Page 49
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
*_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
"Hamma! Hamma!! Hamma Jawaad!!!" ta yi kiran sunasa har sau biyu babu respond, sai a na ukun ne ya juyo da sauri kasancewar ta kai hannu kan kafaɗunsa.
Murmushin yaƙe ya sakar mata tare da riƙo hannunta da ta ɗaura a kan kafaɗunsa ya riƙe.
Ido ciki ido ta jefo masa tambaya har da langwaɓar da kai, "Hamma what's wrong with you? Tun da muka dawo ƙasar yauwa kwana ukun, baka cikin hayyacinka."
Rungumo ta ya yi jikinsa tare da kwantar da kanta a kan ƙirjinsa ya furta, "Ki kwantar da hankalinki, babu abunda ke damun mijinki. Kawai stress ne da kewan gida. Kuma daɗin-daɗawa ga ki kusa dani kina bani farinciki," ya ƙarisa maganar tare da lakutan hancinta.
Ƙara cusa kanta ta yi cikin faffaɗan ƙirjinsa cike da kunya duk da maganar tasa ta mata daɗi. Kuma ita shaida ce ya mugun iya soyayya duk da ba wani lokacinsa take samu ba sosai tun da suka diro ƙasar. Sai dai fa idan ya shigo gida, kawas da duk wani tunani ko damuwa yake cikin zuciyarsa ya bata kulawa. Don tuni ya dirji amarcinsa. Sai dai sam ba ta jin daɗin yadda take ganinsa haka. Idan har suna tare wani lokacin haka zai tafi dogon tunani musamman idan zai yi abinci. Idan ya yi spoon ɗaya yana iya kwasar mintuna biyar kamun ya kai spoon na biyu. Har sai abincin ya huce kamun ya miƙe ya ce Alhamdulillah ya ƙoshi. Abun na damunta matuƙa a zuciya.
"Hamma...." ta kira sunansa a hankali.
"Umm" ya amsa yana kallon fuska.
"Babu wani Ubangiji sai Allah Mai girma kuma mai hakuri, babu wani Ubangiji sai Allah Ubangijin Al'arshi Mai girma, Babu wani Ubangiji Sai Allah Ubangijin sammai da ƙasa kuma Ubangijin Al'arshi Maigirma. Shi kaɗai ne bawa ke baje masa damuwarsa kuma ya yaye masa. Duk wani abu na farinciki ko akasin haka ga bawa, godiya ya kamata ya yiwa Allah, don duk wanda yarabtashi yana gwada imaninsa ne. Ina baka shawara akan ka miƙa duka lamurranka ga Allah cikin wuya ko sauƙi. Ka kusanta kanka garesa kusanta ta gaskiya, ka raya darenka da sallah tare ƙasƙantar da kanka a gare shi, na tabbatar idan har cike da yaƙini kai hakan to za ka samu warakar damuwarka. Ban ce dole sai ka faɗamin matsalarka don tabbas akwaita ɓoyewa kawai kake yi. Ka miƙawa Allah, shi ya san da komai kuma zai yaye maka."
Tun da ta fara maganar yake kallonta har ta kai aya. Bai iya ce mata komai ba sai sake rungume ta da ya yi sosai a jikinsa yana ajiyar zuciya tare da godewa Allah da kuma mahaifiyarsa da ta zaɓa masa Khairat matsayin matarsa kuma Allah ya amsa. Don da wata matar ce, yawan fitar da yake yi ba kuma ya kai dare kamun ya dawo ya isa ya haddasa gagarumar fitina a gidan da zai sakaa ya fice cikin hayyacinsa.
"Allah ya miki albarka!" ya faɗa mata cikin kunne sannan ya sassauta riƙon da ya mata tare da miƙewa da ita a jikinsa sannan ya kuma faɗin, "Na san kina min uzuri a kan yawan fitar da nake yi, don Allah ki ƙara a kan wanda kike min, in sha Allah komai ya kusa daidaita."
Gyaɗa kai ta yi tare da faɗin, "Allah ya baka nasara a kan duk abunda ka saka a gaba."
Da ameen ya amsa sannan ya bataa kiss a goshi tare da faɗin, "Sai na dawo."
"Allah ya tsare ka da tsarewarsa."
"Ameen, Allah ya miki albarka!" yana gama faɗin haka ya fice ya daga gidan zuwa asibiti.
A can asibitin ya taras da Informer ɗinsa yana jirarsa. A sanyaye Informer ɗin ya ƙariso inda yake tare da faɗin, "Barka da safiya yallaɓai."
"Barka Laminu, ka shirya komai?" Jawaad ya faɗi yana kallonsa.
Kai ya sunkuyar tare da faɗin, "Yallaɓai ka tabbata baka buƙatata kusa da kai? Babu amfani tafiyata in barka a haka!"
Dafa kafaɗarsa Jawaad ya yi tare da faɗin, "Idan na riƙe ka a nan ban yi wa iyalanka adalci ba. Ka koma Nigeria Laminu. Duk lokacin da nake da buƙatarka zan kira ka. A can Nigeria ɗin ma za ka mun amfani sosai fiye da zamanka a nan."
Gyaɗa kai Laminu ya yi tare da faɗin, "Allah ya bata lafiya yallaɓai."
Da ameen Jawaad ya amsa tare da miƙa masa passport ɗinsa sannan ya furta, "Muje in maka rakiya zuwa airport."
Da sauri Laminu ya girgiza kai tare da faɗin, "A'a wallahi Yallabai, ka yi zamanka ni zan tafi ba sai ka raka ni ba. Ina yiwa Hajiya fatan dawowa cikin tunaninta da ta manta nan kusa."
Gyaɗa kai Jawaad ya yi tare da faɗin, "Nagode Laminu. Ka gaida iyalan naka."
"In sha Allah!" faɗin Laminu.
Jawaad ɗan rungume sa ya yi sannan ya bubbuga bayansa sanna ya sake yi ya kama hannunsa su kai musabaha ya furta, "Sauka lafiya Laminu."
"Nagode Yallaɓai!" Laminu ya faɗi sannan ya juya ya fita daga asibitin.
Zama Jawaad ya yi tare da riƙe kansa da ke juyawa yana tuno maganar da su kai da doctor jiya bayan fito da Laushi daga theater room."
_Congratulation, the operation was successful! But there is a little problem.The surgery that was done resulted in total memory loss!_ (Anyi nasara aikin ya yi kyau, sai dai sanadiyar aiki ya saka ta mance duk wani abu da ya faru da ita a baya.)
"Gakiya bariki babu riba ko kaɗan!" faɗin Jawaad yana kaiwa kujeran da yake kai duka. Can kuma ya miƙe ya nufi office ɗin likita.
Sai da ya yi knocking aka bashi izini sannann ya shiga. Miƙawa doctor hannu ya yi suka gaisa sannan ya zauna tare da faɗin, "Doctor ka ce matata ta mance abunda ya faru da ita ta baya, kamar me ke nan? Kuma tsayin yaushe ne tunanin nata zai iya dawowa?"
Murmushi doctor ya yi sannan ya gyara zama tare da faɗin, "Sun daga kan sunanta, ita wacece, su waye iyayanta, kai har ta kai ɗinnan baza ta iya tuna kai mijinta bane. Ta mance da komai a ƙwanyanta. Amma hakan ba wai yana nufin ta yi hauka bane, hankalinta na nan a jikinta. Memory loss ne kawai. Misali yanzu, wayar nan da ke hannunka, sai ka yo formating duk abunda ke ciki. Ka ga ai ba wayar bace ta samu matsala, abunda ke cikinta ne kawai ya goge."
Jinjina kai Jawaad ya yi alamar ya fahimta. Sai ya kuma faɗin, "To tsayin yaushe tunanin nata zai iya dawowa?"
"Gaskiya bana ce ba, amma zai iya ɗaukar watanni uku, shekara ɗaya, biyar, goma. Wasu ma shikenan ya tafi bai dawowa. Amma idan har ana ƙoƙarin tuno mata da wasu abubuwa na baya da take sosai, hakan zai taimaka wajen saurin dawo mata da tunaninta."
Miƙewa kawai ya yi tare da ficewa daga office ɗin ya koma ɗakin da aka je Laushi a ciki, kanta duk an saka masa na'ura, hancinta ɗauke da oxygen. Zafafan hawaye ne suka shiga gangaro daga idanunsa bayan ya riƙe hannunta ɗaya da ke kan cikinta. Fuskan nan nata tai wani irin fiyat kamar na ƴar shekaru goma sha biyu.
Ita kanta Laushin gaba ɗayanta a wannan lokacin bata wuce shekaru ashirin da bakwai ba. Don lokacin da ta haifi Meema bata wuce 18-19 ba. Ɗanya ce jaba tsabar rashin ji da bakin uba ne ke bibiyarta don ko da baban ya kore ta daga gidansa she's 16-17.
_Yasaar_
Cike da farincikin ya samu inda Laushi ta ke ya yi parking a ƙofar gidan da ya aje Ladi Katifa sannan ya sauka ya buɗe gate ya shiga ciki da motat sannan ya kuma zuwa ya kulle ya nufi cikin gida wayar Ladi riƙe a hannunsa yana ƙara karanta text ɗin hotel ɗin da Laushin take.
"Za kici ubanki, gani nan zuw gare ki!" ya faɗi yana murɗa handle ɗin ƙofar bayan ya murza key.
Kai tsaye ɗakin da ya Ladi da Layos abokinsa ke ci. Knocking ya fara yi sannan ya murɗa ya shiga. Turus ya tsaya fuskansa na wani irin jaa na tsantsan ɓacin rai ganin babu kowa a ɗakin amma ga kwalba nan a fashe kuma igiyoyin da suka ƙulle Ladin a kwance sannan ga gado a yamutse.
"Ɗan matsiyaciya! Abunda kai min kenan?" ya faɗi yana naushin bango. Sai dai saukar wani ƙarfe a tsakiyar kansa ya saka ya saki wata razananniyar ƙara tare da zubewa a ƙasa jini na zuba.
Ba kowa ya buga masa wannan ƙarfen ba sai abokinsa Layos, don ya jima da farfaɗowa daga sumar da ya yi sakamakon kwalba da Ladi ta fasa masa a kai. Sannan da ma ya riga ya san shirin Yasaar na kashe sa da yake son yi ya bunne a gidan sannan ya kwashe maƙudan kuɗi ya tafi ƙasar Uganda tare da Laushi. Don ita kanta ya ɗauki alwashin ɓakanta mata tare da azabtar da ita kamun ya kashe ta. Don ita ma wani plan ɗin ya shirya mata a ƙasar Ugandar.
Wata mahaukaciyar dariya Layos ya kwashe da ita tare da faɗin, "Kar ka yi mamaki domin cin amana a wajenka na gaje sa. Ni ne nan zan ci waɗannan kuɗin Yasaar. Yanzu a nan wajen zan mayar da kai tako-tako sannan na yi maka cinnen hukuma kamar yadda ka yi wa uban gidanka. Ka san dai nan gidan shim cike ya ke da tabar wiwi d cocaine har da bindigu ko? To yanzu abunda kai wa Sabo da kaza zai maimata kansa. Yana gama faɗin haka ya ja kunamar bindiga tare da toshe salansa sannan ya harbi Yasaar a hannu dama, ya kuma ɗana masa a hannu hagu, ƙafar dama da ta hagu.
Wani irin ihu baƙar azaba Yasaar ya shiga kurmawa yanaa tsiyayar da zufa tamkar shine brodi a cikin oven.
Shi kuwa Layos tattare duk wasu kadarorin Yasaar ɗin ya yi sannan ya bar gidan a cikin motar Yasaar ɗin bayan ya kira hukumar NDLEA kamar dai yadda Yasaar ɗin ya yiwa Sabo da Kaza.
Cikin mintuna ƙalilan hukuma ta zagaye gidan suka kama Yasaar suka tafi dashi asibiti cikin ambulance. Take yanke aka cire masa ƙafafunsa biyu kasancewar bullet ya dagargaza ƙashin guiwar. Hannu ɗaya na hannu dama ma yanketa a kai, na hagun ne kawai bai samu matsala ba. Bayan doguwar jinya kamar ba zai yi rai ba ya samu sauƙi sannan aka tur shi gidan maza (prison).
LADI KATIFA Watanta huɗu da kwana goma a ƙasan gada tana bara don ta yi rantsuwa da Allah har abada babu ita babu karuwanci don bai tsinana mata uban komai bai sai shiga wani mawuyacin hali. Kamun zamanta a ƙasar gada ta yi duk yadda za ta yi domin haɗuwa da Laushi ta bata shawarar komawa ga iyayanta amma bata same ta ba, sai kawai ta haƙura ta soma bara domin haɗa kuɗin motar da zai mayar da ita Kano. Ba ƙaramin wahala ta sha ba a ƙasan gadar nan. Sau huɗu ƴan iskan gada suna mata fyaɗe. Ta yi kuka har ta godewa Allah. Tana haɗa kuɗin mota ta tattara ta tafi Ɓagwai wajen mamanta don ta yi rantsuwa ita da Kunya wajen dangin mahaifita SAI A LAHIRA idan Allah zai musu hisabi.
Ko da ta isa Ɓagwai da kyar da tambaya ta gano idan kakannin nata. Da kuka ta shiga gidan ta tsaya a soro gabanta na faɗuwa tana addu'ar Allah ya sa kar mahaifin mahaifiyarta ya kuma koro ta.
"Wacece wannan kamar Ruƙayya ɗiyar Shafi'u ƴar wajen Uzaibatu!" wata tsohuwa ta faɗi tana riƙe haɓa.
"Ni ce, Inna Kulu." Ladi ta faɗi tana tsiyayar da hawaye.
Da wani irin sauri wacce ta kira da Inna Kulu ta juya ta koma cikin gida kuma da fita za ta yi. Ƙafafuwanta har harɗewa suke wajen faɗin, "Jama'ar gidan nan duk ku fito ga ɗiyar Uzaibatu Allah ya amshi addu'armu ya dawo mana da ita."
Kan kace kwabo gaba ɗaya jama'ar gidan sun firfito tsakar gida kowa na san ganin ɗiyar Uzaibatu yara da manya.......
#Memory loss #Laushi #Jawaad #Khairat #Yasaar #Layos #Ladi Katifa