My Destiny (Ƙaddarata)

Page 47

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

Tafiya su kai mai ɗan nisa kaɗan sannan suka iso wani ƙaramin gida. Meema da ke zaune cikin mota da idanu ta bi gidan cike da sha'awa don gaba ɗaya anyi masa decoration ta waje har da bulbs masu launi daban-daban.

Fitowa ya yi daga motar tare da zagayawa gefenta ya buɗe sannan ya cicciɓota zuwa cikin gidan bayan ya rufe motar da ƙafa ɗaya.

Bai ajiye ta a ko'ina ba sai kan gadon da shima ya sha decoration da zane heart ta ko'ina. Hawowa kan gadon ya yi tare da zame coat ɗin jikinsa sannan ya ɗago kan Meema ya ɗaura a kan cinyarsa tare da soma magana, "My prayers were answered the day that I met you. You are a blessing in my life, and I will be lucky to call you my partner for the rest of our lives. I love you more than anything! You are the woman that I have always dreamed of. From the first day I met you, I knew you were going to be my happy place. I couldn't love you more than I do right now, yet I know I will tomorrow! My heart belongs to you. You are the reason I became stronger, but still, you are my weakness. I would do anything for you to make you happy. I would give you the sun, the moon, the stars, and my whole heart forever. You are the rarest and most beautiful thing on this planet. I am the luckiest man in the world to be able to call you mine. My love for you will last a lifetime. Loving you is my favorite thing. I'd be lost without you, Lulu!"

Yana kawo nan a zancensa ya shiga bata deep kiss. Ko kaɗan ba ta yi ƙoƙarin hana shi ba, sai ma kulle idanuta da tayi tana hawaye itama. Don ta san abunda take shirin yi ɗin zai saka shi a wani mummunar yanayi, sai dai babu abunda za ta iya yi akai don dole ne ta cika wannan buri nata. Idan kuma ta ce za ta biyewa Leo, har abada ba zai taɓa bari ta tafi Nigeria ba sabida ƙaunar da yake mata, ko auren da suka yi ta amince ne gudun kada ya kashe kansa. Ta san shi fiye da yadda shi ya san kansa. Shiyasa ta gama shirya plan ɗinta tun kamun ta san daƙudurinsa sa na son auranta a yau ɗin.

Ganin yana neman wuce gona da iri ta yi sauri ture shi tare da faɗin, "Leo!" cike da muryar shagwaɓa.

"I'm sorry!" ya yi saurin furtawa tare da sauka daga kan gado.

Itama saukowa ta yi tare da saka hannu ta tura shi waje sannan ta jawo ƙofar ba tare da ta rufe duka ba ta furta, "I want to change," sannan ta datse ƙofar tana dariya.

Rigar ta soma cirewa sannan ta tattarosa da ƙyar don yana da nauyi ta ɗaura a kan gado. Dogon takalmi mai tsinin da ke ƙafarta ta cire sannan ta shiga bayin da ke ɗakin ta kunna shower ta hau wanka. Bayan ta gama ta ɗauro towel iya cinya tare da fitowa ta buɗe ƙofar.

Tsaye ta hango Leo yana jera abinci a kan wani kyakkyawar ƙaramin glass table da ya sha kwalli an ɗaura manya kwalaben juice mai kama da giya a kai da red candles suna ci kaɗan-kaɗan.

"Leoo!" ta ƙwala kiran sunanta. Da sauri ya juyo, sai luma ya yi saurin aje plate ɗin hannunsa mai ɗauke da cake ya taho inda take riƙe da ƙofa a hannu.

"My dress," ta furta a hankali lokacin da ya ƙariso bakin ƙofar.

Sai da ya kalleta daga kai har ƙafafu tare da shafa kai sannan ya shafa kai yana yaba black skin ɗinta da ke glowing.

"Dress!" ta yi whispering a kunnansa kamar za ta cije shi.

Da sauri ya dawo cikin hayyacinsa tare da komawa baya ya ɗauko ledan da kaya ke ciki ya miƙa mata. Tana amsa ta rufo ƙofar tana dariya. Shima dariyar ya yi tare da komawa ya shigaba da abunda yake yi yana jinsa tamkar a cikin aljanna.

Bomshort ne kalar baƙi, sai wata arniya riga da ya kasance iyakacinsa daidai inda bomshort ɗin ya tsaya. Riga ce mai hannu ɗaya, ba ƙaramin kuma shara-shara don hatta bra ɗinta ana gani ƙarara. Turare ta fesa sannan ta ɗan ƙara gyara fuskanta sannan ta buɗe ƙofar ta fita.

Wani slow music ke ke tashi a parlourn na wani mawaƙi cikin yaren spanish. Harɗe hannu ta yi tana kallon edges ɗin parlourn saboda yanda ya ƙayatar da ita da decoration ɗin da aka masa.

Shima ya canza kaya zuwa 3quarter da riga armless da ya masa kyau ainun. Takowa ya yi har inda take tsaye tare da jawota jikins gaba ɗaya ya raɗa mata a kunne, "You always look very beautiful, my dear one and only wife," ya ƙarisa maganar tare da bata kiss a goshi sannan ya kawo ta tsakiyar parlourn ya shiga jujjuyata yana rawa da ita daidai da tafiyar waƙar da ke tashi. Sun jima suna rawar kamun ya isa wajen radio ɗin ya canza waƙar zuwa waƙar _Despacito_ kasancewar ya san tana ƙaunar waƙar. Nan da nan kuwa ta cafke ta shiga bin waƙar tana rawa.

Sí, sabes que ya llevo un rato mirándote Tengo que bailar contigo hoy Vi que tu mirada ya estaba llamándome Muéstrame el camino que yo voy Oh, tú, tú eres el imán y yo soy el metal Me voy acercando y voy armando el plan Solo con pensarlo se acelera el pulso (oh yeah) Ya, ya me estás gustando más de lo normal Todos mis sentidos van pidiendo más Esto hay que tomarlo sin ningún apuro Despacito Quiero respirar tu cuello despacito Deja que te diga cosas al oído Para que te acuerdes si no estás conmigo Despacito Quiero desnudarte a besos despacito (kuma ku karanta ku bi 🤣🤣😜 duk da na san da yawanku kun san waƙar don ta yi trending sosai)

Sosai su ka yi rawa kamun suka zauna suna ciye-ciye cikin nishaɗi. Leonardo tun da aka haifesa bai taɓa farinciki kamar yau ba. Don sosai suka nishaɗantu da Meema. Har cakulkuli yake mata tana dariya har tana zamewa, daga ƙarshe suka hau guje-guje suna jifan juna da pillow.

Tare su kai bacci a ɗaki ɗaya, kuma gado ɗaya. Sai dai babu abunda ya shiga tsakaninsu, amma jikinsa ta yi bacci.

*ABUJA NIGERIA*

Wani murmushin gefen baki His Excellency ya saki bayan gama kallon abunda uwargidan tasa ta yi. Ya san ta tamkar yunwar cikinsa, kuma ya san babu abunda ba za ta iya aikatawa ba sabida kishi. Yanzun ma kuma yana da tabbacin ita ce ta aikata ta duk abunda ya faru, kuma ta fito media domin kare kanta saboda maganganun jama'a.

Ajiyar zuciya tsohon gwamna Jihar Kaduna kuma mahaifin Asma'u ya yi tare da faɗin, "Your Excellency, na zo wajenka ne domin nema wa ƴata afuwa akan abunda ta aikata da marasa tunani kuma masu ƙaramin ƙwaƙwalwa. Na zo nan ne a matsayin uba, kuma surukinka. In roƙonka alfarmar ture kujera da kuma office ɗin first Lady da ka bawa ƴata don shine ke ƙara mata ɗagawa da jin isa tare da sauraron zuga wajen ƙawayenta. Sannan don Allah your Excellency ka yi amfani da iko na matsayin shugaba a gidanka ka yi hukunci bisa wannan iskanci da tozarci da ta yi maka. Idan ya kama ka turo ta gida ni kuma zan ɗanɗana mata azaba tare da bambamce mata tsakanin Aya da Tsakuwa! Kanta Asma'u na rawa tamkar na akwalan keke napep your Excellency, don Allah ka saita wannan rawan kan."

Murmushi da ya zame masa ɗabi'a ya yi tare da faɗin, "Ai su mata sai da haƙuri baba, ƙaramin tunani gare su. Duk kuma abunda ya zo ƙwaƙwalwarsu shi suke aikatawa ba tare da tunanin mai zai je ya dawo ba. In sha Allah komai zai wuce!"

Kuka baban Asma'u ya fashe dashi tare da sunkuyar da kai ya soma faɗin, "Wallahi Asma'u har da ni ta tozarta! Ace wai ƴata ce take wannan iskanci a gidan aurenta tana tozarta mijinta a idanun duniya. Yanzu da ba mai haƙuri ta ke aure ba wallahi da yanzu tana gida da takardar saki. Don babu namijin da zai iya zaman aure da mace mara mutunci mai tona asirin mijinta. Tir! Da halinki Asma'u."

"Subhanallah! Don Allah kar kace haka Baba, ka yi haƙuri komai zai zo ya wuce kamar ba ai ba."

Jinjina kai ya yi yana mai kai ƙasan babban rigarsa ya share hawaye.

Har wajen mota His Excellency ya rako sirikinsa sannan ya juya ya koma office tare da kankarawa sakatariyarsa warning a kan kar ta kuskura ta maimaita abunda ta yi a yau, duk lokacin da sirikinsa yazo kai tsaye ta barshi ya shigo garesa. Ko mintuna biyar bai ƙara yi ba ya PA ya tattare komai ya bi bayansa tare sa bodyguard ɗinsa. Cikin bayan haɗaɗɗiyar RR kalar fari fat ya shiga, driver ya ja zuwa cikin Villa.

Wani murmushin jin daɗi ya saki lokacin da ya doshi ƙofar shiga part ɗinta. Security code ya ɗanna sai ƙofar farko ta buɗe, ta biyu kuma d thumb print ya yi amfani itama ta buɗe, sai na kuma shi glass ne irin wanda duk ƙarfin bullet bai iya ratsa shi. Shi fuskansa ta ɗauka sannan ta buɗe. Take wani rantsattse kuma tanƙameman parlour ya bayyana. Komai na parlourn golden colour, wanda bai san gold bama zai ɗauka gold ɗinne. (readers ku hasaso parlourn da kanku don faɗa dai ɓata baki ne)

A jikin bango wani tanƙamemen hotonsa ne sanye da suit, a gefen hoton kuma hoton Laushi ne cikin lafaya onion colour hannunta ya sha lalle ja da baƙi tana murmushi. Ba ƙaramin kyau ta yi ba, don baza ta wuce 30-32 years ba a wannan lokacin. A can saman hoton kuma, hoton Meema ce sanye cikin blouse ranar birthday ɗinta hannunta riƙe da ƙatuwar teddy, kanta babu ɗankwali sai gashinta da aka raba shi gida biyu a kai mata parking. Ɗayan bangon daga gefen hagu kuma, hoton family ne, His Excellency Abdul-Hameed, Zeenat Laushi, sai ƴaƴansu uku, Muslimat wacce babu inda ta baro babanta har da kalar fatar (Meema sak) shekarunta goma, sai Muhaysim wanda shi Laushi ya ɗauko har da hasken fatan, shi shekarunsa takwas, Awwab kuma lokacin yana jinjiri riƙe a shawul a hannun His Excellency Abdul-Hameed, shi shekarunsa biyar. Kallon hoton Meema His Excellency ya yi yana jin hawaye na taruwa a idanunsa. Hannu ya kai ya sharce hawayen yana mai addu'a cikin zuciyarsa sannan ya wuce the next parlour wanda a nan ya ke tsammanin ganin sahibul Qalb ɗin nasa.

To his surprice bata parlourn, sai kawai ya bi upstair. Yana tura sliding door ɗin su kai idanu biyu dashi tana ƙoƙarin tsiyaya ruwa a glass cup.

Murmushi su ka sakarwa juna. Tahowa ya yi itama ta nufosa hannunta riƙe da cup ɗin. Kai tsaye bakinsa ta nufa da ruwa shi kuma ya buɗe baki tare da kurɓan ruwan, sai da ya cika bakinsa sannan ya jawota jikinsa tare da haɗe bakinsu ya shiga juye mata ruwan da ya gumtsa. Tare suka shanye ruwan tass.

Haka ɗabi'ansa yake, duk ta bashi ruwa sai ya gumtsa abaki ya bata a nata bakin sun shanye tare. Hannunta ya kama tare da zama zannan ya zaunar da ita a kan cinyarsa ya furta, "Kika zubar min da waɗannan hawayen naki masu tsada ko? Baki san ban ƙaunar zubar su ba!" ya ƙarisa maganaar yana lakatar mata hanci.

Kau da maganar ta yi tare da faɗin, "Sanin farin halinka ne ya saka aminiyata guduwa jin gaka nan dawowa, shin wai baka san kai ba yaro bane yanzu? Kanaa da 24years daughter fa!" ta ƙarisa maganaar bata san lokacin da hawaye suka wanke a fuskanta ba.

Harshe ya saka ya lashi hawayen sannan ya haɗe goshinsu waje ɗaya tare da faɗin, "Bana so, bana son wannan hawayen suna zuba, Zee-meed. Kin mance alƙawarin da kika yi a kan ba za ki ƙara yiwa Meemanmu kuka ba sai dai addu'a. Don Allah kar ki kuma."

Hannunsa ta riƙe tare da faɗin, "Idan mutane suka aibata ka har cikin zuciya da jijiyoyina nake jin zafi. Ban so inji ana zagin mijina. Na duba social media ɗazu, wallahi har kuka sai da na yi. Sannan kuma na yi mafarki akan ƴarmu jiya, mummunar mafarki na yi. Wallahi tsoro nake ji!" ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka.

Rungumeta ya yi tsam a jikinsa tare da hura mata kunne a hankali sannan ya shiga faɗin, "Magana jama'a a kaina ta dena saka ki zubar hawayen nan masu matukar tsada. Magana mafarki kuma, kar ki saka hakan a ranki, In sha Allah bayyanarta kika gani. Babu wani abu mummuna da zai samu ƴarmu, addu'armu na bibiyarta In sha Allah. Sannan shi mummunar mafarki ba a faɗawa kowa, ki addu'a da sadaka kawai."

Gyaɗa masa kai ta yi tana ƙara maƙalƙale masa. A kunne ya raɗa mata, "Kin ce na tsufa ko? Kuma dai naga har yanzu ina fafatawa a filin daga har in mantar dake a duniyar da kike."

Duka ta kai masa tana ɓoye fuska a cikin ƙirjinsa.

Da daddare duk suna kan dinning suna cin abinci su duka har da First Lady Asma'u kasancewar tsarinsa ne haka. Babu mai magana a cikinsu sai ƙarar cokula kawai. Asma'u ce ta fara miƙewa tare da faɗin, "I'm okay. Sai da safen ku."

Ko kallonta Abdul-hameed bai yi ba, donƙaramin danne zuciyarsa yake a kanta ba. Ji yake kamar ya danna mata saki uku ta bar masa gida, don he hate the sight of her.

Zeenat ce kawai ta amsa mata ita da yara don su har bye-bye suka bita dashi.

Zeenat na kallon His Excellency ƙasa-ƙasa da ya yi cikin-cikin da ransa. Murmushi kawai ta yi tare da girgiza kai.

Miƙewa ta yi domin raka ƴaƴanta zuwa ɗakunansu kasancewar su ma sun kammata, sai da su kai wa baban kiss tukun suka tafi.

Wayarsa ya jawo bayan shigowar saƙon PA ɗinsa, hankalinsa a tashe ya buɗe data, ba ɓata lokaci ya shiga facebook, nan ya shiga cin karo da hotunan Laushi lokacin tana buga bariki, wasu hotunan ita Ladi Katifa da Salma nice, wani kuma ita da Meema na yarinya. Har da hoton ranar suna Meema sai da aka ɗora, da lokacin da Salma nice ya riƙe ƙugun Laushi suna rawan tumbola.

Cikin sauri ya kifa wayan a kan tebur jin takun tafiyar Laushi. Murmushi ya mata lokacin da ta ƙariso tare da faɗin, "Ɗan aramin wayarki mana."

Ba tare da tunanin komai ba ta miƙa masa. Shi kuma ya karɓa ya kashe ta gaba ɗaya tare da sakawa a aljihu tare da nashi sannan ya kama hannunta tare da faɗin, "Muje in kashe arna!"

"Ka ce min in shirya za mu fita duba Babiyo, Baffa Giɗaɗo ya kira Babiyon na son gani ka." ta faɗi.

"Sshhh!" ya furta tare da mata ɗaukar yara.

*COLOMBIA* Ita ta riga shi tashi da safe. Cikin gaggawa ta shiga bayi ta yi wanka tare da fitowa ta shafa lotion sannan ta sha jeans da rigar chantly fara, sosai tai mata kyau. Turare ta fesa a jikinta. Tana cikin saka ɗankunne ta hangi Leo dake kwance a kan gado yana kallonta da idanunsa dake nuna tsantsan ƙaunar da yake mata.

Juyowa ta yi gaba ɗaya tare da ɗaura hannunta a kan drower ta ɗauke wani handkerchief ba tare da bari Leo ya lura ba. Hannu ya miƙo mata, babu musu ta isa garesa. "I love you," ta furta masa sannan ta kai baki kamaar zata masa kiss, sai ta yi saurin ɗaura masa handkerchief ɗin a kan hancinsa. Idanunsa ne suka soma lumshewa a hankali.

Hawaye na zubo mata ta furta, "I'm sorry Leo. I love you soo much."

"Lu....Lu.....Luluu...! Ya faɗi idanunsa na kullewa gaba ɗaya ya shiga sakin munshari.

Sai da ta masa kiss a baki sannan t gyara masa kwanciya tare da sauka a kan gadon ta shiga haɗa kayanta a jaka sauri-sauri don jinin Leo na da ƙarfi, awa ɗaya kawai abun zai ɗauka yana aiki a jikinsa. Kuma idan har ya farka ba zai, taɓa barinta ta tafi Nigeria ba.

Hotunan bikinsu ta ɗaga tana kallo tana hawaye. Cikin sauri ta cusa cikin jaka tare da zugewa sannan ta ɗauki passport ɗinta cikin drawer ta saƙa cikin aljiju. Kallon Leo ta kuma yi da ke bacci sannan ta yi ajiyar zuciya tare da saurin barin ɗaki.

Mota ta shiga bayan ta ajiye kayanta a gidan baya sannan ta tada tare da yin reverse ta figi motar da gudu don jirginta ya kusa tashi gashi a kwai ɗan tafiya tsakanin inda take da aiport.

Tana isa airport saura mintuna biyar jirgi ya tashi. Cikin sauri har da gudu-gudu ta shige tare da miƙa kayanta aka duba sannan ta tafi ta shiga jirgi tare da saka belt. Hankalinta bai kwanta ba har sai da jirgi ya daidaita a sama......

_Hmmm 😯😲 tofaaa! Jama'a ga dai Meema cikin jirgi za ta ƙasar Nigeria, ko mai zai faru idan ta isa? Mai zai fadu idan Leo ya farka babu sahibarsa??🤔 akwai hwa badaƙala tabbass._

#Meema #Leonardo #Laushi #His Excellency #First Lady #Alaji shugaba Babiyo #The Battle #Ƙaddarata #Matar Sayyadee *** [7/30, 3:26 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`