Page 48
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_Mu ɗan waiwayi abunda ya faru a baya da kuma tarihin gidan Babiyo ka mun saukar Meema a jirgi_ ✈
_WANENE BABIYO_ Abubakar wanda ake kira da Lamiɗo haifaffen garin Adamawa yola a ƙaramar hukumar Mayo-Belwa. Cikakken bafulatani ne kuma makiyayi. Mutum ne mai matuƙar zafin zuciya da riƙo tamkar mahaifinsa Isiyaka. Idan ya zana abu a cikin zuciyarsa, to fa babu uban da ya isa ya canza shi ko da kuwa mahaifin nasa ne, hakan ya saka basu fiye jituwa ba. Yana da dukiya mai ɗunbin yawa domin yana da shanaye da tumakai fiye da dubu. Yana da ƙanne maza biyu da mace ɗaya. Musa, Jafaru da Lawisa. Musa, Jafaru da Lawisa ba ƙaramin shakkar Lamiɗo suke ba, ko gigin tsallake umarninsa ba su taɓa yi ba, sun ma fi jin shakkarsa fiye da mahaifinsu. Matan Lamiɗo na aure biyu, Hure da Sakina. Hure ita ce matarsa ta fari, sun kwashi shekaru goma sha ɗaya da aure amma babu haihuwa, hakan ce ta saka ya sake aure ya auro ɗiyar abokin mahaifinsa wato Sakina. Sai dai ita ma haka ta kwashe shekaru uku ko ɓari bata taɓa yi ba. Hakan ce ya sa aka ɗaura rashin haihuwar a kan Lamiɗo. Sai dai cikin hukuncin ubangiji, Sakina bata rufe shekaru huɗu a gidan Lamiɗo ba sai ga Hure da ciki. Ba ƙaramin daɗi Lamiɗo ya tsinci kansa a ciki ba. Wani mahaukacin kulawa ya shiga baiwa Hure tamkar zai suɗe ta tare da yi mata alƙawarin ƙosassun shanaye biyar idan har ta haifa masa ɗa namiji.
Haka rayuwa ta yi ta tafiya suna kula da cikin Hure daga shi har Sakinar don ita ma ta yi farin ciki da samun juna biyu da ƴar uwar tata ta yi. Sai dai me, ciki na shiga wata huɗu ya ta soma ciwon ciki tare da baƙar azaba mai tafe zubar jini. Wahalar da Hure ta ke sha tamkar za ta bar duniya. Hankali tashe Lamiɗo ya sayar da ɗaya daga cikin ƙosasshiyar naggensa ya kai matarsa babban asibitin gamnati da ke cikin Yola. Sai dai tun kan su isa cikin ya riga da ya zube. Gashi Hure ta yi zubar jini sosai wanda ya saka dole aka ƙara mata jini har leda biyu.
Sosai Lamiɗo ya yi baƙin cikin fitar wannan ciki da ya ƙwallafa rai a kai, amma sai ya ɗauki dangana. Bayan sati biyu aka sallami Hure suka tattaro suka dawo Mayo-Belwa. Sai dai bai manta gargaɗin likita a kan duk lokacin da matarsa ta kuma samun ciki ya tabbatar ya kawo ta asibiti akai-akai domin a riƙa duba ta da kuma abunda ke cikinta.
Bayan watanni uku sai ga wani cikin jikin Hure. Wannan karan tsabar farinciki da zumuɗi sai ya tattara matansa duka biyun suka dawo cikin birnin Yola da zama bayan kama hayar ciki ɗai-ɗai. Amma shi ya kan koma Mayo-Belwa domin duba dukiyoyinsa duk da cewar mahaifinsa na can garin, mahaifiyarsa ce shekarunsa huɗu da auren Hure ta amsa kiran ubangiji.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har cikin Hure ya shiga cikin na wata tara, kuma a wannan karon ma ya yi mata alƙawarin shanaye goma idan ta haifa masa namiji. Kuma tun da cikin ya yi wata 9 bai kuma komawa Mayo-Belwa, a cewarsa kada wani abu ya faru bai kusa.
A wani daren litinin naƙuda ta kama Hure, da taimakon Sakina su ka kai Hure asibitin da bai da wani nisa da gidan da Lamiɗo ya kama masu. Nan da nan aka amshe ta a kai ɗakin haihuwa da ita.
Sun kawo ta ƙarfe sha ɗaya na dare, ta sauka ƙarfe uku da mintuna hamsin. Da farin ciki nurse ta fito ta shaidawa Lamiɗo matarsa ta sauka, don Shi da Hure ko matsawa zuwa ƙofar reception ba su yi ba balle su fita.
Da wani irin maɗaukakin farinciki ya nufi nurse tare da faɗin "Mai aka samu? Ta sauka lafiya?"
"Alhamdulillah! Ta sauka lafiya, kuma suna cikin ƙoshin lafiya ita da ɗan da ta haifa."
Sujada ya yi a gabanta kamun ya ɗago tare da faɗin, "Kina nufin Hure ta sauka ta haifi namiji?? Kai Allah nagode maka."
Daidai nan wata nurse ta fito hannunta riƙe da jariri tana dariya. Rige-rige aka shiga yi tsakanin Sakina da Lamiɗo wajen ɗaukar ɗan. Shi ya riga kai hannu ya amshe sa. Tamkar ya yi kaki domin babu inda ya baro sa.
"Kalli Sakina, Barkinɗona da ni ya ke kama!"
Murmushi Sakina ta yi tana ƙara leƙen fuskan Jaririn. Da kyar Lamiɗo ya bawa Sakina ɗiyar ta riƙe sabida yadda yake ji tamkar ya tsaga jiki ya mayar dashi ciki.
Washa gari aka sallame su, kuma a ranar suka tattara suka wuce Mayo-Belwa. Ai kuwa dangi sai tururuwa ake wajen ganin ɗan Lamiɗo.
Tun kamun suna Lamiɗo ya cika alƙawarin da ya ɗauka na bawa Hure Nagge har goma saboda haifo masa namiji da ya yi. Ranar suna kuwa ba ƙaramin bidiri a kai na, domin sosai Lamiɗo ya saki aljihu. Mahaifinsa shi ya raɗawa jariri suna Adam (sunan maigari garinsu), amma kowa yana kiransa da Arɗo saboda kara wa maigari. Mahaifinsa kuma yana kiransa da Arɗo Barkinɗo.
Shekarun Arɗo Barkinɗo uku ya soma wani irin masassara sannan ƙuraje suka feso masa a jiki. Lokaci guda sai ya suma fin biyar. Duk wani abu da aka bashi jiki bai sauƙi. Hakan ya saka Lamiɗo ya ɗebe shi tare da Hure suka tafi cikin garin Yola domin duba shi a asibiti. Tashim farko gwaji ya nuna yana fama ne da ɓakon dauro. Nan da nan aka soma bashi taimakon gaggawa, don cutar har so ta yi ta ɗauke masa jinsa, amma cikin ikon Allah sai ya samu sauƙi bayan jinyar sati biyu a asibiti.
Zama Lamiɗo ya yi ya yanke wani shawara bayan an kai ruwa rana akan zai dawo da zama cikin yola, don sam mahaifinsa ƙin amincewa ya yi da hakan, a cewarsa bai yarda da zamansa cikin yahudawa ba, kasancewar lokacin turawa suna ta yaɗa ilimin boko, yana gudun ɗan nasa shima ya faɗa harkar don babu babba babu yaro wajen karatun wanda a ganin mahaifin Lamiɗon kafurci ne ilimin bokon.
Negge huɗu ya sayar ya shigo birni tare da sayan fuloti, sai dai dukgirman gidan nana ɗakuna ciki ɗai-ɗai ya yi guda huɗu. Sai kuma Nagge da ya taho da su guda sha biyar da tumaki takwas daga cikin dukiyoyinsa. Sai ya barwa Jafaru da Musa su cigaba da kula masa da dukiyarsa haɗe da na su don suma suna da dukiyar daidai gwargwado.
Sam mahaifinsu Isiyaka bai taɓa ƙaunar barin ɗan nasa zuwa garin yola zama ba, haka ya sa ko sau ɗaya bai taɓa taka ƙafarsa domin zuwa ganin inda ya tare ba. Isiyaka na da zafin zuciya da riƙo fiye da tunanin mai tunani. Ko tafiyar Lamiɗo birni sai da Arɗon Mayo-Belwa ya saka baki tukun ya haƙura, shima don ba zai iya musu da Arɗon bane don ban da shi shugaba ne tamkar uba haka yake kallonsa. Amma cikin zuciyarsa ji ya yafe wa cikin Yola Lamiɗon. Kuma tun daga wannan rana Lamiɗo bai sake ganin fara'ar mahaifinsa ba.
Shekarun Arɗo Barkinɗo takwas a duniya Sakina Matar Lamiɗo na biyu ta samu ciki, lokacin Hure har ta sake haifan ƴaƴa biyu Isiyaka (sunan mahaifin Lamiɗo sai suke masa inkiya da Ciroma) da kuma Ahmadu. A wannan lokacin hauhawar dukiyar Lamiɗo ya kusa ninka na garin Mayo-Belwa, don tuni ya kuma saye filoti biyun da ke suka da ginansa ya haɗe da nashi ya zama fuloti uku. Kuma jama'a sai tarewa suke a unguwar tana ƙara cika da mutane. Kasancewar Lamiɗo shine kusan mutum na farko da ya fara tarewa a unguwar, sai aka sawa unguwar sunansa, wato _Unguwar Lamiɗo_.
Arɗo Barkinɗo da ƙannansa biyu duk suna zuwa makarantar boko wanda Lamiɗon ne ya sakaa su don hakaa kawai sha'awar karatun boko ta shigesa sosai ganin yanda turawa ke koyar da ɗai-ɗai kun ƴa. Sai dai ko kaɗan Lamiɗo bai sanar da mahaifinsa haka ba.
Lokacin da cikin Sakina ya shiga wata tara, sai ta haifo kyakkyawar ƴarta mace. Ba ƙaramin daɗi Lamiɗo ya ji ba, don dukkan su kuma sha'awar ƴa mace suke a gidan. Ranar suna yarinya ta ci suna Firdausi.
Mutanan Mayo-Belwa sun zo sosai domin taya Sakina da Lamiɗo murya, kuma a wannan lokacin ne suka fahimci ƴaƴan Lamiɗo suna karatun kafurci (boko). Da yawan su sun ƙagu su koma Mayo-Belwa domin ƙaras da abunda idanunsu ya gani wa mahaifin Lamiɗo.
Shi kansa Lamiɗon jikinsa ya bashi hakan, amma saboda taurin kai da ƙarfin zuciya ko gezau bai yi kuma bai jin ko za a hau sama a faɗo zai cire ƴaƴansa a makarantar boko.
Illai kuwa, matanan suna suna isa Mayo-Belwa suka sanarwa mahaiifin Lamiɗo abunda ke faru. Ba ƙaramin girgiza ya yi ba kuma ransa idan ya kai dubu duk sun ɓaci. Abunda bai taɓa burin ya yi ba shi ya yi, wato tafiya cikin birnin Yola domin gane ma kansa abunda aka faɗa masa. Tare suka tafi da Musa ƙanin Lamiɗo don shi ya san inda Lamiɗon ke zaune kasancewar suna zuwa shi da Jafar.
Lamiɗo bai wani mamakin ganin mahaifin nasa ba don ya san za a rina. Tarba mai kyau ya yi masu tare da umartar Hure ta soye masu zabbi tare da kawo masu damammiyar hura. Sai dai ko kallon kufin ruwan da Hure ta ajiye bai yi ya hau jero masa tambayoyi.
"Ina Arɗo Ciroma da Ahmadu?"
Ko kamun Lamiɗo ya ce wani abu, sai ga su sun shigo da gajerun wandunan da shirt na makaranta. Ƙafarsu da sanye da takalmi masu igiya.
Wani irin waro idanun tsoro da tashin hankali mahaifin Lamiɗo ya yi jin jikokinsa na turanci (kun san dai idan bafulatani ya ji turanci yadda yake karya harshe musamman ma ace turawan da kansu suka koyar dasu).
Jiki na rawa ya miƙe tare da nuna Lamiɗo da hannu ya shiga faɗin, "Ni za ka ciwa amana Lamiɗo? Jikokina za ka tura wajen yahudawa suna koya masu yaren kafurci da kafurci! Ka cuce ni ka cuci rayuwarka da na ƴaƴanka Lamiɗo. Allah ya isa tsakanina da kai Lamiɗo! Allah ya isa!!" ya kuma faɗi yana sharce hawaye.
Hankali tashe Lamiɗo ya riƙo hannun mahaifinsa yana son ya masa bayani amma sai ya wancakalar da hannun tare da faɗin, "Idan har kana so ni da kai mu daidaita, ka cire ƴaƴannan a makarantar Arna ka tattara inaka-inaka mu koma Mayo-Belwa a yau ɗinnan kuma a yanzu, idan kuma ba haka ba, babu ni babu kai, ban yafe maka ba ka ƙara zuwa Mayo-Belwa kuma ka kira ni mahaifinka, dukiyarka kuma zan saka ƙannanka su tattaro su dawo maka da ita!"
Wani irin fitinanniyar zuciya ta soma yunƙurowa Lamiɗo wanda gada ya yi a wajen mahaifin nasa sai kuma ya zarta shi. Ko tari ya ƙi yi balle kuma ya furta wani magana akam abunda mahaifin nasa ya furta.
"Zan ɗau shurunka matsayin bijirewa umarnina, idan kuma na saka ƙafata na bar gidan nan a yau kuma a yanzu, ni Isiyaka na cire ka daga cikin sahun ƴaƴana!"
Duk da jin wannan furuci ko gizau Lamiɗo bai yi ba har mahaifin nasa ya juya fuuu hannunsa riƙe da na Musa da ke tsiyayar hawaye suka fice. Tafiyar da Lamiɗo bai kuma saka mahaifinsa a idanu ba, domin kuwa kwana bakwai da tafiyarsu ƴan fashi suka shiga ƙauyen suka kora duk dabbobin jama'a tare da kashe mutane takwas, daga ciki akwai mahaifin Lamiɗo, ƙaninsa Jafaru, mijin ƙanwarsa Lawisa da kuma wasu daga cikin mutanan ƙauyen.
Ba ƙaramin tashin hankali da kukan fitar hayyaci Lamiɗo ya yi ba lokacin da ya yi arba da gawan mahaifinsa da ƙaninsa har ma da mijin ƙanwarsa ya yi ba har sai da ya zama abun tausayi.
Bayan bakwai, Lamiɗo ya tattara wasu daga cikin dangi da suka amince za su biyo sho tare da ƙaninsa Musa da ƙanwarsa zuwa cikin garin Yola inda ya ke a zaune. Sai dai wasu ƙin biyo shi su kai a cewarsu ba za su bar mahaifarsu ba duk da kuwa ba su da wata sauran dukiya a garin.
Shi kuma Lamiɗo dukiyar da ya tafi da ita Yola, sai Allah ya saka masa albarka suka ruɓanya waɗanɗa ƴan fashi suka tafi dashi har da na mahaifinsu (gadonsu) wanda shi ma yana da dukiya sosai.
Bayan dawowarsu Yola, Lamiɗo ya haɗa kan duk wasu yara ƴan uwa tare da ƴaƴan ƙanwarsa ya saka su makaranta duk da wasu da yawa a ciki ba su so ba, amma babu yadda za su iya don ba ƙaramin shakkarsa su ke ba har da wasu daga cikin ƙannan mahaifinsa.
Haka rayuwa ta cigaba a gidan Lamiɗo, bai taɓa gajiyawa ba wajen ciyar da dangin nasa ba, kuma dukiyarsa ba ta ragewa sai ma bunƙasa take. Eka huɗu gare shi a nan cikin unguwar da ya ke noma da kuma aje dabbobinsa. Gidansa kuma da yake ciki, gine-gine ake ta yi a cikinsa saboda mutanan da suka cika gidan. Kowani magidanci da sasansa shi da iyalansa.
Kuma bayan ƴaƴa uku da Hure ta haifa, Sakina ta, haifi ɗaya ba a kuma sake haihuwa a gidan ba sai bayan shekaru goma Sakina ta sake haihuwar ɗa namiji mai suna, lokacin shekarun Arɗo sha takwas a duniya. Bai ma gida lokacin da aka haifi Safiyanu ƙaninsa, yana Makaranta a Abuja da mahaifinsa ya kaisa yana karanta kasuwanci. Duk da, Lamiɗo shi bai taɓa yin boko ba, yana matuƙar ƙaunar boko don babu wanda bai boko a cikin gidansa. Gaɓa ɗaya gidansa ya zama na ƴan boko daga matan har maza. Kuma ya cusa masu wannan ra'ayin a cikin zuciyarsu amma kuma duk da hakan, hakan bai sa ya taɓa tarbiyarasu ba. Don doka ne a gidan duk wanda aka sama da laifin fasiƙanci (zina), sata ko kuma ha'inci da zanbo cikin amana, hukuncinsa korar mutun ne daga zuri'ar har abada. Kuma kowa taka tsan-tsan yake da wannan doka. Don kamar yanda suke karatun boka hake suke na addini ko ince fiye ma da haka.
Watan Safiyanu biyar a duniya, Allah ya ɗauki rayuwar mahaifiyarsa sakamakon zazzaɓin kwana ɗaya. Sosai mutuwar ta bigi kowa don Sakina mata ce mai sauƙin kai da biyayya. Riƙon Safiyanu sai ya koma hannu Hure mahaifiyar Arɗo. Dama kuma tun can Firdausi ƴar ɗakin Hure ce, sai ta rungumesu duka ta haɗa da nata ƴaƴan ta cigaba da riƙo.
Arɗo Barkinɗo da ya tashi yin nasa gadon, sai ya dame kakansa da mahaifinsa a zafin zuciya da halin riƙau duk da kasancewarsa cikakken ɗan boko. Shi dariya ma ba al'adarsa bace sam, hakaa duk wani kani nasa wanda suke uba ɗaya da ma cousins ɗinsa ba ƙaramin tsoro da shakkarsa suke ba.
Bayan shekaru biyu da mutuwar Sakina, Hure ma Allah ya amshi abinsa bayan jinyar da ta yi na tsawon wata bakwai sakamakon daji da ya fito mata a mamanta. Kusan fita hayyaci Lamiɗo ya yi, don shi zai iya cewa Allah ya azurta shi da mata masu biyayya. Haka Ardo ya yi kuka sosai da mutuwar mahaifiyarsa. Kuma lokacin bai wani jima da kammala degree ɗinsa ba, don ko wata biyu bai yi ba.
Shi ya cigaba da kuwa da Safiyanu, wankansa da komai nasa, don sosai ya ke son yaron. Komawarsa Abuja ne rainon Safiyanu ya koma hannun Inna biyu, matar ƙanin babansa (Musa). Don shima ya yi aure har da ƴaƴa uku. Ita ma Lawisa autar su Lamiɗon ta sake aure a nan cikin Yola, sai dai ƴaƴan tsohon mijinta suna nan a gidan Lamiɗon.
Dalilin dawowar Arɗo Abuja kuwa, aikin gamnatin da ya samu ne a wata ƙaramar ma'aikata. Sai dai bai tsaya a haka ba, faɗawa kasuwanci ya yi ka'in da na'in sakamakon jari da mahaifinsa ya bashi. Kamar wasa ya buɗe ƙaramar ma'aika da ke yin madarar yoghurt ta gora mai suna Barkindo fresh yoghurt. Ai kuwa yoghurt ɗin ba ƙaramin karɓuwa ya yi ba, don a wannan lokaci kaf Abuja babu yoghurt kamarsa.
Ganin yogurt ɗin ya karbu sai suka sake inganta shi. Da na ƙaramar gora kawai suke yi, sai suka soma yin na babban gora litre-litre, Ice-cream da ruwan ruwan gora.
A wannan lokacin kuma ya haɗu da first love ɗinsa Maimunatu wacce itama bafulatana ce ta Yola a ƙaramar hukumar (Girei). Soyayya suka kai mai tsafta da tsananin shaƙuwa wanda ta kai su ga aure. A nan cikin abujan su ke da zama in da ya sayi wani gida four bedroom. Shekara bata cika ba Maimunatu ta haifi ɗanta kyakkyawa mai kama da mahaifinsa.
Ba ƙaramin biki aka yi ba domin mutanan Yola sun zo har da Lamiɗo mahaifinsa kasancewar bikin sunann an haɗa ne da bikin buɗe katafaren kamfaninsa mai suna `Arɗo Barkinɗo Global Company Limited`.
Ranar suna yaro ya ci sunan kakansa babansa wato Abubakar amma suna kiransa da Ɓaleri.
Sosai Allah ya sawa company ɗin albarka, domin kuwa a shekaru uku kawai sun cimma nasara, don company ɗin har suger, spaghetti, maccoroni, magi, gishiri, spices, flour suke yi.
Abun mafi farin ciki kuwa, wani shahararren mai ji da kuɗi Abdurrazaƙ Usman Chawai ya zuba hannun jari a company wanda shike da rinjaye na shares ɗin.
Wani tanƙameman Estate Arɗo ya shiga ginawa domin shi da duk iyalansa. Don ba karamin estate bane. Babu abunda babu a ciki, makaranta, asibiti, kasuwa, masallacin juma'a da sauransu.
Maimuna ta kuma haihuwar ɗa namiji mai suna Abdul-Azeez (Belɗo). shima bai cika shekaru biyu cif ba, ta kuma haifan Huzaifa (Giɗaɗo) kuma a wannan lokacin ne Arɗo ya kuma haɗuwa da matarsa ta biyu, wacce ita ma dai bafulatanar ce amma ta Yobe mai suna Lauratu, ta fito ne a gidan masu matsakaicin ƙarfi. Ta kasance mace mai izza, mugun hali, makirici da son kasancewa ontop tare da burin komai ya zamo nata. Tun shigowarta gidan Maimunatu ta fuskanci ba abokiyar zama bace sam. Don sau huɗu tana haɗa su, gagarumar faɗa ita da Babiyo.
Haihuwar da take a kai a kai ya kuma fasa mata kai, domin cikin shekaru biyar ta ajiye ƴaƴa har huɗu; Tukur, lawal, Mahmud da Jibrila. Hakan ya sa take ganin ai ko yau Arɗo ya faɗi ita ce da rabi da kwatar dukiyar gidan.
Sai dai ita ma shekarunta biyar aka danƙaro mata kishiya, ita ma dai ƴar Girei ce, iyayanta sun san juna da iyayan Maimunatu. Sunanta Latifa (Inna Jume) ƴaƴa biyu ta haifa Maryuda da Huzaifa (Huzaifa biyu babiyo ke da shi. Da mahaifin Habib da mahaifin Jawaad, amma suna da bambamcin sunan gida. Baban Jawaad bobbo ake ce masa, shi kuma baban Habib Giɗaɗo).
Sai matarsa ta huɗu, Karima (Inna Ƙarama) ɗa ɗaya ta haifa Yunusa (Baffa Modibbo na Lagos mahaifin Marwanatu).
Ba ƙaramin mulki Lauratu (Mamiyo) ta ke zubawa a gidan ba. Dom ma Arɗo na taka mata birki, don har shika ɗaya ya taɓa shiga tsakaminsu, dakyar da suɗin goshi ya dawo da ita. Tun daga nan ta shiga hankalinta, sai dai wani mummunar ƙiyayyar matan Arɗo da ƴaƴansa ya huda zuciyarta har ta yi nasarar cusawa ƴaƴanta. Sai ɗaya bai isa ya nunawa ɗaya ba saboda sanin halin mahaifinsu. Akwai biyayya da mutunta juna sosai a tsakaninsu ko da kuwa kwana ɗaya ne a tsakaninsu.
Tashin hankaline ya samu zuri'ar Arɗo Barkinɗo sakamakon rasuwar da Baban Arɗo (Lamiɗo) ya yi. Gaba ɗaya suka dugunzuwa su ka tafi Yola. Baƙaramin mutane lamiɗo ya yi ba sakamakon shi mutum ne na jama'a kuma sananne a Yola.
A kuma wannan lokacin ne Mamiyo ta kutso da Hafiz Informer cikin gidan lokacin bai wuce sa'annin Ɓalerin ba.
Bayan arba'in aka raba gado wanda dukkansu ƴaƴansa ba ƙaramin dukiya suka samu ba. Gaba ɗaya ƙannan nasa sai suka danƙa masa kuɗinsu suka zuba hannun jari a company domin a juya masu kuɗin. Hakan ya sa kamfanin ya kuma shahara don akwai shi a Kaduna, Kano da kuma Lagos.
Dama tuni ƴaƴan Baffa Musa (ƙanin Lamiɗo mahaifin Arɗo) sun dawo nan abuja cikin estate da wasu daga cikin dangi. Kuma halin nasu bai canza ba ko ƙadan akan kyarar ɓarawo, mazinaci, da mai zambo cikin aminci.
Gaba ɗaya ƴaƴan Arɗo Bussiness suka karanta domin tallafar kamfanin mahaifinsu.
A cikin ƴaƴan Arɗo kaf Ɓaleri ne ya yo komai na shi kamar ya yi kaki har ya so ya zarta shi ma har da baƙar zuciyar da taurin kan.
Shine Chief Executive Officer (CEO), na `Arɗo Barkinɗo Global Company Limited`. Belɗo kuma Chief Financial Officer (CFO) yayin da Huzaif ke da muƙamin, Chief Operations Officer (COO).
Wannan manyan muƙamai da Arɗo ya baiwa manyan ƴaƴan kishiyarta ba ƙaramin tada hankalinta ya yi ba, don ta so a ce ƴaƴanta ne ke riƙe da su. Ta rasa zaune ta rasa tsaye.
Lokaci guda Arɗo ya fitar masu da matan aure su duka a cikin dangi, Ɓaleri ƴar wajen ƙanin (Ahmad) Hafsatu ya aura masa, Belɗo kuma ƙuma ƴar wajen Ilyas wan Ahmad aka bashi wato Saudatu, shi kuma Giɗaɗo aka aura masa Halima ƙanwar Saudatun.
Ba ƙaramin ɓarin Naira ya yi ba lokacin bikin nan, kuma a wannan lokacin Modibbo ɗan wajen matar Arɗo ta huɗu ya koma Lagos da zama domin cigabaa da kula da companynsa da ke can tare da matarsa don shi ma lokaci ɗaya su kai aure da su Ɓalerin.
Bayan shekara guda ƴaƴan Mamiyo su ma Arɗo duk ya fito masu da nasu matan su kai aure, kuma suma a company suke aiki kuma suna riƙe da manya office duk da bai kai na ƴaƴan Maimunatu ba.
Matar Belɗo ce ta soma haihuwar ɗa namiji ya ci suna Abdul-Hameed. Arɗo ya ɗauki son duniya ya ɗaurawa Abdul-Hameed tun yana jaririnsa. Bayan wata bakwai matar Bobbo ta haifi ɗanta namiji ita ma, aka saka masa suna Jawaad. Matar Giɗaɗo ita ce ƙarshen Haihuwa don sai da Jawaad ya yi wata huɗu tukun ita ma ta haifi ɗanta namiji Habibu. Ɓaleri ne dai bai samu haihuwa ba.
Habib, Jawaad da Abdul-Hameed kai ɗaya suka taso, komai na su ɗaya ne. Kuma makaranta ɗaya suke zuwa. Dalilin kiran Habib da Girei, shi kuma Jawaad da Kaita saboda sunan mahaifinsu ne da ya kasance iri ɗaya. Sai Habib ya yi amfani da sunan garin mahaifiyarsa, shi kuma Jawaad ya yi amfani da sunan wani ɗan ƙwallo da ke tashe a wancan lokacin wato _KAITA_ kasancewar ya fito ne daga jihar katsina. Amma abokai ne kawai ke kiransu da wannan sunan sai kuma ya su ya su a junansu.
Kwatsam sai ga mutuwar uwar gidan Arɗo babu ciwo. Tashi kawai aka yi aka ga gawarta da safe. Family ruɗewa ya yi da koke-koken jama'a domin Maimunatu mace tagari mai haƙuri ga kau da kai. Uwa-uba ga tausayi da kuma kyauta.
Babiyo sai da ya yi ciwo har na tsayin wata guda saboda mutuwar ta jijjiga shi. Haka ƴaƴanta huɗun nan maza sun shiga tashin hankali. A hankali kuma komai ya daidaita suka cigaba da bin mahaifiyar ta su da addu'a.
Tun bayan rasuwar Maimunatu da wata biyu abubuwa suka fara canzawa. Babiyo ya zama wani irin bauɗaɗɗan mutum, ya kuma yafa rigar zafin rai da tsanani a kan wanda yake dashi. Mamiyo kuma ta zaba ta gaban goshi, duk abunda zai faru sai da say ɗinta.
Cikin shekara guda tal gidan Arɗo Barkinɗo ya rikice. Kowa ɗari-ɗari yake a cikin gidan. Ba ƴaƴa ba, ba jikoki ba, haka ba surukai ba. Babiyo ya kuma zama wani boss!
Sai da su Jawaad su kai shekaru huɗu sannan Ɓaleri ya samu ƙaruwar ɗiya mace mai suna Maryaamu. Tana yaye Maryamu ta samu cikin Sa'adatu. Sa'adatu na da wata takwas ta samu cikin Zeenatu.
Ranar da Hafsatu matar Ɓaleri ta haifi cikin Zeenatu, a ranar wani gagarumin abubuwa abu ya soma faruwa da iyalan gidan, na farko haka kawai aka ga Babiyo ya haɗa kayan Inna ƙarama (Mahaifiyarsu Baffa Modibbo na Lagos) akan ta tafi wajen ɗanta a Lagos sai ya neme ta. Tana kuka ta bar gidan cikin mota Hafiz ya kai ta airport ta hau jirgi zuwa Lagos wajen ɗanta. Inna Jume mahaifiyar Huzaifa baban Jawaad kuma, ga ta a gidan ita ba sakakka ba kuma ba aurarra ba, domin dai Babiyo jingineta ya yi a gefe ko bi ta kanta bai yi. Sannan ta koma ba um ba um-um.
Ranar da Zeenatu ta cika biyar da haihuwa, a ranar aka kama Ɓaleri dubu da satar kuɗin kamfani har naira million ɗari huɗu. Jikin Babiyo har wani tsuma yake yi tsabar ɓacin rai da fushi mai tsanani. Tuni ya kira zaman fadarsa, a gaban kowa ya tsittsinewa Ɓaleri ba tare da bashi damar kare kansa ba, sannan ya kore shi kora ta har abada a cikin zuri'arsa.
"Ɓaleri babu ni babu kai har abada. Ban yafe maka ba idan ka kuma tako ƙafa ka shigo wannan gida nawa ko kuma ka yi amfani da sunana. Idan har ka kuskura ka kuma amfani da duk wani abu naaa da zai danganci na haɗa jini da kai, sai na wulaƙantaka kuma sai na tozartaka a idanun duniya. Babu ni ba ɓarawo cikin zuri'a ta, kuma duk wanda ya bashi mafaka cikin zuri'a ban yafe masa ba kuma idan har na samu labari sai ya bishi!"
Ko da Babiyo ya gama faɗin haka, sai ya amshe duk wani dukiya da ke hannun Ɓalerin tare da takardun makarantarsa sannan ya kore sa a gidan shi da iyalansa da matarsa ƙafa ko takalmi babu gaban rigarsa a yage. Ba ƙaramin baƙin ciki Ɓeleri ya haɗiya ba don ya san shi naira biyar ɗin kamfani bai taɓa ci ba har sai idan ɗauka Babiyo ya yi ya bashi kyauta ko kuma albashinsa. Albashinsa kawai ya ishesa ya ciyar da mutane hamsin ba tare da ya jijjiga ba, to mai kuma zai saka shi ya yi sata! Wannan abu da mahaifinsa ya yi masa ya ƙona masa rai, kuma dama duk cikin ƴaƴa shi ya ɗauko Babiyo a baƙar zuciya har ma ya ɗara shi. Shiyasa ya yi fushi tare da alƙawarin yin nesa da Babiyon har ƙarshen rayuwarsa.
Bayan tafiyar Ɓaleri, sai Babiyo ya mayar da Belɗo mahaifin Abdul-Hameed akan kujeran da ya sauke Ɓalerin.
Mamiyo kusan haukacewa ta yi domin kuwa ba haka taso ba, so ta yi a ba ɗanta Mamuda ko Tukur ta yadda za ta riƙa yayimar dukiyar tana tarawa kanta da ƴaƴanta har su ma su buɗe wani kamfanin ba tare da sanin Babiyon ba.
Ƙwafa ta yi tare da faɗin, "Kai ma zan yi maganinka!"
Kuma dama ta fi tsanarsa duk cikin ƴaƴan Maimunatu kasancewar Babiyo a fili yake nuna tsananin soyayyar da yake wa ɗansa Abdul-Hameed.
Bayan wasu shekaru, Mamiyo babu yadda bata yi domin ganin bayan Belɗo amma Allah bai yi ba. Tana ta neman hanya Allah bai nuna mata. Kwatsam wata rana Hafiz ɗan leƙen asirinta ya kawo mata labarin ganin da ya yiwa Abdul-Hameed tare da wata karuwa a garin Bauchi kasancewar shi ɗin ɗan Bauchi ne ya je ziyartar ƴan uwa. Ba ƙaramin jin daɗin wannan labari Mamiyo ta yi ba, sai ta ce masa ya cigaba da bibiyarsa yana kawo mata report.
Ba ƙaramin so Abdul-Hameed ya ke wa Laushi ba. Ya fara ganinta ne a wani zuwa garin Bauchi da ya yi domin duba abokinsa. Tare suke da Ladi Katifa lokacin tana ganiyarta a gidan magajiya. Tunkarar farko da ya mata ta ɗauka da fasiƙanci ya zo, amma abunda ya matuƙar bata mamaki shine yadda shi gaba ɗaya ba ta jikinta yake ba, hasalima ko sha'awar taɓa hannunta bai yi.
Sai ya biya kuɗin awa biyar ya su shiga ɗaki amma babu abunda ke haɗasu sai zama da yake ya yi ta kallonta yana mata nasiha.
Taɓe baki take yi tana hararsa, don tana kyalesa ne kawai saboda kuɗin da yake ba ta masu yawan gaske. Amma da tafiya tai tafiya, sai wani mugun shaƙuwa ya shiga tsakaninsu wanda har ya kai tana shakkarsa tare da tsoron ya ganta da wani. A hankali shaƙuwarsu ta koma zazzafar soyayyar da ko Safiyanu saurayin da ya yaudareta bata taɓa jin ƙaunarsa kamar yadda take jin Abdul-Hameed ba.
Sosai Ladi Katifa ta ke ta cusa masa ra'ayin amincewa da Abdul-Hameed ɗin domin ta yi aure ta bar baƙar rayuwar da suke yi.
Ta kuma yi na'am da zancen don har ta shaidawa Abdul-Hameed ta amince za tai istibra'i su yi auren su. Kuma ta masa alƙawarin kai sa gidansu ne bayan ta gama istibra'i kasancewar bata ɓoye masa komai daga cikin rayuwarta ba.
Sai da a wata zuwa da ya yi har ya kwana a wajenta a wani gida da yaka mata, ya buƙaci kwanciya da ita, ita kuma ta bashi kanta duk da can cikin zuciyarta bata son haka. Tun daga wannan ranar da suka rabu basu ƙara tuna junansu ba.
Sai dai kamun haƙarta ya cimma ruwa akan Abdul-Hameed ɗin ta samu galaba a kan mahaifinsa sakamakon kama mahaifin nasa da aka yi da mace a office babu kaya a jikinta da kuma kwalaban giya da a cikin fridge ɗin office ɗin har guda goma masu matuƙar tsada.
Ƙaramin hauka ne kawai Babiyo bai yi ba, don nan take ya yanke jiki ya faɗi don Zina yana daga cikin mummunar laifi mai baƙin fenti a cikin zuri'arsa. Bayan farfaɗowarsa ya ce ba zai iya shaƙar numfashi ɗaya da mazinaci jefaffe ba kuma mashayin giya.
Sai dai abunda ya matuƙar baiwa Mamiyo mamaki shine ganin bai masa korar kare ba kamar yanda ya yiwa Ɓaleri, sannan kuma babu wanda ya san inda Belɗo yake tun bayan watsewa a parlourn Babiyo. Hakam ya fusata Mamiyo sosai ganin Abdul-Hameed na cikin Estate ɗin yana yawonsa. Kuma ƙa'ida ce idan aka kore ka haɗe da iyalanka za ka bar gidan.
Cikin gaggawa Mamiyo ta kira Malaminta mai huluna ta shaida masa abunda ke faruwa, tashin farko ya ce mata sai an saka muguwar sha'awar budurwar da Abdul-Hameed ɗin ya ke so ya zuciyarsa har ya kusanceta tukun, don soyayya kawai suke yana kuma janyo ita karuwar kan hanya madaidaiciya domin ta natsu ya aure ta, kuma ya yi nasarar haka jiran lokaci kawai yake yi. Lokacin da yake kusantarta za a tura masa aljanji domin ɗebo ruwan jikinsu su duka biyun, idan har akai aiki a kan haka to Mamiyo za ta samu nasara a kan Babiyo, domin zubar ruwan hawayen Babiyon kawai ake so wanda shine za ayi amfani dashi domin juya ƙwaƙwalwarsa.
"Ayi hakan!" Mamiyo ta faɗi cike da son cikar burinta.
Hakar yadda malam mai huluna ya faɗi haka ce ta kasance. Abdul-Hameed ya kwanta da Karuwa kuma an ɗebi maniyinsu su duka. Sannan kuma aka zaga aka faɗawa Babiyo Abdul-Hameed na zuwa gidan karuwai amma sai suka boƴe garin da yake zuwan. Haƙarsu ta cimma ruwa domin kuwa Babiyo ya zubda hawaye wanda nan take malam ya yi aiki a kansa.
Aikin da suka yi a kan Babiyo shine mayar da ƴaƴan Mamiyo ɗin ontop sannan duk abund Mamiyo ta gindaya kada babiyo ya yi musu a kai, na biyu shafe tunanin babiyo ɗin akan zancen Abdul-Hameed na zuwa gidan karuwai domin muddin ya tuna hakan komai zai rushe. Wannan dalilin ne ya saka Mamiyo ta yi wa Abdul-Hameed da Laushi farra'u gudun kawo ta gidan bayan ta gama istibra'i su yi aure kamar yanda ya ƙudurta a ransa. Sannan ta ce a saka masa sha'awar rayuwarta ta baya ninkinsa sau goma ta, ta yi gaba domin cigaba da buga karuwanci.
Wannan ne sanadiya mance Laushi da ya yi a rayuwarsa kaf, itama kuma ta mance shi, Babiyo ma ya mance da maganar yana zuwa gidan Karuwai.
(Taƙaitacciyar tarihin gidan babiyo, a next page za mu koma bayaa domin jin yadda Laushi ta auri Abdul-Hameed)
#Babiyo #Mamiyo #Abdul-Hameed #Laushi #Family Saga #My Destiny #Matar Sayyadee #Ƙaddarata *** 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`