. Ba ƙaramin kuɗi suka bashi ba kamun ya amince zai ɗaura masu aure.
A gabansa suka tsaya shi kuma ya soma babu ɓata lokaci, "``Dearly beloved, we are gathered here today...'' - ``Do you, (Leonardo), take (Lulu), to be your lawfully wedded spouse?"
Washe baki Leo ya yi yana jijjiga kai tamkar ƙadangare tare da furta, "To have and to hold from this day forward, for better for worse, for richer for poorer, in sickness and in health, to love and to cherish, till death us do part"
Kallon Meema pastor ya yi tare da faɗin, "Do you, (Lulu), take (Leonardo), to be your lawfully wedded spouse?"
Da murmushi a fuskanta take kallon Leo da sannunsa ke riƙe da nata tare da faɗin, "for better for worse, for richer for poorer, in sickness and in health, till death us do part."
"I pronounce you as husband and wife, you may now kiss your bride!" pastor ya faɗi.
Take Leo ya jawo ta jikinsa tare da bata wani deep kiss na tsayin minti ɗaya sannan ya janye tare da rungumeta a jikinsa tsam. Su Diego kuwa wani irin fito suka saki dagaa inda suke.
Suna fitowa daga church suka iske photographer da Diego suka kira, shi kuma ya shiga ɗaukar su hotuna. Hotuna suka yi sosai sannan Leo ya sakaa matarsa cikin mota ya ja motar suka bar wajen.
(Gaskiya rashin sanin addini bai yi ba saam! Har na soma jin zazzaɓi ni matar sayyadee!🤒 Mai kuma ya haɗa ɗiyar musulmi da auren kahiri a coci😭 gaskiya an cuci rayuwarki Meema. Jama'a ku taya ni duba, wannan auren mai za mu kira shi? Ya ɗauru ko kuwa? Har da su kiss {the most annoying part} 😡)
_A nan zan tsaya sabida ni ma jiya ba ku haukatan da zafafan comments ba_
#Meema #Leomardo #Marriage #Heartbroken #My Destiny #Matar Sayyadee [7/30, 3:25 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`